Free chapter · Read without an account
Page 4,5 and 6
[9/19, 3:58 PM] Rahma Kabir: ZAMANI...
*Riga kowa da irin nashi*
Na
Rahma Kabir mrsMG
Wattpad @rahmakabir
Page 4.
Mahmood bashi yabar gidan ba sai gab da sallar la'asar saboda yana so yaje makarantarsa na islamiya ya duba dalibansu masu yin haddar karatun Al-Qur'ani, shine shugaban makarantar wato headmaster, sannan nashi ne wanda ya samu dalilin gadon da babansu ya rasu ya bar musu, da yake Baba soja ya bar musu kadarori sosai, babban gida ne sai ya gyara shi ya maidashi makarantar islamiya mai suna Hudallahil islam, kasantuwar shi mutum ne mai matukar sanin abinda ya shafi addini, ya karanta Arabic har matakin digree sannan yaje saudiya yayi karatun addini na tsawon shekara biyu, hakan yasa makarantarsa ya samu karbuwa sosai a wajen al'umma, layi uku ne ke tsakanin makarantarsa zuwa gidansa, wanda da albarkan makatantar ya samu ya gidana gidan duk a nan kabala. A dalilin busabakar Al-Qurani ne ya hadu da Saudat, makarantar tahfizul Qur'an ta gayyacesu dake unguwar mu'azu, ya tafi da hazikan dalibansa domin su fafata. Saudat tana cikin masu yin gasar busabakar yan uzu biyar, sunyi nasu sun gama suna cikin yan kallo da yake a babban masallacin dake kusa da makarantar ake yi, Saudat macece mai yawan surutu hakan yasa bakinsa yaki shuru ta dinga magana da kawayenta, masu tsaron bangaren mata suna ta gargadin ta amma bata ji ba, hakan yasa malamarsu Fatima tace ta fita, ta kai ta wajen headmaster dinsu a waje ga wasu malamai a gurin ciki harda Mahmood, Headmaater malam Yusuf ya soma yi mata fada, Saudat har da kuka saboda sam ita bata taba yarda tayi laifi balle ayi mata fada kasantuwar ita ce auta a gidansu, ta taso cikin gatan iyaye da yayyi maza da mata sosai, su shida ne gidansu mata hudu maza biyu, duk matan aunyi aurensu sai namiji daya yi auren, sai wanda take bi shine yayi saura. Mahmood ganin sun rufeta da fada sai ya basu hakuri ya shiga yi mata nasiha wanda yasa ta daina kuka har take ganin kirkinsa duk cikin malaman, haka suka sallameta ta koma wajen taron. Tana tafiya Mahood ya tambayi malam yusuf in da take, nan ya fada masa komai wanda gidansa yana makotaka dasu a nan unguwar Mu'azu.
Mahmood Allah ya daura masa son Saudat a ganin farko kuma yayi dace da itama tana sonsa, domin shine mutum na farko da Saudat ta mai da hankalinta akansa harya samu karbuwa saboda ita tana da ruwan ido, ganin Mahmood bai da wata makusa yasa ta amince duk da bata taba zaton taza iya soyayya da ustaz ba, a hankali Mahmood ya jefa soyayyarsa a zuciyar Saudat har ya zamana ta makasance akansa saboda iya kalaminsa.
Shekara daya da wata uku suka kwashe suna soyayya kafin ya kaisu ga aure, duk da da kyar mahaifinta ya amince domin yaso sai ta fara jamia, har karatunta yayi nisa kifin zai yi mata aure, ganin ta kafe yasa ya kafawa Mahmood sharudda akan dole ya barta ta cigaba da karatun boko domin yaransa suna yin karatu mai zurfi, Mahmood ya amince duk da a tsarinsa baya son ya auri mai zurfin karatun boko yafi son wacce take da na addini sosai, amma saboda tsantsar son da ya ke yiwa Saudat yasa shi amince har suka yi yarjejeniya a rubuce lokacin da waliyyansa suka zo. Bayan aurensu da wata tara da kwana biyar Saudat ta haifi Walid, tana yin arba'in da kwana uku ta fara zuwa jami'ar KASU, shekarar Walid daya da rabi ta kuma saminci wanda ta haifi Amir, ganin karatunsu yayi zafi sosai tana karanta english yasa dole ta soma yin family planning, domin ta samu ta gama karatu da kula da yaranta kafin ta kara wani haihuwar, ba haka Mahmood yaso domin shi yana son yara amma saboda ya faranta mata ya sa shi amincewa, yanzu gashi gar tana matakin karshe na kammala karatunta.
****
Hibba duk yadda taso ta fita zuwa gidan hajiya amma haka ta hakura bata je ba. Bangaren hajiyar tayi zaton ganin Hibba amma shuru har washe gari bata zo ba, sai tayi ta saka tana warwarewa domin kuwa ita dai tana son hibba kuma bata burin ta bata mata tarbiyya, sai dai tana so ta nunawa Innar Hibba cewar bata isa ta rabasu ba duk da ita ce ta haifeta, dan haka ta dauki aniyar kara jawo hibba cikin rayuwarta.
Karfe daya da minti goma Hibba ta dawo daga hadda ta shiga dakinsu tana cire uniform sai ga kiran Hajiya sa'a ya shigo wayarta. sai da taji gabanta ya fadi ta dauko wayar tare da leka waje ko inna bata kusa, sai da ta tabbatar da haka kifin ta dauka murya a can kasa take maganar dan kar a jita, Hajiyar tace cikin sakin fuska.
Hibba da alama dai innarki ta rabamu, ace tun jiya ina zuba idon ganinki amma shuru gashi har girki na daura dake baki zo ba.
Kiyi hakuri Hajiya wlh na shigo gidan na tadda abinda banyi zato ba, inna ta bani tsoro sosai da irin fushin data nuna, shiyasa nace bari na hakura har zuwa lokacin da zata sauko.
Ba damuwa nasan magulmata ne suka ci galaba akanmu, dama kiran da nayi miki ina so zaki rakani wani biki. kawata ke aurar da 'yarta a unguwar rimi, za suyi party anjima kamar ma dinner ce, amma tunda ga halin da kike ciki na hakura zanje ni kadai kawai.
