Free chapter · Read without an account

2

by Halima Zakariyya Haruna · KUKAN KURCIYA (WA GARI YA WA YA?)

*KUKAN KURCIYA...!*

_FITA NA BIYU(BATCH 2)_


*GAMJI WRITERS ASSOCIATION*

_{Home of exceptional writer's}_


```TAKEN LABARI:-```

*WA GARI YA WA YA?*


```JIGON LABARI:-```

*ABUN AL'AJABI.*


```MARUBUCIYA:-```

*Halimahz(MissAnyway)*



*(2)*


"Ya Subhanallah!".

Alhaji Musa da Baba Sabitu suka taso da sauri suka yo kan Mujahida da ta sume a wajen.

Iya ta fita daga parlon cikin tashin hankali taje ta ɗebo ruwa ta kawo, Baban Mujahida dai na zaune kawai ko motsawa daga inda yake bai yi ba, idonsa ma na kallon can wani gefe na daban, shi kaɗai yasan abunda yake ji a zuciyarsa, takaicin abunda matarsa da ƴarsa suka aikata kawai yake yi, ya sn akwai ƙaddara amma a wannan fagen sai dai ya alaƙanta hakan da ganganci, domin da ace ba su kai kansu ba da babu wacca zata tsinci kanta a halin da take ciki.


har tsawon wucewar mintuna 5 kafin nan Mujahida ta farfaɗo.

ina buɗe ido na ƙara fashewa da sabon kuka, nayi kan Ummanta wacca ta riƙe kanta da hannaye duka biyu, banda hawaye masu zafin gaske babu abinda ke suntiri a saman kumatunta, zuciyarta danƙare da baƙin ciki, ƙunci, danasani tare da nadamar abunda take aikatawa a ɓoye, abunda ta ɓoyewa jininta banda mahallacinta da ke kallon duk wani motsinta.


na damƙi kafaɗunta ina yi mata wata iriyar girgiza ina faɗin,"Ummana kiyi magana, idan kika yi shiri su Baba Musa za su yi miki kallon mutuniyar banza, don Allah Umma ki buɗe baki ki faɗawa Baba yayi kuskure, ba kece matar da yake zargi ba, hasalima ke ba ki haifi wani ɗa Auwal ba, kiyi magana Umma ko Baba zai maida igiyar aurenku, Ummana idan kika bar gidan nan ina zamu saka kanmu, ke ɗaya ce gatanmu, ba zamu taɓa samun wacca zata bamu kulawa irin wadda kike bamu ba, don Allah Ummana ki faɗa musu ke ba ce".


maganar Baba ta katse ni da abunda nake faɗa. "ni zancen da nake son sa ni waye Auwal?, a ina kika samo shi?, kuma waye ubansa?...".


bai ƙarasa zancensa ba Ummana tayi saurin tarar numfashinsa,"haba Habibu karka yi min mummunan zato mana".

sai tayi shiru tana saka gefen ɗankali ta goge hawayen fuskarta, sai dai tana gogewa wasu na zubowa.


sai kawai na kifa goshina a saman cinyarta, tausayinta da tausayin kaina suka kamani, duk a girgiza nake, nema nake na ɗimauce, na san wace mahaifiyata, macece ta ƙwarai mace ta gari, su kuwa waɗancan matan da ke rubutun batsa sun fi kama da karuwai, to taya za'ai ace wai Ummana ke rubuta irin wancan rubutun da yay sanadin lalacewar tarbiyata.


cikin dasashshiyar murya nake faɗin,"me yasa Ummana?".


"ba komai yaja min faɗawa wannan musibar ta harkar rubuce-rubucen bariki ba illa don neman ɗaukaka da kuma neman kuɗi. sai dai gashi kashh na aikata abunda har mutuwa ba zan daina zubar da hawaye ba, domin ba kowa na illata ba sai kaina, ni kaina sau tari maza karuwai na kiran wayata su na nemana da yin lalata, wanda in ace ban ɓarar da mutumcina ba da babu wani kwarton namiji da zai kira ni ina matsayin matar aure da sunan zai yi lalata da ni, sai gashi a bayan fage kuma ba tare da sanina ba ƴata na aikata maɗigo, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".


sai kawai tayi shiru ta kasa ƙarasa maganar, kuka sosai take yi, parlon yay tsit hatta ni kaina na daina yin kukan saboda ciwon da zuciyata ke yi min, ba komai nake hangowa ba sai lokacin dana fara karatun littafin batsa, ina tunawa tun ina ɗauke kai daga ina kawar da ido har nazo na kwaɗaitu da son karatun, kuma dana zo na fara sai ya zamar min tamkar yunwar ciki, idan ban karanta ba bana samun natsuwa, duk da nasan abunda nake karantawa ɗin haramun ne, ya ilahi ka yafe min ka yafewa mahaifiyata.


