AYI DAI MU GANIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

AYI DAI MU GANI

  • 1views
  • 8chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

I am hafsat chindo sodangi from plateau state nigeria.

More from @hcsodangi12

Sample · Book 1 (Farko)

AYI DAI MU GANIAl'amarin ya taso ne tun daga ziyarar da na kai wa Likita don ya kara jaddada in cikar lafiyata kamar yanda ya saba yi min a can baya. Sai dai a wannan karon maimakon ya yi min hakan cikin yabawa da nuna gamsuwa da cikar lafiyar tawa sai ya shiga yi min wasu tambayoyi masu tsanani da fadar da gaba har yana bani wasu gwaje-gwaje da ban gane dalilin yinsu ba. Karfin hali nayi na danne damuwar dake cikin zuciyata ban bari ya gane tsananin tsoratar da nayi ba na daga ido na kalle shi cikin atsuwa na ce mishi me wannan abin yake nufi Dakta? So kake ka nuna min cewar lafiyar tawa da nake ta tattali tana cikin barazana? Ko kuwa so kake ka fahimtar dani cewar na riga na kamu...." Bai bari na karasa maganar tawa ba ya katse ni ta hanyar cewa, "ba haka nake nufi ba Hajiya, kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki zan yi miki bayanin da zaki gamsu ki kuma dauki komai ya zamo ba komai ba ne. Nima ban tsaya sauraron bayanin nashi ba nasa hannu na dauke jakata dake jingine gefen kujerar da nake zaune, na mike tsaye cikin natsuwa na kalle shi 12                                                                                                   na ce mishi, "mu bar duk wata magana sai bayan na dawo karbar test din da aka yin, Laraba ka ce ai ko?" Ya gyada kai a hankali don tabbatar da hakan a fuskarshi kuwa ya saki murmushi sannan ya ce, "Laraba za ki dawo Hajiya wacce mutanenmu ke yiwa kirari da tabawa ranar samu, ban saurari murmushin Likitan ba don nasan kokari yake yi wai ya kawar dani daga damuwar da ya riga yayi min dalilin fadawa a cikinta.A gida rannan zama nayi cikin kunci da damuwa zuciyata takai matuka wajen kuntata saboda nauyin da tayi, naje ziyara don in kara samun kwanciyar hankali abu yana nema ya zama tamfar allura ce take nema ta tono gainma.Kai kawon da zuciyar tawa take yi shi yai dalilin da na shiga kokarin yin waiwaye wato adon tafiya' kan lamurran nawa don ganin ko zan iya hango wani abin da zai bani haske. Shekaru ashirin baya da suka wuce, shekaru goma ne kacal dani a duniya a wancan loka cin tasowa nayi gaban iyayena biyu wato uwa da uba wadanda suka riga suka manyanta wato shekaru suka yi musu yawa. Ga kuma mas'alar babu, ina kuma da wa mai suna Buhari wanda 13  yake akwai tazarar shekaru har guda bakwai a tsak...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters8
premium7
02

Book 2 (Karshen)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
03

Book 2 (Farko)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
04

Book 2 (Karshen)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
05

Book 3 (Farko)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
06

Book 3 (Karshen)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
07

Book 4 (Farko)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
08

Book 4 (Karshe)

Premium
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play