INUWAR JIYA

Chapter 15

by @khairatup01

INUWAR JIYA
NA
UMMULKHAIR S PANISAU 
(KHAIRATUP)

015

*

Tana haɗa kaya tana mita yana daga ƙwance a kan gado yana aiki a laptop ɗin sa.

"Hello. Kamar kin manta ina nan sai magana kike gaya min?"

"Haba, kana sane ka san bana so ,ka san bana son ana zubar da kaya a ko ina amma kai in ka dawo ka dinga zubar wa kenan. Me amfanin kwandon da na ajiye a nan?"
"To na ji ki yi haƙuri zan gyara in sha Allahu."
"Kamar gaske kullum haka kake cewa."
Lokacin ta dauko wandon shi tana juya shi daidai daga bai-bai ɗin da yake. Sai ta ji irin ƙamshin semen a jikin wandon tana duba aljihun wandon ta ji abu ta sa hannu ta zaro waje.
Da mamaki ta bi hannunta da kallo. "Condom ne." Ta kalle shi cike da mamaki hankalinsa yana kan laptop ɗin shi. 
Jin shirun na ta ya mai yawa ya saka ya ɗaga kai ya kalle ta. Sai ya ga condom ɗin a hannunta da wandon sa nan da nan hankalinsa ya tashi ya gyara zamansa ya ji komai ya ɗauke masa ɗif, ya rasa ma ta ina zai fara.

"Saj...mene wanann?"

Ya sosa kai ya zamo daga kan gadon yace "Babe... Saurare ni."

"Ina sauraron ka ai cewa nayi mene wannan?"

"Ba abinda kike tunani ba ne zan iya yi miki bayani."

Ta yi wani kalar murmushi haɗe da ajiye wandon sannan tace "Ka yarda da ni ba zaka iya yi min bayani ba."

Ƙoƙarin kamo kafaɗarta yake yi ta sa hannu ta buge masa hannunsa tace "Kar ka soma kar ka kuskura ashe ka san me kake aikatawa shi ya sa kake so ka min kulle kake kaf-kaf da ni? Shi ya sa kake tsoron kar nayi mu'amala da kowa saboda ka san me kake aikatawa a faƙaice? Sajjid da gaske?"

Ya lashe leɓɓensa yana cike da jin haushin kansa da ya ajiye codom bai yarda da shi a can ba bai ma san me yasa ya ajiye shi ba Wallahi.

"Babe, na san ba zan iya miki bayani ba, amma don Allah ki yi hakuri ki yafe min ba zan kuma ba wannan ne na farko kuma shi ne na ƙarshe."

"Sajjid, ka gaya min da me na rage ka don Allah? Don Allah da me na rage ka? Me na yi maka? Me nayi maka ka min wanann sakayar matan banza ka koma bi gani a gidan ka na killace maka kaina na riƙe maka amana ashe kai kana can kan bin matan titi Sajjid are you for real?"

Ya kama kansa ya rasa yadda zai yi ,ya rasa inda zai saka ransa ya ji daɗi bai san ta yadda zai wanke kansa ba wanann shi ne ga samu ga rashi taya ya ya samu ya shawo kanta ace ya sake baƙanta mata.

"Babe am sorry! Don Allah ki yi haƙuri."

Ta ɗaga hannun ta alamar ya dakata da surutan da yake yi mata. Kawai sai ta nuna masa hanyar waje. Alamar ya fita.

"Bab.."

"Ka fita Sajjid."

Sum-sum kamar munafuki ya fita daga ɗakin. Yana rufe ƙofa sai ta saka sakata ta zauna ta saki kuka. Sai ta fara murna ta samu kwanciyar hankali sai ya sake kawo wata rigimar yanzu kuma abin ya tashi daga komai ya koma bin mata. Wallahi bai isa ba, ya bi matan banza ya zo ya hau ta ita ma gaskiya ba zai yiwu ba.Iska ya kai wa naushi. Cike yake da jin haushin kansa,ba fa yana da na sanin yana bin mata ba ne tashin hankalinsa yadda za ayi ya wanke kansa a wurinta,yadda za ayi ya samu ya shawo kanta bai san ya aka yi ya yi wautar barin abin nan a aljihun wandon sa ba. 

