FreeArewaPen original
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA ƊAYA Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin."Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.