Free chapter · Read without an account

A

by M.Kwalisa · Idan Rabo ya Rantse





SHIMFIDA  

TSATSON LABARIN

R

ayuwa tsere ce, tun daga cikin mahaifiya har zuwa duniya.Qauyen mu can nesa yake da qwaryar birni. Amma duk da haka muna amsa sunan ‘yan jihar kano.

Abubuwa biyu jama’ar qauyen mu suka iya, sai kuma idan damuna ta wuce su koma farauta. A ya yin da yara maza daga sun xan tasa ake xaukar su akai almajiranci,mu kuma ‘ya ‘ya mata daga mun xan xaga sai a soma xora mana dafaffen rogo ko gyaxa muna kawo wa birni muna siyarwa, idan muka kai shekaru sha uku sai a aurar da mu.

Jama’ar qauyen mu sam ba su aminta da karatun book ga xiya mace ba. Domin suna ganin ita rayuwar xiya mace kawai zaman aure da bautar tarbiyantar da yara shi ne aikinta.

‘Ya ‘ya maza ma ba kasafai ake barinsu su yi karatun boko ba bare kuma mu mata, hakan ya saka sam ba su damu da rashin makarantu boko da asibiti da muke da shi a qauyen mu ba.

A wata majiya mai tushe dana ji, ance mun mai garin mu shi ne yake yaqi da barin xiya mace ta samu ilimin zamani. Acewar bari mace tayi karatu ya savawa da tarbiyar kakaninsu. Don haka yake yaqi da duk wani abu daya shafi ilimin boko.

Idan har uba zai saka xansa a makaranta boko dole sai da amincewar mai gari. Haka kuma sai yaro ya yi tafiyar kilomita huxu daga qauyen mu zuwa wani gari daga gaba da mu kafin ya isa makaranta. Suma iyayen mu mata idan lalura zuwa asibiti ta kama su sai sun yi tattaki mai nisa.

Barewa bata gudu xanta ya yi rarrafe, kasancewar mahaifiyata ta xanyi karatun boko kafin mahaifina ya aureta, sai nima na ta shi da burin zama mace ta farko da zata yi karatu a qauyen mu. Burina bai tsaya ga sakandire ba ina fatan zama qaramar likita mai amsar haihuwa.

Ba komai ne yasa nake son zama qaramar likita ba sai domin ganin irin wahalhalun da iyayen mu mata ke sha a yayin lokacin haihuwa. Domin bas a zuwa asibiti yin awo, hakanan idan haihuwa ta zo sai dai a kirawo unguwar zomo ta amshi haihuwa. Idan haihuwa ta zo da tangarxa mace ta mutu, kamar yadda yayata Atine ta mutu domin sakaci na unguwar zoma. Ba ita kaxai ta mutu ba a kullum adadin mata ma su mutuwa yayin haihuwa qaruwa yake yi a qauyen mu.

A lokacin dana gabata da burina ga iyayena mahaifina sai daya yi kamar ya rufe ni da duka, ya yi ta faman sababi akan ina son zubar masa da mutunci, wacce mace na tava gani a karkara ta yi karatun boko? Kuma mene ne amfanin karatun xiya mace? Ita dai zaman aure ne ya kamaceta. Ta inda Babana yake shiga bata nan yake fit aba, har sai dana gwamace kixa da karatu.

Gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, mahaifiyata ta fahimce ni ta kuma bani goyon baya.

Kasancewar mahaifiya mowa ta yi amfani da soyayyar da mahaifina yake mata ta sassauto da shi ya aminta na yi karatu, amma akan sharaxi ko sisi kwabon shi ba zai bayar ba.

“Zan tuntuvi mai gari muji yadda za mu yi da shi” Tunda naji ya ambaci sunan mai gari gabana ya yanke ya faxi.

**

Da dare Babana ya dawo kallon fuskarsa kawai na yi nasan akwai matsala, na masa sannu da zuwa bai amsa ba ya shiga xakin mahaifiyata na ci gaba da zama a qofar xakin daga inda nake ina jin abinda suke tattaunawa.

“Mun kai ruwa rana, amma mai gari ya qaqashe qasa ya qi yadda. A qarshe ma cewa ya yi shi ya nemawa xansa auren yarinya”.

“Aure kuma?” Cikin mamaki mahaifiyata ta tambaya ta ci gaba da Magana.

“Allah tsari gatari da saran shuka, duk garinan wane bai san xansa tantirin xan iska bane. Ko zan mutu ‘yarta ba zata aure shi ba, karatu zata yi ko mai gari yana so ko baya so ai ba shi ne ya haifa mun ‘yar ba.”


Mata iyayen giji, cikin dare mahaifiyata ta sauyawa mahaifina tunani. Washe gari ya xauke ni ya kai ni makaranta.

Tun rana dana soma zuwa makaranta boko jama’ar qauyen mu suka soma qananun Magana. Amma muka yi kunnen uwar shegu, na duqufa wajan karatu ina fatan cikar burina.