Ya dinga jera tsaki yana kallon ƙofar ɗakin, maƙogwaronsa na sama da ƙasa yana jin kamar ya shiga cikin ɗakin a tunanin shi kuka take yi tsoron shi ɗaya kar ta fetsare tace zata tafi wurin Daddy don shi bai ga me raba shi da Rania ba sai mutuwa. Bin mata ya saba amma bata taɓa sani ba saboda ba koyaushe yake bin ba tunda ya aureta ya koyi ɗauke kai daga mata sai dai irin jifa-jifa idan ya ga wadda ta masa har cikin ransa. Wannan ma ƙyawunta da dirinta ne ya janyo shi.

Ya sake yin wani tsakin gabansa ya sake faduwa da ya ji wayarsa na ƙara ya zata Daddy ne ko kuma Aunty sai ya ga Ni'ima ce. Ya sauke ajiyar zuciya ya so ya ƙi ɗaga wayar sai kuma ya kasa bai san lokacin da ya sa hannu ya danna ya amsa kiran ba.

"Sugerna."

"Bana cikin halin yin waya da ke yanzu zan kira ki da safe."

Ta ji ba daɗi sai ta kashe wayar a fusace. Bai so haka ba amma da gaske yake ba ya cikin hayyacinsa da zai iya yin waya da ita ba saboda yanzu ta sarauniyar zuciyarsa yake,duk da akwai wani sashi na zuciyar shi da yake ingiza shi kan ya kira ta kamar ana hura masa wuta haka yake ji. Tun da ya shiga jam'iyar Ni'ima ya ji komai ya sauke mai don ta sauke masa hadda ta na da wani irin sirri da baiwa baya jin zai iya rabuwa da ita amma dole ne ya shawo kan Rania.

Daga Sajjid har Rania bacci ɓarawo ne ya sace su shi a falo kan kujera ita kuma a kan gado.

Da asuba ta tashi tayi sallah yadda ta saba. Haka ta taushi zuciyarta wurin gyara kan gadon ta wanke banɗaki ta saka wata riga armless ta saka da yake yau asabar babu inda zata je tana gida.  Ta haɗe gashinta wuri guda ta saka hula ta fita daga ɗakin. Kallo ɗaya tayi masa a kwance yake kan kujera kana ganin kwanciyar ka san ba ta dadi ba ce. Ta so ta wuce shi sai kuma ta kasa haka ta isa ta taɓa ƙafarsa a hankali. 

Ya buɗe ido da sauri yana ganin ita ce ya yi wuf ya miƙe zaune.

"Babe."

"Na'am." Ta amsa masa a sanyayye babu wani emotion a kan fuskar ta hakan ya sake ɗaga masa hankali bai ga hakan a matsayin normal abu ba. Ya za ayi ya mata haka ya amsa shi so calmly anya kuwa? Ya tambayi kansa.

"Ka tashi ka je ka yi Sallah yau ka makara."

Ya bi ta da kallon mamaki Wallahi bai yarda ita ce ba haka ya saka ya sa hannu biyu ya murza idanun shi ya sake buɗe su alamar wai ko mafarki yake yi.

Duk da haka ta yi controlling ɗin ka bata nuna wani emotion akan fuskarta ba gata nan dai.

Kasa jurewa ya yi haka ya saka yace da ita "Babe,bana son haka ki fito sak a mutun ki hukunta ni na amsa laifina amma kuskure ne kuma in sha Allahu ba zan sake ba wanann ma tsautsayi ne Babe."

Ta masa wani irin kallo sai kuma tace "Ba komai Allah Ya yafe mana kurakuren mu."

A hankali yace "Amin." In disbelief ba haka ya zata ba, ba haka ya ɗauki abin zai zo masa da sauƙi ba bai san cewa a haka zata amshi abin ba."

Kan ya sake magana ya bar masa wurin ta shiga kitchen. Yana jin yadda take dauko abubuwa tana ajiyewa.

"Sajjid ka tashi ka je ka yi sallah ka makara fa sallar asuba ce."

Cikin ina-ina yace "Erm..t..to... to."

Ya tashi ya kai ƙofa ta leƙo tace "Me kake so a breakfast?"