Dagaske dan Allah? wlhi ina son zuwa na san bikin masu kudi ne ko?
Masu kudi ma sosai, dan gaskiya akwai manya mata masu ji da aji da naira, amma bana son ki sabawa innarki da sai na ce kizo mu je.
Aiko wlh zani, ni nasan karyar da zanyi mata, ba zan bari wannan damar ta wuce ni ba, ina son ganin bikin masu hannu da shuni wanda nake mafarkin gani.
A'a fa hibba, bana son tashin hankali jiya nan mamanki ta yi min wankin babban bargo.
Allah zani ki shirya min kawai.
To sai ki fito da wuri da yamma zamu bayan la'asar ki sameni a shagon saloon dina dake unguwar shanu.
An gama hajiya, ki tanadar min kayan da zansa.
Wannan karki samu damuwa ke dai sai kin zo kawai.
Sai hajiyar ta kashe wayar tana sauke wani shu'umin murmushi ganin ta shawo kan hibba cikin kankanin lokaci. Hibba kuwa ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar ta gama cire kayan makarantar tasa wasu ta fito dan tayi alwala, sai taga Inna tana wanke tsaki tace cikin walwala.
Inna dambu zaki yi mana ne?
Eh hibba na zogala zanyi, yaushe kika dawo ne?
Ban jima da shigowa ba, na tsaya cire uniform ne shiyasa ban leko dakinki ba.
Aiho nima yanzu na fito daga bandaki. Kiyibsallah kizo ki amsheni in samu nayi nima.
To Hibba ta amsa kafin ta dauki buta ta shige bayi. Sai wajen karfe biyu da rabi dambun ya sauka, suna zaune a dakin hibba suna ci ita da Inna Ali yabi Baba kasuwa can inda yake harkokinsa sai yamma zai dawo yaje islamiya, Hibba ta kalli inna ta ce cikin sanyin jiki.
Inna Malam Hamza ya kirani yace zan rikewa daya daga cikin malamanmu mata ajin yamma, wai ba tada lafiya shine yace inje, amma nace masa sai na tambayeki tukuna.
Allah ya bata lafiya, ai da kince masa zaki je din tunda lalura ce, kuma ba yau ne kika saba rike musu aji ba, sai kiyi kokari ki kirashi ki ce masa zaki zo.
Nagode inna, kuma nayi hakan ne domin na nima izininki kar nayi gaban kaina.
Kin yi kyan kai hibba, kuma haka nake so ki rika yin abu da tunani, Allah ya kaimu anjiman
Hibba ta amsa da amin, cikin ranta tana wani jin farin ciki, yanzu ita inna sai da dubara ake samun kanta.
Hibba tana idar da sallar la'asar ta shirya tare da sanya dogon hijab dinta da safa har da nikaf, ta fito ta yiwa inna sallama sai ta wuce. Tana isa bakin titi ta karya kwana kamar zata islamiya sai da ta dan yi nisa kafin ta sauya hanya ta shiga wani layi ya bille da ita kan titin da zata shagon saloon din Hajiya.
Hibba tana isa shagon ta sameta a ciki ga yarinyar dake zama mata wacce take aikin saloon din, Hajiyar ta mikawa Hibba ledan kayan data dauko mata tace ta shiga da sauri ta shirya sai ta fito Beeba ta yi mata kwalliya, Hibba ta shiga daga cikin wani karamin daki dake cikin shagon ta sanya kayan riga da sikrt ne yan kanti farar top ne mai dogon hannu wanda ya matseta sai siket mai fadi wanda yake dauke da manyan fulawa baki da rashin blue da pink, kayan sunyu matukar amsar jikinta ta saki murmushi ji take kamar ta dauwama dasa irinsu, ta fito hajiya da Beeba suka hada baki suna badin tubarkallah tare da yaba kyan da kayan suka yi mata, da sauri hajiyar ta mike ta daura mata pink din lafaya a saman kayan, Beeba kuma tayi mata kwalliya nan danan Hibba ta fito ras kamar ba ita ba, ba dankwali dan haka beeba ta gyara mata gashinta tayi parking dinsa da rebom, kana suka dauketa hoto a wayoyinsu saboda kyan da tayi, sai suka fito suka shiga motar hajiyar kana suka wuce wajen bikin.
Tun a farkon layin hibba ta rude ganin jerin gwanon motoci a cikin layin, da kyar Hajiya sa'a ta sami wajen parking sai suka fito dan su karasa gidan bikin, Hibba dai sai kama jiki take yi saboda rashin sabo, lura da hakan ne yasa hajiya tace mata.
Ki saki jikinki fa karki bada mu, saboda nan gun manyan attajirai muke ratsawa, kila kafin mu tafi kiyi arba da wani babban hamtsaki ya ɗafe miki.
Hibba dai murmushi tayi domin ta kasa cewa komai, sai kawai ta daga kai tana kallon gabanta tana jan kafa kamar kwai ya fashe mata, a haka suka isa gidan su ga cike yake da mata da maza abin dai ba a cewa komai, kowa da shigar ke ce raini, sai dai abin mamaki shigar hibba ya samu karbuwa sosai ga mutane dan sai kallonta suke saboda ta burgesu, suka isa falon gidan sai ga wata mata da gudu ta rungume Hajiya sa'a tana fadin.
Sai yanzu kika ga damar zuwa bacin anci an cinye bikin.
Kiyi hakuri Hajiya Jamila kema kin sanni da hidimomi, amma gani nazo a kare komai dani.
To kin kyauta, ina kika samo kyakkyawar yarinya haka?.
Hajiyar jamila ta kare maganarta tana kallon hibba.
'Yar sister dina ce ta zo min shi ne nace ta rako ni.
Kin kyauta amma ina ganin zan yiwa Babangida kamu gaskiya.
