Free chapter · Read without an account

EYOON ƘALBI page 6

by Hajja ce · EYOON ƘALBI

*EYOON ƘALBI.....*



*Page* 6


Washegari zaune Hajja take akan ƴar madediciyar katifarta dake shimfiɗe a ɗakin da take, da alama kuma nan ne ɗakin nata, hannunta riƙe da 40 rabbana na addu’o'i tana karantawa lokaci zuwa lokaci hawaye kan gangaro a saman fuskarta, gaba ɗaya ta rame ta zabge idanuwanta manya sun ƙara girma Tubarkallah, da haka Ummah ta shigo ta sameta, jinjina kai Umman tayi kafin ta janyo ƴar wata kujera agefe ta zauna zuciyarta ɗauke da tausayin tilon ƴartata mace, cikin sanyin murya take cewa. 


“Hajja sana’ar taki kike ne?”


“Uhm...Uhm...Ummah.” Cewar Hajja cikin muryar kuka.


“Bagashi nan ba muryarki ta nuna, haba Hajja! uhm haka zaki zauna kenan kullum cikin damuwa akan abunda ba hakan bane? Ni dai ba haka nasanki ba da Hajja idan nace kiyi abu da sauri zakiyi wani lokacin ma tun kafin nace kingane kinyi koma menene ba kyamin musu, amman yanzu halin nan naki ya canzu sai...” Kafin ummah ta ƙarasa Hajja tayi saurin tareta tana girgiza kai,


“Kiyi haƙuri Ummah na Allah ba zancan su nasa a rai ba, tunda kikace nadena na denayi kawaidai tunani nake Ummah akansu ji inda muka dawo, muna zaman zaman mu a unguwar mu shekara da shekaru sunsa mun taso Ummah, kuma duk akaina ne fa Ummah shi yasa abun yake damuna, amman kiyi haƙuri Insha Allahu bazan sake yi ba...”


“Yawwa ƴa tagari haka nakeso kuma kisani ba akanki bane muka baro waccan unguwar ba, bakiji abunda Abban ku yake ce miki ba kenan jiya? Allah yayi dama can ɗin ba gidan zaman mu bane, kisani har kullum duk abunda yasamu bawa wala kyakkyawa ko mummuna to muqaddari ne daga Allah, saboda haka kedai kiyi hakuri karki ƙara saka komai a cikin zuciyarki, haka kawai ki janyowa kanki wani Ciwon. Kuma kisani komai nisan dare gari zai waye, Hajja Allah zai bayyana mai gaskiya Insha Allah dan bazamu sake tozarta a banza ba, kicigaba da haƙuri da addu'o'in da yayanku ya baki kuma kicigaba dayi kinajina ko?!” Kaɗa kai Hajja tayi tana sake rintsa ido tana cewa. 


“Eh Ummah inayi Insha Allah kuma zan ƙara dagewa..”


“Yawwa Hajja Allah ya yi miki albarka.” Cewar Umman tana ɗaukar mafici. Hajja ta amsa da. 


“Ameen Ummah.”


Da wannan Umma ta zauna ta dinga jan Hajjan da hira har dai ta samu ta rage mata wata damuwar suka shiga hirarrakin duniya. A haka Abba ya shigo ya samesu aka cigaba da hirar dashii da yake Abba irin iyayen nan ne masu janyo ƴaƴan ajiki sosai. Sai da akai kiran sallar la’asar sannan suka tashi Abba yafita masallaci su kuma sukayi tasu a gida. Abba be dawo ba sai bayan an iddar da sallar isha’i ya shigo hannunsa riƙe da leda baƙa ƙarama ya miƙawa Ummah dake zaune gabanta da radio tana jin shirin kowane gauta na freedom radio.

  

“Alhaji sannu da zuwa ka dawo?!”


“Nadawo.. Kina nan kijin shirin naki ne yauma?!”


“Wallahi...” Cewar Ummah yayin da take gyara zaman ɗankwalin kanta. Miƙewa tai ta shiga kitchen ta haɗo masa abincinsa da ruwa ta tsugunna a gabansa ta ajiye.


“Gashi Alhaji..”


“Yawwa Umman Hajja godiya nake Allah ya saka da alkhairi..” Ummah tai murmushi inda sabo ta saba kullum ne takawo abinci ko idan tai masa wani abun tofa maigidan nata wajibi ne seya yi mata addu'a tare da sanya mata alkairi. 


“Mune da godiya Alhaji Allah ya ƙara buɗi.” Ɗan murmushi yai irin nasu na manya sannan ya janyo ƴar ledar gabansa ya miƙa mata. 


“Ah’a ah me muka samu a cikin ledar?!” Cewar Ummah tana ƙoƙarin buɗe ledar. 


“Ɗan tsire ne ba dai yawa gashinan asawa kowa a miya yaci..”


“Angode Alhaji Allah yakara buɗi, mungode kwarai dama bakina kwaɗayi yakeji yanzun zan ɗakko yaji na cinye nawa."


“Toh yayi kyau..” Cewar Abba. Ummah taje ta ɗakko babban tray a kitchen ta shiga rarraba naman kowa ta saka mashi nasshi cikin abinci ta miƙawa Hajja nata ɗaki wadda ke karatun alqur’ani. 


“Laah Ummah da kanki? ai da kirana kikai nazo na karɓa da kaina..”


“Toh na hutassheki ƴar gidan Ummah tashi kici da zafinsa kafin ya huce.” Hajja tace. 


“Tohm Ummah nagode.”


Da haka tabiyo bayan Ummah suka dawo waje, wajen Abbanta ta tsugunna tana masa godiya. 


“Abbah mungode Allah ya ƙara buɗi..” Yace, 


“Ameen Hajja.”


Suna gamaci kowa ya kama gabansa, itama Hajja ta shiga cikin ɗakinta, tunani take gashi sam bata jin daɗin jikinta rabon da taga ƙawarta Atika yau kwanaki uku kenan, tana son ganinta tana son gaya mata damuwarta amma babu dama.


*****

Dare ya koma safiya, safiya ta koma yammaci, yammaci ya koma dare gari yana wayewa ranaku suna daɗa shuɗewa, lallai Allah abun tsoro ne domin shi ɗin mabuwayi ne kuma gagara misali. Gabaki ɗaya rayuwar gidansu Hajja sai daɗa bunƙasa takeyi, tunda suka baro wancen tsallaken suke samun falala da bunƙasar arziki, domin yaya Jazuli ya siyawa su Ummah deep freezer mai kyau da ita, Ummah suka siyo irin ƙananan fararen robobin nan suke yin zoɓon siyarwa me ɗan karen daɗi da sanyi ga kuma pure water me sanyi kuma Alhamdulillah Allah ya sanyawa kasuwancin nasu albarka abun sai daɗa haɓaka yake yi. Successfully Hajja tayi jamb ɗinta ta kumaci inda ta fito da maki ɗari biyu da ashirin(220 marks) kuma dama mass communication cut off marks ɗin 180 sukeso na jami’ar bayero university dake jihar kano. Karatu take yi ba dare babu rana domin samun damar sake tsallake jarabawarta ta biyu wato post utme, kuma Alhamdulillah burinta ya cika ranar asabar da safe ƙarfe goma da rabi suka zana jarabawar a sabuwar sashen makarantar bayeron wato new site.


Sam yanzun gidan su Hajja sunfitar da zancen gidan Alhaji Marwan a cikin ransu na batun cewa Hajja mayya ce, wata irin sabuwar shafin rayuwa suka buɗe mai cike da nasara da annashuwa, kowa ya samo wani abun rabawa ake bashi, kowa ya dogara da kowa a cikin gidan. Haka abun yake ga wajan Hajja domin yanzun ta karatunta kawai takeyi, ta cire komai daga ranta ta tabarwa Allah ya mata sakayya kuma tunda suka zo unguwar ba'a taɓa kawo ƙararta na cewar ta lashe koda kazar unguwar ba. Karatun arabi da boko kuwa sun kulla da Hajja don sam bata sakiya dasu. Yaya Mubarak ne ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi yai sallama kafin ya samu gefan Ummah ya zauna yana tanƙwashe ƙafarsa, Hajja dake gefe ta miƙe tsaye ta ɗakko masa zoɓo takawo masa tana masa sannu da zuwa. 


“Sannu da dawowa yaya Mkay..” Mubarak yace, 


“Yawwa sannu sister..” Ya buɗe murfin robar ya kafa kai yana kwankwaɗa tare da basmala a cikin zuciyarshi, sai da ya shanye tas kafin ya ajiye robar yana murmushi yace,


“Tabbas wannan zoɓon na yau Ummah ce tayi shi dan ko ba’a faɗa min ba naji hakan a cikin bakina.” Hajja ta kyalkyale da dariya, Ummah tai murmushi tana kallonsu kafin tace,


“To yau dai kam kafaɗi ne kawai, don Hajja ce tayi abunta da kanta babu hannuna a ciki.”


“Kai Haba?” Cewar ya Mkay yana dariya. 


“Allah nice nayi ya Mkay, I deserves some accolades ya?.”


“Tabbas kuwa dama nazo da daddaɗan labari, sai Jazuli ya dawo amman zan faɗa kowa yaji.” Daga haka suka shiga wata hirar har Jazuli ya shigo sai da sukaci abinci tukunna sannan Mubarak yai gyaran murya yana cewa. 


“Ina zaune a shago Mail ya shigo na jami’ar bayero kan cewar Hajja ta samu gurbin karatu akan abunda ta cike na karatun jarida sai...”


Ai be gama faɗa ba Hajja tai saurin yin sujjada tana godiya ga Allah, hakama Ummah ta shiga murna sai kuma ga hawayen daɗi ya biyo baya. Mubarak da Jazuli sai murmushi suke fuskokinsu ɗauke da murmushi kowannensu daɗi yakeji na cikar burin tilon ƙanwartasu. Cikin hawayen farin ciki Hajja tafara ummah godia kafin ta juya ga yayyun nata,


“Nagode yaya Jay da Yaya Mkay Allah yabar zumuncin mu da so da kauna, haƙiƙa kun tsaya akaina don nayi karatun nan kuma Insha Allahu rabbi bazan baku kunya ba, zanje na tsaya tsayin daka wajen ganin na cika burina nima..” 


Duk suka yi murna suka yi mata fatan alkairi tare da jin daɗi a cikin rayuwarta. Hakama Abba ya shigo shima aka labarta masa abinda ya faru shima ya sanya albarka har dare zancen ake yi kowannensu da farin cikin abun ya kwana.


*BAYAN WASU SHEKARU....* 


Internship su Hajja sukeyi wanda ita a freedom radio take yin nata, kuma sosai take mai da hankali ganin ta kware, wanda Alhamdulillah har program aka bata takeyi mai taken ‘ƙalubale’ nan freedom ɗin suka yaba da kwazonta suka kuma bata offer na idan tagama makaranta tazo sun bata gurbin aiki a gidan radion tasu. A cikin wannan shekaru jama'ar gidan Alhaji Marwan ɗan kwangila suka koma adamawa can asalinsu, lokacin da mahaifin Hajja yaji labarin tafiyar ba ƙaramin mamaki yayi ba domin lokacin watan su ɗaya da barin unguwar su kuma suka tafi. Yau gashi tsawon shekaru uku basa cikin unguwar. Yau kam yana zaune tare da Malam Ayuba sun fito daga masallaci suka ga motoci sunyi parking a ƙofar gidan. Abban Hajja ya kalli Malam Ayuba yana cizon leɓansa na ƙasa yake cewa.


"Malam Ayuba kaga sun dawo ko? gashi Hajja tana gidan Malam Lado gurin ƙawatar Atika Allah dai ya temake mu karsu fito a yanzu." Malam Ayuba ya jinjina kai yana faɗin. 


"Amin kaga dai tunda suka tafi yarinyar nan take zuwa unguwar nan babu kuma wanda ya taɓa cewa yayi ciwon kai bare ai mata sharri, Allah ya kuma tsare mana ita har ta fito." Alhaji Mustapha yace. 


"Amin." A can ƙasan zuciyarsa kuwa banda harbawar fargabar kar Hajja ta fito babu abinda take yi dan baya san wani abu da zai sake shiga tsakaninsu. Alhaji Marwan suka fito daga cikin motocin, wannan karan suna da yawa maza da mata yara da manya. Lionman ne ya fito daga tasu motar sanye cikin suite dark blue sunyi masa matuƙar kyau, gefen wuyansa kuwa zanan tatoo ne har wajan ƙeyarsa ya ɗauki wata kyakyawar yarinya kamar Hanan ko kuma ita ɗin ce oho dai sabida 3years ba 3days bane ba. Suna ta shiga cikin gidan kawai saigasu Hajja sun fito ita da Atika suna ta dariya da alama hirar tasu ce tayi daɗi har suke irin wannan dariyar. Abbanta dama idanunsa suna kallon ƙofar gidan su Atika yana ganin fitowarsu kawai ya rintsa ido yana addu'a. Ai kuwa kamar jira suna fitowa karaf ta hango jibga-jibgan motoci a waje, bayan lionman kawai ta gani shima bata san ko waye ba kasan cewar ya shiga cikin gidansu, hakan yasa ta koma da gudu cikin gidan su Atika tana faman dafe ƙirjinta hankalinta a tashe ta jingina bayanta jikin bangon zauren gidan zuciyarta cike da rashin jin daɗin dawowar mutanen gidan can.


"Hajja meye hakan?"


Cewar Atika tana kallonta cike da mamakin dawowar da tayi da baya. Shiru kawai Hajjan tayi domin ita kaɗai tasan irin takaicin da takeji sannan ta kamo hannun Atika suka koma cikin gidansu Maman su Atika ta kallesu, bata yi magana ba kasancewar tasan sun saba fita su kuma sake dawowa, suka shiga ɗaki jikin Atika jikin Hajja duk a wani irin sanyaye.


"Hajiya...! Hajiya....!! ƴan gidan ɗankwangila sun dawo wallahi."