Da sauri ya juya jikinsa bai ba shi wanann abin normal ba ne duk hankalinsa a tashe yake wanann ai silent killing ne wato ta san ya aikata kuma ta bar shi da halinsa to me take nufi? Ya tambayi kansa tambayar da ba shi da amsar ta.

"So kake yi sai rana ta fito zamu ɗora break?"

"Idan akwai arish ki soya min da ƙwai sai ki min tea da kayan ƙamshi."

"To."

Ya shiga ciki yana saƙa da warwara. Haka ya yi wanka ya yi alwala ya zo ya yi sallah a cikin addu'a har roƙon Allah ya ji yana yi kar Rania ta tada zancen nan na condom ,Allah Ya sa an gama fadan kenan. 

Ya saka t-shirt da wando karami iya guiwa. Zai fita wayarsa ta haska sai ya ga Ni'ima ce ya yi tsaki yana mamakin yadda bata da hankali ya za ayi ta dinga kiran shi anyhow. Ya fara buɗe ƙofar ya leƙa ya ga dai tana kitchen bata fito ba.

Ya mayar da ƙofar ya rufe ya amsa kiran murya ciki-ciki.

"Wai baki ga safiya ba ce ba?"

"Na kasa jurewa ne ka yi haƙuri."

"To mene ne?"

"Uhm da ma na ji ina kewar ka ne nake son na gan ka shi sa na kira ka amma ka yi haƙuri."

"Wai ke ba ki san irin wannan harkar ba a matsawa ba? Ta yaya za ki yi expecting zan na ganin ki in na ga mace sau daya ni shi kenan."

Ta shiga shock sosai. Amma sai ta dake da yake yar bariki ce ita ma.

"To na ji sai an jima."

Bai bata amsa ba ya katse kiran.

NI'IMA

Tana sauke wayar ta ji wani irin abu ya caki ƙirjinta kamar mashi. Ba zata bari wanann mutumin ya ƙubuta daga hannun ta ba ashe aikin bai kama shi ba tunda har ya bata irin wanann amsar duk yadda za ayi sai anyi sai ta sake janyo shi jikinta so take yi ta mallake shi, ta lura yana son matarsa kuma baya son ɓacin ranta. Tunda ta ɗanɗane shi ta gane cewa na ta ne ita ɗaya don ita aka yi shi don ya kasance da ita kuma. Ba zai yiwu ba. Zuciyarta ta kwaɗaita mata shi kuma ta lashi zumar sa ba zata bari ya bar ta ba saboda haka zama bai bar ta ba yanzu ne ya dace ta soma planning ɗin yadda zata ƙwato shi.

Wayarta ta sake ɗagawa ta soma kira.

"Ƙawas."

"Ni'ima ya?"

"Akwai matsala ina son ganin ki."

"Matsala kuma?"

"Matsala ma babba a wurina."

"Subahanallahi. Ba dai wani abun kika rakito ba?"

"Mtsw! Na ce ki zo koma meye za ki ji."

"Ba zancen in zo zan ji ba ne. In fa tarko za ki haɗa min kin san layin nan na mu ni fa ba zan shiga abin da zan zo in tsugunna ba kin sani."

Ji tayi kamar ta zuba mata ashar mai zafi amma ita ke nema dole ta sauke kai sai ta ce da ita "Wallahi ba abinda kike tunani ba ne ke, wanann ni ya shafa taimakon ki nake nema bana son muyi a waya ne na fi son ki zo ina ganin ki kina ganina."

"Shi kenan ina zuwa bari wannan Alhajin ya sallame ni tukunna tun jiya ina nan duk na gaji."

"Na ji ki zo za ku wartsake a nan zan dafa miki better ina da sauran cow leg a fridge sai na ɗumama miki."

"Yauwa ko ke fa da ma yunwa nake ji sosai da sosai. Ki haɗa min da doya da ƙwai."

"Na ji." Ta faɗa tana hararar wayar ta ajiye.

"Yar hau." Ta furta a fili. Dole ta miƙe ta shiga kitchen ta fara fere doya ta ɗora ta koma ta ɗan yi yan gyare-gyaren da za ta yi. Cikin awa ɗaya ta gama komai ta saka a fulas.