Hajiya Jamila tace tana dariya, wato babban danta kenan zata yiwa kamu, Hajiya Sa'a itama dariya tayi sai suka shige ciki, a zuciyarta tana fadin ai hibba tafi karfin Babangida sai hamtsaki, suka samu waje suka zauna nan Hajiya jamila tasa aka kawo musu abinci, waina da miyar agushi ga fried rice sannan ga kwanon farfesun ganda da kayan ciki a hade sannan ga kwanon soyayyan naman kaza, Hajiya Sa'a tace a kaisu wani daki daba mutane dan su ci a natse, Hajiya Jamila tasa mai aikinta ta kaisu dakinta dake sashin mijinta saboda ta san can ba kowa, sanin hajiya Sa'a babbar aminiyarta ce shiyasa ta kaisu can ba tare da tunanin komai ba. Suna shiga cikin falon Hibba taga katon hoton mijin a jikin bango ga kuma na Hajiya Jamila a gefensa sannan ga wanda suke tare da yaransu uku, Hibba tabi hoton Alhaji Bukar da kallo ita dai yayi matukar yi mata kyau har ta kasa dauke idonta ta tsaya tana kare musu kallo, hajiyar ta juyo tana kallonta dan har ta isa kofar dakin da zata shiga, dan mai aikin a bakin kofa tayi musu nuni da dakin ta koma, hajiyar ta kai idonta in da Hibba ke kallo sai taga hoton Alh. Bukar take kallo, ta saki murmushi kana ta kira sunanta, firgigit hibba ta waigo tana murmushi, sai ta isa inda hajiyar take tsaye rike da babban tire din abincinsu suka shiga dakin, suna zama hajiya sa'a ta kalleta da kyau tace cikin muryar gargadi.
Hibba kin ga ki rufa min asiri mu bar gidan nan lafiya, ba karamin yarda dani hajiya Jamila tayi ba data ce muzo nan, wannan mijin nata tsoka daya ne a miya a wajenta, ba karamin shege shige take yi ba akansa duk dan kar wata ta shigo gidan nan a matsayin kishiya, shiyasa har yau bai kara aure ba kusan shekara ashirin da biyar kenan da aurensu, babban danta Yusuf suna ce masa Babangida shekarunsa ashirin da hudu yana u.s yana karatu, sai mai bi masa Safara'u tana nan kasu tana karatu sai Autarta Husna bana take gama secondry mate din ki ce. Amma kin ganta nan har yau bata ganin ta tsufa saboda kudi da muka mugun son mijinta da take yi, da kyar ta yarda Safara'u zata yi aure yanzu, a ganinta zata sanya ana ganinta ta manyanta tunda gata da suruki.
To ni hajiya me nace daga kallon hoto sai cibi ya zama kari, kawai dai yayi min matukar kyau ne kamar ba shine mijinta ba dan ya fita kyau sosai.
hakan yasa take mugun kishinsa, kuma da yake Bukar din yana da kudi sam tsufansa baya nunawa dan ya kai shekara hamsin fa.
Uhum to kinji fa aini ya min ma tsufa.
Hibba ta fada tana 'yar dariya, hajiyar ta ta yata dariyar a ranta tana fadin.
Tsoho da kudi yaro ne a gun yan mata irin ki.
Hibba sai ta soma cin waina tana santi, tana cin guda daya ta koma cin shinkafar, ganin karta cika cikinta da abinci sai ta jawo kwanon farfesu ta soma ci, da yake su kadai ne a dakin hannu baka hannu kwarya take ci kamar wani zai shigo ya hana ta ci, hajiyar sai dariya take yi mata ganin yadda ta kasa boye maitarta a fili, wato gida babu makota sai dai dai, shiyasa ta barta ta ci da kyau dan ta san sai sallah sallah take ganin nama haka har ta yi masa cin tsiya, sun bata tsayin lokaci a wajen kafin suka gama ci, Hibba dai ta shaida tazo bikin masu kunbar susa wanda ya zama na farko a tarihinta.
________
Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. ***
*Idan kuna bukatar a tallatar muku hajar ku a pages ko a daura a status ku tuntubi wannan number ***, zaku samu akan farashi mai sauki.*
[9/20, 12:31 PM] Rahma Kabir: ZAMANI...
*Riga kowa da irin nashi*
Na
Rahma Kabir mrsMG
Wattpad @rahmakabir
Page 5.
Hibba sai wajen karfe shida da rabi kafin ta farga da yamma tayi har ana gabda kiran sallar magrib, haka ta matsawa Hajiya akan zata tafi sai ta bata kudin mota ta rakota har titi ta hau napep ta wuce. Lokacin da ta kai shagon salon din an kira sallah har an shiga masallaci, cikin sauri sauri ta sauya kayan jikinta ta sanya nata ta sanya hijan tare da daura nikaf ta ajiyewa hajiya kayanta gaba daya sai ta wuce gida cikin sauri kamar zata kifa, sai yanzu take yin fargaba da tunanin fadan da inna zata yi mata, addua take Allah yasa Ali baije makaranta ba dan ta san in har yaje to zai gayawa inna bai ganta a makarantar ba, da zullumi ta isa gida da yake gari yayi duhu kwalliyar dake fuskarta babu wanda ya fahimta bayan ta daga nikaf, ta shiga dakinsu tana hura iskan bakinta saboda gajiya ga gumi daya rufeta na saurin da tayi, tana kokarin cire hijab sai ga Inna ta leko dakin da sauri ta juya tana kallon bango dan karta ga kwalliyar fuskarta Inna tace.
Sai yanzu kike dawowa? gaskiya ki daina kaiwa wannan lokacin, da Ali yaje makaranta da kin ganshi na aiko shi akam ki dawo.
Au Ali baije ba kenan?
Ta tambaya cikin zakuwa.
Ina kuwa ya dawo daga kasuwar, yau dai ban san me ya hanashi dawowa ba, ni dai karki kara kai wannan lokacin.
Inasha Allah zan kiyaye bari nayi sallah.
Cewar Hibba cike da jin dadin rashin zuwan Ali makaranta hakan ya bata tabbacin asirinta ya rufu, inna ta saki labule ta wuce kitchen dan ta tuka tuwo ita kuma ta fito tsakar gida ta dauki buta ta yi alwala ta samu sabulu ta wanke fuskarta kafin ta shige daki tayi sallah.
