BIYU A ƊAYA

Chapter 51

by @barista

BIYU A ƊAYA 

B2 p51
***
Sayyada barrister 


Lumshe idanunsa ya yi kamar me bacci a zahiri, amma ba bacci bane ya faɗa a duniyar tunani, shin haka za su ci gaba da zama sakanin sa da matarsa ko ya abin zai kasance? Shin wannan hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke in ya taka ya tsaɓawa mahaliccinsa ko bai ba? In kuma ya bi ra'ayinta ya juyawa matarsa baya hakan daidai ne a musulunci? Duk ya shiga ruɗani. To ya matsayin haƙƙin dake kansa na matarsa, yana jin motsin ta sai jujjuya wa take yi, ta kasa sakin jiki, bai buɗe idanun ba amma zuciyarsa ke ayyana mata yanayin ta, duk da yarinya ce yasan ta san ba haka ake rayuwar aure ba kawai ta biyewa ra'ayin sa ne...

Bilqees tana jinta a takure, ta kasa bacci, idanunta a buɗe suke tana kallon ƙofar toilet, damuwarta ɗaya ganin mijinta cikin damuwa, bata so ta yawaita yi masa tambayoyi ganin ya ce baya so ta tambaye shi, amma tasan tabbas yana cikin damuwar. To me yasa yake guje wa shinfida? Duk da tana tsoron ya ce zai raya aurensu amma kuma ta fahimci yana bada rata a sakaninsu, ta sauke numfashi ya lumshe idanunta tana jin tausayinsa ganin ya shirya kareta ko ta wane irin hali ne. 

Ganin ya sha maganin da ya rage masa raɗaɗin sha'awa yasa a hankali ya sanya hannu ya janyo ta jikinsa, ta ɗago suna kallon juna ya kura mata idanu, yana jin ta kamar ya maidata cikin don so, ya zame mata hular kanta tare da cire mata rigar sama da ta sanya a kan rigar baccinta, kunya ta kamata, ya juyo sosai yana kallon yadda take sudda kanta ƙasa ya ɗago da haɓarta ya ce

"Ba ki jin bacci ko?"

"Ina ji"

Ta ce a hankali, bakinta na rawa, ya ɗan sauke numfashi ya ce

"Kin wuni bacci ko?"

Ta gyaɗa masa kanta alamun eh sannan ta ce

"Amma ba sosai ba da su Majada muka wuni"

Ya shafi lips nata yana jin taushinsu ya ce

"Uhm sun ɗebe miki kewa ko?"

Ta gyaɗa kanta alamun eh, ya ɗan yi murmushi gefen laɓɓe ya ce

"Jibi weekend za mu je shopping"

"To"

Ta ce, sannan ya sake cewa 

"Zan yi miki siyayya, me da me kike buƙata"

"Ba komai"

"A'a sai kin faɗa"

"Yallaɓai likita ai ka saya min komai"

"Bana son wannan sunan a sauya"

Ta sudda kanta ƙasa ya ɗago da haɓarta ya ce

"Ba za a sauya min ba?"

"Za a yi"

"Yawwa to sauya min"

"Mon amour"

"Ɗaya, a sake faɗa min wani"

"Zaujee"

Dariya me sauti ya yi sannan ya sake cewa 

"Da kuma...

"Hayatee"

Ya rungume ta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, yana jin ƙaunar ta har cikin ransa, jin tamkar rarrashinta yake yi ya sa Angel yin bacci yana jin ta yi bacci ya sauke numfashi bai yi bacci ba ya kusan raba dare sannan ya samu ya runtsa...


**************

A nutse yake shirya wa cikin baƙaƙen suit, ya yi kyau ya feshe jikinsa da turare ya ɗaura wrist watch nasa ya, sannan ya maƙale side bag nasa ya riƙe wayar sa ya juyo ya kalli Angel dake zaune bakin bed tana kallon sa, ya iso kusa da ita ta miqe ya riƙe hannunta cikin kulawa ya ce

"Na shirya zan wuce"

"Allah ya bada sa'a"

Ya ɗan yi murmushi sannan ya yi kissing nata a ƙuncinta ya ɗago yana kallon fuskar ya ce

"Mu je mu gaida Mommie"

"To"

Ta faɗa, sanye take cikin doguwar riga, ta yafa mayafi suka fito ɗakin Mommie suka shigo da sallama tana zaune kan carpet Suhaima ta haɗa mata tea tana sha, ta amsa sallamar su, Bilqees ta rage tsawonta sosai ta ce

"Barka da safiya Mommie"

"Ai ni har fushi na yi na ce amarya ta kwace min ɗa kuma taƙi shigowa mu gaisa"

Murmushi Angel ta yi sosai ta dubi Mommie da alama kamar matar bata da cikakkiyar lafiya, a kunya ce ta ce

"A'a Mommie ayi hakuri"

"An tashi lafiya Mommie"

"Alhamdulillah an fito?"