A haka kwanaki suka zama satika, sati ya zama wata shi kuma wata ya zama shekara. A kwana a tashi ba wahala wajen Allah shekaruna suka kai daidai da yadda ake aurar da yarinya hakan yasa Garzali xan mai gari soma zuwa wajena zance wai baban sa ne ya aiko shi. Ni kuma na tabbatar masa ko ana ha-maza-ha-mata ba zan aure shi ba.

Hakan ya qona masa rai, zuciyar sa ta riqa tafarfasa kamar na watsa masa wuta.

“Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Za ki gani” Ya kaxa kai ya yi gaba.

               **

Wata uku ya yi yana fakona kafin sa’a ta faxa masa, ni kuma mummunar qaddara ta faxawa rayuwata. Bayan na dawo daga makaranta na yo ratse ta cikin gonaki, kasancewar lokacin damuna duk anyi shuke-shuke da wannan damar ya yi amfani wajen xaukata ya shiga can cikin gona ya yi mun fyaxe.

“Naga wanda zai aureki a haka” Yace da ni a lokacin da numfashina yake shirin xaukewa.

Sai dare aka tsinto ni a sume, kafin safiya labari ya watsu a qauye. Babana kamar zai saki babata domin duk laifin akanta ya xora.

Mai rai baya rasa motsi, jin abinda ya faru hukumar makaranta kai abun ga hukuma, su kuma suka tsaya kai da fata don kamawa da kuma tabbatar da an hukunta mai laifi.

Ganin abin yakai ga hukuma mai gari ya kirawo ni da mahaifina da mahaifiya ya so yayi mana barazana akan idan muka bari maganar ta tabbata to lallai zan rasa mijin aure don haka mu qaryata hakan shi kuma zai tilastawa xansa aurena.

“Daman na faxa muku babu abinda ya kamaci xiya mace banda aure, da yanzu kun aura da ita ai hakan ba zata faru ba…” Bai qarasa ba mahaifiyata tace masa cikin fusata.

“Koda zata rasa mijin aure sai mun tsaya mata an kwatar mata ‘yancinta” Daga nan ta kama hannuna muka bar wajen.


Hukumar makaranta da ta ‘yan sanda sun taka rawar gani sosai har aka kama Garzali ashe ba wannan ne karo na farko daya aikata haka ba yasha aikatawa akan yara mata sai Babansa ya yiwa iyaye barazana su kuma su ja bakin su suyi shiru.

Qaramar hukumar mu sun shiga lamarin su ka kuma tsaya kai da fata a karatuna har sai dana samu cikar burina na zama qaramar likita mai amsar haihuwa, a yanzu a qauyen mu da ni ake alfahari. Tabbas idan da Rai akwai Rabo.

Fauziyya ta kasa mancewa da wannan labarin da ‘yar tsohuwa mai ran qarfe Dada ta ba, a cikin wani yammaci suna zaune a tsakar gida.





BABI NA XAYA

Y

anayin yamacin yanayi ne mai qunshe da sassanyar iskar Fauziyya, wacce take kaxawa da busa ni’imatacciyar tatacciyar iska, xaukacin kowace halitta mai numfashi a doron qasa suna cike da alfahari da gamsuwa da tsabtacciyar iskar da suke zuqa zuwa cikin huhunsu.

‘yar kyakkyawar matashiyar budurwa tana tafe ne cikin nutsuwa, ta biyo ta wani lungu dake bayan layinsu, cikin rashin tsammani ta ji an ambaci sunanta a hankali, gabanta sai da ya faxi kaxan, jin baquwar murya data ambaci sunan ta a cikin lungun da babu yawan jama’a. sai masu wucewa jefi-jefi dake hakan ba sabonta bane, tsayawa a hanya, in har baya zama dole ba, wannan ya sa tsoro da fargaba ya cika zuciyarta da sauri ta qara taku domin tabar lungun kamar abin qaddara. Sai ta ji an sake ambaton sunan ta a karo na biyu hakan ya haddasa mata tsayawa ba shiri cikin faxuwar gaba, a hankali ta juyo fuskarta cike da alamomin neman sanin wanda ya dameta da kira tamkar baquwar budurwa, wani saurayi ta gani xan kyakkyawa a tsaye yana mata tattausan murmushi, suka zubawa juna idanu a hankali ta xauke kanta, daga kallonshi sannan ta juya, taci gaba da tafiyarta abinta, har zuwa lokacin zuciyarta bata daina bal…bal ba har ta fice daga lungun, a daidai lokacin da saurayin ya xauke kanshi daga kallonta ya girgiza kanshi haxe da yin murmushin jin daxi.

Tana shiga da sallama, ta shiga ta samu mahaifiyarta, Umma tana zaune tsakar gida tana faman tankaxen gari, da hanzari ta qarasa wajenta ta karva ta ci gaba da yi kamar yadda ta saba. Bayan ta faxa mata saqon da ta aiketa, sai Umma ta shiga kicin ta ci gaba da yin sauran aikace-aikacenta.

