FreeArewaPen original
A WANI COMPANY
- 1views
- 33chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Arewabooks@cutiemeerat
Sample · 1
# SQUAD 2024A WANI COMPANY BYHAUWAU OMAR CUTIE MEEYRATMARUBUCIYAR A'ISHA LABIBA. AND NOWA WANI COMPANY.MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS *"Wannan labarin mallakin mai shine kawai ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ta kowace sigaba idan kuma hakan ta faru bazan kyale ba"**BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM**Duk kan yabo da godiya sun ta* *bata ga Allah Subhanahu wata'ala* *mamalakin sammai da ƙasai* *Allah kai daɗin tsira a bisa shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama tsira da aminci su tabata a garesa da Ahalinsa da sahabbansa dama wainda suka bisa a tafarki mai kyau daga yanzu har izuwa ranar alƙiyamaEp one.Yau ta kama Ranar lahadi a yau kuma duk kanin wasu ma'aikata ke hutawa a gidajensuHadarine Sosai ya haɗoGarin yayi baƙi wata irin iskace ke kaɗawa mai haɗe da ledoji da ƙura mai baɗe idanun mutane. Gajimare ta yi wani irin baƙi tsawa ake mai haɗe da walƙiya yanayin yadda garin yayi duhu na iya tabbatar maka dacewa ruwa na iya sauka a kowane irin lokaci.tsugune ta ke a jikin bishiya ta kifa kanta a kan gwiwarta duk da wannan hadarin da ya haɗo hakan bai sa taji tsoro ba wani bawan Allah ne yayo gurin, da sauri ya karasa ya na tambayarta lafiya?Ɗago kai ta yi ta kallesa da rinanin idanunta wanda suka yi wani mugun ja daga gani kasan ba ƙaramin kuka ta yi ba Woww Masha Allah tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yayi Wannan halita farace tass gashinta ya kwanta har gadan bayanta gawani saje da ya kwanta a gefe-gefe n fuskarta tana da ɗan ƙaramin baki sai hancinta dogo mai tsini masha Allah yarinya ta haɗu matuƙa ta na da tsayi sosai ga wani uban Sharpe da ya fita a jikinta. Tashi ta yi bata ce masa komai ba ta fara tafiya jijiga kansa kawai yayi yai gaba abinsa ya na tinanin ko me yasa yarinya kamar wannan tafito tsakiyar layi tana kuka duk da wannan uban hadarin da ya haɗo wanda a koda yaushe ruwa zai iya zuba.. Tafiya take a hankali kasan cewar ita ba ma'abociyar sauri bace wata tsawa da akayi yasa tai saurin rintse idanunta tana toshe kunnanta sunan Allah ta ke ambata cikin yar ƙaramar Muryarta wadda idan ba kana kusa ba bazaka taɓa jin abun da ta ke faɗa ba,ta kai kusan 5 minute a haka kafin a hankali ta buɗe idanun na ta kamar mai tsoron wani abu Ruwane ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya yayin da ruwan ke zuba tare da wata tsawa da ke tashi cigaba da tafiya ta yi a hankali duk da ta'taka abu a ƙafarta hakan baisa ta tsaya ba harta ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidan nasu dake anguwar lokogoma.Da sauri ta ƙarasa cikin ɗakin tana haki faɗawa kan wata yar taɓarma tayi dake shimfiɗe a tsakar ɗakin a hankali kuma jikinta ya fara wani irin rawa tana fitar da wani irin wahalala numfashi Gaba ɗaya ta fita hayyacinta babu abin da take ambata sai Mamah Mamah washh Allah na mutuwa zanyi shine kaɗai a...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.