Free chapter · Read without an account

Farko.

by Aysha · Waye Shi?


(☆_☆)

"Nanne! nanne! nanne!!...ki tashi nace koh?"

Yarinyar da aka kira da nanne ta motsa sannan ta cigaba da baccinta,

"Zaki bude ido ko sai na tashe ki da ruwa..."

Inna ta fada tana dad'a girgizata, jin haka yasa ta zumb'ura baki sannan ta mike tana murza ido ta cikin dogon gashin kanta daya hargitse ya rufe fuskarta.

"Ki tashi ki wanke ido ki fita tun kan salisun ya tafi, kin san tun jiya muka yi haka dake."

Nanne ta dago ta kalli agogon dake kafe a dakin, k'arfe takwas da kwata na safe, gabadaya baccin da tayi bayan sallar asuba ma bai kai fi na awa biyu ba. Kwata-kwata ta manta sunyi da inna cewar yau zata je da safe ta gayawa salisu irin audugar da zai d'ebo mata a gonar baffansu wajen daza'a fitar da auduga yau kafin masu siyen kamfani su d'ebe masu kyan ciki, wai da ita zata yi sak'ar mayafan da amare zasu yafa ranar wankan amarya (Hakan wata al'adarsu ce ta wata kabila daga nijer)

"Allah inna da kin san gajiyar da na kwanta da ita da kin hakura wani daga cikin su yaya umar kawai ya fad'a masa.

"Kema kin san ba ganinsu zanyi kafin su fita ba don haka ki tashi ki d'auraye ido kije tun kan salisun ya tafi na san zasu fara yin gaba, don tun dazu nake jin dirin motoci zasu fara tafiya."

Nanne tasa hannu ta tattara gashinta baya sannan ta tufke shi, ta shiga band'akin dake jikin d'akin ta zuba ruwa a buta ta wanke bakinta da fuska sannan ta fito, inna ta miko mata hijabi daga inda take zaune.

"Haba dai, wannan ya cukurkude, bari in duba wani."

Ta bud'e wardrobe ta janyo wani mai d'an tsaho ta zura sannan ta karbi k'atuwar ledar da innan ke nuno ta dashi.

"ki masa bayani kamar yadda na fad'a miki jiya dan Allah."

Yadda ta marairaice murya yaso ya bata dariya sanda ta fita daga dakin, da yake a hawan farko suke tana iya hango k'aton tsakar gidan da ba mutane sosai saboda safiya sai daidaikun 'yan aikin dake wucewa akai akai.

Ginin gidan nasu dake cikin wata unguwa a katsina, dad'ad'd'e ne da akayi shi da dakakken gini da ko k'usa ba kasafai take huda shi ba, sannan gabadayansa hawa uku ne, daga bakin gingimemen gate din dake jikin zungereriya katangar data zagaye gidan, faffad'ar haraba ce da tsaf zata d'auke bikin masu dangi, akwai manyan rumfuna na ajiyar motoci da kuma shukar fulawowi data zagaye filin gabadaya.

Daga can jikin ginin gidan kuma doguwar baranda ce data bi tsawon fad'in wajen inda d'akunna ne a jere guda shida na yayyansu maza, a tsakiyar su kuma k'atuwar kofa ce data shigo ciki zuwa bangaren baffansu dake daga dama, inda ya had'a da k'aton falo na saukar bak'insa da kuma d'akuna biyu a ciki da bandaki, daya gefen hagu kuma k'aton kicin din gidan ne wanda shi kansa waje biyu ne dashi, da b'angaren da aka kafe da durowoyin ajiya, sai madafi inda ake jibge tarin itace da kuma manya-manyan tukwanen girki.

Bayan shi babu komai a k'asan sai manyan sito guda biyu, da ake ajiyar kayan gona, matattakalar hawa sama mai fadi ce data d'auka daga tsakiyar katon tsakar gidan kuma ta rabu hagu da dama saboda kowanne b'angare a zagaye yake da d'akunan matan baffansu su hudu ras!, inda kowacce take da falo da kuma manyan dakuna guda biyu kowanne da band'aki a ciki, sai wajen inna wato mahaifiyar baffansu inda itama take da katon falo sai dai daki daya ne da kuma band'aki.

