FreeArewaPen original
Sune Silar Ƙaddara Ta
- 1views
- 6chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
الحمد الله While others talk, I write… turning feelings into words and silence into stories 🖤 because my pen never lies ✍️ and my mind is full of stories waiting for the right moment to be told 🔥
Sample · 001
✦ 𝗦𝗨𝗡𝗘 𝗦𝗜𝗟𝗔𝗥 𝗞𝗔𝗗𝗗𝗔𝗥𝗔 𝗧𝗔 ✦𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷𝐌𝐈𝐊𝐈𝐘𝐀 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎𝐂𝐈𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍بسم الله الرحمن الرحيمPαιԃ BσσƙAlhamdulillah Allah ya nufa mun dawo, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya ƙara bani ikon dawo muku da sabon littafi Mai suna *Su ne Silar Ƙaddara Ta* Wannan labarin wani bangaren ya faru a gaske.𝚃𝚂𝙾𝙺𝙰𝙲𝙸Littafin ya kunshi abubuwa da dama a ciki sha ciki akwai:Shaye-shaye, illar bin malaman tsubbu/boka, zazzafar ƙiyayya, Haɗi da tsaftacciyar kauna. Akwai darasi mai zafi a cikin. Karku bari ayi tafiyar nan babu ko balle a baku labari.🤞Fateyzahraah ce👯Allah yasa sakon da nake son isar wa yaje. Allah yasa mu gama da duniya Lafiya. Allah yasa yadda na fara Lafiya in gama lafiya.#War#lovestory𝑮𝑨𝑹𝑮𝑨𝑫𝑰Ban yadda wani ko wata su juya min littafin ta kowacce siga ba, ba tare da izini na ba.Book 1𝑷𝒂𝒈𝒆 1_5--KADUNA STATE, NIGERIA.Around 2:00Am Matashiyar budurwa ce tafe a cikin jeji da tsakiyar daren waige-waige take yi ji tayi kamar abu na bin ta juya wa tayi dan dubawa MACIJI ta gani biye da ita a razane ta juya ta nufi baya ta fara gudu. Gudu take yi sosai a cikin dajin juyo wa tayi ta kalli bayan ta har yanzu macijin na biye da ita a bayan ta, cigaba tayi da gudun, tafiya mai nisa tayi har bata iya ƙiyastawa adadin ta tuntuɓe tayi da wani abu ta faɗi ƙasa a kiɗime ta juyo tana kallon baya macijin ne ya taho inda take gadan-gadan yana Matsowa kusa da ita baya ta fara Matsawa a kiɗime sai ihu take tana kuruwar neman taimako ji tayi ta jingina da abu juyawa tayi taga menene Bishiya ce tayi karo da ita ihun ta cigaba da yi tana neman taimako ba kowa haka macijin ya cimmata tana ihu da kururuwa tare da matsawa ko zata iya wuce wa kan fuskar ta ya nufa bai tsaya a ko ina ba sai idon ta a take ya cire mata ido guda ɗaya wani gigitaccen ihu ta ƙara saki kamar zata cika garin da ƙara..... A firgice ta farka daga nannauyan baccin da take tana ƙara taɓa fuskarta tayi tana shafo idon ta, gani tayi yana nan. ajiyar zuciya ta sauke "Ashe mafarki nake" ta faɗa a zuciyar ta gefen ta ta kalla budurwa ce kwance tana baccin ta bata san inda take ba. A hankali ta tashi daga inda take ta fice daga ɗakin... ᴡᴀsʜᴇɢᴀʀɪ Kyakkyawar Matashiyar Budurwa ce zaune a bakin gado baƙa ce ba can sosai ba tana da cikakkiyar fuska shiryawa take yi a gaggauce daga gani kasan fita zata yi a ƙalla zata kai shekara talatin zuwa da biyar a duniya. Turo kofar ɗakin akayi ɗagowa tayi da dara-daran idanunta ta kalli mai shigowar wata budurwa ce ta shigo a ƙalla zata kai shekaru sha takwas zuwa ashirin fara ce tass kyakkyawa dan tafi wadda ke zaune a ɗakin kyau atamfa ce a jikin ta riga da skirt wanda suka kamata kamar sa fashe a ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.