FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Nainarh KD – Nkd's “Every heart has a story — I only give it words.” 📞 Phone Number: *** or ***
Sample · 1
*🔥❤️ TSANTSAR SO ❤️🔥****"Ita ce fa wannan Budurwar jikar Mai martaba Sarkin mu da tazo daga ƙasar waje kwanaki biyu da suka wuce."Ya yi maganar wa abokin nasa da ya yi masa tambayar gaba ɗayan su kowanne yana kuma hangame baki wurin kallon kyakyawar fuskarta da kuma haɗaɗɗiyar surar da Ubangiji ya azurtata da shi. Outfit dake jikinta normally Jean's ne sai kuma Riga Top white ta ɗaure rigar sanyi a ƙugunta ƙafafunta sanye da Boots irin na fita training na safe ga dukkan alamu daga training take. A hankali take lumshe kyawawan idanunta yayin da take ƙara buɗe su. Hannu takai tana gyara gashin kanta da ya leƙo tana ci gaba da faɗi cikin daddaɗar Muryarta mai daɗin saurare."Tabbas ba son gaskiya yake miki ba shawara anan ita ce ki rabu da shi Allah ya haɗa kowa da rabon sa."Ta ƙari sa maganar sannan ta gyara Bicycle nata tana faɗin."Ohya Teema zo mu wuce.""'Yar uwa na gode sosai da shawara kuma in Allah ya yarda na rabu da shi har abada, dama tun tuni nake zargin ba tsakani da Allah yake ƙaunata ba."Kallon Yarinyar tayi ta ce."Ina miki fatan haɗuwa da wanda ya fisa kuma mai ƙaunar ki da gaskiya domin akasarin mazan yanzu ba tsakani da Allah suke tare da mace ba sai dan cika wasu burika nasu, sai dai matan basa ganewa domin ruɗin Duniya rufe musu ido yake yi. Nayi farin ciki da ke kika fahimci hakan.""Wannan gaskiya kika faɗa 'yar uwa domin kaso 80 na samarin yanzu ba tsakani da Allah suke tare da Budurwa ba sai dan cika wani buri nasu cikin su kuwa harda wannan tur da Irin wannan Rayuwar."Tayi maganar tana nuni da saurayin nata cike da tsanarsa domin yau ya nuna ma ta Asalin kalansa."Toh tun da an gama komai kowa sai ya watse ko. Su Labib ɗan gayu harda Kai ne a hangame baki to a gyara dai kafin ƙuda ya shige."Budurwar da ta kira da Teema tayi maganar tana kallon gaba ɗaya mutanen wurin da suka tattaru ana kallon abin da ke faruwa. Sannan ta hau Bicycle ɗin kana ta fara tafiya da su suka bar wurin."HHhH Lallai ma wannan Teema ko yaushe bakin ta ya buɗe da zata dubeka ta gaya maka magana, amma fa kaima ka bani Dariya Kawai daga ganin wannan kyakyawar Baturiyar Budurwar da tazo Garin nan sai ka nema ka kasa controlling kanka kodai.."Katsesa ya yi da faɗin."Kodai Mene karma ka fara wannan tunanin domin kafi kowa sanin Hazel ita ce kaɗai a zuciyar Labib ko dai ka manta ne?."Ɓoye dariya Abokin nasa ya yi suna ci gaba da tafiya ya ce."A'a kam ban manta ba Aikuwa ga ta can ma mutuniyar taka sai ka ƙari sa kuyi irin gaisuwar taku da kuka saba Kullum."Ya yi maganar yana masa nuni da ita da take tsaye daga can cikin jama'a 'yan kallo, ganin kowa ya watse ne, yasa ta gyara Book's ɗin dake a hannunta ta rungume su a chest nata sannan ta fara tafiya a hankali cikin nutsuwa kamar yadda ta saba tana kar...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.