Free chapter · Read without an account
LAIFIN ƁOYE Chapter 4
by Aysha Ɗansabo · LAIFIN ƁOYE
*LAIFIN ƁOYE* Arewabook@ayshadansabo
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
Free page's
Chapter 4
Kiran sunansa yayi a hankali,"Shureimm." Yadda ya kirasa da suna Shureim ɗin shi ya sanya Shushu sanin cewa tabbas Daddyn magana mai muhimmanci zaiyi dashi,hakan ya sanya shi amsawa da,"Na'am Daddy."Daddy ya cigaba da faɗin"Shureim ina so ka bani hankalinka da nutsuwarka nan,abinda yasa na zaɓi wannan lokacin sabida inaso abinda za mu tattauna ya zama sirri,ina nufin ko Mummynku ban yarda taji wannan sirrin nawa ba,nasani a yanzu kana jin tsanata Shureim,kana ji inama ba nine mahaifinka ba a yanzu,domin duk ɗa mai tarbiyya irinka bazai so ace na zama uba a garesa ba."Abbah ya ɗan dakata da kalamansa muryarsa na rawa hawaye masu zafi na sauka a saman kafaɗun Shureim,wanda har zuwa lokacin idanunsa a runtse suke.Jin ɗigar hawayen ya sanya shi buɗe idanunsa yana kallon mahaifinsa na zubda ruwan hawaye,kallonsa yayi tare da sauka ƙasa ya kwantar da kanshi a saman ƙafafun Daddyn.A hankali ya furta,"Daddy ina jinka."Daddyn ma ƙasa ya sauka ya zauna Shureim ya zuba masa idanunsa yana sauraren yaji mene ne Daddyn yazo dashi a daidai wannan lokacin? Dad ɗin ya fara magana yana faɗin,"Shureim tunda aka haifeka ka taso ka ganka cikin arziƙi ne baka taɓa sanin miye babu ba,duk abinda ka nema kana samu har zuwa lokacin daka zama mutum,na baka dukkanin kulawa tare da gata,nayi ƙoƙaringanin na inganta tarbiyarka,cikin hukuncin Allah ka zamo cikin Yaron da duk wani uba nagari zaiyi alfaharin kasancewarka matsayin ɗa a garesa." Dad ɗin ya dakata yana kallon yadda Shureim yayi ƙasa da kansa yana saurarensa.Cikin sake kwantar da murya Dad ɗin ya cigaba da faɗin,"Shureim kamar yadda ka taso ka sani ni ɗin hamshaƙin ɗan kwangila ne kuma ɗan kasuwa,da waɗannan sana'a biyu na tara duk wani arziƙi daka sani Shureim,tun kafin na auri Kubrah ina cikin mazajen da za a lissafasu cikin masu rufin asiri sosai,wannan mummunar harka da muka fara ta samo asali ne wani lokaci da muka nemi wata kwangila mai tsoka ni da abokina Alhaji Adamu sai aka haɗamu da wani minister,a matsayinmu na manyan ƴan kwangila bamu sha wahalar ganawa dashi ba,sai dai koda muka sami ganinsa ya bamu address ɗin guesthouse ɗinsa ne,inda a wata ranar Sunday bani mancewa misalin 4pm na yamma muka samesa ni da Adamu a guesthouse ɗin." Alhaji Shu'aib ya sake dakatawa yana kallon yadda Shushu ya ɗago ya zube masa idanunsa da suka sauya sosai yana saurarensa,ya cigaba da faɗin,"Koda muka isa akai mana iso zuwa cikin falon,abin mamaki mun samesa ne tare da ƴan mata kusan guda uku,baya ga wata gogaggiyar Hajiya wacce alamu ya nuna cewa tare da waɗannan ƴan matan suke,ganinmu yasa ya sallami wannan Hajiyar tare da waɗannan ƴan matan ya basu umurnin shigewa ciki,yanayin shigarsu da tafiyarsu kaɗai zai sheda maka cewa cikakkun ƴan bariki ne,bayan shigewarsu ne minister ya dubemu bayan mun gaisa cikin aminci da mutunci,muka sake shaida masa mune dai masu neman a bamu kwangilolin da sanata ya shaida masa,daga lokacin ya fara shaida mana tsarinsu shi da sanata, tsarin kuma shine indai muna son wannan kwangila dole ne mu cika sharuɗan da za su bamu..." Dad ya sake dakatawa da kalamansa yana sake duban Shushu da duk ya zaƙu yaji wasu sharuɗa aka kafa musu? Dad ɗin ya ɗan lumshe idanunsa tare da sake buɗesu a saman kyakykyawar fuskar Shureim Aji ya cigaba da faɗin,"Sharaɗi na farko shine kodai suyi lalata damu sannan ayi signing wannan kwangila tazo garemu,ko kuma mu amince zamu dinga kawo musu abokan harka maza da mata domin su riƙa hutawa dasu,idan kuma har bamu amince da