Tunda ta ji horn ta tashi da sauri ta fita.Daga ita sai shimi da wani ɗan karamin wando da bai kai ko guiwa ba kanta ba ko ɗankwali ta buɗe mata gate ta shiga ciki ta faka motar.

Ta fito tana taunar cingum da akwai chiffon abaya a jikinta. 

"Shegiyar ƙawata. Anya kin yi bacci kuwa? Kin ga fuskar ki kuwa?" Ta faɗa tana fashewa da dariya.

"Bana son Iskanci shiga muje ki ji."

"Ai sai na karya tukunna."

"Na gama ai shiga ki ci mayya."

Ta sa.dariya.

Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta yi wanka ta koma kan kujera ta zauna.

"Wash!" Ta faɗa sannan ta kalle ta tace da ita "To mene ne ya faru?"

"Wani gaye ne yake nema ya hana ni sakat."

Ta ƙwalalo ido waje sanann tace "Hana ki sakat kamar yaya kenan?"

Ta gaya mata komai da yadda suka yi a ƙarshe.

"Chab! To ke ai gaskiya ya gaya miki. Kin san a wannan harkar ba wani naci ko bibiya idan buƙatar ka ta biya shi kenan mu cash muka sani kawai."

"Kayya! Ba za ki gane ba ne ƙawas a yanzu haka ba ki san irin tashin hankalin da nake ciki ba ne Wallahi mafarkinsa nake yi ya haɗu fa ba wai ina nufin kyawun aljihu gare shi ba kawai fuskar ta shi ma sha Allah ce."

"Mtsw! To yanzu barikin za ki yi ko soyayya?" 

"Duka zan yi."

"To me kike so ayi?"

"Ya dawo hannuna."

"Turƙashi! Ya dawo hannun ki kamar ya?"

"Ina son na dinga mu'amala da shi ni kaɗai ke ni son sa nake in son samu ne ma na mallake shi na aure shi ni na yarda zan bar komai amma fa sai ya saki matarsa don ba zan iya raba shi da kowacce mace ba."

Ta kama haɓarta tace "Gaskiya kin zaƙe Ni'ima ke yanzu akwai mai kwasar ki? Akwai mai auren ki?"

Ta yanka mata harara sannan tace "Ban ce ki zo ki ɗaga min hankali ba mafita nake nema. Tunda ya min gardama kuma har yanzu bai zo ba to aikin da yake kama sauran in sun shiga wurin nan bai kama shi ba."

"A koma gurin Malam kenan?"

"Haka nake nufi."

"Sai ki shirya amma ki tabbatar da aljihun ki a cike yake."

"Ba ki da matsala."

"To madalla ai ni ina son harkar tuwon girma."

*

Duka-Duka sauran wata ɗaya ya bar ƙasar London wa'adin aikin da ya zo ya kusan cika. Wannan karon ya kudurce a ran shi in ya koma Nigeria zai nemo ta da kan shi don ya ga Hadi ma wasa yake yi masa da hankali.  Ya saki wani siririn tsaki ya tashi ya je ya ɗauko lemo a cikin fridge mai sanyi ya ɗauki cookies ya sa a plate ya fita falo ya zauna. Ko tv bai kunna ba ya kashe duka lights ɗin gidan dama ya yi zuru babu yadda za ayi na waje ya ce akwai mutum a cikin gidan. Kuma ya yi hakan ne saboda Yasmeen don yanzu ya lura bata tsirar zuwa sai dare ya yi sai ta ɗauko yan'matan ƙafafuwanta ta zo wai kawo masa abinci kamar da ita ce take ba shi, duk yau faɗa-faɗa yake ji da ma.

Wayarsa ce ta soma haske mayyar ce zuciyarsa ta raya masa sai da kuma ya faɗi sunan sai ya ji wata dariya ta zo mai kawai sai ya waske ya ƙi ɗaga kiran na ta ba ya son ganin ta bare ya ɗaga wayarta tunda abokan aikinsa suka ankarar da shi da ganin wai ko soyayya yake yi da ita ya saka ya ɗauki aniyar yin baya da kan shi daga jikinta.
Haka ta ƙaraci kira ta katse ta sake kira ta sake katsewa sannan ta haƙura. A fili yace "Yarinyar nan ban sani ba ko akwai mayu a ahalinsu ita bata san shi malamin ta ba ne ba? Da zata dinga ƙoƙarin cusa kanta jikin shi ta san waye shi? Ya kuma yin wani tsakin.