Hawa na biyu kuma na karshe faffadar baranda ce inda wajen yafi ko'ina a gidan girma, a d'an zagayeta da gini daidai misali yadda in ba d'age mutum yayi ba ba zai iya gano k'asa ba, a nan suke shanyar kaya, kayan miya da kuma zaman shan iska kasancewar akwai kujeru kala-kala harda 'yan furanni na tukwane. Kuma daga nan kana iya hango gabad'aya kewayen unguwar da tsilli-tsillin gidaje ne kawai wanda da yawansu ba mutane a ciki, wasu ma ba'a gama ba.

A kaftanin 'ya'yan baffansu Nanne ce ta goma sha bakwai, sannan akwai mutum biyu mata 'ya'yan aunty amarya data girma a k'asanta.

Uwargidan baffa ta farko, hajiya Nasiba da ake kira da hajiya babba, 'yar maigidansa ce dake can cikin garin katsina, kasancewar baffansu d'an asalin nijer ne ya shigo katsina. tana da 'ya'ya shida, Ahmad, Nasir, Muhammad, ishaq, farida da kuma Aisha. Maza hudu mata biyu, kuma 'ya'yanta sune manya a gidan, don Ahmad da farida sunyi aure saura maza uku da mace daya Aisha.

Sai Mama Rabi wadda ita kuma 'yar uwarsa ce ya auro daga nijar, ita 'ya'yanta hudu, Ibrahim, sulaiman, umar da macenta daya jamila. itama ta aurar da babban d'anta ibrahim. Sai Mama halime wadda itama 'yar nijar d'ince amma ba 'yar uwarsa ba, 'ya'yanta hudu duka mata, khadija, maryam, nafisa, da kuma zainab. Khadija ce kawai tayi aure a cikinsu.

Sai aunty Amarya mai 'ya'ya biyar kasancewar haihuwarta ta farko tagwaye ne maza, salim da suraj, sai mai bi musu sadiq, safiya da kuma surrayya.

A duk cikin 'ya'yan baffan, nanne ce kawai bata da uwa a gidan, mahaifiyarta bafulatanar adamawa ce kuma tana can tare da 'yan uwanta, baffansu ya aureta ne lokacin da wani sab'ani ya shiga tsakaninsu da mama Rabi har ya sake ta, toh a wannan lokacin ne yaje adamawa halartar wani taro na manoman nijeriya da akayi kusan sati ana gudanarwa, anan yaga mahaifiyarta a d'aya daga cikin masu goge-gogen wajen da suka kwana.

Farko abokananshi ne suka fara tsokanarshi da cewar ya kamata ya koma gida da bafulatanar adamawa tun lokacin da suka ganshi yana tambayarta wani abu, shikenan kuwa zance ya koma gaske inda a satin basu baro adamawa ba sai da suka je har gidansu nuratu aka tabbatar musu kuma an bashi ita, anan suke ji ma ashe bazawara ce ta taba aure harda yara biyu.

Ko da ya dawo, ya sanar da inna mahaifiyarsa, bata hana shi ba sai dai matansa da suka nuna rashin son abin, hankalin mama rabi yafi na kowa tashi tunda a lokacin tana ta yawon bin 'yan uwa kan a bashi hakuri ta koma darajar 'ya'yanta.

Sai dai ubangiji ya riga ya tsara al'amarinsa don ba'a fi wata daya ba aure ya tabbata tsakanin baffansu da nuratu, ta kuma tare a b'arin mama rabin, duk da kasancewar nuratu bazawara, amma baffa ya nuna mata so wanda har hakan ya dinga b'atawa matansa rai, kasancewar baya b'oyewa koda kuwa a gaban 'ya'yansa ne.

Shekarar nuratu daya da rabi a gidan, ta haifi diyarta mai kama da ita, sai dai ta d'auko hasken fatar baffan tunda ita nuratu ba fara bace, baffa ya sanya mata Sa'adah nuratu kuma ta lak'aba mata Nanne wanda shine ya bita.

Tun daga haihuwarta ne kuma nuratun ta sauya hali, ta fara rashin mutunci kala-kala a gidan, rashin kunya tun daga kan baffan har inna ba wanda ta kyale. Nasiha da kyaliya ba wadda baffa baiyi ba amma a kullum abin gaba yake. Ganin haka, ya sawwak'e mata saki d'aya ba da son ransa ba, don har a lokacin yana k'aunarta, tayi niyyar tafiya da nanne amma ya hana. Saboda haka ta dire ta ta koma adamawa, daga baya ne suka samu labarin cewa ashe gidan tsohon mijinta take son komawa kuma ta koma d'in bayan ta gama idda.