hakan ba to sai dai mu haƙura da wannan kwangila,wanda hakan na nufin za mu yi asarar riba ta miliyoyin kuɗaɗe ba kaɗan ba,nan take na shaida ma minister cewa bamu aminta da waɗannan sharuɗa ba,yayi dariya sosai tare da fara kashe mana kashedin daya sanya muka aminta dashi da kuma dukkanin abinda ya buƙata,domin ya shaida mana cewa tunda ya riga ya fallasa mana asirinsu,to dole ne mu zaɓa abu guda ɗaya cikin abubuwa guda biyu daya lissafo mana,bijirewa hakan kuwa yana nufin toshewar duk wata kafa da za mu iya samun kwangila koda ko ta taroce,hakan ne ya ɗaga hankalinmu ƙwarai da gaske,ba tare da dogon nazari ba muka aminta da ƙudirinsa na 2 wato mu dinga kawo musu mata da kuma matasa suna holewa dasu."Abbah ya kai aya yana mai kasa duban Shureim.Cikin tsananin tashin hankali Shushu ya kalli mahaifinsa,tuni har ya fara ji kansa na sarawa da matsanancin ciwo."Wannan wace iriyar ƙazamar sana'ace?"Ya tambayi kansa zuciyarsa na sake rufewa da tsananin shiga tashin hankali.Alhaji Shu'aib ne ya katse tunanin Shureim ta hanyar cigaba da faɗin,"Shureim bamu baro gurin minister ba saida muka tabbatar masa da cewa mun amince da ƙudirinsa,Adamu shine ya sake ba minister tabbacin cewa a cikin satin zai ga manyan kaya,wanda nasan a lokuta da dama kana ji idan ina waya ina yawan cewa an sami manyan kaya,to ba kaya nake nufi irin na business ɗina daka sani ba,a lokuta da dama manyan kayan da nake faɗi mata ne da kuma matasa,tun daga lokacin muka zama tamkar masu safaran ƴan mata da matasa muna rabasu hotel-hotel ga manyan ƙasarnan,mu kuma muna samun manyan kuɗaɗe da kwangiloli naban mamaki,kafin kace haka mun zama manyan kawalai kuɗi kota ina muke samu duk wata kwangila da za ta fito daga state ko federal mune kan gaba,tunda muka fara wannan harkan Shureim ban taɓa sama zuciyata zan iya lalata da wata 'ya mace ba,hasalima idan aka kawosu ba kasafai nakan buƙaci ganinsu ba,sai dai mu bada umurni a rabasu zuwa hotels bayan mun tabbatar da kayayyakin sun wanku za ku ma a yaba dasu matuƙa,Alhaji Adamu shine mutumin da azal ya fara faɗawa kansa watarana an kawo mana manyan kaya masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali,waɗanda idan mutum bai yi da gaske ba to tabbas shaiɗan zai iyayin nasara a kansa,lokacin da aka basu kaya domin gyarasu kamar yadda akeyi kafin ayi posting ma senatocinmu da ministers ne shaiɗan yayi nasara akansa har ya keta mutuncin ɗaya daga ciki wacce take sabuwace ba a taba komi da ita ba." Ya sake dakatawa yana jin ɗaci da kunyar idanun Shushu da yayi masa ƙuri yana saurarensa.Cikin ƙarfin hali ya cigaba da faɗin,"Kasancewar yawancin kayan da ake buƙata sun fi son sabbi fil aledarsu ne,tunda ga lokacin Adamu ya fara harka mata,duk kayan da za a kawo sai ya ɗauki ɗaya a ciki,sai dai bai taɓa sha'awar neman jinsinmu ba sai dai mata,sannu a hankali kasancewarsa abokin tafiya kuma amini a gareni yau da gobe yana kwaɗaitar dani irin daɗin zumar da yake lasa yasa tun ina masa faɗa har na daina nima na fara sha'awar nima in lashi garɗin zuman da yake kwaɗaitar dani,wata rana nima an kawo wasu ƴan mata kyawawa amma irin gogaggun Yarannan ne da idanunsu ya buɗe da harkar sosai,ɗaya daga cikinsu da kanta tayi sha'awar kasancewa dani,Alhaji Adam ta tunkara da maganar domin shine nasu,a lokacin ya sanar da ita cewa nisam bana wannan hakar,amma da yake ance mace shaiɗaniya ce hakan yasa suka sakamun magani a cikin lemu,a wannan ranar komi ya fara a ranar na ƙara lasar zumar wata ƴa mace wacce ba Kubrah ba,yanayin data tafi dani ya ƙara jefani cikin wani hali,daga ranar sheɗan ya cigaba da jan ragamarmu da zaran an kawo mata saimun huta dasu kafin mu aikasu inda ya kamata,sosai suke bamu haɗin kai