"Eh Mommie"

"To Allah ya tsare"

"Amin"

"A ina take zama ita kaɗai"

Ya dubi matarsa tare da cewa 

"A ɗaki take zama"

"Ayi haka, ai ta dinga shiga cikin mutane ya fi"

Angel ta sudda kanta ƙasa Dr Waahab ya ce 

"Haka ne amma yanzun akwai ƴan'uwanta suna tayata fira"

"Ah to madallah hakan ma ya yi kyau, da ƴan rakiya take kenan?"

"Eh"

Ya bata amsa, Suhaima ta gaishe shi, ya amsa Mommie ta ce to ba zata gaishe da matar yayansu ba, da ƙyar ta gaishe ta, Angel ta amsa suka fito side na Mamie suka shigo, tana kwance kan bed sai dai ganin da matarsa ya shigo ya sa ta ɗan sauya fuska, ya gaishe ta kamar yadda yake yi kullum ta amsa sai dai bata amsa gaisuwar Angel ba, hakan bai yi wa Dr Waahab dadi ba, ko ba komai ai ta amsa gaisuwar, haka suka fito jiki a sanyaye, side na Ammie ba laifi ta amsa gaisuwar ba yabo ba fallasa sannan suka fito, bangaren baƙi suka shigo da sallama suka tadda duk suna kan dining suna breakfast, suka amsa sallama da amarya da ango su ka yi, ALAJA ta ce

"Yallaɓai likita morning"

Ko a kularta ita mantawa ma take surkinta ne, cin abinci take abinta, ya amsa da 

"Morning ALAJA ya gajiya"

"Wane gajiya? Ai kai ne da gajiya ni da 24 hours nake hutawa ba inda nake zuwa, daga ci sai bacci duk na lalace jiki ya sake ba exercise"

Ya numfasa ya dubi tulin jikinta dake motsi in tana magana ya ce

"Sannu ya kamata ki fita motsa jiki, ko side ko yaran su yi miki rakiya kan hanya ki yi tattaki sai ku dawo"

"Hakan ma yayi, ina be side?"

Ta tambaya ya ce

"Wajen motsa jiki ne"

"A'a gwanda na fita cen waje na sha iska"

Su Laraba suka gaishe shi ya amsa, ya amsa ALAJA ta ce

"Yawwa an yi kirana cen Ghana ana nemana"

Ƙirjin Bilqees ya buga jin ALAJA zata tafi, hankalinta ya tashi ta dubi ALAJA ta ce

"Maa tafiya za ki yi?"

"A'a zama zan yi tun da gidan ubana ne"

Laraba da Jummai suka sanya dariya Dr Waahab ganin damuwa kan fuskar Angel ya ji ta bashi tausayi ya ce

"Ku yi hakuri ku ƙara koda sati guda ne"

"A'a Yallaɓai likita ɗana aka kama a station ana nemana"

Ta faɗa tana taunan abinci, ya numfasa in dai wancen yaron ne ai zai iya aikata komai, ya ce

"Allah ya rufa asiri, yaushe za ku koma?"

"Jibi"

Ta ce, ya miƙa musu kuɗin fita tattaki ko za su buƙaci wani abu, sannan ya mik'e tare da cewa 

"Zan wuce"

"To Yallaɓai likita a dawo lafiya"

"Amin"

Jin za su fita tattaki ya sa bai bar Angel a wajen su ba yasan ba ƙaramin hankalin ALAJA bane ta fice da ita, har ƙofar ɗakinsu ya kawo ta sai da ya tabbatar ta shige ciki ta rufe ƙofar sannan ya fito ya shige motar sa ya wuce hospital. Yamma lis ya dawo kamar yanda yake yi, sai da ya zaga ya gaishe da iyayensa sannan ya shigo ɗakinsa ya tadda Angel ta yi kyau sosai cikin riga da wando na yadi maroon, ta iso a nutse ta yi masa sannu da dawowa tare da karɓan side bag nasa da ledan da ya shigo da shi ta ajiye, ta dawo ta kusa da shi ta ce

"Ina wuni"

Hannu ya sanya ya dawo da ita kan cinyarsa yana kallon fuskarta ya ce

"Matata barka da gida"

A kunya ce ta ce

"Barka dai, ya aiki?"