"tabbas a yau nayi danasanin ƙin karɓar gaskiyar da aka jima ana faɗa mana, gaskiya da nasihar da bayin Allah salihai ke ta faɗa mana, sai dai muka toshe kunne muka zauna akan zugar ayarin ƴan abi yarima asha kiɗa, muna rubutawa dan mu lalata aure, mu lalata yaran wasu, namu kuma muna yi musu nasiha akan su guji aikata hakan. sai gashi reshe ya juye da mujiya, na rubuta abu da kaina wanda ko mijina ba zan so ya karanta shi ba balle kuma ƴar dana haifa, na san bamu isa mu yiwa Allah wayo ba sai dai ban taɓa tsammanin sakamakon zai zo min ta haka ba. Yanzu *WA GARI YA WA YA?*, kamila kuma salihar ƴata ta lalace ta sanadin karanta baɗalar da nake rubutawa, an fasa aurenta, ta kamu da ciwo me muni, ni kuma mijin da nake taƙama da shi ya sake ni, Hasbunallahu wani'imal wakil😭😭, ga kuma hukuncin ubangiji da yake jirana domin Allah kaɗai ya san adadin Al'ummar da suka ɓaci, Allah kaɗai yasan adadin da suka yi min Allah ya isa a akan hakan, Allah kaɗai yasan adadin tsinuwar da ke kaina, na shiga uku ni Bilki, Muhajida ki yafe min don Allah da Annabinsa, ba kiyi sa'ar uwa ba Mujahida ki yafe min".


Ummana ta ƙanƙame ni sosai ajikinta, sautin kukan mu kawai ke tashi acikin parlon. muryar Baba da tsananin ɗacin zuciyar da ke ƙara tugunzumarsa ya ɗaga murya yana cewa da Umma,"nace aina kika samo Auwal?".


cikin shashsheƙar kuka muryan Umma na fita da ƙyar take cewa,"Baban Mujahida da kai ɗaya na taɓa haihuwa kasan da wannan, ni kaina Auwal ɗin ban sansa ba, yankarsa nayi na ɗora kawai saboda na ɓoye identity na...".


bata ƙarasa ba Iya tace,"mutuniyar banza da wofi, mayaudariya macuciya, wallahi albasa dai bata yi halin ruwa ba Bilki, kuma babu makawa sai Allah ya sakawa iyayenki domin har suka faɗi suka mutu shaidar kirki ake yi musu akan ingantacciyar tarbiyar da suka yi miki, tarbiya iyaka gwargwado kin sameta, ashe jira kike su faɗi su mutu ki dinƙa saka su kuka a ƙabaruruwan su, kina gefe da ɓoyayyar fuskar shaiɗanu, shaiɗan ya buga miki ganga daɗin kiɗa yasa kina aikata saɓon Allah babu ko kunya babu tsoron ranar da zaki tsaya a gaban mahaliccinki kiyi bayani, wallahi kin yi asarar rayuwa Bilki, daga ke har masu biye miki wajen karatun duk ƴan uwan karuwai ne, don gwara ma ku fito ku faɗawa duniya ne karuwai ne ku".


cike da takaici Baba Sadisu ya ɗora da cewa,"albarka dai an riga an kwasheta kam, domin duk ɗiyar mutunci, wadda tasan mece kunya a musulunci, tasan darajar kanta matsayinta na ƴa mace, ba za ta tsaya irin wannan rubutun banzan ba wallahi. to yanzu da kika yi asarar manyan lokuta na cikin rayuwarki menene ribar da kika tsinta a cikin hakan?, yin sunan banza da wofi ko me?, ai ɗaukakar duk da bata hanyar Allah ba wallahi a banza take, ko musulunci da bai bar koyarwar komai ba bai fito ya bayyana ƙururu yanda ake kwanciyar aure ba, a'a sai ku la'annanun Allah da ba zaku fasa ja mana musiba ba a duniya. sai ku fake da kuna faɗakarwa kuna gyara, a ina faɗakarwar yake aina gyaran yake?, kuna dai neman abokan iskancinku a fakaice, shin baku tuna mutuwa ne?, baku tuna kwanciyar ƙabari?, baku tuna cewa akwai ranar hisabi?, ranar da ayyukan ƙwarai ne kawai za su tsallakar da ku, in kuna tunanin zaku tuba kamin mutuwa shin kuna da notice ɗin ranar mutuwar taku ne a hannu?, kaf duniya babu mahaluƙin da ya san ranar mutuwarsa da lokacin mutuwarsa, ballatana yace zai jirayi wannan lokacin tukunna, na rantse da Allah kuyi saurin tuba, ku tuba tun kamin ƙurewar lokaci...".


Maganar Babana ta katse ta Baba Sadisu. "ai Sadisu ba iyaka su masu rubutun ba kawai har da su masu karantawar. fisabilillahi kana karanta irin wannan saɓon Allah'n taya kuwa zuciya ba zata mutu ba?, taya idanu ba za su mutu ba?, taya gangar jiki ba zata ruɓe ba?, taya ba za'a kamu da munanan ciwuka ba?, ta ya ba za'a daina zinace-zinace da yiwa yara fyaɗe ba?, taya mazaje ba za su dinƙa tunanin kin san wani namiji ba kamin su?,. to ke Mujahida yanzu da kika zauna kika ɓata lokacinki akan karatun wanne irin darasi kika ɗauka dan uwarki?, banda ma yanda zaki lalata kan ki, yanzu ai gashi nan kin jawa kanki bala'i, ciwon ɗoyin farji da sanyin mara da cutar ƙanjamau duk ke ɗaya, kuma baku da zarafin da zaku kira hakan da ƙaddara, ko mene kune ku ka jawa kanku. dama ai masu iya magana sun ce mugunta fitsarin faqo, ga shi nan komai ya ƙare akan ƴarki ai, idan har kuna da rabon shiriya Allah ya shirye ku, in kuwa baku da rabo ubangiji yay mana maganin ire-irenku".


yana gama faɗar hakan ya miƙe ya bar parlon, na bi bayansa da kallo cike da tsananin tausayinsa, domin tafiya yake yi kamar zai kifa ƙasa.


Baba Musa yay gyaran murya bayan yaja gwauron numfashi yace,"kun sani amma kun take sanin!, an tunatar da ku ta hanyar alqur'ani da hadisi amma kun buɗi baki kunce baƙin ciki da hassada ake muku. ya subhanallah, to wallahi summa tallahi Rubutun batsa da Karanta shi da yaɗa shi dukkansu Haramun Ne, duk wanda bai sani ba ya sani, rubutun da yaɗawa da karantawa duka babu abunda suke janyowa sai musiba, saboda Wannan Rubutun Yana Daga Cikin Manyan Zunubai Masu Hatsari ga Rayuwar Mai Aikata su da me watsawa, Domin Abu Ne da Za su Zamo Masa Zunubi Mai Gudana. saboda ko Bayan Mutuwarsa Duk Wanda Ya Karanta Wannan Littafi To Yana da Wani Kaso Na Zunubi Daga Cikin Zunuban da Wanda Ya Karanta Zai Samu. Yin Waɗannan Rubuce Rubuce Suna Daga Cikin Yaɗa Fasadi a Doron Ƙasa, Domin Hanya ce da Zata Haifar da Aukuwar Zina tsakanin Matasa Har ma da Ma'aurata. A Shari'ance Kuma Dukkan Wata Hanya da Zata kai ga Aikata Ɓarna Bin Wannan Hanyar Haramun ne. Sannan Karanta Littafin Shima Haramun Ne Babba, ko da Kuwa tsakanin Ma'aurata Ne, Ballantana Kuma Waɗanda Suke Gwauraye Basu da Inda Za su Huce Sha'awarsu, kamar haka ne kuma Aljanu na iya shafar masu karanta irin wannan rubutun. kuma duk Wanda Yake AZUMIN Farillah Ya Karanta Littafin nan Har Ya Fitar da Maniyyi, To Wajibi ne Akansa Sai Yayi Kaffarar Azumi Sittin Bayan Ya Rama Azumin Wannan Ranar. haka Ubangiji Ya Faɗi a Cikin Littafinsa Cewa: _*“Ka da Ku Kusanci Zina, Lallai Ta Kasance Alfasha Ce, Kuma Abin Ƙyama, Sannan Hanya Ce Mummuna”.*_ Babu Hanya Mafi Saurin Jefa Mutum Cikin Zina Kamar Hanyar da Zata Motsa Sha'awar Mutum, musamman ta hanyar kallon tsiraici ko kuma karanta wani rubutu da yake da alaƙa da hakan, abunda ya kamata ku rubuta kenan wajen nusar da al'umma ba wai ku nuna musu hanyar bin aikata alfasha ba, hatta kuɗin da kuke samu ta hanyar wannan rubutun na rantse da tsarkin mulkin Allah kuɗin haram ne, ba halal ba ne, haram kuke ciwa cikinku, haram kuke sakawa jikinku muddin ku ka saya tufafi da waɗannan kuɗin, shin ba ku tuna musiba da bala'in da ke cikin cin kuɗin haram ne?. ƙalu innalillahi!, Kuma wallahi a shari'an ce wannan ba faɗakarwa bace ta Addinin Musulunci, faɗakarwa ce dai ta sheɗan da tawagarsa, don haka ke Mujahida ki faɗawa sauran ƴan uwanki mata ku Nisanci ire-iren Waɗannan rubutun da Sheɗanun Mutanen da suke rubuta shi, ba abokan hulɗa ba ne, ba mutane bane na gari, ba za su kai ku ko'ina ba sai ga halaka, a masifar rayuwa kawai zasu afka ku, muddin kuna so goben ku tayi kyau to tun wuri ku yiwa kanku karatun tanatsu ku gyara, ku mutu ana yabon ku ana faɗar alkhairin ku yafi ku mutu ana Allah wadarai da ku, yafi ku mutu al'umma na farin ciki da mutuwarku, ga littafai nan da yawa a gari da ake rubuta su masu cike da darasi, kuma ayi amfani da hikima wajen tsoratarwa akan abunda kake aikatawa ba daidai ba. kai kai kai, ban san kuma me zan ƙara cewa ba, wannan dai izina ce ga sauran ƴan'uwanku, ka aikata da kyau kaga da kyau".


yana gama faɗin hakan ya miƙe yana gyara zaman babbar rigarsa ya fice shima ya bar ɗakin. 


Baba Sadisu da Dr Bashir suka mara masa baya, Iya ta miƙe tana karkaɓe zanen jikinta, cikin jimanta al'amarin da ya faru take cewa,"Allah dai ya dubi zuri'armu da ta sauran al'ummar musulmi, ya tsare su ya tsare musu imanin su, ya shiryar da su, ya hane su bibiyar irin waɗannan rubutukan banzan, waya(phone) na da amfani amma kuma ta zamar mana musiba a rayuwar mu... to yanzu *WA GARI YA WA YA?*, Habibu dai ya sake ki, kya sami damar tashi ki bar masa gida, ƴarki da kika lalata kuma gata nan kya nema mata magani, tunda kin san hanyar da zaki lalata ai ba kya rasa sanin hanyar neman maganin gyarawa ba. jama'ar gari kuma kya san me zaki faɗa musu ah tou, idan da kin ɓoye ainihin sunanki saboda kar ayi miki kallon mutuniyar banza, kin yi fuska biyu, kina yaudarar mu da ta ƙwarai, to yanzu kuma ma ga ta yanda za ki ɓoye gaskiyar da bata taɓa ɓuya, don komin daren daɗewa sai ta bayyana kanta wallahi, kuma shawara gare ki gwara ki tuba tun wuri don baki san ranar da mala'ika azara'ilu zai zare miki rai ba".


sannan ta kalle ni ta sake cewa,"ke kuma kaɗan kika gani, ai indai karatun batsa ne ba kiga komai ba sai sanda idanuwanki suka mutu kika daina gani gaba ɗaya, kya nemi ɗan jagora daga nan".


ta kaɗe zane tayi gaba tana cewa,"ubangiji yay mana katangar ƙarfe da irinki Bilki, su kuma yaran mu ya hane su bin irin tawagar ku".


aka barmu daga ni sai Ummana, Amira da Mujtafa suka shigo suna tambayar me ya same mu me ya faru da mu amma duk mun kasa ce musu komai. hankalin su ya tashi suma suka fashe da kukan sosai, Umma ta rungume mu ajikinta kukanta na ta taɓa zuƙatanmu.


Baban mu ya shigo ransa a ɓace, cikin harzuƙa ya dokawa Umma tsawa da cewa,"ina ce na datse igiyar auren ko?, ki tashi ki bar min gida tun ba ki ƙarasa lalata tarbiyan sauran yaran ba, kar na dawo daga masallaci in same ki acikin gidan nan wallahi idan ba haka ba kuma kotu ce zata raba mu".


muna ji muna gani Umma ta miƙe jiki a saɓule, tayi hanyar cikin ɗakinta ko magana ta kasa yi, sai dai shigarta bedroom ba wuya muka jiyo sautin faɗuwa, da gudu muka miƙe muka bita ciki, muna isa muka tarar ta yanke jiki ta faɗi. 


"Mujahida gwara mutuwata da ganin wannan ranar, Mujahida tun daren jiya dana ganki cikin wannan mummunan yanayin nake acikin tashin hankali, dama ance duk abunda ka shuka shi zaka girba, na shiga uku ni Bilki, Ya Allah ka kula min da sauran ƴaƴana, wadda na ɓata kuma ka yaye mata, ka bata lafiya.


ganin yacca take kuka haiƙan, cikin tsananin gigita na fita da gudu ina ƙwalawa Babana kira.



*TAMMAT BIHAMDULILLAH!!! anan na kawo ƙarshen wannan gajeran labari, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min, waɗanda suka karanta Allah ya bamu ikon amfana da darussan da ke cikinsa.*



```ƊAN TSOKACI:-```

*KUKAN KURCIYA JAWABI NE.,* taƙaitattun labarai ne da gamayyar ƙungiyar Marubuta na *GAMJI* za su dinƙa kawo maku a kowanne sati, ranakun litinin zuwa juma'a, anyi shi ne domin faɗakarwa, ilmantarwa, wayar da kan al'umma akan al'amuran rayuwar mu na yau da kullum, daga ƙagaggun labarai zuwa wanda suka faru a gaske amma masu tarin ma'ana, labarin ba wani mai tsawo ba ne, kowanne labari zai zo ne a page biyu kawai daga kowacce marubuciya, tarin darasin da yake ciki kawai muke so a duba a amfana da shi da mu da ku baki ɗaya. zamu yi iyar ƙoƙarinmu wajen ganin mun rubuta abunda ba zai haifar da wata ɓarna ba acikin al'umma sai dai ya kawo gyara insha'Allahu.*


_akwai program group wanda wannan ƙungiya me tashe ta GAMJI WRITER'S ta buɗe domin wayar da kan ƴan'uwa mata, a cikin shirin Mazan ko Matan?, in da ake tattauna manyan batutuwa da suka shafi matsaloli na rayuwar Matan Aure da Ƴan Mata, batu akan fannin lafiya daga gogaggun masana ma'aikatan lafiya, shirin yana zuwa ne duk sati...ga duk me sha'awar shiga wannan group sai yay magana a wannan lamba domin ayi adding nasa, (***) or (***)...ga waɗanda kuma ke son shiga FANS GROUP na novels namu sai kuyi magana a wannan lamba (***) or (***)._


*MUNA MIƘA SAƘON GODIYA, JINJINA DA YABAWA GA DUK WANI MAKARANCIN LITTAFAN MU, ALKHAIRIN ALLAH YA ISA GARE KU A DUK INDA KUKE, HAƊIN KANKU DA GOYAN BAYA SHI MUKE BUƘATA A KO YAUSHE.*


Repost and Comment.


*Halimahz(MissAnyway)*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.