Free chapter 路 Read without an account
TSORON DA BAI MUTU BA
by Secretwriter 路 ZUNUBIN UBA
馃挐ZUNUBIN UBA馃挐
Novel by secretwriter 馃挐
Sarki Saif yana zaune a kujerar baya ta motar da ke fita da shi daga harabar asibitin, idanunsa suna lumshe yayin da yake jin ra蓷adin raunukan jikinsa. Karan wayar hannun Zahir dake zaune a mazaunin direba ya ratsa shurun motar. Zahir ya duba wayar sannan ya kalli madubin tsakiya don satar kallon Saif. "Oga... Lamarin ya sauya salo. Yanzu nan sa茩on ya zo min cewa Judge Luca ba ya 茩asar nan gaba 蓷aya, ya fita zuwa wani taron sirri na shari'a. Kuma abin da mamaki, duk da na riga na samu appointment 蓷in zama da shi, amma an soke shi."
Saif bai bu蓷e idanunsa ba, sai dai wani murmushi mai cike da ha蓷ari ya gitta a fuskarsa. "Hmmm... A.A Rumfa ya fara ta蓳a sassan da bai kamata ba kenan. Mu koma cikin asibitin."
A can babban dandalin cin abinci na makarantar su Noor (Cafeteria), surutu da hayaniyar 蓷alibai sun cika wajen. Noor ce ta shigo cikin takun isa, tana raba idanu har sai da ta hango Faris Al-Kaseem zaune a can kusurwar tebur na 茩arshe shi ka蓷ai. Cikin natsuwa da sanyin jiki ta taka har zuwa gabansa.
"Sannu dai... Sunana Noor," ta fa蓷a tana tsaye tare da gyara hular hijabinta na alfarma.
Faris ya 蓷ago kai ya kalle ta da idanuwansa, ya gyada kansa cikin ladabi. "Ehh... Na gane ki, ai class 蓷inmu 蓷aya." Noor ta kalli saman teburin, ta ga biscuit na naira hamsin da robar lemo dake gabansa. Nan da nan ta murtuke fuska, ta kalli mai sayar da abincin wajen tare da 蓷aga murya cike da steeze. "Kai! Baya cikin matsayi na da aji na ace 蓷alibin ajinmu yana cin wannan abun a gabana. Kawo masa dukkan mafi tsadan abinci da lemon da kuke da shi a wajen nan, yanzu 蓷innan zan biya komai!"
Faris ya zuba mata idanu cikin tsananin mamaki da rashin fahimtar irin wannan nuna isa, amma bai ce uffan ba har aka kawo ha蓷a蓷蓷en abincin, suka zauna suka ci. Bayan sun gama, Faris ya mi茩e ya yi mata sallama ya tafi aji.
Kafin ma ya 蓳ace, 茩awayenta Aliya da Nahad suka rugo da gudu suka dawo kusa da ita, fuskokinsu cike da tsananin mamaki da son tsegumi. Nahad ta dafe 茩irji, "Yanzu Noor, don Allah kinsan nawa kika kashe a kan abincin wannan yaron yanzu nan kuwa? Wlh ku蓷in sun yi yawa!"
Noor ta ta蓳e baki cikin sha茩waba ta 茩wace jakarta, "Ban sani ba, kuma hakan bai dame ni ba. Amma dai na sani cewa kashe ku蓷i a kan wanda kake so... ai ba laifi ba ne gaba 蓷aya!"
Aliya ta turo baki, ta harare ta. "Tunda ba ku蓷inki ba ne da kika samu da kanki ba, shi yasa zaki ce ba laifi ba ne! Amma ta yaya zai kasance mace ce zata rin茩a kashe wa namiji ku蓷i a cikin makarantar nan? Ina ajinki ya tafi?"
