Free chapter · Read without an account

Page 2

by Nasreen Muhammad · ALƘALAMIN SO

ALKALAMIN SO


        BY


  DIJAHAM(Oum Amani)


Page 2


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



  Ko motsi bai yi ba sai hannu daya sa yana zagaye baya na fuskar sa dauke da murmushi wanda Ina daga cikin mutane kalilan da nake samun ganin sa, a hankali sa cire hannun sa daya zagaye bayana yana dago fuska ta.


Tura masa baki nayi a shagwabe nace "Uncleee......"


Yadda taja karshen sunan nasa ne yasa shi dan bude idon sa yana kallon ta murmushi mai fadi yana bayyana a fuskar sa har fararen hakoran sa suna fito wa, Jan dogon hanci na yayi yace "mene little ynxu kika dawo daga school je kiyi sallah tukun"


Juya ido nayi wanda habit dina ne bama in Ina tare da Uncle nace "ai nayi sallah a school kuma yau ba islamiyya gidan Ya Kareema zamu je da Ya Kausar"


Hannu na da nake yawo da shi a arm dinsa ya cire yace "ban hana ki ma wai zuwa ki dinga rungume ni haka kamar zaki fadar dani ba baki ga kin fara girma ba, ya fada yana kallon cikin idon ta".


Bubbuga kafa nayi Ina narai narai da ido kamar zan yi kuka nace "to ai kai ne Uncle bayan kai bana rungume kowa ai sai dai kawai na rike musu hannu".


Murmushi kawai yayi yace "wuce ki shiga kiyi wanka sai warin rana kike".


Kamar zanyi kuka nake kallon sa Ina shinshina jikina nace "Uncle Allah bana warin rana"


Daga min kai kawai yayi yace "Toh shikenan naji bakya warin rana je ciki bari naje gurin Umma"


Turo baki nayi gaba nayi na ratsa gefen sa zuwa cikin palon, a zaune na samu Mami tana kallon TV zama nayi a kasan kujerar da yake zaune nace "Barka da yamma Mami"


Murmushi ta sakar min tana dafa kai na tace "lafiya qalau Shatu ya makaranta?"


Shagwabe fuska nayi nace "ai ba dadi Mami ni kam na matsu na gama dmakarantar nan na huta Wallahi".


Dariya Mami tayi tace "saura shekara biyu ai sai ki huta kuma kafin a fara university"


Marairaice fuska nayi nace yncu "Mami baza kısa baki ba Uncle ya bar ni nayi WAEC dita a Ss2 ba, Sultan fa yce mun shi a Ss2 zai abin sa Maryam ce dai tace ita Daddy baxai yadda ba amma ni ai dana fada wa Dada bai ce komai ba".


Dan Murmushi Mami tayi tace "to nidai baxan nada magana ba ai kowa a gidan sai ya kai Ss3 yake Waec shi Sultan din nasan abinda yake fada yayan nasu bai sani ba daya sani ta tuni maganar ma baxai sake ta ba".


Tagumi nayi Ina kallon Mami kamar nayi kuka gashi da yawa a class din mu duk sun ce a SS2 zasu gama.


Ya Kausar ce ya fito a shirye cikin doguwar Riga da Mayafi tayi kyau sosai abinka da farar bafulatana.


Kallona tayi tace "au wai baki shirya ba dama ba naji maganar ki kina wa Ya Aliyu suruta na da zata ma kin shirya".


Kallon fuskar ta nayi naga yadda ta hade rai tana kallo na, turo baki nayi na kalli Mami wacce take kallon TV abinta ba alamar zata shige mun.


Ajiyar zuciya na sauke na tashi Ina daukar school bag dita nace "Allah ya baki hakuri na tsaya Ina shawara da Mami ne amma yncu zan fito".


Kwafa tayi tace "kar ma ki fito Aisha wallahi kika fi minti 10 tafiya ta zanyi kin ji na rantse tun da safe naso tafiya ta Mami ta tsayar da ni"


Mami ce ta juyo ta kalle ni taga na zuba mata idona da suka Soma çıka da hawaye ta kalli Kausar taga ta nemi waje ta zauna tana danna waya, dauke kan ta tayi daga kan ta ta kalli Aisha tace "je ki kin ji Shatuna in ma ta tafi ta barkı ba sai nasa a kai ki ba"


Dariya nayi cikin farin ciki na wuce dakina don ni ganin Uncle ma dana yi sai naji bana son zuwa gidan Ya Karimar, wanka nayi na fito na zira atampa doguwar riga mai dogon hannu, nayi kyau sosai ban shafa komai ba bayan mai dana shafa a jikina sai dan turare don Uncle ya hana ni sa turare da yawa in zan fita.


Mayafi na dauka kalar atampa ta na yafa a kafada ta, nayi kyau sosai yarinya y ta sake fito wa ga fuska ta luwai luwai kamar ka latsa jini ya fito.


Har naje bakin kofa na tuna ban dauki waya taba na koma da sauri na dau waya ra dake kam mirror.


Already na dau takalmi na don haka sallama kawai muka yiwa Mami muka fita.


Kallon Ya Kausar nayi naga tana waya sai wani Lumshe ido take tana Langwabe kai ita a dole shagwaba take wa saurayin ta.


