Free chapter · Read without an account

08

by Khadeeja Candy · ZAKI

Sai da ruwan suka dan tsagaita sannan na samu damar mikewa tsaye ina daga Nana daga jikina. Ta galabaita sosai har wani lumshe ido take tana budewa amman wani abun mamaki idan ta kalleni sai tai min murmushi, wata kila so take ta kwantar min da hankali ganin irin yadda na ke ta kuka kamar ba gobe, a saman bargon na kwantar da ita duk kuwa da irin sanyin ruwa sama da ke jikinshi na nufi inda kayanmu suke na dauki Hijab dina da shima ya gama jikewa na saka a haka na fita daga kangon gidan da gudu zuwa nemam nepep, bakin titin gawon nama na fito duk wacce na tara bata tsayawa wata kila saboda ruwan be gama daukewa ba gashi dare ne, daker na samu wata wacce babu kowa a ciki ta tsaya da sauri na shiga ciki ina fadin. 


“Mu bi ta nan marar lafiya za mu dauko”


Kamar yasan halin da nake ciki sai ya shiga kwanar Clapperto road da gudu muna kawowa kangon gidan na ce ya shigo ciki, da taimakon mai napep din muka saka ta ciki sannan na nufi jakar da kudin suke ciki na bude na daukosu gaba daya sun jike har sun hade guri daya, ni da Lukman muka shiga da sauri mai Napep din ya ja zuwa Uduth wato Usmanu dan fodio teaching Hospital, kamar yasan daman can nake son kaita. Ta sabon gate din emergency ya shiga da mu, ba laifi nurse din sun karbo mu hannu biyu sannan suka ce na je na karbo kati, da gudu na bazama cikin asibitin neman inda ake siyar da katin domin ban sani ba, hasali ma ban taba zuwa asibitin sai dai na bi na wuce, wata mace ce ta nuna min gurin da na isa ban samu layi sosai sai yan kwarorin mutane wata kila saboda yana dare ne. Amman a haka sai na kasa bin dan karamin layin na shiga rokonsu ina ta kuka. 


“Dan Allah ku taimaka min na karbi kati mamana zata mutu dan Allah”


“Zo nan a baki”


Wanda ke layin gaba ya fada sauran kuwa kallona kawai suke jikina shakaf da ruwa har diga suke a kasa. Gabansa na shiga na mika dari biyar a bani katin sai ya ce min basa son kudinbda suke jike, mutumen nan ya ciro dubu daya sabuwa hul ya miki na karba hannu biyu na ba mai bayar da katin sannan na rubuta sunanta ya miko min katin da chanjina kusan dari hudu ya cire har da yan kai, a wautata sai na mikawa mutumen canjin.


“No rike, Allah bata lafiya”


“Amin na gode”


Na juyo da sauri zuwa inda mahaifiyata take, ina isowa likitan ya hau min tambayar ciwonta nai mishi bayani. 


“Maciji ne ya tsare ta wata biyu da yan kwanuka da suka wuce, shi ne na kaita asibiti likitan yai mata tiyata ya cire dafin macijin, amman yace ta daina taba ruwa bata son sanyi shine yau ruwan sama ya doketa ta fara tarin jini”


“Dafin maciji ake yiwa tiyata? Allura dai ko?”


“Aa tiyata yana nan a cikinta ma”


Na fada ina girgiza masa kai. A take ya rubuta mana wasu abubuwan ya dauko wata takarda ya miko min. 


“Ku dauke ta yanzu kuje a mata hoto”


Sai nurses din suka dora min ita akan wheelchair na soma turara muka fito daga dakin ina rike da takardar, daman Lukman na tsaye bakin kofar be shiga ciki ba. Da tambaya na isa gurin da aks hoto sai suka ce sai naje can wani guri na biya kudin sannan na kawo musu shaidar biyan, haka na barta a gurin na isa inda suka kwantanta min na bashi takardar da wacan mai hoton ya bani sai ya fada min kudin da zan biya. 


“Dubu biyu da dari bakwai”


Na ciro kudin na bashi shi ma sai ya ki karba wadanda suka jiken wai basa son irinsu.


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Shine abunda na fada na ji kamar na dora hannuna a kai na kurma ihu iya karfina. 


“Kawo kudin haka”


Ya fada yana mikon min hannunsa wata kila yaji tausayi na ne, a haka na mika masa dubu uku ya bani canji tare da shaidar biyan kudin sannan na juyo da guduna na dawo na kawo ma mai dauka hoton, sai da akai ma mutun hudu sannan aka shiga da ita aka dorata akan wani gado suka shafa mata wani mai a jiki suka dora mata wani abu mai kamar dutsin guga suna ta yawo da shi a cikinta. Bayan sun gama suka dora a kan kujerar wheelchair suka ce na fara zuwa na kaita can gurin likitan sai na dawo na karbi hoton. 