Cikin dare Hibba ta kasa barci sai tunanin hoton nan data gani gidan biki take yi, a zahiri bata san ya zata kamanta so ba amma kuwa hoton mutumin ya tsaya mata a rai, daga wani bangaren zuciyarta tana kokarin ya kice hakan dan bata ga dalilin da zaisa ta damu kanta ba akan mutumin cikin hoton, saboda yayi mata tsufa sannan ba zata iya aurensa ba ga kuma yadda Hajiya ta fada mata akan kishin hajiya Jamila, sannan kuma a yanzu ba soyayya a gabanta tunda babanta ya hanata tsayawa da kowa, har sai karatunta na yayi nisa, shiyasa lokacin da Kamalun layinsu ya ce yana sonta taki bashi fuska daya matsa mata ta fadawa Inna, takakkiya baba yayiwa mahaifinsa akan aja masa kunne ya rabu da hibba karatu zata yi, tun daga lokacin ya kiyayeta, itama tunda baba yace ba ruwanta da soyayya ya sanya ta kita, gashi kuma tanada farin jinin samari da wuya ta fita ba nikaf ta dawo wani bai tare ta yana sonta ba sai dai bata bada fuskar da za a zo wajenta, duk kawayenta in suna labarin samarinsu a boko haushinsu take ji domin ita cewa take bata da lokacin kula wani namiji, sai dai kuma hakan yasa ta zama koma baya a cikinsu domin sai dai taga abubuwa na sha'awa a hannunsu kama daga waya sutura da dai kayan kwalliya, da yawansu samarinsu ke siya musu ita kuwa ba tada mai bata shiyasa har kawo yanzu wayarta mai touchlight take rikewa karamar nokia, duk wani abu na zamani to Hibba tana a baya har yau bata waye ba, shiyasa hakan ke damunta tana son taga tana kashewa kanta kudi tasa kaya masu kyau da tsada tayi rayuwa irin na yan matan zamani amma duk babu dalin haka, har gobe tambayar kanta take yi sai yaushe zata yi rayuwar freedom kamar yanda yan matan zamani suke yi, ta san dai duk abinda take so ba zata same shi ba wajen iyayenta tunda ba su da karfin siya mata, ita kuma ba zata iya kula samari ba yanzu tana ganin lokacin yin hakan bai taso ba, sannan da yawan samari masu kashewa yan mata kudi suma sai sun moresu kafin suke basu, to ta wace hanya zata samu kudin yiwa kanta hidima musamman ma da take kokarin shiga baban makaranta, kullun da wannan tunanin take kwana take tashi, ita ba sana'a take yi ba balle ta yiwa kanta tanadi, amma kam tana ji a ranta ba zata iya jure cigaba da rayuwar karma karma da suke yi ba, nan gaba dole ne zata samawa kanta hanyar samun kudi, wanda zata wanke goma ta tsoma biyar saboda kaf kayanta ba zata jure zuwa jami'a dasu ba dole zata sauya su, ire iren wannan tunanin suke manne kullun a zuciyarta.
*****
Bayan wata biyu.
Exam dinsu waec ya fito wanda ta samu duk abinda ake so hatta jamb dinta yayi kyau, hakan yasa Baba ya soma nima mata kakaranta, cikin nasarar Allah ta samu admission a nan kadpoly dake tudun wada, sun bata Computer sience, ba bata lokaci baba yayi mata registration, ya biya komai hatta kudin handout ya bayar saboda ya jima yana yiwa karatunta tanadi. Bayan ya dawo gida ya sanar dasu cewar ya gama komai ranar monday zata fara zuwa makaranta, Inna tayi addu'a sosai da sanya albarka, Hibba ba karamin murna tayi ba ganin basu sha wuya sosai ba wajen samun makarantarta, duk da ta san Baba ba karamin shige shige yayi ba da har ya sama mata admission, sai dai kuma a wani bangaren ta damu sosai saboda rashin wadatattun kaya da ba tada su ga kuma makatanta ce ta kece raini, sannan ma lokaci ya yi da zata fara yin amfani da gyale saboda ta shiga zamani itama, amma ta san inna ba zata barta ba, hakan yasa ta yi tunanin zata samu hajiya sa'a ta rika aron wasu kayanta da gyale in taje shagonta saita sauya ta wuce, haka ta dunga tunani kala kala akan yadda zata fara zuwa makaranta.
**
Ranar monday.
Da sassafe Hibba ta shirya ta sanya atamfa riga da siket ta dinyi kwalliya kadan sai ta zumbula hijab kana ta dauki jaka wanda inna ta bata duk ta yakushe jakar, amma ya zata yi dole ta amsa tunda ko arzikin jakar yan mata ba tada shi, ganin yadda jakar yake duk ya fice hayyacinsa saita sanya cikin hijab ta rike handout dinta a hannu ta fito daga daki ta shiga wajen inna ta samu suna karyawa ita da Baba, ita tun dazu tayi karin saboda ita ce ta dama kokon Ali ya siyo musu kosai, Baba ya kalleta bayan ta zauna yace cikin wasa.
Yan makarantar bokoko kenan, da fatan kin dauki duk takardunki.
na dauka gaba daya baba.
to madallah Allah yayi wa karatun albarka sannan ki mai da hankali sosai, banda wasa saboda wannan ba karamar makaranta ba ce kinji.
Insha Allah baba zanyi abinda kace.
Yauwa yar albarka.
Yace tare da daukar kofin koko yana kurba, Inna kuwa ta daura da cewa.
Hibba wlh ki mai da hankali banda jajibe jajiben kawaye, bana son kula samari kiyi abinda ya kaiki, sannan wlh naga wani sauyi a tattare dake to zaki bar karatun nan dan ba zaki ja mana zagi ba, sannan ki rika dawowa akan lokaci banda yawo banza dana wofi, Ni wlh dan malam ya dage ne sai kin yi karatun nan amma da aure kawai muka yi miki.
Haba inna meyasa koda yaushe bakya yimin matan alkhairi ne a lamurana, addu'a kawai nake bukata kuma na san ba wajen da zanyi wasa bane insha Allah zan kiyaye muku mutuncina.
Ai dama ke ba yadda zan fada miki kiji sai kinyi korafi, Allah dai yasa ki mai da hankali.
Ke Indo meyasa kike hakane ki mata addu'a kawai yafi ki tsaya wannan surutan.
Cewar baba yana duban Inna, Hibba kuwa ta turo bakin nan kamar zata zubguri sama, gaba daya gani take inna bata son farin cikinta tana son takura mata sosai, Inna ta kade baki tana cewa.
Ai kaji, na san sai ka shigar mata, sai ki tashi ki tafi kar kiyi latti Allah ya bada sa a.
Hibba ta amsa da amin kana ta mike, baba ya mika mata kudin mota dana abinci dari bakwai, ta amsa tana godiya kana ta wuce, tana fita ta tsaya tayi waige waige taga ba wanda zai kaiwa Inna gulmar ta shiga gidan hajiya, sai ta wuce ta shiga da sauri, ta samu falon bude sai dai ba kowa aciki, ta bude murya ta kwada sallama har sau biyu, daga ciki aka amsa mata sai ga Hajiyar ta fito daga ita sai kayan barci riga da wando tana hamma ta zauna kujera tana cewa.
Yan makaranta har kin fito kenan.
Eh wlh ina kwana, dama na zo ki bani aron Gyale ne dan gaskiya ina bukatar na sauya sheka nima a dama dani a jami'a.
Hajiya tayi dariya ta mike ta shiga ciki ba jimawa ta fito rike da milk gyale ta bata. hibba ta amsa tana godiya ta sanya a jaka tama cewa.
Beeba ta fito Shago yanzu kuwa?
Eh tana fitowa da wuri saboda yin shara da gyara wajen.
Yauwa can zan tsaya na sanya gyalen daga nan tayi min kwalliya.
To a dawo lafiya, ni bari na shiga ciki dan barcin bai isheni ba ke ce kika tashe ni.
Hibba ta wuce da sauri bayan sunyi sallama, kamar dai yadda ta fada sai da ta biya shagon hajiya ta sauya hijab ta sanya gyale Beeba tayi mata kwalliya kana ta wuce makaranta.
___________
MAHMOOD
Sai bayan sallar isha'i ya dawo gidan tare dasu walid ya shigo da mashin dinsa cikin gida ya rufe kofar kana ya wuce ya shiga falon, ya samu Saudat taci uban ado ta daura kafa daya kan daya tana kallon tv, ga kuma kofi a hannunta da tsolali a ciki wanda yake da yAkinin complex ne a ciki ko tea, ya zauna kusa da ita da yake a two seater take zaune, su walid kuma suka wuce dakinsu dan suyi barci saboda za suje hadda da safe, sannan irin koyarwar da Mahmood yayi musu kenan da su rika barci da wuri, Saudat bata ko kalli inda yake ba yayi murmushi dan ya san kwanan zancen in daI fushi ne to Saudat ta ciri tuta, ya muskuta yace cikin sigar lallashi.
Saudatyyy wai har yanzu fushin kike yi ne? ina ce komai ya wuce tun dazu, yanzu dai ki aje kofin nan ki kawo min abinci, su walid sun ci a gidan Umma, nima tayi mib tayi nace ina sauri zanci a nan.
Saudat ta kalleshi shekeke.
To banyi girki ba ko ka ce nayi ne? Hasalima banda karfin yin girki dan assignment din da nayi dazu yasa na gaji.
Haba saudat yanzu dole sai kin hukuntani akan abinda ya faru dazu, wai meyasa ke ba zaki taba amsar laifinki ba, karshe sai ki tattaro komai ki daura min ko kuma fushi dani, wannan bai isheki ba har sai kin mini izaya da yunwa.
Ummm wannan kuma kai ka jiyo.
To ni dai kiyi hakuri ki tashi ki shiga ki dafa min ko taliya ce nasan ita ba zata dauki lokaci ba pls.
Wallahi yadda nayi kwalliyar nan ba zan shiga kitchen ba, ai ka iya girkin sai ka shiga ka dafawa kanka ko ka sha tea.
Saudat nifa kika yiwa kwalliyar ko da kin bata bai tashi abanza ba tunda lada zaki samu.
To sai kayi ai, amma ka sani inna fada ba wanda ya isa ya sauya ni ehe.
Mahmood ya dafe kansa yana jin wano tukukin bakin ciki ya sauke ajiyar zuciya ya mike jiki ba karfi ya wuce dakinsa, ba jimawa ya fito sanye da jallabiya ya shiga kitchen ya soma kiciniyar dafawa kansa indomie, yana yi yana goge gumi, rabin lokaci ya bata kafin ya gama ko barinta bai yi ta gama tsotsewa ba ya juye a plate ya dauki ruwan pure water a fridge yazo falon ya zauna a carpet ya soma ci, ba dan yunwa ba babu abinda zai sa shi yaci indomie, haka ya tura badan yaji dadinta ba yana gama ci ya wuce dakinsa ya watsa ruwa yabi lafiyar gado bai sake bi takan Saudat ba, ita kuwa sai da ta gama bata lokaci wajen kallon tv kafin ta wuce dakinta ta sauya kaya ta kwanta tare da daukar wayarta ta kunna data ta soma charting a wani group dinsu ita da kwayenta su Hudu, Safara'u da Jidda sai Aisha da kuma Sajida, suna ganin ta fara typing Safara'u ta turo da imoji na dariya, tan cewa.
Matar malam ya kuka kwashe ne daya dawo?
Saudat tayi saurin goge rubutun data fara yi ta bata reply da cewa.
Ai shine na hau na baku labari, in gaya muku wlh naki yin girki yace ina abinci nace banyi ba, yace na dafa masa nace ya shiga ya girka ai ya iya.
Nan dai ta kwashe komai ta fada musu tana dariya, suma suna taya ta, dama tun fadansu na dazun ta basu labari shiyasa suke ta tsumayen jiranta ta hau ta fada musu yadda suka kaya, gaba daya Saudat ba ta boye musu duk wani zancen gidanta su kuma suna kara karfafa mata guiwa akan karta yarda ya rainata ta rike class dinta tunda yana sonta dole zai bita, Sajida tace.
