Free chapter · Read without an account
Trailer
by Ayusher Muhd · BAQEER
“Baqeer! Baqeer! Baqeer” Kalaman da kunnuwansa kawai suke juyo wa kenan, a hankali wasu hawaye suka gangaro gefen fuskarshi, shi kenan yanzu ƙafafunshi sun tafi? Shi kenan haka zai karashi rayuwarsa a keken guragun? Runtse ido yayi babu abinda yake gani sai babban amininshi tsaye gefen matar da yake shirin aura kafin wannan ibtila’in ya faɗa mishi, gasu nan tsaye suna murmushin soyayya. Shikenan shi yanzu komai nashi ya ruguje? Sake maida idon yayi ya rufe, me zai kuma gani? Ƴan uwanshi ya gani da matan mahaifinshi suna kallonshi suna yi mishi dariya “Yau ina son da aka daɗe ana nuna maka Baqeer? Ina bambanta ka da aka daɗe ana yi?”
Wani zazzafan kwalla ce suka sake zubo mai, yayinda ya sake maida idanunshi ya rufe, tsaye ya hangota cikin idanuwanshi tana sakar mishi wani ƙayataccen murmushi wanda ya sagar da duk wata gaɓa dake jikinshi.
“Baqer! Kada ka kuskura zuciyarka ta mutu dan ka zama gurgu, shin baza kayi farin ciki da Allah ya barka da rai ba? Ina waɗanda Allah ya jarabce su da makanta? Ina waɗanda Allah ya jarabce su da ciwon hauka? Ina waɗanda Allah ya jarabce su da ciwon da a haka zasu mutu a kwance basu san inda kansu yake ba? Ko ka manta yarda da kaddara na cikin shika-shikan imani?” Yadda ta sa hannu ta rungumeshi ne yasa yaji wani irin sanyi a cikin ranshi.
Tabbas ba zai bari nakasar gurguntaka ta illata rayuwarshi ba, dole ne ya amshi ƙaddararshi ya nunawa mutane a hakan ma zai iya rayuwa. Yana kokarin maida rungumar da tayi mishi yaji an ja keken guragunshi ta baya…….
Hmmm ai wanda bai karanta ba dole a barshi a baya, Baqeer labari ne dake tattare da ilimin rayuwa, kaddara, ganganci, talauci, rashin ilimi, soyayya, siyasa, cin amana, ranar nadama, yan ubanci da sauransu, kada ki bari a wuceki gun share hawayen tausayi, murmushin kauna da kuma ƙaƙƙarfar alaƙar so wadda aka ginata cikin tsafta.
Ku dai ku biyo alƙalamin tagwayen marubuta Umm Asgar da kuma Ayusher Muhd don kada ayi wannan tafiyar babu ku...
SABON LITTAFIN MU KENAN DA ZAI FARA ZUWAN MUKU 20TH NOVEMBER INSHAA ALLAH NAIRA 500 NE KACAL GA MASU SON BIYA SAI KU TURA TA WANNAN NUMBAR 0020428430 ishaq a fatima GT bank. Aika shaidar biya ta daya daga cikin numbobin nan
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
KATIN MTN Ta👇
***
Shaidar biya