FreeArewaPen original
MIJIN TA CE
- 1views
- 9chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I am hafsat chindo sodangi from plateau state nigeria.
Sample · Book 1 (Farko)
MIJIN-TA-CE “Humaira! Humaira!! Humaira!!! Bata jin wannan kiran ne ko kuwa?” daga can cikin gidanmu nake jiwo waxannan maganganun. Abinda yayi dalilin da na fasa shiga cikin gidan na qara ja da baya na tsaya ina sauraron mai maganar. Cikin takaici da vacin rai na yanda ita kullum babu dama ta kira wani ta xan sa shi wani abu don ni ma in xan samu in huta komai sai dai ta kira Humaira. Can cikin zuciyata na sake jan wani mummunan tsaki a daidai lokacin da haushinta ya sake kama ni a dalilin zuba wa kwanon dake hannuna ido da nayi, cikin takaici nace sai kace ba ita ta aiken ba, tun kafin in kai ga kawo mata aiken da tayi min xin har ta mance tana sake nemana don ta sake aikena tanfar dai babu kowa a gidan sai ni. Maimakon in hanzarta shiga cikin gida in kai mata aiken nata, musamman da yake ina jin yanda ta kasa daina qwala wa sunan nawa kira, sai kawai naja na tsaya cikin zauren na maqale jikin bango ina sauraro tare da yin tsokaci kana wasu al’amura da suka addabi zuciyata. Ko yaushe ne ni ma zan samu in xan huta in samu in rinqa watayawa irin na sauran yaran gidanmu, in mallaki ‘yancin rayuwa irin na yanda nake ganin sauran ‘yan uwana suna dashi? A kullum zuciyata ta xan samu wani sarari ko wata dama da zata yi min wata tambaya, to ba tayi yi min tambayar da ta wuce waxannan tambayoyin, yaushe ne ni ma zan huta? Yaushe ne ni ma zan samu ‘yancin rayuwa irin wacce sauran ‘yan uwana ke da ita? A lokacin da nake yarinya ‘yar qarama, na xauki halin da nake ciki na takura da qunci da rashin hutu tanfar hakan ya same ni ne a dalilin ni xin ni ce qarama cikin yaran da suka kai munzalin moro. Don haka sai nayi ta fata da buri waxanda suke biye da ni su kawo sanda za su karve ni, amma daga baya sai na gane a’a ba haka ba ne tunda ai akwai wasu qannen nawa da tazarar watanni goma ne kawai a tsakanina da su. Kamar irin su Suwaiba, kuma su xin ba ayi musu irin aiken nan da ake yi min na sayo min kuka, sayo min daddawa, sayo min kanwa, komai ma dai ba kuma wannan ne yafi komai vata min rai ba, sai irin wai ko a gida xaya abubuwan da ake buqata suke to ba za a haxa min aiken ba, sai na kawo xaya a sake maida ni. Duk a dalilin dai wai kar a ganni a zaune ina hutawa, ko sanda nake yarinya ‘yar qarama wannan jeka-ka-dawon kan ci min rai, to balle yanzu da na soma sanin abinda ke min ciwo, ga kuma wasu qannen nawa da yawa da suka taso bayana waxanda su ba hakan ake yi musu ba, waxanda su suke ma da ‘yancin a aike su su ce ba za su ba. Babana Malam Surajo mazaunin unguwar Jahun ne dake cikin jihar Bauchi, Jahun gaba take kaxan da Nasarawa, in har ka biyo ne ta qofar Nasarawa ne, gaba xaya ta nan kewayenmu har unguwannin dake kewaye damu mutane da yawa sun san shi, sun kuma san gidanmu. Saboda kasancewar shi xin a shekarun da suka gabata yana cikin ‘yan kasuwar da k...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.