Sallamar Maimuna daga can qofar gida ya saka Fauziyya ta xago kanta tana kallonta, haxe da tsagaitawa da tankaxe, Maimuna ta qarasa cikin murna da fara’a baki har kunne, ta xaga hannunta, cikin dariya ta ce “Yaya Fauziyya kinga kuxina wani mutum ya bani yace na gaishe ki” Kafin Fauziyya ta yi Magana Umma ta fito daga kicin xin cikin sauri ta katse Maimuna ta ce “Ya ki zo mu gani me kika samo?”

Maimuna tana matsowa ashe Umma ta voye bulala a bayanta, ba zato sai ta hau tsulawa Maimuna a jikinta, Maimuna ta saka ihu da kuka gaba xaya tana “Wayyo Allah na dan Allah ki yi haquri Umma ba zan qara ba” Fauziyya ta wancakalar da rariyar tankaxen ta miqe da sauri ta nufi Umma tana bata haquri ita kuwa sai faxa take “Dan gidanku Abban Fauziyya bai hanaki yin roqon abin hannun mutane ba, kullum ana faxa miki kunenki baya ji…”Anan Abban Fauziyya xin ya katseta da sallamarsa yana kallonsu yace “Lafiya me ya faru?” Maimuna ta je da gudu ta rungumeshi cikin shisshikar kuka Abban Fauziyya ya shafa kanta yana rarrashinta. Sannan ya dubi umma, yace “Na faxa miki bana son dukan nan, duka baya ladabtar da yaro sai dai ma yau da gobe ya daxa kangarewa,idan laifi ta yi miki ai sai ki bari sai na dawo ki faxa min,bana son yawan duka,musamman akan ‘ya mace”

Umma tace “Allah ya huci zuciyarka Abban Fauziyya amma Maimuna bata ji shegen kunnun qashi gareta, haka kawai ta je wajen wani ta roqe shi kuxi ba a san wanda ya bata ba. Haka kika ga ‘yar uwarki tana yi? Ai kina da wayo da duk abinda na faxa miki zai shiga kunnenki” 

Abban Fauziyya ya dubi Maimuna cikin vacin rai “Mutuniyar banza ashe abinda kika yi kenan?” Maimuna ta sake tsorata taja da baya,cikin kuka tace “Allah Baba ba roqonshi na yi ba,na zo zan wuce ya kirani yace na gaishe da yaya Fauziyya in ce mata inji Abdul, shi ne ya bani kuxi nace masa aa a gida za a dake ni,shi ne ya matsamin yace ai ba roqon shin a yi ba shi ya yi niyya, ya yi ta yi min magiya har na amsa”

Abban Fauziyya ya kalli Umma fuskarshi xauke da alamar murmushi,sannan ya jawo hannun Maimuna suka wuce xaki, ita kuma Fauziyya sum-sum ta shige kicin,zuciyarta taf da tunane-tunanen barkatai akan wane ne Abdul xinan? 

              **

Fauziyya ta fito daga gidansu, cikin wata baqar abaya, da hijabi fari tana riqe da ‘yar Jakarta a hannu a hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya, a daidai kan kwalbatin fita daga layinsu ta ganshi a zaune cikin wasu riga da wando na shadda. Yana zaune akan kwalbatin gaba xaya hankalinsa da murmushin farin cikin ganinta, ganinshi a wajen ya saka ta kuma xaure fuskarta, sannan ta xauke kanta kamar bata lura da wata halitta a wajen ba. Sai data zo daidai wajen da yake zata wuce taji yace “Barka da asuba Hajiya Fauziyya” Bata amsa ba bare ta kula shi sai ma tayi kamar bata ji shi ba, ya zubo mata idanuwansa zuciyarshi tana daxa ruruwa da wutar qaunata,duk da bata kula shi. Amman yana cike da xumbin farin cikin ganinta, tare da cikar burin zuciyarsa na xora qwayoyin idanunshi akan macen data mallake zuciyarsa.

Awani huxu suka yi a makaranta suna tilawar karatu,, qarfe sha xaya daidai aka tashe su, Fauziyya tana tafe a hankali zuciyarta cike da tunanin rashin ganin Rashida. Ba shakka Rashida bata son zuwa makaranta sam,shaixan ya gama yi mata fitsari a kanta, amman tabbas zata yi iya qoqarinta dan yi mata nasiha,domin komai a nasihance ya fi karvuwa a zukata kamar yadda malamai suka ce addinin ma kanshi nasiha ce.