 Haka na turata na koma da ita a dakin da ke cike da majiyanta na tsaya a inda likitan ya saka aka sauketa dazun na kira wasu nurses suka zo suka taimaka na dorata saman gadon, sannan na kama hanyar komawa, abun ka da mai hankali tashe sai hanyar ta bace min ita kaure mutane ba tare da na kula ba. Har na kai ga yin kaura da wani likita zan wuce na ji an fisgoni an dawo da ni. 


“Ke ba ki ga ni ne hala?”


Sai na kalleshi amman bana iya ganin fuskarsa saboda hawaye na cika min ido. 


“Hoto zan karbo kuma gurin ya bace min”


Na fada cikin kuka mai karfi. 


“Wow cute girl”


Ya fada kadan-kadan sannan ya nuna min gurin. 


“Doc Muhseen yi sauri pls”


Wani mutumen mai sanye da uniform din nurse ya fada sai mutumen ya sake ni da sauri yai gaba ni kuma na nufi inda ya nuna min. Ko da na koma har an fitar da hoton sai kawai na karbo ma juyo na dawo inda nurse din suke na mika musu sai suka nuna min dakin likita. 


“Can za ki shiga ki kai”


Na doshi dakin da sauri na tura na shiga ina sallama can ciki saboda kuka.


“Ga hoton”


Na mika masa sai ya karba yana ta turanci da wani mutumen dake zaune a daya daga cikin visitors chairs, likita yai rubutu cikin wata farar takarda ya miko min. 


“Idan ki siyo ka bawa nurse su saka mata”


Na karba da sauri sannan na fice duk abunda nake Lukman na biye da ni a baya a duk inda na saka kafata dana dauke sai ya saka tasa. A nan ma sai da na tambaya aka nuna min pharmacy sannan na kai takadar su ma suka ce sai na je wani guri kusa da inda ake bata kati na biya kudin maganin da suka rubuta min a jikin takardar, haka na juyo cike da jin haushi irin tsarin na nu na wahalar da mai rai na je na mika takardar sai ya fada min cewar zan ba shi dubu biyar da dari uku da naira arba'in, a nan ma sai da nai ta roko sannan ya karbi jikakkun kudin ya bani yan canjina sai na koma can na kaiwa mai pharmacy ya bani amfanin da ledar sakawa. Kamar yadda likita ya fada min haka na mikawa nurses din sai suka hau dora mata ruwan suna saka maganin a ciki sukai nata allurai sannan suka dora ragowar maganin akan wani dan karamin abu mai kamar bedside drawer, sai ta sauke wani irin ajiyar zuciya bachi yai gaba da ita. Ni kuma na koma dakin likitan Lukman na biye da ni a baya na tura na shiga, har yanzu magana yake ta yi da mutuman dazun.


“Na ba su sun saka mata”


Sai ya dago ya kalleni yana dago hoton ya ce. 


“Ba dafin maciji ke damun matar nan ba, gurin da aka cire mata koda ne ke mata zafi maybe ayi aikin yadda ya kamata ba”


Ji nai kamar ban ji abunda ya fada daidai ba, har sai da na sake tambaya cike da tantamar. 


“Ban gane ba koda kuma?”


“Yes an yi mata tiyatar koda ko?”


“Aa ba ayi ba”


“Gashi nan hoto na nuna matar nan bata da koda ďaya, kuma gurin da aka cire kodar ne ke mata ciwo”


“Ba a mata tiyatar ko da ba likita, maciji ne kawai ya tsareta aka cire dafin”


“Ba ama cizon maciji tiyata allura kawai ake, wannan tiyatar koda ce aka cire mata”


Ji nai kamar ba a duniyar nan na ke ba, sama na ke kasa na ke sai na kasa tantancewa yawu suka cika min baki daman can ido suna ta aikinsu na hawaye. Kar dai ace likitan nn ya da taimake mu kodarta ya cire? Kar dai duk taimakon da yai mana na siyen kodarta ne? 


“Amman dan kara tabbatarwa ki je ki yi wannan babban hoton”


Ya miko min wata takardar. Da na cira kafar na je na karbo sai na ji kamar an rike ni kafafuwan suka lauye gurin daya suka min majiyar kamar wacce ta shekara a tsaye. 


“Wane likita ne yai mata tiyatar yace za a cire dafin maciji?”


“Wa... Ni... ”


Na amsawa likitan maganar na fito min a rarrabe. 