Yanzu dai ya kamata ki sauko kije ki same shi ku daidaita tunda kin hukuntashi.
Wlh ba zanje ko ina ba, ba zan taba yarda malam yaga damata ba, dole sai ya jure duk abinda zanyi masa bai isa ya rika juyani ba Allah, shi din banza.
Take it easy my friend, ki sassauta, mijinki ne fa kuma na san kina sonsa.
Cewar Aisha, Saudat tayi murmushi.
kaza ma tana son danta take tsakuransa dan haka ku barni kawai.
Kina wuta kawata gwara ki bashi karatunmu mai zafi dan mazan yanzu ba ayi musu sakwa sakwa, da zarar sun ga lagon mace sai su raina ta dan haka kija zaranki yadda kike so tawan.
Cewar Safara'u, Saudat ta tura mata imoji na jinjina daga haka suka cigaba da caccakar maza, ko wanne da irin yadda yake juya mijinsa, gaba dayansu suna da aure, Saudat da Aisha duk kusan lokaci daya suka yi aure itama yaranta biyu, sai Sajida da shekararta biyu da aure yaronta daya sai kuma Safara'u da bata jima da aure ba bata wuce wata uku, ajinsu daya a makaranta, ƙawancensu ya samo asali tun farkon shigarasu Kasu, wanda a hankali suka zama shakikan aminai ba mai jin kansu, ko da sunyi fada suke shirya kansu kuma gaba dayansu iyayensu suna da rufin asiri shiyasa rayuwarsu ta zo iri guda.
_________
Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. ***
[9/28, 5:29 PM] Rahma Kabir: ZAMANI...
*Riga kowa da irin nashi*
Na
Rahma Kabir mrsMG
Wattpad @rahmakabir
Jazakallah khair da addu'o'inku Allah ya jikan duk kan musulmai yasa sun huta ya kyautata tamu bayan tasu.
Page 6.
Da safe.
Tunda Mahood ya dawo daga masallaci bai koma barci ba ya shiga kitchen ya daura musu abin kari, saboda su walid zadu tafi harda sannan ya san Saudat ba lallai ta girka ba tunda tana fushi da shi, ya hada musu custard ya soya musu irish kana ya soya kwai ya sanya musu a lunchbox dinsu ya dauko sauran ya fito dashi falo ya shiga dakinsu Amir, ya taimaka musu suka shirya sai suka fito suka karya gaba daya sai ya shiga daki yayi wanka shap shap ba bata lokaci ya shirya ya fito cikin shigar manyan kaya ya ajiyewa Saudat kudi dari biyar akan center table sai ya tasa su walid suka wuce makaranta, suna isa ya ajiyesu a ajinsu shi kuma ya wuce ofice dinsa na mudir ya samu a bude an yi shara an gogo komai ya zauna yana duba sa hannun malamai da suka shigo da wuri, minti biyar da zamansa sai ga Malam Muktar ya shigo suka yi musabaha kana ya zauna yana cewa.
Malam yau dai kayi latti ko madam ce bata sallameka da wuri ba.
Mahmood yayi murmushi kana ya muskuta ya soma bawa malam muktar labarin abinda Saudat ke yi masa, amininsa ne shi baya iya boye masa matsalarsa haka shima Muktar din, suna shawara da juna duk abinda ya shafi rayuwarsu, Malam Muktar ya jinjina lamarin yace cikin damuwa.
Mahmood hakuri zaka kara yi da ita insha Allah zata bari, sai dai ni ina ganin anya babu zugan kawaye kuwa dan da ba haka take maka ba.
Ba abin mamaki bane in dasu, domin na kula da kawayen ta na makaranta gogaggu ne, amma ko na kawo mata magana akansu cewa take yi suna da kirki ba suda matsala.
To ina ganin ka kara bata lokaci in kuma taki saika kara aure dan dama bai dace ka zauna da mace daya ba sai kace pastor.
Muktar ya fada yana dariya, Mahood shima dariya yayi.
Kana so ka tado min da wani rikici kenan, nifa wlh Saudat dina ta isheni bana sha'awar kara aure amma ban sani ba ko nan gaba naji ra'ayin karin.
Kana matsayinka na babban Ustaz aiko kari ya zama dole, kai dai kawai yanzu kana tsoron Saudat ne.
Babu zancen tsoro kawai dai ina son matata kuma bana son abinda zai hargitsa mana farin cikinmu.
To Allah ya zaba maka mafi alkhairi, ni bari na leka aji na karawa dalibai karatu.
To masha Allah a fito lafiya.
Cewar Mahmood, sai muktar ya tafi shi kuma ya fara duba wasu takardu.
Saudat tana tashi daga barci ta yi wanka cikin sauri ta shirya saboda tayi latti dan akwai test din da zasuyi a makaranta, ta fito ta duba kicin ta hada tea ta dawo falo ta sha cikin sauri, tana gamawa ta koma ciki ta sanya hijab ta dauko jaka sai ta fito, centre table ta ga dari biyar ta dauka tare da juyata tasan ba haka ya saba ajiye mata ba taja guntun tsaki.
Uban me dari biyar zata yi min? Aiko wlh zanyi amfani da kudina kuma ranta maka nayi sai ka biya ni.
Ta fada cikin fada kamar yana wajen, sai ta fice ta rufe gidan gaba daya ta tari napep ya wuce da ita kamaranta.
Mahmood bai dawo ba sai gabda sallar magrib shida su Walid, ya yi parking mashin ya isa kofar gidan yaji shi a rufe hakan ya bashi tabbacin Saudat bata dawo ba sai ya ciro key dinsa ya bude gidan suka shiga yayi parking mashin dinsa sai suka dauro alwala suka wuce masallaci. Saudat ba itace ta dawo ba sai ana kiran sallan ishai, akan idon Mahmood ta dawo dan lokacin ya fito ya sake yin alwala daga nan ya kira sallah, bata ganshi ba dan haka cikin sauri ta shiga gida tana addu'ar Allah yasa bai dawo da wuri ba dan tasan lokuta da dama in dai tana fushi dashi to yana wucewa gidan Ummansa ne da yaran sai sunci abinci suke dawo wa.