A lokacin da hakan ta faru, mama halime tana shayar da autarta zainab, baffa ya roki da ta hada da nanne amma kiri-kiri ta rantse ba zata shayar da 'yar kishiya ba sai dai in itama ya saketa.

Aunty amarya ma da bata dad'e da yaye d'anta na biyu sadiq ba tace bata san zancen ba. Hajiya kuwa ba mai tunkararta da irin haka, kasancewar ba shirgin kowa take shiga a gidan ba har dashi baffan kuwa, kuma ma 'ya'yanta duk sun riga sun girma a lokacin. Daga karshe dai inna ce ta dauki nanne, duk da cewa da farko itama bata shiga zancen ba don tana cike da d'acin abinda nuratun tayi musu.

Da taimakon tatacciyar madarar shanun da a kullum ake tatsowa daga gonar baffa nanne ta girma a hannun kakarta, inda kuma innar ta dauki son duniya ta dora akan nannen, ya zama tamkar bata da jika ko d'aya a duniya sai ita, har ta kai ma in kana son farin cikinta to ka yiwa nannen wani alkhairi.

Sannan tun tashinta sau uku baffa yasa aka kaita adamawa wajen mahaifiyarta, sai dai ita nuratun tana yawan yi mata aike ta hanyar turo 'yan uwanta.

Gabadaya ilahirin jama'ar gidan baffa, har kuwa da tulin ma'aikatan dake cikin gida da gonaki, nanne zata iya kirga masu nuna mata kulawa a cikin 'yan yatsunta kawai, don daga wad'anda suka tsane ta sai masu nuna cewa Allah baiyi halittar ta a cikinsu ba, saboda kuwa dalilai biyu, na farko ta tashi a cikin bakin fentin mahaifiyarta daya shafeta, don da yawansu tsanar da suke mata ta samo asali ne daga irin abinda nuratu tayi a gidan bayan haihuwarta, sai kuma saboda tsananin rashin kunyarta da ba ta kan wanda bata bi in abinta ya tashi, harda manyan mazan gidan kuwa da take d'an shakkarsu.

Hakan kuwa ya samo asali ne daga rashin kwab'ar data samu daga inna, don duk gidan har baffa ba wanda ya isa yayi mata tsawa akan wani abu in tayi ba daidai ba sai anga b'acin ran inna, wani lokacin ma ta yini tana sababin cewa don anga yarinya bata da uwa a gidan ne.

Shi yasa ta tashi kusan a sangarce, saboda kowa a gidan na shakkar bacin ran inna, don in bata yi da kai shi kansa baffan baza ka samu fada a gunsa ba. Mutane da yawa in suka kalli fuskar nanne baza su ce tana da magana bama balle rashin kunya, tafi kama da irin miskilan nan dake takama da wani abu nasu, amma yini d'aya tare da ita zai rusar da wannan ma'anar.

Duk cikin jama'ar gidan, babu wanda nanne take ganin tsana b'aro-b'aro a wajensa irin mama rabi da 'ya'yanta, kasancewar baffa bai dawo da ita gidan ba sai bayan an yaye ta. Amma hajiya babba babu ruwanta da ita in ba aiken inna ne ya kaita wajenta ba, haka ma 'ya'yanta, shi yasa su take ganin mutuncinsu.

Mama halime kuwa nunawa take yi Allah bai halicci inuwarta a gidan ba, bata ko ambatar sunanta balle tabi ta kanta a duk harkokinta, tafi karkata ga yadda baffa zaifi fifita ta a cikin matansa, hakan yasa suma 'ya'yanta basu damu da ita ba, sunfi damuwa da samun harkar kyale-kyale kamar yadda ta d'ora su akai, sai dai kuma duk randa wani abu ya had'o su da nannen, kowa sai ya san ana tashin hankali a gidan kasancewar da sauran 'yan uwansu ma ba mutunci suke ba.

Aunty amarya ce mai kyararta da kuma hantara in bata ga idon inna ba, wanda ita kuma nannen in dai babu 'yan biyunta da take shakka a wajen zata rama ne da irin maganar data fito bakinta kafin ta bar wajen, ita kuma ta bita da zagi.

Ma'aikatan gidan ma basa shiga harkarta, don data had'a ka da inna hanyar samunka a wajen baffa ta fara rawa kenan.

●﹏●

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.