Can ya sake ganin haske sai dai wanann karon ba ita ba ce Hadi ne ya ji kamar yana ɗauka ya lailaya masa ashar tukunna sai kuma ya sa hannu ya shafa ƙirjinsa yace "Calm down Rayyan."

"Hello, Mr.Hadi Hassan Fillo."

"Rayyan Zayd mutanen Turai ka guje mu shekaru biyu kenan da barin ka ƙasar mu ta gado wai yane?"

Ya yi murmushi har Hadi yana jin sautin murmushin.

"Mutumina ina nan dawowa sauran wata ɗaya kacal in sha Allah za ku gan ni duk nayi kewar ku."

"Gaskiya ya kamata ka dawo. Ko ka san aikin nan na ku ya kamallu?"

"Na sani amma kuma na ji Alhaji Nasir na neman takarar gwamna a karo na biyu."

"Uhm...eh haka na ji ni ma."

"Mutumin ne ban yarda da shi ba hakan nan."

"Aikuwa ana faɗen ƙirƙin shi musamman a Jos."

"Well,Allah Ya sa ya yi abinda ake so a kan mulkin idan ya samu."

"Amin. And na samu labari a kan ta fa."

Sai da ya ji wani dum! Zuciyarsa ta buga ya ji wani abu kamar an maka masa shi a ka a kwance yake a kan kujerar haka ya miƙe da sauri yace "Hadi...idan wasa ne ka shiga hakkina idan kuma da gaske kake to maza-maza ka gaya min yaya aka yi."

"Da gaske nake yi maka ka san ban taɓa yi maka irin haka ba."

"Tana ina?"

"Kano."

"Kano." Ya maimaita sau biyu sanann yace "Ka gan ta?"

"A'a amma an san wadda ta san ta."

"A ina?"

"Aisha Bello."

"Wacce ce?"

"Aisha ta fa matar da zan aura."

Sai ya sake yin jim sannan yace "Kana ja min rai, ka gaya min a numfashi ɗaya tana ina?"

"Tayi aure..."

Kalmar da ta zame masa tamkar guguwa, yace da shi "Na'am?"

"Tayi aure tana zaune a garin Kano da Mijinta Sajjid Ibrahim ita kuma tana aiki da gidan jaridar su ta reshen Kano a matsayin mai kawo rahotanni ta suka daga wancan post ɗin tun bayan mutuwar Hamza Bello wanda ya kasance abokin aikinta kuma amininta. Aisha ƙanwarsa ce na ga hoton ta ne a wayar ta duk da ban san ta ba sai na tambayi sunan ta to ka san kishin mata tuni tace min "Ba ruwan ka da ita, matar aure ce sunan ta Rania Sulaiman ita ce suke yi aiki da yayana a Jos har Yaya ya rasa ran sa mutuwar Yaya ta taɓa ta sosai don abin sai da aka haɗa da roƙon Allah she was depressed."

Da ƙyar ya iya lasar leɓɓensa na ƙasa saboda ya bushe masa. Kafin ya san me yake ciki ya ji gishiri-gishiri a bakinsa alamar hawaye ne suke bin kumatunsa.

Hadi daga cikin wayar yace "Hello! Hello! Hello! Rayyan Kana ji na?"


Kit ya kashe wayar ya ajiye ta ya kifar da ita ma ta koma kallon ƙasa don kar ma ya sake ganin hasken wayar da zai saka ya ɗauka. Lokaci guda wani irin zazzaɓi ya shige shi ya soma rawar sanyi ya kasa tashi daga inda yake duk da yana son ya tashi cikin mintuna da basu wuce biyar ba Rayyan ya fita daga hayyacinsa numfashinsa na fita da ƙyar.