Sai bayan sallar ishai suka dawo ya shiga ya sameta a falo tana cin indomie da lipton, bai ce mata komai ba yaranne suka ruga wajenta suna yi mata oyoyo ta tarbesu cike da murna kana ta mike ta shiga cikin ta sa musu indomie dinsu dan dasu ta dafa, koda ta fito bata ga Mahmood ba ya wuce dakinsa, ta zauna suka ci suka koshi da yaran kana ta sallamesu suka wuce dakin barcinsu kafin nan ta kwashe duk kayan ta kai kicin sai ta fito ta isa dakin Mahmood, ta same shi yana zaune a gefen gado yana duba wani littafin musulunci, ya dago ya kalleta fuska muruketa.
Daga makaranta ina kika biya har kika yi dare haka?
Da muka tashi sai muka wuce sunan wata yar ajinmu, na manta ban sanar da kai ba dama nace inna dawo zan sanar maka.
Saboda kin dauke ni dan iska shiyasa zaki tafi ba tare da izini na ba, ko kin mance duk takun da kika yi mala'iku na tsine miki, gaskiya Saudat kina matukar kure ni na gaji da halin, zan dauki matakin da bazai taba yi miki dadi ba muddun ba zaki sauya ba.
Haba Mahmood meyasa kake maidani karamar yarinya ne, nifa ba yarka bace da zaka yita min fada, karatun nan dai sai da aka yi yarjejeniya dakai kace ka amince zanyi kuma...
kinga ki rufe min baki kafin in bata miki rai, kuna ki fice min daga daki.
Mahmood ya katseta cikin tsawa, Saudat taja tsaki ta wuce kamar guguwa ta rufe masa kofar da karfi tana surutai, Mahmood yayi kwafa yana cewa.
Wlh zanyi maganinki.
A ranar tea kawai ya iya sha ya kwanta duk zuciyarta a dagule da tunanin irin hukuncin da zai yi mata, sai dai wani bangare na zuciyarsa yana jin ba dadi saboda son da yake mata yana nukurkusansa, da ace zata dawo a lokacin ta bashi hakuri tuni zai sauko ya yada makamansa saboda yana cike da tsananin bukatarta. Bangaren Saudat kuwa koran da yayi mata yasa ranta ya baci sosai har take tunanin ya jawa dafa abincinsa na sati, a zuwan da tayi dakin tazo ne dan su shirya akan abinda ya faru jiya, amma kuma yadda yayi mata yqnzu yasa ta kara hawa sosai wanda take son sai ya biyota har daki ya bata hakuri kafin zata saurara masa akan hukuncin data yanke, a ganinta ba ayi namijin da zai jata kasa ba sai dai ita ta jashi domin tasan itace da mulki tunda yana tsananin sonta.
Sai da suka dauki mako guda a zaman doya da manja, Mahmod yayi zaton yanda ya nuna fushinsa Saudat zata sauko ta bashi hakuri sai yaga sabanin haka, ta sakar mishi komai na gidan ko shara ta daina yi shike shirya yara makaranta ya dafa musu abinci ya gyara gidan, dakinta ne kawai bai shiga ya share, kuma bata fasa zuwa makaranta ba sannan dole ya bata kudin transpot, Saudat ko a jikinta gani take wlh dole shine zai sauko ya bata hakuri kuma ba zata yi masa komai na gidan ba in yasha wuya sosai zai nemi sulhu, a irin wannan zaman ne Rahma kanwarsa ta je gidan da safe, akan zata fara koyarwa a makarantar islamiyarsa na safe, saboda malamar aji biyar tana makarantar boko to ba wanda zai rike ajin shine ya yiwa Rahma magana akan tazo yau lahadi suje ya nuna mata yadda tsarin makarantar yake, da yake duk kannensa suna da sanin addini sosai boko ne kadai ba suyi zurfi ba dan a cikinsu Rahma ce kawai ta kammala secondary, Amina da Zainab duk a aji uku suka tsaya. Shigarta falon da sallama sai ta tsaya tana mamaki yadda yayi kaca kaca kamar ba mace a gidan, ta kara yin sallama sai ga Mahmood ya fito daga kichen yana amsa mata, yace cikin fara'a.
Yauwa Rahma nayi farin ciki da zuwanki yanzu, zoki karbe ni wanke wanken nan in samu in gyara dakin sai nayi wanka mu wuce.
Rahma ta kalleshi cike da mamaki tana cewa.
Ita kuma matar gidan tafiya tayi ne tabarka da hidimar gidan?
A'a bata dan jin dadi ne shiyasa nake yi mata ayyuka, karaso mana ciki kin tsaya a kofa.
Saudat dake tsaye a bakin kofa ta kwashe da dariya jin yadda ya zabga karya yana matsayinsa na malami, sai duk suka kai kallonsu gareta Mahmood ya daure fuska yana yi mata nuni da ta koma daki da ido, sarai ta gane me yake nufi amma sai ta nuna masa bai isa ba ta karaso falon ta zauna a kujera tare da daura kafa daya kan daya tana cewa.
Ni lafiyata kalau karka daura min ciwo ina zaman zamana, ni da nake shirin yin birthday dina kana son daura min lalura.
Mamaki ya kara cika Rahma ta saki baki tana kallonsu, Mahmood bai ce komai ba ya juya zuwa dakinsa danya shirya su wuce kawao dan ta riga ta barar masa da gari, tunanin yanda zai batar da tunanin Rahma yake saboda yana gudun taje ta sanar da Umma a halin data ganshi. Rahma ganin ya shiga dakin ta kalleta shekeke rai a matukar bace tace.
Amma kuwa Saudat kinyi asara Ki rasa wanda zaki bautar sai mijinki, lallai ki kara biyan bokanki domin aikinsa yana ci, Allah ya shiryeki.
Ke ke malama baki isa kizo gidana kina gaya min magana ba, kuma ke ce kika yi asara mara mutunci, dan haka fice min da ga gida.
Wannan ne kuma kika yi kadan baki isa ki koreni daga gidan dan uwana ba.
Nan dai suka cigaba da musayar magana sunata cacan baki, Mahmood dake wanka Allah Allah yake ya fito, ko soso bai goga ba sabulu kawai ya yi amfani dashi ya watsa ruwan cikin sauri ya fito ya shirya, a falon ya karasa sanya boturin rigarsa da hula ya daka musu tsawa.
Meye kuke yi hakane? Ya kuke so ku maida min gida wajen yaki, ke Rahma wuce mu tafi ke kuma zan dawo zamu gauraya in kin so ki bar gidan haka karki gyara.
Ya wuce cike da bacin rai Saudat tana binsu da dogon tsari tare da kananun magana, Mahmood ya fita da mashin dinsa, Rahma ta hau bayansa suka wuce ba tare da sun yi magana ba, tunaninsa kawai yasan yadda zai shawo kan rahma dan karta je ta sanar dasu Umma dan yasan da wuya bata fada musu ba tunda dama suna da cikin saudat din, abinda yake gudu kenan kar matsalar gidansa ya shafi yan uwansa, ya rasa wani tunani zaiyi akan matakin da zai dauka ga Saudat duk wanda ya hasasho sai ya ga ba mai billewa bane, a haka suka isa makarantar.
________
HIBBA
Tun daga kofar gate din makarantar ta fara raina kanta domin ganin mutane da yawa maza da mata masu shiga iri daban daban, sai ta kame jikinta tana tafiya tamkar kwai ya fashe mata a ciki, gyalen a kai ta sanya saboda rashin sabo dan gani take yi in ta daura a wuya kamar ita kawai ake kallo, ta kare kankame yabiɗaɗɗen jakar a hammata, a tamfarta yar masaka dameji wacce baba yayi mata da sallah, gata da duhu sai duk ta rainawa shigarta tare da tunanin rayuwa ba zai yuwu mata a haka ba tana bukatar ta sauya tsarin shigarta domin a dama da ita sosai, bayan ta shiga cikin makaranta sai ta tambayi department dinsu, aka sanar mata sai ta wuce direct ta shiga, taga mutane sosai a ciki maza da mata sai kallo ya dawo gunta wanda da yawa sunyi mata kallon matar aure ce ganin gyale a kai ta daura duk da kankantar jikinta, Hibba sai duk taji ta muzanta a ganinta babu mai kaskantaccen shiga irinta a ciki, haka ta ja kafa ta shiga ciki ta samu waje ta zauna, ba jimawa saiga malami ya shigo musu ya gabatar da kansa tare da soma yi musu karatu, bashi ya fita ba sai wajen karfe sha biyu saura sai duk yan ajin suka fita saboda ba su da wani lecture sai karfe daya da rabi, hibba taga sai fita suke ita dai ta gyara zama da tunanin karta fita wani malamin ya shigo yi musu karatu, duk sun fice sai tsiraru ne suka zauna wanda maza sun fi yawa, Hajara ce ta taso harta wuce Hibba ta juyo ta kalleta tana cewa.
Sannu, ke ba zaki fita bane? ba mu da lecture sai nan da karfe daya da rabi zo muje mana mu samu abin da zamu ci.
Hibba mike tare da daukar jakarta suka fice tare, sai da suka isa wajen cin abinci kafin suka yiwa kansu mazauni a wajen, Hajara ta sanya aka kawo musu snacks da drink ta biya kudin, hibba tayi mata godiya hajara ta ce mata.
Amma kamar yau kika fara zuwa ko?
Eh hibba ta bata amsa a takaice.
Ni sunana Hajara Nuhu, ina nan tudun wada, tun last week na fara zuwa. Ga timetable dinmu ki duba ko in anjima za mu je ayi miki copy ki rike a hannu ki kema.
Nagode sosai, ni sunana Hibba Alhasan, ina zaune a unguwar shanu.
Nice to meet you.
Mee too, Allah ya yiwa karatunmu albarka.
Hibba tace tana murmushi, Hajara ta amsa ameen tare da mika mata wayarta iphone 11 data sanya mata number dinta, Hibba ta amsa sai dai bata san yadda zata shiga ta saka ba saboda rashin sanin babban waya, ganewar haka yasa Hajara tace ta bata nata saita saka mata in yaso saita yi mata flashing suyi saving numbobin juna, Hibba sai da taji wani iri a ranta da kunyar bata wayarta domin karamar nokia ce wanda ta yi maneji da robali saboda murfin bai zama, ta dauko a jaka ta mika mata, sai da Hajara ta dago ta kalleta tana mamakin wayar da take rikewa ta kasa rike abin a ranta tace cikin zolaya.
Kina yan mata kina rike irin wannan wayar, haba Hibba ai ko dan karatu kya sauya waya, saboda yin assigment zai miki amfani.
Uhum zan gayawa Baba ya siya min.
Baba kuma? Haba karki ce min ba kida saurayin da zai siya miki waya. Kinga ni wannan wayar tawa saurayina ya siya min ita, ke hatta kudin registration na makaranta shi ya cika min rabi mamata ta ban rabi nazo na biya saboda ni babana ya rasu. Yanzu haka dan yayi tafiya ne amma da ya dawo dan amsa wasu kudi a hannu na dinka sabbin kaya.
Kinji dadi amma ni ko saurayi banda shi, baba yace karatu yake so nayi baya so na soma kula samari sai zuwa nan gaba.
Tafdijam sannu hibba gaskiya ke zubin yan da ce, amma kiyi kokari ki fadawa Baba ya siya miki waya ko da karamar android touch ce ki samu na yin assignment.
Insha Allah nagode da shawara.
Haka suka cigaba da hira Hajara tana bata labarinta tamkar ta jima da Hibba, tana da surutu ba ruwanta da rufi, ita kuwa hibba ta kasa sake jiki saboda ita tana da tsoron sabo da mutane, haka suka kare ciye ciyensu suka bar wajen zuwa masallaci dan yin sallah.
_________
Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. ***