"Alhamdulillah sai godiya, yau a gajiye nake"

"Sannu"

Ta ce, ya kwantar da ita a jikinsa ya ce

"Yawwa thanks"

Yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗago da ita ya sanya hannayenta jikin maɓallin rigar sama na suit ɗin suka ɓallewa tare ya cire ta kai ta rataye masa sannan ta dawo ta kai takalmin ma'ajinsu kamar yadda take gani yake yi, ta dawo ta cire masa Safar ƙafarsa ya yi murmushi ta ajiye su a inda taga yaje ajiye waɗan da ya saka ta dawo ya nuna mata rigar jikinsa ya ce

"Saura wannan"

Yana nufin ta ɓalle masa botton na rigar, ta sudda kai ƙasa, ya janyota ya ce

"Cire min ita mana"

Jiki a sanyaye ta ɗago suna kallon juna, ya sanya hannayenta a jikin, ta soma ɓalle su, ta sudda kanta ƙasa bayan ta ƙarashe ɓalle su, ya cire rigar ya ce 

"Ita ma a sama mata waje"

Ya saura vest ta kasa dawowa a jikin wardrobe ta tsaya, ya juyo ya dube ta yana murmushi ya ce

"Madam zo ki ƙarashe aikin ki"

Ta kasa motsa wa, ya taso zuwa inda take tsaye ya ɗago da haɓarta ya ce

"Kunya kike ce Mon Ange?"

Bata ce komai ba, ya cire vest nasa ya saura ba riga, ta juya zata bar wajen ya janyota jikinsa ta faɗa cikin lausassun gashin dake kwance a ƙirjinsa wani iri taji ya rungume sosai yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗago da fuskarta a hankali yana kallon lips nata ya ce

"Kin yi kyau"

Ta rufe idanunta, ya yi murmushi a hankali ya ce

"Yau wanka za ayi min"

Da sauri zata bar jikinsa ya ƙanƙameta yana murmushi ya ce

"Ina kuma za a tafi a barn?"

"Ba...bu"

Ta faɗa jiki a sanyaye bakinta na rawa, ya zaunar da ita bakin bed ta sudda kai ƙasa ya rage sauran kayan jikinsa ya shige toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ɗaure da towel tana zaune ya shirya cikin baƙar jallabiya ya zauna kusa da ita sai ƙamshi ya ke yi ya dubi kulolin abinci dake gefe an jera su ya ce

"Me aka girka?"

"Abinci ne"

Ya riƙe hannunta ya ce

"Mu je na gani"

Tare suka iso wajen kulolin ya zaunar da ita kusa da shi ya buɗe bai ga abincin da ya shiga ransa ba ya rufe, siyayyar da ya yi musu ita kawai suka ci, ya sa aka shigo aka fidda abinci anan kiran sallar magriba ya fice sai da ya idar da sallah ishai sannan ya shigo bai idda zama ba, Dr Faisal ya yi kiransa a waya ya sanar da shi sun iso da matarsa, Dr Waahab ya faɗa wa Angel shi kaɗai ya fito ya yi musu isowa main palour, bayan sun gaisa ne ya shigo ɗakinsa ya ce Angel ta fito su gaisa. Sannan Angel da matar Dr Faisal suka shigo ɗakinsu don babu in da za su zauna sai nan ɗin, nan suka sake gaisawa cike da farin ciki don tana son Angel jininsu ya haɗu suka yi exchanging na contact na juna sannan Dr Waahab ya shigo ya ce su je bangaren baƙi ta gaishe da Alaja kusan tare ma suka shigo, ALAJA tana ganin Dr Faisal ta shaida shi ta ce

"Yallaɓai me soyayya"

Dariya ya yi ya ce

"ALAJA de ALAJA"

Ta yi dariya tace 

"Ashe anan kuke tare?"

"Eh a gari ɗaya muke"

Suka gaisa, nan fa sai hira kusan 10:00 pm sannan Dr Faisal suka tafi, Dr Waahab ya ce zai je wajen Daddy, Angel ta dawo ciki ta watsa ruwa ta yi shirin kwanciya, ganin jiya ma tare suka kwanta ya hanta ta kwanta a ƙasa ya sa, ta kwanta kan bed ta lulluɓe jikin ta da duvet, bacci ya fara ɗaukanta ta ji shigowarsa.