A hankali idanunsa ke lumshewa tun yana gani kaɗan-kaɗan har ya koma gani dishi-dishi, daga nan kuma ya daina ganin sosai abu guda ya tuna fuskarta cikin farin gilashi da baƙin mayafi tayi rolling da shi cikin suit baƙa da wando buɗaɗe da takalmi tana ce masa "Captain Ray!" Tana blinking idanunta a wuyanta kuma ID ɗin ta ne a saƙale. Daidai lokacin ya daina gani gabaɗaya.

*
"Kaina ne yake ciwo ka bari sai da safe."

"Ba haka bane."

"To yaya ne?"

"Na san dalili ke ma kin san dalili."

Ta juya masa baya ya yi saurin juyo da kanta ta kalle shi kusan seconds biyu sai kuma ta janye kallonta daga kansa.

"Wallahi Babe na san hukuntani za ki yi cikin ruwan sanyi na san na miki laifi ban kyauta ba."

"Hmm! Sajjid kenan ni ba ka min laifi ba. Baka ji tsoron Allah ba sai ni?"

Ya yi shiru ya san gaskiya ta faɗa amma ya zai yi?

"Tsautsayi ne ba hali na ba ne don Allah ki manta."

Ta masa wani irin kallo sai kuma tace "Ba zan iya mantawa ba."

"Hah! To yanzu me kike so ayi?"

"Am sorry Sajjid na san ba za ka ji daɗin abinda zan faɗa ba amma i want you to see the doctor ayi maka test don na tabbatar da lafiyar ka saboda ba zai yiwu kana mu'amala da wasu a waje sannan ka zo ni ma ka shige ni ba ina son kaina ban shirya mutuwa saboda kuskuren ka ba."

Baki ya saki yana kallon ta irin mamakin abin da ta faɗa.

Ta kalle shi ita ma ta sake cewa "Yes! I need a clean sheet."

"Abin ya kai haka Rania?"

"Kar ka ja abin ya zama wani iri ka sa na ji ban kyauta maka ba kai ne ka siya ka godewa Allah na danne zuciyata har na ji zan maka adalci a matsayin wanann ne na farko."

Ta gyara bedsheet ta kwanta ta juya tace masa "Please in ka tashi ka ɗan kashe fitilar ka zo ka kwanta don ka tashi da wuri." Daga haka bata sake cewa komai ba.

Ya bi bayanta da kallo cikin hasken wata riga ta saka wadda duk ta motsa masa da kwantaciyar maitarsa. Gabaɗaya bayanta a waje yake yana hararasa ya lashe leɓɓe kamar maye ya kasa jura yace da ita "Babe,wai da gaske kike yi ba za ki bari na yi abin da Allah Ya hallata min ba?"

Bata kula shi ba kuma ya kasa taɓa ta saboda yana jin tsoron yadda al'amarin zai juye. Shi test ɗin da ta faɗa ne ma ya saka ya ji wani tsoro ya kama shi kar dai da gaske wani abu ya shige shi? Idan kuma da gaske hasashen ta ya zo daidai fa? Da sauri yace "A'uzubillahi." Ya tashi ya shiga banɗaki bai dade ba ya fito ruwa ya zuba a jikinsa ya kashe fitilar kamar yadda ta umarce shi yana ji yana gani haka ya kwanta ba tare da ya samu abinda yake so ba.

Hadi ya sake bin wayar Rayyan amma bai daga ba sai ya kasa samun nutsuwa ya san waye Rayyan ya kuma san irin soyayyar Rayyan ga Rania da yadda yake dakon son ta wanda ya hana shi gani ko son wata ɗiya mace a rayuwarsa.  Haka ya saka ya nemi ainihin headquarters ɗin su Rayyan cikin sa'a aka ɗaga wayar.

"Hello Adam Aminu speaking."

"Hello,Mr.Adam Ina buƙatar taimakon ka,muna waya da Rayyan sai wayar ta katse ina son a duba shi ina ganin ba lafiya ba."

"Captain Rayyan dai na mu? Na ga gidan na shi da duhu kamar ya fita."

"A'a yana nan yana ciki yanzu muke waya sai wayar ta katse da na sake kira kuma bai ɗaga ba."

"Okay ka kwantar da hankalin ka yanzu zan shiga na duba."