kasancewarmu masu arziƙi komi najin daɗin rayuwa muna tanadar musu,bamu taɓa sha'awar kusantar jinsinmu na maza ba sam,sai dai mu nemosu mu rabasu gasu minister da manyan ƙasa,ko kaɗan ban taɓa buɗe wata ƙofa ko kafar da Kubrah za ta gane ina mu'amala da wasu mata ba,sai dai ance rana dubu ta ɓarawo ne rana daya tak na mai kaya,sai gashi tsayin shekaru muna sheƙe ayarmu tare da da kawar da hankalin mutane da muke da harkar business ɗinmu shigo da motoci da kayan gina-gine,amma kuma a ɓoye harkar da muke gudanarwa shi yafi komi kawo mana arziƙi,wallahi Shureim wannan ƙasar tamu lalacewarta ya wuce inda kake tunani,manyanmu sun ɓaci ta yadda ko aiki kake neman ƙarin girma ko wani muƙami mai tsoka sai kabi hanyar lalata ko fasadi kafin su baka dama kakai inda kakeso,sai dai wanda Allah ya tsallakar da kuma wanda bai biyewa son zuciya da kuma kwaɗayin tara dukiya ba,Shureim ka yafemin ka kuma rufe sirrina,baniso Kubrah taji wannan mummunar labarin,idan kai mini hakan tabbas zan san cewa kai cikakken ɗane nagari a gareni,kuma daga yau na yima alƙawarin cewa na daina wannan harkar,zan rungumi kasuwancina zan haƙura da naiman duk wata ƙazamar kwangila matukar saina sabi Allah kona kauce hanya zan sameta."Alhaji Shu'aib ya ƙare kalamansa yana kallon yadda Shureim ke kuka sosai.
Sosai Shushu ke kuka tamkar wani ƙaramin Yaro,da kyar ya iya duban Daddynsa kafin ya tsaida kuma ya fara faɗin,"Dady haƙiƙa kun aikata mafi munin fasadi a doran ƙasa,kun zaɓi gwama dukiyarku ta halas da ƙazantacciyar dukiya,a yau ina ƙyamatar duk wani abu daka mallakamini koka ciyar dani da kuɗin ƙazaman kwangilolin da kuke samu,meyasa kuka biyema son zuciyoyinku da neman tara ɗinbin dukiya ta hanyar kauce hanya? Dad a yau ina jin nadamar kasancewata jininka,ina ji inama na fito ne a cikin tsatson talakawa waɗanda suke nema da ƙyar sannan suci su sha,da irin wannan ƙazamar dukiyar daka haɗa halas da haram kana ciyar damu ka shayar damu,meyasa Daddy ka zaɓi aikata LAIFUKAN ƁOYE don kawai ka tara arziƙi?Daddy ina mai bakin cikin kasancewata jininka,kuma kasani cewa wannan abinda kuke aikatawa mu za ku barma mummunar tabon da bazai taɓa gogewa ba,idan ni ban tona asirrinka ba tabbas Allah zai tona Daddy."Shureim ya ƙare kalamansa yana cigaba da kuka mai matuƙar motsa zuciyar mai saurarensa.Alhaji Shu'aib gabaki ɗaya ya gama muzanta a gaban ɗan nasa,ji yake tamkar ya maida hannun agogo baya ko ya kasance cewa komi cikin mafarki yake kasancewa ba a gaske bane.Sai dai muryar Shureim ne ya dawo dashi cikin hayyacinsa time ɗin da yake cigaba da faɗin,"Dady inaso nayi maka nasiha daka sadaukar da duk wata dukiya daka tarata ta wannan hanyar,kayi gaggawar sadaukar dasu domin tsarkake dukiyarka ta halas,ka rungumi dukiyarka ta halas ka cigaba da juyata koda ko hakan na nufin samun karayar arziƙi ne a gareka,duk wata ƙaddara da kasan ka bani a cikin wannan ƙazamar dukiyar daka tara ina son ka janyeta daga gareni Daddy."Yana kaiwa nan yayi gaggawar tashi ya nufi bedroom ɗinsa,yana mai rufo ƙofar da ƙarfin gaske ya faɗa bisa bed yana sakin kuka sosai.Yasan cewa yana son Mahaifinsa,amma ya zama dole ya juya masa baya,hakan ne kaɗai zaisa ya saduda ya kuma tuba daga wannan mummunar fasadin da suke aikatawa a doron ƙasa.
Cike da mutuwar jiki tare da damuwa matuƙa Daddy ya miƙe ya baro part ɗin Shureim ɗin,yana mai nadamar duk abinda ya aikata a rayuwarsa.Gashi farin cikinsa na nema ya ruguje domin baya ji zai iya jure juya bayan Shushu daga garesa,yasan cewa tabbas barin wannan harkar itace kaɗai rufin asirinsa matuƙar yana buƙatar son cigaba da ganin ƙaunarsa a cikin idanun ɗansa saɓanin ƙiyayyarsa daya fara gani a yanzu kwance cikin idanun Shushun.......✍🏻