“Ya cuce ku ne kawai ko kuma an gada kai da shi an cuce ku, amman dafin maciji ai ba a masa tiyata”


Daker na karasa na karbi takadar ya juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga dakin likitan ina hawayen da ban ta ina ake turo min su ba. Ban san nawa hoton zai ci ba amman tun da ya ce babban hoto nasan sai ya ci fiye da dubu da wani abu da wacan karamin hoton ya ci, gashi sauran kudin da ke hannuna ba su kai ma dubu uku ba. Da wowa nai kusa da ita na zauna a kujerar roba da ke gabanta, ta bude baki tana sheda da nan da alama numfashin da ke fita daga hancinta baya isarta. Wani irin tausayinta ne ya lullube ni ina ta kallon fuskarta kamar yau na fara ganinta, taya zan iya fadawa Nana ya cire mata koda? Taya ma zata rayu ba koda? A tunani idan mutum ya rasa wani abu daga sassan jikinsa mutuwa zai yi. 


“Shikenan Nana shikenan”


Na fada ina jan Lukman na rumgume, sai na saka kaina cikin jikakkar rigarsa na fashe da kuka marar sauti, ganin haka ba yasa shi ma ya fashe da kuka yana ta kallonta. 




ALIYU POV. 


 Babbar asibiti ce kuma kwararriyar a duk fadin duniya, tun da aka ce za a mata dashen a can a cire dayar wacce ta fara lalacewa sai ya hankalinsa ya kwanta domin manyan likitocin ne za su mata aiki kuma sun san kan aikinsu. Within week din da suka je London aka yi mata aikin cikin iyawar Allah da ikonsa aka yi nasarar cire wacan kodar aka dasa mata wata. A can aka cigaba da kula da ita har na tsawon wata daya a ciki wata na biyu ne suka sallamota ta dawo gida Nigeria tare da mijinta da kuma mahaifiyarta wacce sukai tafiyar tare. 

 A nan gidan ma kusan kullum sai Doc Asim da wani likitan Doc Jonah sun zo dubata, sosai ta so su tare a Abuja tun dawowarsu daman a can suke zama, amman Aliyu ya ki saboda yana son ya koma Abuja da zama a halin da matarsa take bukatar lokacinsa, ya san duk yadda ya ke son bata kulawa idan har suka je Abuja dole ne sai ya leka office amma a nan yana tare da ita tun safe har dare. 

 At early morning ya farka yau kamar yadda ya sabawa kansa tun da suka dawo gida. Da kansa ya shiga kitchen ya saffara mata abunda zata ci idan ta farka sannan ya dawo falo ya zauna yana duba wasu abubuwan a laptop dinsa. 


“Aliyu...”


Ta kwala masa kira daga dakin da take kwance duk da tasan ba zai amsa ba amman ta san zai ji ta, daman can baya amsa kira idan aka kira sunansa, sai dai idan yana kusa da kai ya kalleka ko kuma ya taso ya zo idan shine a kasa da kai, idan kuma kai ne a kasa da shi sai dai ka je ka same shi. Laptop din ya aje ya mike tsaye ya nufi upstairs fuskarsa ba yabo ba fallasa. 

Zaune ya sameta saman gadon ta dukunkune da bargo ta wani bata fuska kamar karamar yarinya. 


“Sanyi na ke ji waya ce ka kunna ac”


Sai ya kai hannu ya kashe ac ya hauro saman gadon ya yaye blanket din da ta lulluba da shi yai kissing fuskarta. 


“Ta so muje ki karya kin san sun ce ki rika karyawa ba sai kin ji yunwa ba”


“Me ka dafa min”


“Doya da madara ka san kina so ai”


“Ba ka iya ba fa”


“I try ”


Ya fada, yadda yake amsa maganar sai na rantse da Allah ba a bakinsa take fitowa ba, domin babu wata alama da ke nuna cewar magana yake. Saukowa yai da ita saman gadon ya nufi bandaki da ita da kansa ya wanke mata baki as usual sannan ya fito tare da ita. 


“Gidan nan duk yai datti kuma bathroom din ma yai wata ba a wanke ba ni kyamar Shiga ma na ke”


Ta fada masa a daidai saitin kunnensa ba ce da ita komai ba ya ja suka nufi hanyar fita daga bedroom din. 


“Ka ji?”


Nan ma be ce komai ba har suka sauko downstairs, daman can haka yake kamar wanda maganar take masa wahala, kujera yaja mata ta zauna akan dinning. 


“Ba ka ce komai ba”


“Za mu samu wanda zai rika mana shara da gyara gida”


Ya fada sannan ya zauna ya shiga serving dinta, da kansa yake feeding dinta har ta koshi sannan ya zuba ma kansa ya ci. 


“Yaushe za ka samo?”


Haka ta dinga tambayarsa amman be ce mata komai ba, har ya gama cin abincin ya tashi. 


“Ni wannan miskilancin na ka damuna ya ke”


A dai-dai lokacin da zai stairs ta fadi haka, sai kawai ya juyo ya sakar mata murmushi gefen fuska ya juya ya haye sama. 


________

An ciye kidney din wata an raya wata 😪


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.