"Na gode ina jiran kiran ka."

"To shi kenan."

Koda Adam ya isa ya yi ta bugu ba a buɗe ba sai ya soma leƙewa ta jikin glass ɗin window akwai duhu,ya zaro wayarsa ya kira layin Rayyan ya ji tana ringing daga ciki sai a lokacin ya gane cewa eh lallai Rayyan na ciki. Ya soma ƙoƙarin buɗe ƙofar da ya ga ma zai ɓata lokaci sai ya ɗaga carpet dake waje ya ga mukullin ya ɗauka ya buɗe ya shiga ciki.
"Rayyan!"
Ya kira sunan sa yana shiga cikin falon. Ganin Rayyan ya yi a ƙasa kwance baya ko motsi. Hankalinsa ya tashi ya tsugunna a gabansa yana ƙoƙarin taɓa shi amma ba wata alamar numfashi a tare da shi. Nan take ya saka hannunsa a cikin aljihun wandon sa ya yi dialing number emergency services.
Bayan wasu mintuna motar asibiti ta iso apartment ɗin su. Ma'aikatan lafiya suka yi gaggawar duba yanayin Rayyan kafin suka ɗora shi a kan gadon ɗaukar marasa lafiya. 
Adam ya bi su cikin motar zuciyarsa cike da fargaba da ace Hadi bai kira su ba fa? Da shi kenan sai dai su tashi da munmunan labari? Tuna hakan kaɗai ya sa jikinsa ya yi sanyi.

Aka garzaya da Rayyan sashen kula da marasa lafiya da gaggawa,yayin da Adam ya ke ta kai-komo a waje. Kusan mintuna arba'in suka ɗauka kafin wani likita ya fito daga ɗakin yace "Kai ne ka kawo shi?"
"Eh ni ne abokin aikina ne. Yaya jikin an shi doctor?" (Da Turanci suke magana)

Likitan ya gyara tsayuwarsa. "He's stable now,Amma akwai gwaje-gwajen da za a sake yi masa. Lokacin da aka kawo shi heartbeat ɗin sa was irregular kuma jikinsa ya yi low."
Adam ya haɗiyi yawu. Yace "Me ya same shi?"
"Ba zan iya cewa ga ainihin abin da ya same shi ba, amma abinda muka yi observing shi ne severe emotional distress,exhaustion and dehydration may have contributed to his collapse. We need to monitor him closely."
Adam ya sa hannu ya dafe kai sanann yace "Zan iya ganin sa?"
"A'a ba yanzu ba sai zuwa anjima ko gobe."
Adam yace "Na gode doctor." 

A can kuma an mayar da Rayyan wani ɗakin  an sa masa ruwa idanunsa a rufe, fuskar sa tayi wata yar kuyat a iya wanann awannin.
A hankali ya fara motsa yatsunsa sannan ya buɗe idanunsa abu na farko da ya fara gani shi ne farin rufin ɗakin da yake kwance.Ya juya kansa a hankali,ganin drip ɗin dake hannunsa ya saka ya ɗaure fuska. Kansa ya tambaya "Where am I?"
Daidai lokacin wata nas ta shigo cikin ɗakin don ta duba shi sai ta ga idanunsa a rufe. Ta koma da baya ta kira doctor ya dawo ya sake duba shi ya masa tambayoyi yace komai lafiya yake ji. Ya tambaye shi waye ya kawo shi ya gaya masa abokin aikinsa ne.
Ba a jima ba Adam shigo ciki.
"Alhamdu lillahi! Adam  ya jikin na ka?"
"Me ya faru da ni?"
"Faduwa kayi mutumina. Allah Ya so Hadi ya kira ni da bamu san me zai faru ba."
Rayyan ya kumshe idanunsa. Kamar wanda ya tuna da wani abu sai kuma ya buɗe idanunsa da sauri yace "Adam.."
"Na'am."
"Ka san...ka san.." ya kasa ƙarasawa saboda wani abu da ya tokare masa makogwaro.
Adam yace "Me na sani?"
"Ba komai." Ya faɗa amma cikin zuciyarsa,tambaya guda ce ke mai yawo a kai yaushe Rania zata fita daga cikin zuciyarsa?