Ni ba shagwabar bace take bani mamaki yadda ya dage tana wa katon gardi shawaba ne yake bani mamaki nidai, kallon ta kawai nake dai da ta galla min harara sannan na dauke ido na Ina murmushi.


Waya take har muka isa gidan Ya Karima, sai da muka sauka a adaidaita sannan ya kashe wayar ta biya kudin motar.


Cikin gidan muka shiga shiru ba kowa a compound din sai mai gadi daya fito daga dakin sa ganin mu ya Washe baki da sauri yana gaishe mu, amsa masa Ya Kausar tayi ta shige gidan ni kuwa sai da na isa har gurin sa na tsaya muka dan yi hira sannan na shige palon.


Gaishe da Ya Karima nayi dake zaune tana sawa autan ta Noor pampers, yana gani na ya fara zillo yana kira na da daga hannu na dauke sa.


Dariya nayi na karasa cikin palon kusa da su, hannu nada na rike nasa Ina masa wasa sai dariya yake, daga ido nayi na kalli Ya Karima nace "Ammah(kamar yadda yaranta suke kiran ta nima wani lokacin haka nake kiran" ta bani shi na karasa shirya sa"


Murmushi tayi tace "karbe sa don Allah dama na gaji tun dazu yaki yadda ko su Yasmin ne su dauke sa sbd tsabar kiwa"


Dariya nayi Ina karbar sa nace "wai su Yasmin din yake wa Kiwa har ynxu Ammah", mai da kallona kan Noor nayi Wanda yake ta mun murmushi na ja kumatun sa don Tubarkallah yaron ba dai kumatu ba.


Zama na gyara muka shiga hira da Ammah Ina cin abincin dana zubo a kitchen, ita dai Ya Kausar kallon mu take kawai sai in abin ya shafe ta sannan zata bada amsa gajera.


Haka take ita kaf familyn mu zan iya cewa ita kadai ce tayi halin Uncle na rashin magana, wai a haka ma gwanda ita tana maganar na shi uncle wani lokacin ina Jin yana iya yini baifi yai kalma goma suma gaisuwa ce duk maganar da body language ne, nice ma kawai nake sashi surutu nima in na ishe sa cemin yake naje na kwanta ko ya sani wani aikin daban ko kuma ya Mike kawai ya rufe mun baki ya tasa keya ta har bakin kofar dakin sa sannan ya rufe kofar.


Sai bayan magriba muka tafi gida hannu na rike da ledar dambun naman da Ammah ta bani na Mami kuma tasa mata a container mai kyau itama.


Misalin karfe 9 na dare Ina kwance a dakina Ina assignment aka bude kofar, ajiye pen din hannu na nayi na juya Ina kallon Ya Haidar.


Murmushi na saki mai fadi sosai na sauka daga kan gadon a shagwabe nace "Yaya tun safe ban ganka ba yau"


Hannu yasa a habar sa yace "Ina tausaya wa Wanda zai aure ki gaskiya Aisha ke a rayuwar ki baxa ki iya magana ba sai kin yi shagwaba"


Hannu nasa na rufe fuska ta cike da kunya nace "kai Yaya ka daina irin wannan maganar mana yar karama ta dani zaka fara min maganar aure in Uncle yaji ka ai yace zaka lalata masa yarinya"


Dariya yayi sosai yace "Allah ya shirye ki, kije shine ma yace na Kira masa ke yana kiran wayar ki baki dauka ba"


Dan zaro ido nayi nace "Wayyo tana wajen ya Kausar na bata tasa min wani series tana can tana waya ba lallai ma ta gani ba"


Saukowa daga kan gadon nayi na Dora Hijab akan rigar bacci na wacce ya ke iya gwiwa mai taushi.


A part din mu na bar Ya Haidar ni na wuce compound din gidan gaba daya, direct part din mazan gidan na nufa daku nan mazan gidan a jere yake banda na Uncle Wanda shi nasa sai ka hau wata yar baranda sannan zaka bude kofar dakin sa.


Knocking nayi sannan nasa hannu na murda kofar, sanyin AÇ da kamshin freshener din daya doke ni yasa ni Lumshe ido na kafin na bude su akan Uncle, yana zaune Akan katuwar katıfar da wacce aka shinfida wa bedsheet navy blue mau mugun kyau gefe kuma duvet a gefen gadon, sai katuwar wardrobe din sa da mirror, set din gado ne kawai ya siya gaba daya amma ba gado, nidai ban San me yasa Uncle baya son gado ba tun da na budi ido na katifa nake gani ko zai gyara dakin sa katipa still yake sawa ba gado ba. Da akwai kujera amma mai L ita ma navy blue sai TV wacce aka dora Akan TV stand. Dakin sa gaba daya ba tarkace ko yaushe zaka gansa tsaf sbd tsabtar Uncle.


Kallonta kawai ALIYU yake ganin yadda take ta karewa dakin kallo bai dai ce komai ba.


Mai da kallona kan sa yayi ganin yana kallona yasa ni murmushi na nufi inda yake zama nayi a gefen katifar kusa da shi sosai cikin shagwaba nace "Uncle"




(Oh ni Dijee nace wannan diya kin cika yiwa wannan Uncle din naki shagwaba baki san Uncle din ki bane ba)



DijahAM🥰

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol