SON ZUCIYAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

SON ZUCIYA

  • 1views
  • 20chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Marubuci ba makaryaci ba ne

More from @maryamlitee

Sample · Chapter 1

*SON ZUCIYA*NO.1MARYAM LITEEIna farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsira da aminci su tabbata bisa shugaban mu mai ceton mu manzon tsira Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam. Godiya ga Allahu subhanahu wata'ala da ya raya ni har zuwa yau ya ba ni iko da basira na fara wannan labari ina rokon Allah ya sa yadda na fara lfy ya ba ni ikon gamawa lfy.Godiya mara adadi gare ku masoya masu bibiyar rubutuna da yabawa.na gode na gode na gode.*Mu tsunduma cikin labarin Zahra da Raliya har da Hadiza masoya, kun san wani abu za ku sha labari* Kawaye uku da ke tafiya a gefen titi cikin shigar uniform na makarantar islamiyya, riga da *** da hijab ta karshe daga hagu ta taba ta tsakiya sai ta dube ta dan manuninta ta daga ta nuna mata can hannun idanuwanta kuwa suka yi kyakkyawan gani, mahaifinta ne zaune a teburin mai shayi bayan kofin tea da ke gaban shi da sunkumemen bread akwai soyayyar Indomie da aka cakude ta da kwai.Wadda ta nuna matan ta kwashe da wata irin dariya abin da ya ja hankalin ta karshen daga dama ta ce "Dariyar me kike Raliya? Sai da ta kara dariyar sannan ita ma ta nuna mata, ita da ta gani maimakon dariya daure fuskarta ta yi "Haba Raliya meye haka? "To me na yi? Ke fa Zahra akwai son mayar da kurji ya zama gyambo. Kuma ni sunana Rali ba Raliya ba. Ta kare fadi tana kada ido.Wadda aka kira Zahra ta kara tamke fuska "Ba dai kyau haka.Hadiza da fuskarta ta cika da rauni ba ta ce komai ba suka ci gaba da tafiya sai dai suna zuwa kofar gidan su Hadiza da shi ne farko kana shiga layin ta ja tunga tana musu sallama, Zahra ta ce "Amma ba gidanmu kuka ce za ku ba ku kalli maimaicin shirin kwana casa'in daga hadarin da ya sa aka taso mu da wuri ya baje? Ta girgiza kai tana zare hannunta cikin na Zahra "Za ni gida na bar Inna tana ciwon kai."Suka wuce ta shiga gidan na su gidan haya ne, irin gidan yawan nan ne dakuna bila adadin don mata goma sha biyar ne cif. Ta tsallake wawukekiyar kwatar da ta raba tsakar gidan ta isa dakin su da ke can karshen gidan, Innarta na tsugune a kofar dakinta tana dirzar kayan jama'a da aka kawo mata wankau. "Sannu Inna har kin ji sauki kike wanki? Ta daga kai tana ma yar ta ta wani busashshen murmushi "Na ji sauki Hadiza." "To kin sha magani? Ta girgiza kai "Zan sha idan na kammala." Cike da tausayi ta cusa kai dakin nasu da ba su mallaki komai ba sai shinfidun kwanciyarsu gami da yan tsummokaran sawar su ita da yan'uwanta.Tana sauke mayafinta ta tsinkayi sallamar babbar yayarsu da ke fita tallar abinci za a iya cewa ma ita ta dauke nauyin cin su da shan su da tallar da take, sai wankau din da mahaifiyarsu take . Ta shigo dakin suka dubi juna da Hadizata ce "Kin dawo Yaya SA'a? Ta daga mata kai tana neman wurin zama da daidai sauran kannensu su uku suka fara sh...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters20
premium17
03

Chapter 3

Premium
Updated 7 months agoAvailable now
04

Chapter 4

Premium
Updated 7 months agoAvailable now
05

Chapter 5

Premium
Updated 7 months agoAvailable now
06

Chapter 6

Premium
Updated 7 months agoAvailable now
07

Chapter 7

Premium
Updated 7 months agoAvailable now
08

Chapter 8

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
09

Chapter 9

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
10

Chapter 10

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
11

chapter 11

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
12

Chapter 12

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
13

Chapter 13

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
14

Chapter 14

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
16

Chapter 16

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
17

Book 2 chapter 16

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
18

Chapter 18

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
19

Chapter 19

Premium
Updated 3 years agoAvailable now
20

Chapter 20

Premium
Updated 3 years agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play