A karo na uku ta sake xora qwayar idanunta, akan na shi Allah mai qudura, wannan karon sai ta kasa janye idanunta daga kallonsa har sai da ta yi namijin qoqarin xauke kanta gaba xata, haxe da sunkuyar da kai tana kallon gabanta a cikin kunuwanta taji murya shi ta ratso cikin zuciyarta, wannan karon murya ta sa gaba xaya ta sauya mata salo savanin baya, a hankali ta ji yana faxin “Sannu da dawowa Hajiyata” Wannan karon ma bata amsa masa ba, sai ma daxa qara taku da ta yi, da hanzarinsa ya miqe ya sha gabanta, hakan ya bata damar tsayawa cak a wajen haxe da xago kanta tana kallon shi idanuwanta akwai alamomin tambayar dalilin daya sa ya tsaida ita.

Idanunshi suna tsaye tsaf akan nata, bai iya furta komai ba, sai wani salo kallo-kallo da suke yiwa juna mai cike da sirrika da dama. A cikinsa a lokaci xaya gabanta ya faxi ya yin dani tsohon tsiron halitta dake kwance a can qasan zuciyarta, ya motsa da qarfi a take qwaqwalwarta ta xau caji cikin qiftawar ido vangaren dake adana tunanin da ya gabata ya watso mata da wani al’amari da ya shuxe. Kamar a fefen majigi hakan ya haddasa mata wani canji na wani irin yanayi,wanda a cikin ‘yan daqiqu irin kwatankwacin wancan shuxaxxen yanayin. Sai dai ko shakka babu wancan tsohon yanayi ya ninka wanda take ciki yanzu kwatankwacin sau ba adadi,tabbas ba iyaka,duk kuwa da cewar a wancan lokacin tana cikin lokaci ne na quruciya, ba zata iya tantance gaskiya da qarya ba, duk waxannan abubuwan da suka faru sun faru ne cikin daqiqa xaya kacal. Wannan ya sa ta xauke kanta gefe guda,fuskarta tana cike da nuni da wani yanayi a hankali ta bi ta gefenshi ta wuce abinta, yayin da shi ma ya juyo a hankali yana dubanta har ta qule.

            **

Tana kwance akan gado rigingine, ta xora pillow akan cikinta, idanuwanta quri suna duban saman xakin. Ta matsanta wa kanta tunano dalilin daya hadassa taso abin dake can qasan zuciyarta duk kuwa da cewa abin ya kan tava zuciyarta, a lokutan da dama, sai dai takan jure ta cije domin ta daxa haqiqancewa abin halittane a cikin zuciyarta babu yadda bata yi ba ta manta a ranta, amman ta kasa. Har kuma zuwa yanzu koda xiso xaya bai tava gogewa ba.

Ta rufe idanunta a hankali hoton yanayin rigar fulanin ya bayyana tar tar a cikin idanunta lokaci xaya kuma ta dinga kallon yanayin yammacin a cikin lokacin ,sararin samaniyar yana cike da lilimi sakamakon curarren gajimare da ya yi wa sararin shuxiyar samaniyar subahanahu wata’ala qawanya, hakan ya haddasa wata sassanyar iskar dFauziyya busowa a hankali haxe da sanyaya zukata,hoton fuskarshi ya hasko shu’umin idanun da suka dinga firgitata. Suka bayyana tartar kamar tana ganinsu a zahiri ta sauri firgigit ta buxe idanuwanta, abin mamaki shu’umar fuskar tashi take gani hakan hakan ya sa ta tashi zaune da sauri, tabbas gizo yake mata. A hankali ta saki ajiyar zuciya daddaxar sassanyar busar sarewa ta riqa jiyo amsa kuwwarta,a cikin daddaxan yanayin yammacin da farkon al’amarin ya fara samo tushe a zuciyarta. A hankali ta riqa ji a ranta kamar tana cikin wancan tsohon yanayin ne slow music xin Salisu yana ratsa mata zuciyar da ruhinta,a sannu-sannu ta tuno da kakarta a hanakali kuma ta dinga tuna kalaman Dadar na qarshe data yi mata. Wanda kuma suka tsaya mata a rai, hawaye suka dinga fita daga idanunta, tambayar data adabi zuciyarta,shin yaushe ne zata kuma ganinsa duk da cewar Umma tasha faxa mata a lokuta da dama ya sha zuwa amman suna tafka savani da shi domin duk zuwan da zai yi tana can makaranta, sai dai ta samu labara a wajen umma. To idan ma ta dawo ta same shi wane amfani ganin na shi zai mata? Yana da kyau ta sakawa kanta haquri da kuma juriya da fidda rai da shi da kuma bai Allah zavi akan lamarin.

Tana duba agogo taga qarfe xaya da rabi na dare ta je ta xauro alwala, ta yi sallah sannan ‘yar qanwarta Maimuna ta shiga xaki ta kawo mata abinci har xaki ta ajiye ta fice abinta.