Ganin tana bacci yasa ya shige toilet ya watsa ruwa ya fito ya yi shirin kwanciya, ya duba side bag nasa don shan maganin da yake sha yake jin sauƙin wajen rage masa sha'awar sa sai ya ga babu, magani ya ce ɗauke ni, da mamaki ya duba sama da ƙasa babu, ya tuna a kan dest ya ajiye ashe bai saka cikin jakarsa ba, jiki a sanyaye ya dawo ya kwanta daga gefe, yana sauke ajiyar zuciya, ya lumshe idanunsa bacci ya gagare shi ya fara juyo shi kaɗai sai musu² yake yi, abin kamar wasa ya nemi nutsuwar sa ya rasa, hankalin sa ya tashi ya rasa ya zai yi ga shi Mamie ta hana shi kusantar matarsa, ya yi ta maza zai jure ya kasa. 

Jin yadda yake motsi yasa Angel juyowa ta kalle shi taga ya ɗaura hannunsa kan goshinsa yana rike wa sosai, ta yi tunanin ko ciwon kai ne ta sauƙo ta kunna haske ta ɗauko magani da ruwa ta kawo nasa tare da cewa 

"Yallaɓai likita ga maganin ciwon kai, paracetamol ne"

Da ƙyar ya ɗago yana kallon hannunta da ta miƙa masa maganin sai ya dubi fuskarta ya ji yana son jin ɗumin jikinta don zazzaɓi ya fara ji, ya tashi ya zauna ya sanya hannu ya karɓi maganin da ruwan ya ajiye a bed side drower ya riƙe hannunta da take ƙoƙarin barin wajen, ta tsaya kallon sa ta lumshe idanunsa ya buɗe su ya zuba masa su, yana kallon rigar bacci dake jikinta a hankali ya janyota kusa ya sanya hannu ya cire rigar samar ya saura ƴar ƙarama ta ciki, ya sauke ajiyar zuciyar da ya sa Angel rawan jiki, ɗauƙota ya yi daga tsayuwar da take yi da ƙafafunta kan carpet ya ɗaurata saman bed kan cinyarsa, ya ɗago da haɓarta suna kallon juna duk ta nemi nutsuwarta ta rasa, jikinta na rawa, za ta yi magana ya girgiza mata kansa alamun a'a, ya sanya hannu ya cire ribon da ta tufke gashin kanta da shi ya ajiye shi ya sanya hannu cikin gashin kanta yana wasa da gashin, ta yi sauri ta yi kasa da kanta, sosai ya sanya ta cikin jikinsa tana jin yadda yake sauke numfashi ƙirjinsa na bugawa, ga shi jikin nasa da zafi, ta ji sauƙar muryar sa cikin kunnenta yana yi mata magana a hankali cikin salo

"Baby nah, uhmm ki saki jiki kin ji"

Yana yi mata abubuwan da suka fi karfin brain nata ta sanya kuka, da ƙyar ya ɗan daka ta ɗago da haɓarta yana share mata hawaye, tana kallon yadda idanunsa su ka yi ja, ta sake fashewa da kuka tana cewa 

"Yallaɓai likita ba ka da lafiya ne?"

Kai ya gyaɗa mata alamun eh, ya kasa yin magana, cikin tausaya wa ta ce

"Sannu, ga magani ka sha"

Ya girgiza mata kansa alamun a'a, yana kallon lips nata, a hankali ya ce

"Ba zai yi min magani ba"

Ta ɗan waro fararen idanunta waje ta ce

"Haka za ka kwana?"

"Ke ce maganin"

"Ni Yallaɓai likita?"

"Uhmm"

Ya faɗa ya haɗe goshinsu nan ya fara neman yadda zai ji ya ji sassauci, ita ko sai kuka gani take zai haɗiye ta ɗanye, yana samun nutsuwa ya mirgina gefe yana sauke numfashi, ya yi mintuna sannan ya fara gane in da yake, ya janyota ya rungume ta sosai yana rarrashinta har ta yi bacci...


_______________

Ina ga zan rage shiga ɗakin yaran nan🫣 Dr Waahab ya daina jin kunya ta😄 za su maidani tsohuwar banza😂

Ayi hakuri da typing errors 


Comments and share fisabilillah