Noor ta tsaya ta kalle su 蓷aya bayan 蓷aya, ta sanya hannu a kwankwaso cikin takun isa da barkwanci. "Ehh! Naji ba ku蓷ina ba ne, amma kuma ina da wa蓷anda suke bani ku蓷in, kuma a shirye suke su narkar min da dukiya a kowane lokaci! Idan har su ba su kashe min ba, wa kuke so ya kashe min? Nima kuma idan ban kashe wa Faris ba... wa kuke tunanin zai kashe masa a makarantar nan?" Ta fa蓷a tana musu fari da idanu, wanda ya sanya Nahad da Aliya ha蓷a baki wajen sakin salati saboda halin Noor na nuna iko da girman kai na ban dariya.
A can harabar asibitin kuma, Barrister Jannat ce ke takawa da sauri tana shirin fita daga asibitin bayan ta bar ofishin Nazra. Ba zato ba tsammani, tana daidai wani lungu na 蓷akin jiyya, ta ji an janyo ta da 茩arfi ta baya. Kafin ta sami damar yin ihu, aka sanya mata takunkumin rufe fuska na asibiti (Face Mask) wanda ke 蓷auke da wani irin magani na sanyaya jiki.
Gaba 蓷aya idanunta suka fara dishi-dishi.mutanen da ta gani da 茩yar ta cikin duhun idanunta... mutane ne daban sanye da fararen suit na alfarma, har da mata a cikinsu. Abin da ya fi tsoratar da ita shi ne, hular kowannensu tana 蓷auke da zanen Zaki na zinari a jiki. Suka rin茩a tafiya da ita cikin wani irin salo na tsari da kariya, suna kare ta ka蓷an-ka蓷an daga kowane 蓳angare kamar wata shugabar 茩asa. Duk wanda suka gani da ba茩aken kaya zai zo wucewa ta layin, sai su canza mata hanya cikin dabara.
Haka aka shigar da ita 蓷akin tiyata (Theater Room), aka cire mata suturarta aka saka mata kayan 蓷akin tiyata na kore. Jannat tana ta fizge-fizge tana kuka da muryar raki, amma babu tausayi aka danna mata allurar bacci mai 茩arfi a gwiwar hannunta. Cikin da茩i茩o茩i kalilan, duhu ya gauraye komai, bacci ya yi awon gaba da ita.
Bayan wasu sa'o'i, Jannat ta fara bu蓷e idanunta a hankali. Hasken rana ya dake ta, sai ta tsinci kanta a zaune a kan kujerar guragu (Wheelchair) daidai 茩ofar fita ta asibitin. Abin da ta gani ya sanya jikinta rawa da tsoro; fararen motoci na alfarma masu sulke (Bulletproof) sun zagaye su, dukkan ma'aikatan tsaron dake tsaye sanye da fararen kaya da gilashi sun bada baya suna jiran umarni.
A can gida kuwa, mahaifiyarsu Jannat Hajiya Jawahir ce ke ta kai-da-kawowa a tsakiyar falon gidan, fuskarta 蓷auke da tsananin damuwa. Larai, mai taya ta aikin gida, ta leko daga 蓷akin girki tana kallon mahaifiyar tasu. "Hajiya lafiya kuwa? Tun dazun na ganki kin kasa zama guri guda."
Hajiya Jawahir ta ja da baya ta dafe 茩irjinta, "Larai... Har yanzu Jannat ba ta dawo ba fa! Kuma kinsan halinta, ba ta taba kaiwa wannan lokacin ba tare da ta shaida min ba. Na kira wayarta sau babu adadi amma a kashe take gaba 蓷aya. Har Nazra na kira ita ma ban same ta ba. Ban san me ke faruwa ba, na san ba halinta ba ne kashe waya."
A daidai wannan lokacin a asibiti, Jannat ta yi amfani da dukkan ragowar 茩arfinta ta mi茩e tsaye daga kan kujerar guragun, duk da yadda 茩afafunta ke rawa saboda tasirin allurar baccin da bai sake ta ba gaba 蓷aya.
Ta jefa idanuwanta cikin mutanen, sai ta hango Sarki Saif tsaye, sanye da ba茩aken kaya, yana kallonta cikin natsuwa. Jannat ta tako da 茩yar har zuwa gabansa, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta. "Meye hakan?!" Ta fa蓷a cikin muryar kuka mai ratsa zuciya. "Ko saboda na mare ka 蓷azun ne ya sanya kake son nuna min iko ta hanyar hukunta ni da kisa? Me na yi maka?"
Saif ya matso kusa da ita ka蓷an, fuskarsa babu alamar wasa. "Bani da niyyar kashe ki, Barrister Jannat. Taimakonki nake son yi a halin yanzu. Yau da a ce ban bada umarnin a baki wannan tsauraran kariyar ba... da tuni makiya sun riga sun kawo 茩arshen rayuwarki a cikin asibitin nan."
Jannat ta saki wata dariyar takaici da daci, ta girgiza kanta tana goge hawayenta. "Na mutu kuma? 茦arya kake yi! Kai ne ma kake son kashe ni da kanka!"
Saif ya 茩ara matsowa kusa da ita sosai, har tana iya juyo dumin numfashinsa mai sanya fargaba. "Nan da kwana biyu ki shirya... zamu je gaban kotu domin shigar da wannan babban 茩arar. Amma ki kwantar da hankalinki, ba shari'ar za a fara yi kai tsaye ba. Akwai wani babban aiki na sirri da zamu fara gudanarwa kafin mu taka kofofin kotun."
Jannat ta ja da baya da gudu, tana kuka sosai cikin tsananin rauni da firgici na baya. "Ba zan yi ba! Wallahi bani da wani buri ko sha'awa a kan wannan shari'ar taka! Ka tafi ka nemi wata lauyar amma ba ni ba!"
Saif ya zuba mata idanu, muryarsa ta koma 茩asa-茩asa. "Haba Barrister Jann... Dole ne fa zaki yi min wannan aikin."
Jannat ta dakatar da shi cikin wata irin muryar tsawa mai cike da kuka da ra蓷adi dake fita daga can 茩asan ranta. "Koda kuwa zaka tilasta min, wallahi na tsane ka! Iya yau ka蓷ai... dukkan wahalar da mutanenka suka bani ba zan taba yafe maka ba! Can you imagine... har 蓷akin tiyata (Theater Room) suka shigar da ni da 茩arfi! Na tsani ashibiti a rayuwata! Idan kaga na shiga asibiti, to rashin mafita ce ta 茩arshe ke kaini! Ba na son a saka min kayan ashibiti bare har na tsinci kaina a kan gadon asibiti... Amma yau saboda kai, ba ma gadon ashibiti na hau ba, a kan gadon tiyata na farka!" Ta fa蓷a tana dur茩ushewa a 茩asa, tana kuka mai ban tausayi.
Saif yana kallonta, nan da nan tunani ya ziyarce shi. Ya fahimci cewa har cikin zuciyarta take fa蓷ar wannan maganar, akwai wani mummunan abu na baya (trauma) da ya taba faruwa da ita a asibiti ko a 蓷akin tiyata da ya sanya take tsanar kowane tsarin asibiti a rayuwarta.
Wani sanyayyan murmushi ya sake yi, ya matso kusa da ita sosai har tana iya jin bugun zuciyarsa. "Barrister Jann... Tun kafin ma mu fara ainihin aikin namu na gaskiya, har kin riga kin tsane ni haka? Ba kiyi gaggawa da yawa ba kuwa?"
Jannat ta 蓷ago da sauri, ta tura 茩irjinsa da dukkan 茩arfinta. "Ka fita daga rayuwata, 蓷an iska kawai!" Ta fizge jakar hannunta dake ri茩e a hannun Rayyan, ta juya da sauri ta shiga motarta ta bar harabar wajen da gudu.
Saif ya bi bayanta da kallo na wasu da茩i茩o茩i, sannan ya juyo ya kalli Rayyan, ransa a ha蓷e. "A tsara mata kariya mafi inganci da ta dace da rayuwarta... amma kar a kuskura a bari ta gane hakan."
馃挐ZUNUBIN UBA 馃挐
Novel by secretwriter 馃挐