KUKAN KURCIYA (WA GARI YA WA YA?)Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

KUKAN KURCIYA (WA GARI YA WA YA?)

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Sunana Halima.hz, ni marubuciya ce, kuma ƴar kasuwa mai siyar da nau'in sutturun sawa. Ina rubutu don in rayar da abubuwan da mutane ke ji. Ba na rubutu don nishaɗi kawai, ina rubutu don motsa tunani. Kowanne labarina yana ɗauke da murya...

More from @halimahz

Sample · 1

*KUKAN KURCIYA...!*_FITA NA BIYU(BATCH 2)_*GAMJI WRITERS ASSOCIATION*_{Home of exceptional writer's}_```TAKEN LABARI:-```*WA GARI YA WA YA?*```JIGON LABARI:-```*ABUN AL'AJABI.*```MARUBUCIYA:-```*Halimahz(MissAnyway)**(1)*"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".Kalmar dana ambata kenan ina me saurin dafe bango saboda hajijiyar dake neman ɗibana ta watsar a ƙasa.a lokaci ɗaya jina da ganina suka ɗauke na tsawon daƙiƙu, na ƙara rumtse idanuwana da tartsatsin wuta ke ambaliya a cikin su.ƙafafuna suka min nauyi na kasa ko da motsa su balle na iya ɗaga su na nemi madafar tsayuwa, zuciyata ta matse, ƙirjina ya shiga bugawa tamkar ana buga mandiri, wucewar daƙiƙu biyar ina dafe da bango kafin na samu na dawo hayyacina, zuciyana da bakina ba su fasa maimaita kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba."Nura!". na kira sunan da wani irin amon sauti da ban san ina da shi ba. kuma tunda na ambaci sunan nasa sai na ƙara ƙafewa tamkar gunkin da aka sassaƙa, yawun bakina ya bushe.a wannan lokacin da nake manne da bangon ƙofar gidan mu, a jikin rila, iska ce me sanyi take kaɗawa ta ko'ina, duk mutanen da suke wucewa jikinsu lulluɓe yake da rigunan sanyi suna ƙanƙame jikinsu saboda mashahurin sanyin da ake zubawa a garin, irin sanyin nan da haƙora ke caccakewa da juna, amma ni a lokacin wani uban gumi ne ke keto min na kata'i, wanda lokaci ɗaya ya jiƙa min jiki naji tamkar an watsa min ruwan zafi.idanuwana da basa gani sosai acikin gangamin hazon da ake yi, na kanne su ina bin bayansa da kallo, ina kallon yanda yake takawa yana tafiya yana barin kusa da ni, cikin kaina ina ƙirga kowanne taku na tafiyarsa, yayinda zuciyata ke matsewa tana ƙara cunkushewa da sautin takun tafiyar tasa.sai da ya isa bakin motarsa ya buɗe zai shiga, sannan na samu wani ɗan guntun kuzari a tare da ni, na sulale gwiwoyina suka zube a ƙasa, ƙarar sautin bugun simintin yay duka har cikin dodon kunnena."Nura! ka dakata Nura don Allah". bakina ya motsa da ƙyar wajen faɗin hakan, kuma furucin ya fito tattare da matsanancin sabon kukan da ya kufce min.na dinƙa bin Nura da kallo ta cikin ruwan hawayen da ya taru a idona, kallonsa nake amma wani sabon mutum na daban nake gani a tare da shi, domin asalin Nura dana sani ba zai taɓa iya ruguza zuciyar mace ba, macen ma wacca ta aminta da shi, ta shaƙu da shi, tayi dukkan amanna da shi akan cewar shi ɗin nata ne, kuma ita ɗin tasa ce, macen da suka shafe shekaru biyar suna tsafatatacciyar soyayya, wannan macen da a kullum yake furta cewa kece uwar ƴaƴana, kece mafarkina, macen da baida wani buri da ya wuce yaga ya mallaketa, amma a yau ita yake kallo yake furta mata cewa babu ni babu ke, *ME YA ZAMA SILA WANDA BAN SA NI BA?.*"kiyi haƙuri Mujahida...".furucin nasa ya yanke dukkan tunanina, ya kuma nemi yay raga-raga da zuciyata, nayi saurin ɗaga hann...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play