Free chapter · Read without an account
Chapter 15
Hadiza na ta shirin makaranta Mahaifiyarsu ta shigo dakin da murmushi ta tare ta tana mata barka da dawowa, sai da ta zauna Hadiza ke tambayarta ya suka yi da Baba Rabi'u Yayan Babansu ne da innarsu ta lura Habu zai gagare ta shi ne ta yanke ta kai mashi shi ta roƙe shi ya kula mata da tarbiyyarsa.
Cikin murmushi Innar ta ce "Ya karɓe shi Hadiza ya kuma yi alƙawarin zai tsaya iyakar iyawarsa kan Habu."
Hadiza ta ce "Alhamdulillahi, Allah ka dube mu don isar ka ka taro mana Habu."
Innar ta ce "Amin. Hadiza ta yi mata sallama da fadi mata daga can za ta wuce gidan Sa'a.
Ta fita gidan.
Ana tashi kuma ta hau mota zuwa gidan Sa'a, tana zama Sa'ar ta tare ta da zancen ƙanen wata da suke abin arziƙi ya ga Hadizar yana so, kuma mutum ne nagari ta yi ta cusa mata ta hakura da Sagir da ya kammala karatu ba aiki, ta auri Abdul basiru mutum mai nagarta da abin yi.
Hadiza ta ji ta ne kawai har ta tafi gida. Sai dai komawar ta Abdul basirun ya zo ya kuma samu babansu ganin shi cikin rufin asiri ya karɓi maganarsa.
Sa'a kuma ta tsaya kai da fata wurin shawo kan Hadiza ta amince da auren Abdul basiru har aka sanya rana, Hadiza ta amince ba don tana son shi ba sai don ganin family ɗinsa suna karatu matan yayunsa duk karatun suke ita ɗin ma ya ce karatu sai idan ita ta ce ta gaji.
Hakan ya sa ta ji idan ta aure shi burin ta zai cika. .
Sa'a ta tsaya kamar yadda ta saba aka yi ma Hadiza komai sai katifa da Babansu ya saya ita ɗin ma bashi ya ciyo a wurin wata dillaliya a cikin gidan nasu.
Aka sha biki aka miƙa amarya ɗakinta da ke ƙofar Marusa Zarah ce babbar ƙawa ita har yanzu ba tsayayye tun suna zuwa da an tsegunta masu ita din Sikla ce daga bakin yan unguwa sai su arce yanzu ma shiru ba mai zuwa sai karatun da ta dage tana yi.
****************
Ƙarfe uku da rabi kamar yadda ta saba tashi ta yi ibada ta tashi.
Cikin sanɗa ta sauka gadon don kar ta tashe shi sai ta ga idonsa biyu cikin mamaki ta ce
"Alh lafiya? Ya ce ciwon kai ne ya matsa mashi ta fita ta samo magani ta kawo mishi sai ta fita ta koma la ɗaura alwala ta hau sallayarta ta nace a cikin sujjadarta da karshen tahiya tana roƙon Allah ya tsare mata yaranta har ma da na abokiyar zamanta da ta fita ta bar mata tun suna yara sanadiyyar bin Alh da ta yi Hotel ta kama shi da mace.
Tun yaran suna ƙanana ga shi yanzu sun zama Yammata.
Ita ma tana zama ne saboda yaranta su huɗu ne: Hindu ce babba sai Salma mai bi mata sai Faruq, Musty ne karami.
Amaryarta na ta mata ne su biyu Amina da Intisar da suke ce ma Imtee.
Hankalinta ya tashi da yarta Salma ta fara bauɗewa daga tarbiyyar da take tsaye kan ba su, ta kama ta tana kallon film na tsiraici ta kama ta tana karanta labaran batsa. Sai da ta fara fita ba da sanin ta ba ta yi kokarin tsare ta a gida ta kuma hura ma uban wuta sai ya aurar da Salma a lokacin tana shekarar farko a jami'a, ya so ya ƙi ta faɗa mishi abin da Salma ke aikatawa, ba don ya so ba ya amince da mutumin da Salmar ta kawo malamin jami'a.
Aka yi aurenta Hindu na shekarar karatunta ta uku ita din nutsattsiya ce hakan ya sa hankalin uwar yake kwance a kanta sai dai addu'a da take yi musu.
Ta kammala karatu tuni har ta samu aiki bisa kokarin mahaifinta mijin aure bai zo ba tun dai waɗanda suka yi ta zuwa tana tashen budurci, yanzu ko sun zo ba maganar aure sai ta ya za a yi a shaƙata.
Mahaifiyarta tana mata addu'a Allah ya haɗa ta da na kirki ya kuma kare ta da aikata saɓo.
Ta daɗe cikin ƙanƙan da kai gaban mahaliccinta har aka fara sallah ta miƙe ta fita ta tayar da yaranta sai ta dawo ta yi ta ta sallar nan yaran suka zo suka gaishe ta suka yi azkar tare masu matsalar karatu ta koya mishi sai da ta sallame su ta kira Hindu, cikin farin-ciki hindu da ke duban Ado yana bude idonsa ta ce ya farka Mommy.