Cewar wani yaro ƙanin Atika da suke uba ɗaya ya shigo da gudu yana gayawa mahaifiyarsa dake wajan girki tana sakin ɗanwake. Zama suka yi bakin gado Hajja ta rafka uban tagumi zuciyarta banda bugawa babu abinda take yi, sosai tashin hankali ya bayyana a fuskarta, Atika ta riƙo hannunta cikin tausayawa take cewa. 


"Ƙawata dan Allah ki dena sakawa ranki damuwa, ni nama kasa gane wannan sarƙaƙiyar wallahi, ace duk bakwa kama gidan uban kowa sai gidan ɗankwangila? Wannan abun da mamaki wallahi, shi kuma wancan lionman ɗin ɗan iska kawai izgilancinsa yayi yawa, dan koda ace kin tabbata ke ɗin mayya c...." Cikin sauri Hajja ta toshewa Atika baki tana girgiza kai tace.


"Karki ƙaryata su Atika domin basa yin ƙwansu sai da zakara, babu ta yadda za'ayi ace ni ba mayya bace idan kika duba da yadda idan na tsallake mutum yake tashi lafiya lau. Atika wallahi bana jin ɗanɗanon komai a cikin zuciyata, Atika idan aljanune zan sani domin zan gane idan na farfaɗo naga mutane a kaina, sai dai amma basu bane Atika duk cin mutuncin da za'ayi ina ji kuma ina cikin hankalina ake yi minshi, shin meke faruwa dani?"


"Ki dena damuwa Hajja insha Allahu hakan ba zata sake faruwa dake ba, kisa aranki abinda ya faru a baya ma kaddara ce kawai, amma yanzu babu abinda zai sake faruwa dake makamancin abinda ya faru a baya shekaru uku kenan." Hajja jiki a sanyaye take cewa. 


"Amin Atika, amin amma dole zan ɗauke ƙafata daga shigowa cikin unguwar nan saboda kare mutuncina da samarwa kaina lafiya, sai dai ke ki dinga zuwa can gidan mu idan ranar banida aiki."


Kaɗa kai Atika tayi alamar toh sannan ta miƙe dan ɗakko kayan saƙarta tana yi suna hira har aka yi magrib suka yi sallah, suna idarwa aka aiko yaro ana ƙiran Hajja a ƙofar gida, tana fita taga Abbanta ne yace taje ta fito su tafi gida dama jira yayi duhu yayi sannan yasa ta fito da yaga sunyi dabarar komawa cikin gidan ɗazu.


Har zaure Atika ta rakota suka gaisa da Abban Hajja sannan ta koma ciki ita kuma ta hau bayan mashin ɗin Abbanta suka tafi gida. Saboda karewa kai mutunci da kuma ƙima kota ƙofar gidan su lion basu biba suka tafi ta baya kawai dan su tsira da mutuncin kansu. Suna komawa gida Abba ya sanar da Umman Hajja maganar dawowar su Alhaji ɗankwangila da iyalinsa, ya zauna yana kallon matar tasa tare da faɗin.


"Sun dawo gari wannan karan suna da ɗan yawa bana son fitina kinga dai tun tafiyar bayin Allah nan babu abinda muka sakeji, sannan duk zuwan da Hajja keyi unguwar ba'a sake samun matsala ba, dan haka hanyar lafiya sai a bita da shekara kar Hajja ta sake zuwa unguwar can." Cike da tsoro Umma ke faɗin. 


"Tab aikuwa ta dena zuwa wallahi, ke Hajja karki sake kallon kada gate ɗin gidan bare suyi miki wani sharrin, ni wallahi ina mamakin ace wannan abun baya faruwa akan kowa sai da ƴan gidan kawai, ban sani ba kodan su kyawawa ne tunda ance dama sunfi kama kyawawa alhaji?"


Abban Hajja ya kalli matar tashi cikin takaici sannan ya miƙe tsaye yana gyara zaman hularsa yace,


"Kinjiki dan Allah da wata maganar banza, duk garin nan babu kyawawa sai su? Ko Hajja bata shiga mutane kyawawa sai taga ƴan gidan? Kima dena wannan maganar sam ba haka bane ba wallahi, Allah ne kaɗai masani kuma munanan muna addu'a Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take."


Cikin ɗaki ya shiga yayin da Hajja taje tana shirin kayan tafiya gurin aikinta na gobe kasancewar program ɗin da zatayi na safe ne shi yasa tun dare take harhaɗa komai dan karta manta da wani abun me muhim man ci. Da wuri take tafiya dama wajan ƙarfe shida me napep ɗinta zai zo su tafi wanda duk wata take biyansa idan lokacin tashinta yayi wato ƙarfe ɗaya zaije ya ɗauketa ya dawo da ita gida hankalinta a kwance....





*HAJJA CE* 👈

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol