FreeArewaPen original
FARAR TASKA
- 1views
- 95chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Uwa Manazarciya Marubuciya Ƴar kasuwa Chocolate addict 🍫 Bookworm📗 Introvert 😚
Sample · 1
Gudu gudu, sauri sauri haka take haɗa tafiyar ta, tana yi tana waigawa bayanta tana hango yanda yara suke biye dashi suna mashi waqa, wasu ma riƙe da babbar rigarsa suna jansa sai tangaɗi yake kamar zai faɗi ƙasa, tana shiga gida ta nufi inda mahafiyarta ke ƙoƙarin kunna gawayi domin ta ɗora girki, ta ajiye mata markaɗen gari a gabanta da sauri ta juya zata fice tace " Saurin me kike haka, ina zaki je, ba yanzu kika shigo ba? ta shagwabe fuska kamar zata yi kuka cikin damuwa da bacin rai, tace " Innar mu yanzu na hango yara suna bibiyar baba da waqa ina tunanin yaje ya sha wannan abin da bakya so yana sha a kullum" batare da tayi magana ba taja dogon tsaki ta juya tana cigaba da gyara wuta, ganin haka yasa yarinyar yar kimamin shekara goma da haihuwa fita da sauri ta nufi inda mahaifin su yake, yaran suna hangota suka soma gudu suna faɗin " ga Meelah ta zo kowa ya gudu kada ta fasa masa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.