Ado ya zura wa kyakkyawar matashiyar ido yana tunanin inda ya santa ta ƙara matsowa gabansa "Ya jikinka? Bai amsa ba sai ƙoƙarin rufe idanunsa da ya yi ya koma barci.
Amadi bai shigo daga masallaci ba hakan ya sa ta fita neman likitan da ya kwana tana waiwayen shi.
Kwana uku Hindu da Amadi suka kwashe suna kula da Amadi tare da taimakon mahaifiyarta yana farkawa ya yi ta kallon mutane amma ba ya magana.
An yi hoton ƙwaƙwalwa lafiya lau take, likitan da ke kula da shi ya ce kar su damu zai yi magana duk wani abu da ya kama sai an taimaka mishi Amadi da ma'aikatan su maza ke mishi ko masu aikin gidan su Hindu.
Sai da ya fara magana Amadi ya kira Baffan Ado ya faɗa mishi a ranar suka yo mota guda.
Gaban gadon suka tsaya suka zuba mishi ido ganin yadda Allah ya mayar da shi duk da ya fara samun sauki.
A hankali yake magana yana nuna Hindu yana faɗin su yi mata godiya ita ke ɗawainiya da shi ita da Amadi.
Da suka juyo kanta sai ta noƙe kanta ta ce a yi hakuri ita ta kaɗe shi. Suka ce haka Allah ya ƙaddara suka yi mata godiya ta nemi su Arɗo su je gidansu su kwana suka ce yau za su koma garinsu Tudun Fulani.
Sai la'asar suka bar asibitin bayan sun bar yaron Arɗo matashi su biyun ke kula da shi yayin da Hindu ke tsaye ita ma da duk wata ɗawainiya ta magani da abinci karayar hannunsa ta kusa warkewa ta kafaɗarsa ce ta sanya suka yi ta zaman asibitin.
***********
Sai da suka shafe kwanaki arba'in da biyar aka sallame shi bayan sun tattara kayansu direban su Hindu ya kwashe komai ya sanya a mota Hindu cikin aiki take ta bi su har wurin motar kamar za ta yi kuka tana roƙon Ado a kai su gidansu sai gobe ba ta da aiki ta yi mishi rakiya har gida.
Ya ce ta yi haƙuri ga waya za su dinga gaisawa kuma duk san da ya shigo birnin Kano zai neme ta su gaisa.
Suka shiga mota bayan shi da Amadi sun ƙara godiya a gare ta, tsaye take shiru har suka shiga motar, direban ya ja sai da suka fita asibitin ta koma.
Sun isa rigarsu karfe sha biyu na rana tuni Baffan Ado ya sanya an gyara mishi ɗakinsa dakin katifa ce da Adon ya saya an share tsakar ɗakin tas kwanciya kawai ya yi ya juya baya.
Jama'ar gidan na ta shigowa suna kara gaishe shi duk da da yawan su sun je asibiti, ana ta shigo da abinci daga kowane sasa.
Amadi ya ce bari ya je gidansu ya huta kwana biyu kawai suka yi ya zo wurin Ado ya shaida mishi zai koma birnin Kano, akwai wani dan garinsu mazaunin Kano da suka yi magana zai dawo dakinsu da zama ya nemi sana'a don shi ma ya yanke barin Alh daga abin da ya aikata ma Ado.
Ado ya yi mishi fatan alheri suka fita yana taka mishi ya dubi Ado "Shi kenan yanzu Ado ka kafe ba za ka koma Kano ba mun saba rayuwar birni ina za ka iya cimar ƙauye?
Ya runtse ido ya buɗe abin da Raliya ta yi mishi na mashi ɗaci a rai "Ba zan koma ba Amadi, zan zauna a gida in rungumi noma, ban ga ribar da na samu a zaman bariki ba."
"Ka yi hakuri Ado."
Ya faɗi yana jin kunya na mashi lulluɓi don kansa yake ɗora ma laifin ƙaƙaba Raliya a rayuwar Ado, duk da yana ce mashi abin muƙaddari ne haka Allah ya rubuta mishi.
Sun yi nisa ya ce "Ka koma Ado ba ƙarasa warwarewa ka yi ba. Suka tsaya suka ƙara tattaunawa Amadi ya yi gaba da kakar kayansa shi kuma ya koma.
Ranar Lahadi da ta kama kwanan Ado biyar da dawowa saboda gajiya da yake da kwanciya yana bin yaran gidan zuwa gona ba komai yake ba sai zagayawa cikin shukoki da shanu masu kiwo.
Yau ma yana cikin Shanu ga garin an kwana zubar da ruwan sama ko'ina ya yi lub-lub da korayen ciyayi da shukoki yanayin wurin ya sa zuciyarsa yin sanyi kallon ko'ina yake cikin shauƙi.
"Yaya Ado an zo wajen ka."
Muryar wata yar budurwa ɗiyar Baffansa ta faɗi tana tsallakowa inda yake ya dubi inda ta biyo sai Hindu ya hango tana yi masa murmushi
Ya ce "Lale ku ƙaraso mana."
Ta noƙe kafaɗa tana nuna mashi Shanu murmushi ya yi ya tsallako inda take yana mata barka da zuwa.
"Ku zo mu je gida."
Ya faɗi yana kama hanya ta girgiza kai "Yanayin nan ya yi daɗi, mu zauna ƙasan bishiyar can."
Suka ƙarasa yana tambayar Imtee da suka zo tare Mommy.
Hira da zaman su suka shiga yi saboda zaman su asibiti ba ƙaramin sabo suka yi ba.
Ta ce: Me ya sa ka dage ba za ka koma Kano ba?
Ya girgiza kai "Na bar Kano, zan ci gaba da zama rigarmu ina noma da kiwo kamar yadda muka gada."
Ta jinjina kai " Na rasa me aka yi maka mai zafi haka a Kanon.".
Ya busa iska ya furzar "Kamar yadda na taɓa faɗa miki al'amari ne ya ratsa kan aure na yi abin da sakamakon da ya zo da shi shi ne sanadin da zaman Kano ya fita a raina."
"Ni dai ina biko ka yi haƙuri ka koma ni ina ganin da zama a ruga gara ka koma can ka kafa naka kasuwancin, saɓanin baya da ka ce mini kana tsaron shago kake yi."
Ya yi ɗan shiru daga bisani ya ce " Na gode da kulawarki a kaina, ina Mommy fa? Tana gaishe ka saƙonta ma na mota da ta ce a kawo maka."
Ya ce "Ina godiya. Ya miƙe "Mu je gida hakanan."
Ta tashi suka jera Imtee na biye da su a baya.
A dakin uwargidan Arɗo Baffan Ado kenan suka yada zango aka kawo masu hura da Nono ga kindirmo daban.
Hindu ce ta sha ita Imtee cewa ta yi ba ta iya sha ba.
Sai kusan La'asar suka tashi tafiya Ado ya sa aka ɗebo musu ƙwan zabbi aka ba su man Shanu, su kuma suka bude Boot aka yi ta ciro da sayayyar da ta yo ma Ado.
Kamar wasa sai zuwa Ruga ya zama jiki wurin Hindu sun shaƙu da Ado wata irin shaƙuwa kuma kullum ta zo ba ta gajiya da ba shi shawarar ya koma Kano ya kama kasuwanci tun yana jin ta har abin ya fara shiga kansa da ita ya yi shawara yadda zai ɓullo ma abin don ya nuna mata amfanin gonarsa da filin da ya saya a Kano sai Shanu da ake masa kiwo yana da su sun kai sha biyar.
A hankali ta shawo kansa ya amince ya samu Baffa da zancen ya ce Ba laifi.
Hadiza na shan amarci cikin kwanciyar hankali mijinta na kula da ita da komai ta cika da ɓacin rai a ranar da ta samu labarin Babansu ya ƙi cika kuɗin katifar da ya saya daga dillaliyar nan har ma cikin gidan ana zuga matar ta zo ta ɗauke katifar, Hadizar ta ba da cikon kudin gudun kar a zo a yi mata tozarci.
Cikin matuƙar ɓacin rai ta ce ta zo ta ɗauke a wulaƙanta ta ba za ta bayar ba daga shi dai har abada bai da abin yi sai wanda zai tozarta su.
Ƙarshe dai Sa'a da ta ji ta aiko da cikon kudin a ka ba matar.
Ƙalubale na farko da Hadiza ta fara fuskanta da ta bijiro da son komawa karatu ya ja ya tsaya kan bai san wannan batu ba sun kai ruwa rana ta ga ba nasara sai ta hakura ta ce za ta koma islamiya sai ɗinki da take zuwa koyo wurin matar kawunsa da take son ta Ibtida'iyya ta koma ta ci gaba da karatunta.
Zahra ma na ci gaba da karatunta Allah ya taimake ta ciwon ya lafa mata har ta ƙare shekarar farko ta kuma haye ba ta samu carry over ba har ta kammala diploma.
A wannan halin Faisal ya diro ƙasar ya kuma dawo gare ta yana kan bakansa sai ya aure ta.
Da yake yana da girman jiki ya yi girman da ba za ka matso da shi kusa da ita ba, ta ɗan saki jiki da shi saboda ita ma zuwa yanzu tana so ta yi auren, don Sakina da Murja tun suna shekarar farko aka yi musu aure, ga Hadiza ta tafi ita ma.
Kullum suka keɓe yana faɗa mata da zarar ya samu aiki kuɗi zai fara tarawa indai ana warkewa daga cutar ta ta ta amosanin jini zai nemo mata maganin.
Ba zato daga Zarah sai ga aiken kudin aure daga gidansu Faisal, ta sakankance har ya samu aiki gwaji iyayenta suka tura su yi aka kuma samu grp din jininsa AA ne shi da Zarah sun yi murna don in AS ne ba halin aure saboda za su haifi Sikla, kuma ko ita ba ta ma abin da za ta haifa fatan ya zo a Sikla.
An kawo sadaki har an sanya rana lokaci na ta ƙaratowa
15