Da magariba Abban ta ya shigo da sauri bayan ya xau buta ya yi alwala sai ya shige xakinsa, ya qwallawa Fauziyya kira da sauri ta nufi xakinsa. Da sallama ta shiga ta durqusa yana tsaye yana murza wani turare a hannunshi al’adarsa kenan in dau zai yi sallah sai ya goga turare nan, ya dubeta yace “Idan kin idar da sallah isha’i kije gidan Alhaji kice masa ya jira ni gobe qarfe bakwai na safe” Ta amsa a ladabce “To Baba” sannan ta fice,shima Abban Fauziyya xin fitowa ya yi da sauri ya nufi masallaci dake nan qofar gidanshi domin liman ya hau mumbari. jam’i suka bi da yake masallacin a qofar gidan makwabtansu yake,sai da ra ci abinci qarfe takwas ta fara kallo labarai, sai ta miqe a hanzarce ta je ta xauko gyalenta ta yi wa umma sallama ta fice dan tasan halin Baban su. Mutum ne da baya son vata lokaci haka zalika baya qaunar sava alqawari ko kaxan. Gidan Alhaji Lukuman yana nan tsakanin su layi uku ne, ta kusa isa gidan kawunta, sai ta ji an kirawo sunanta a hankali, sai da ta xan tsaya wannan karon ranta ba daxi, sabida ta tsani takurawa a rayuwarta hakan ya saka ta waiwayo gaba xayanta sai da gabanta ya faxi. Suka tsaya suna kallon-kallo, wannan karon ma bai ce mata komai ba amman salon da fuskarshi ya nuna ya isa gamsar da zuciya tarin alamomin ximbin qaunar da yake yi mata a zahiri da baxini, a hankali ya zaro wani abu daga cikin aljihun wandon shi ya sunkuya a hankali ya ajiye a daidai kusa da inda take tana binshi da ido fuskarta cike da mamaki sannan ya miqe ya yi mata tattausan murmushi, mai ruxa zuciyar masoyi, ya juya yabar wajen sai data daina ganinsa ta juya ta kai idonta ta sake kallon abinda ya ajiye a waje, ta xauke idanunta ta juya ta soma tafiya sai data yi taku biyu ta tsaya cak. Ta juya ta kalli abun har lokacin yana wajen daya ajiye shi. Ta koma ta tsugunna ta xauka da yake akwai hasken florescent xin gidan Alhaji tana iya ganin komai a wajen ta duba sai ta ga wani xan qaramin kati cike da rubutun ruwan gwal an rubuta kalamai da suke nuni da tsananin qauna da nuna bege ta ja tsaki, a hankali tayi jim ko me take tunani oho? Sai kawai yanayin fuskarta suka canza, kwalla sun ciko mata a idanu, sannan ta cije leventa,a hankali ta yayyaga katin ta sake su qasa suka tarwatse a wajen, ta kaxa kanta ta bar wajen.

Tana sallama a gidan Alhaji Hajiya Mariya ta amsa, ta tsuguna har qasa tana gaisheta, sannan ta faxa mata saqon Abban su tace “To shi kenan in ya zo zan faxa masa, wata qila ma kina nan wajen ‘yar gidan naki ya dawo” Tana gama rufe bakinta Rashida ta leqo daga can barandar saman bene tana dariya ta ce “Na jiyo murya qawata” Duk suka kwashe da dariya Fauziyya ta miqe ta nufi saman tana “Gani nan ai zan hawo saman”.

Suka koma cikin xakin Rashida, can cikin xakin barcinta suka shige, Fauziyya ta zauna a gefen gado, yayin da ta kai qwayoyin idanunta kan kayan mayukan da turare baja-baja akan gadon, ta maida kallonta kan Rashida yi murmushi “Hidimar xan bawan Allah kenan Mustapha” Fauziyya ta yi murmushi tace “Zai iya daman na yi tsammanin haka” Ta xanyi jim alamar wani abu yana tava zuciyarta, Rashida tace “Fauziyya ana baki shawara kina qin karva, dan Allah ki yi facali da duk wani buri da shi ki tsaida hankali waje xaya ki fito da miji tun kafin ran Abban ku ya vaci dake, kinsan mai haquri bai iya vacin rai ba. Kuma burin mutum baya qarewa a duniya, ba lallai sai kina son mutum ba in dai kin ga wanda ya dace da irin rayuwarki shi kenan, yaushe za ki zauna ki zama dundurusun dusu, ki jawa kanki fushin iyaye”.

Fauziyya ta sauke ajiyar zuciya ta dubi Rashida ta girgiza kai tace “Rashida ki gane shi aure ba haka yake ba, ni a wajena da ra’ayina ban ce ra’ayinki ba, ban kuma ce ra’ayin wani ba, ni a karan kaina na fi son na auri wanda nake qauna wanda ya kwanta min a rai, saboda aure baya xorewa sai da kyakkyawan tushen qauna kyakkyawar fahimtar juna, ta haka ne kowa zai fahimci manufifin kowa, kima sai ki ga an samu kyakkyawan zaman lafiya mai ban sha’awa da xorewa”.

Rashida tace “Haka ne to amman yanzu ina kika sawa gaba ne?” Fauziyya ta kalleta “Eh to, ni a yanzu bani da taqamaimen tudun dafawa,domin wanda nake qauna a raina qauna ta fisabililahi, ban san a in azan kuma ganinshi ba, a salima na haqura da fidda rai da shi kwata-kwata. Na biyu shi ne ina son zuwa qaro Ilimina, sannan abu na uku ban san yadda zan iya cike gurbin nan da son wani ba, domin abin ya zame min kamar wata hallita a cikin zuciyata, amman na tattara komai na miqawa ubangiji zavi domin zavin Allah shi ne kyakkyawan zavi kuma a shirye nake da gode masa, a cikin dukan abinda ya bani, ni nasan shi ne alheri wallahi ban tava fushi da yin Allah ba, bana fushi da abinda Allah bai bani ba, duk tsanani duk rintsi ina nan ina neman tallafinsa,da yardarsa da zavinsa”.

Rashida ta sauke numfashi tace “Eh gaskiyar maganar ki ne, amma batun da zan baki shawara akai shi ne mai zai hana ki nemi wanda za ki huta, Iyayen ki su huta kinga baki aure shi dan so ba amman ta vangaren abin hannunsa, ai kya huce takaicinki, amman kin auri talaka ga qunci da wahalar rayuwa ga tsananin qiyayyarsa a ranki ina kika ga ta zama bare batun jin daxin rayuwa” Fauziyya ta girgiza mata kai “Wallahi ko kaxan bani da ra’ayin haka, domin manzon Allah (s.a.w) ya ce, ku auri mace dan asalinta ko domin kyanta ko arzikinta ko iliminta, to amman mafificiyarsu ita ce mace mai addini da tarbiyya irin ta musalunci it ace mafi daraja da amfana ga mijinta da ‘ya ‘yanta mai ladabi, tsafta da alkunya, amma kasha casa’in a cikin mazan wannan zamanin kyawawan mace suke da tasiri wajen tafiya da imanin su da xauke hankalinsu wajen mace sa suke son aura”.

“Haka suma mata an hore su da su lura da dalilan da aka bayar wajen neman auren mace kamar shima namijin akan auren shi don sarautar shi, domin kyawun shi, arzikinshi, amman kuma mafificinsu shi ne mutum mai addini da kyautata ibadarsa, mai xa’a, nutsuwa,hankali da dai sauransu to amma kasha casa’in mai arziki shi ke da tasiri akan mijin da suke son aure”

“Don haka ina fargar dake, idan har kina da irin wannna ra’ayin da ki tsaya ki yi aurenki da zuciya xaya tsakani da Allah ki fidda kwaxayin dukiya, da dogaro da abin wani, domin su kuxi da kyau abubuwa ne waxanda kwatankwacinsu tamkar kumfar kogine, idan ka xebo shi kin ajiye wata rana za ki wayi gari ya bushe” Rashida ta xan yi kasaqe da alama ‘yar nasihar Fauziyya da ta yi zata yi tasiri wajen wargaza mummunar aniyarta, ta numfasa tace “Lallai kam dukkan jawabanki abin dogaro ne, Allah ya zava mana mafi alheri, amin” Anan qanin Rashida ya shigo yace ana sallama da ita, suka fice tare suka gaisa da Mustapha haxe da xan tava hira, sannan suka yi sallama ta wuce gida. A can kan kwalbatin dai ta sake ganin Abdul a zaune, tana zuwa daidai inda yake sai taji yace.

“Mu kwana lafiya Fauziyya” Bata amsa ba, amma kuma wannan karon sai ta ji xan tausayinsa a ranta. Tana shiga gida Abban su yana kishingixe yana sauraron rediyo ta tsuguna a gefe tana yi masa bayanin saqon daya bata, ya rage qarar rediyon kaxan sannan ya saurareta bayan ta gama yi mishi bayanin sai yace.

“To madallah sannu ko?” Har ta miqe zata wuce xaki sai ya kirawota ta dawo ta tsugunawa a gefe Abban su ya kalleta yace “Zauna mana sosai magana nake so mu yi ai” Fauziyya ta zauna a kusa da shi gabanta yaci gaba da faxuwa domin ta san dai tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi, malam ya kashe rediyo gaba xaya sannan yace “Daman maganar dazan yi miki, wai Fauziyya me kike ciki ne? kinga na baki damar ki domin ban son takurawa rayuwarki ne shi yasa kika ga na zuba miki idanun, ina sauraronki akan ki fidda wanda kika gay a kwanta miki ranki, sam bana qaunar takewa kowa haqqinsa yanzu kinga ‘yar uwarki ta fidda mijinta amma ke ban san mene yake damunki ba, mene ne ra’ayinki ne?” Ya tsagaita yana dubanta ta sunkuyar da kanta qasa zuciyarta tana cike da fargaba da vacin rai to me zata ce wa Abban Fauziyya?.

Abban Fauziyya ya katseta “Fauziyya ina alfahari dake domin na shaida ke xiya ce mai hankali da nutsuwa da biyayya waxannan halaye naki sune suke qara qaunarki a kullum a zuciyata, abin daya sa na dameki da maganar aure, ba don na gaji dake ba ne, sai don in inganta rayuwarki domin aure shi ne daraja da qimar dukkanin ‘ya mace, kuma ina matsanta miki badan komai ba sai don idan yau mune gobe ba mu bane, don haka na yanke shawara a zuciyata, amma ba zan gabatar da qudurin ba har sai da yardarki da amincewarki idan kina ganin baki da wani zavi naki to ni na shirya zava miki miji da kaina, kar kuma kiyi tunanin zan zubar miki da daraja da qima, don kin san Hausawa sukan ce matar shige bata daraja, to kar ki yi tunanin wannan anan gida na yi miki zavi kuma xan uwanki ne wanda na tabbatar shima ya jima yana qaunarki, me kika gani akai, kin amince?”.

Jikinta ya yi sanyi laqwas zuciyarta ta cika da tam ta quntata da qunci da baqin ciki hankalinta ya dagule, ranta babu daxi qwaqwalwarta ta hargitse ta cakuxe ta kasa tunanin komai. A hankali ta ji zuciyarta ta yi rauni tabbas ba zata yi musu da malam ba. Bata san sanda qwalla ta cika mata idanu ba, tax ago kai ta dubi malam har yanzu kallonta yake yi alama yana karantar wani abu a fuskarta, hakan ya saka tayi saurin sunkuyar da kai. “Na amince malam” Abban su ya xan yi jim kaxan sannan kuma sai ya ce “Ba komai kar ki damu kinji tashi kije Allah ya yi miki albarka” da qyar ta miqe tabar wajen hankalinta a tashe, tana shiga xakin ta faxa kan gado zuciyarta tana azalzalta kamar ana hura mata wuta, lokaci guda qwaqwalwarta ta shiga aiki, shi kenan abinda take gudu dai shi ne daga dukkan alamu zai faru, malam ya gaji da sanyi mata idanu zai bayar da ita ga wanda yake so, anan hawaye ya samu nasarar kufce mata, ciwon da yake kwance a zuciyarta yi motsa ta sake jin wani baqin ciki ya mamaye dukkan zuciyarta, jikinta ya yi sanyi zuciyarta ta yi rauni irin na wanda ya yi rashin wani muhimmin abu na vangaren rayuwarshi a hankali ta fara saqa tana kwancewa, mene ne abin yi? Gashi ta furtawa malam ta amince domin ba zata iya sava masa ba, asalima tag a wani abu na vacin rai ya shiga tsakaninta da malam kuma tana da yaqinin kome Baban su yace ta yi ba makawa zata yi koda kuwa wuta ya ce ta faxa, bare kuma ta san halin sa yana da tsananin tausayi gashi babu wuya ya saka abu a ranshi, ya dinga damuwa hakan ne yasa tunda ta mallaki hankalinta take kaffa-kaffa da shiga gonarsa, musamman da yake tasan yana da wannan mummunan ciwon nan na hawan jini, wannan tunanin da ta yi ya sa ta haqura ta sallama ta amince da zavin malam. A hankali ta ji gabanta ya faxi a lokaci xaya tayi Allah wadai da rashin tsayawa ta saurari xan saurayin da yake ta faman nacin binta a gindi a gindi ba, tabbas bashi da wani makusa kyakkyawane da cikar mutunci don daga ganinsa bai yi kama da mutanen banza ba, ta yi ajiyar zuciya cikin nadama me yasa ma bata amince da shi ba? Ta tsaya vata lokaci da tunanin gaibu, jiran gawon shanu,jiran da bashi da tabbaci, gashi ta riga ta amincewa zavin mahaifinta,hawaye ya zubo mata, ita kam bata cikin mataye masu sa’a a rayuwarsu ya zata yi da qaddara ne?

Shi kuma har yanzu mahaifinta yana kishingixe tun bayan ‘yar tattaunawar da suka yi da xiyar tashi yake jin wani bala’in tausayinta, musamman da yake Fauziyya duk tafi shiga ransa ainun saboda ladabi da biyayya gata da haquri da dogaro da Allah, tamkar kasa take wajen haquri, tabbas barewa bata gudu xanta ya yi rarrafe. Halaye tsaf nashi ta xebo ba kuskure haqiqa ya san batun yanzu ba, tana da wani voyayyen lamari na ta a can qasan zuciyarta kuma ya san zavin da ya yi mata fuskarta ta nuna bai kwanta mata a rai ba, amman ya sani ta sadaukar da kai ne domin ta faranta mishi rai. Allah sarki...anan wani yaro ya katse masa tunanin da sallama bayan ya amsa sai yaron ya durqusa ya gaishe da shi xan na maqwabtansu ne, sannan yace wa malam “Wai ana sallama da Fauziyya inji Abdul” Malam ya xanyi shiru jim kaxan sannan yace wa yaron “Kaje ka ce masa ya shigo ciki”.

A daidai nan Fauziyya ta fito ta nufi gindin famfo don ta yi alwala saboda tana son taxan tava karatun alqar’ani kafin ta kwanta ko zata ji sa’ida a ranta.

Minti xaya kacal murya Abdul ta kwararo sallama a cikin gidan, gabanta sai daya faxi da qarfi saboda ba zato taga Abdul yana sanye da fararen shadda da hula mu gamu a banki,ya iso wajen malam a cikin nutsuwa ya tuve takalminsa ya koma gefe yana gaishe da malam , malam ya miqe yana nuna masa wajen zama gefen tabarma kusa das hi yace.

“Zauna mana ga waje nan” Bai yi musu ba, ya zauna haxe da sunkuyar da kai daga nan kuma suka yi shiru kaxan, malam xin ne ya katse shirun yace “Kaine kake son ganin Fauziyya?” Abdul ya amsa cikin ladabi har lokacin kansa yana qasa,malam ya ji daxi a ransa don ya yaba nutsuwarsa qwarai, malam yace “MadAllah yanzu yanzu zan yi maka wasu tambayoyi” Nan ma Abdul shiru ya yi yana sauraro hakan ya bashi damar ci gaba da yin bayyaninsa “Da farko na yaba da hankalinka, kuma tambaya ta farko da zan maka shin wane dalili ne ya kawoka wajen Fauziyya?” Abdul ya daxa sunkuyar da kai cikin nutsuwa yace “Baba ina son Fauziyya qauna ta fisabillah wato ina sonta da aure bada wasa na zo ba” Baban su ya xan yi murmushi yace. “Madalla saura tambaya ta biyu, ina son sanin mahaifinka, da inda yake da zama?” Abdul yace “Sunan mahaifina Alhaji Usman gidanmu yana nan a unguwar Tudun murtala, layin masallaci sanan mahaifina yana sana’a anan wapa ‘yan canji dake nan fagge” Ya yi shiru yana mai da numfashi.

 Baban Fauziyya yace “To madaAlla na gamsu da dukkan bayaninka, kuma na yi maka izini kaje ka nemi soyayya a wajen Fauziyya idan ta amince, falilahi hamdihi haka ake so, amma ina da sharaxi bana son yaudara, idan ta aminta da kai ka riqe amanarta, kuma ka riqe alqawari bana son saba alqawari,saboda girmansa, bana son wasa a cikin lamarin aure, domin shi aure ba abin wasa bane kamar yadda ake yi masa riqon sakainar kasha, matsalolin dake damun mu kenan a yau mu Hausawa ba wuya an yi aure ba wuya anyi saki, saboda tun farko akwai sharuxxan da matakai, Manzon Rahama yace mu bisu tun a wajen neman auren kanshi to amma baa bin wannan abinda ake la’akari da shi daban tun farko ba a gina abin akan tushe ba,don haka ne ake samun matsalolin birjik kuma an rasa yadda za a gyara su, saboda haka in har kun amince da juna, nima zan yi nawa binciken kamar yadda shari’a ta gindaya yanzu sai kaje ka jirata, Allah ya taimaka” Abdul ya sake duqawa yana godiya, zuciyarsa tayi fari qal, ya riqa jin daxin jawabin malam. Haka yake son mutum irin malam wayayye wanda ya iya tafiyar da kowane irin mutum, ya fice cike da murna da qwarin gwiwar tunkarar Fauziyya don gani yake kamar an mallaka masa ita ne gaba xaya.

Ya qwalla wa Fauziyya kira ta fito da hijabinta baqi, ta durqusa malam yace “Kin yi baqo sai kije minti talatin tunda dare ya soma yi”. Fauziyya tayi jim ta kasa tashi a hankali tace masa “Malam ai na amince da zavin ki, ina ganin shi ne mafi alheri a gare ni” Ta sunkuyar da kanta qasa, malam ya yi murmushi yace “Ba komai Fauziyya ai dama cewa na yi na yi shawara a raina, amma ba lallai bane sai kin amince, to na fuskanci wani abu xin ma na aminta na gamsu da nutsuwarsa, don haka idan har kin gay a kwanta miki a ranki shi kenan nima na amince da zavinki ko?” Ya yi dariya, bata ce komai ba sai tayi murmushi tace “To Baba shi kenan na gode” “Ba komai ki daina damuwa kin ji” tace “To”.

A daidai nan Umma da Maimuna suka dawo daga unguwa, Baban su ya kirawo Maimuna yace ta xauko makullin shago taje ta buxewa baqo ta amsa ta tafi da hanzari.

Fauziyya kuwa don tsananin jin kunya sai ta kasa miqewa ta tafi malam ya gane hakan don haka sai ya miqe yasa takalmanshi ya fice abinsa.

          ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol