Free chapter · Read without an account
Chapter 3
INUWAR JIYA
Ummulkhair S Panisau
Rania baccinta rabi da rabi ne. Tunani ne fal cikin ranta game da saƙon da aka aiko mata. "Kada ki fara da Captain Zayd."
Da asuba ta tashi tun kan alarm ɗinta ya tashe ta. Sai da tayi sallah sanann tayi wanka tayi brush ta shirya cikin atampa doguwar riga ta samu wani mini hijab fari ta ɗora a kan kayan jikin ta.
Ta sake tozali da hoton jiya ta shiga tunanin cewa ba ita kaɗai ba ce ke son bankaɗo sirrin da aka ɓoye ba amma wasu basa son ta sani why? Ta tambayi kanta.
Ta saka hoton cikin littafin ta,sannan ta ajiye cikin jakarta.
Ta saƙala jakarta ta sauka kasan bene harbar hotel ɗin ta nufa daidai lokacin da Hamza ya tsaya da mota.
Tana ganin shi ta ƙarasa gaban shi ya buɗe mata motar ta zagaya ta shiga ciki.
"Tun kan na kira ki har kin ji a jikin ki saurin me kike ne?"
"Bani da lokacin ɓatawa Hamza jinkiri ba namu ba ne."
"Na sani."
"Mu je." Ta faɗa haɗe da ɗaure fuska.
Bayan sun yi dogon tafiya sai ya tambaye ta.
"Kin shirya haɗuwa da tsohon ma'aikacin?"
"Eh."
Rania ta juya ta kalle shi.
"Da gaske?"
"Eh,amma akwai matsala."
"Ya daina magana da manema labarai."
Rania tayi murmuhshi.
"Shi yasa muke zuwa wurinsa ai."
Hamza ya girgiza kai.
"Ba kya gajiya."
"Idan gaskiya ta gaji ni Rania ban gaji ba."
Hamza ya yi dariya.
"Allah Ya taimake shi."
Rania ta koma kallon titi.
Tsaunuka,iska mai sanyi,gidaje da tsofaffin tituna. Wani abu game da garin ya bata wani irin yanayi d ba za ta iya fassara shi ba.
Baƙo ne a gare ta. Amma duk da haka...kamar akwai wani abu a cikinsa da yake jiran ta.
Wani tsohon gida suka isa mai nisa. Yankin babu hayaniya ga shiru da nutsuwa.
"Nan ne gidan." Hamza ya faɗa yana kashe engine motar.
Ta sauke numfashi. Ta ɗauki jakar ta.
"Sunan sa fa?"
"Idris."
"Meye alaƙarsa da Flight 217"
"Ya kasance cikin ma'aikatan da suka kula da jiragen."
Rania ta gyara zaman hijab ɗin ta.
Hamza ya buga ƙofa.
Bayan wani dan lokaci,wani dattijo ya buɗe ƙofar.
Ya kalli Hamza.
"Waye?"
"Hamza Bello."
"Kai ne Idris?"
"Ni ne."
Hamza ya nuna Rania.
"Wannan kuma ita ce..."
"Na san wacce ita ku shigo ciki."
Ya faɗa yana basu hanya.
Rania da Hamza suka cika da mamakin sanin da yace ya yiwa Rania duk da ba wani abin mamaki ba ne kasancewarta Yar jaridar da sunan ta ya yi ƙaura.
Lokacin da suka shiga ciki.Ta lura da wani tsohon hoto da aka rataye a bangon falon. Hoto ne na wasu ma'aikatan jirgi . Ta tsaya idanunta suka tsaya a kan wani mutum guda ɗaya a jikin hoton. Wannan ne karo na biyu da hoton ya bayyana a kan idonta.
Dattijon da ke gabanta ya lura da yadda take kallon hoton.
"Kin san shi ne?"
Rania ta girgiza kai tace "A'a."
Ya yi shiru. A hankali yace "Ya kamata ki bar wanann binciken."
Rania ta kalle shi da sauri tace "Me yasa?"
Bai bata amsa ba.
Ya juya ya nufi kitchen ya dawo da cup ɗin tea a hannu guda biyu.
"Ku zauna ga tea na yi tsammanin baku karya ba."
"Akwai abubuwan da suka faru shekarun baya da suka shuɗe."
Ta kafa masa idanu y kalle ta yace "Zasu fi kyau a rufe a matsayin matattu."
Rania ta matso kusa da shi.
"Amma idan ba su mutu ba fa?"
Dattijon ya juya ya kalle ta. A cikin idanunsa akwai tsoron da Rania bata taɓa gani a idon wanda take hira da shi ba.
"Baki san abinda kike nema ba."
Rania ta rufe littafin ta.
"Shi yasa na zo."
Shiru ya ratsa falon.
Ya samu wuri ya zauna.
"To. Ina jin ki."
Raina ta gyara zamanta, ta kafa kai ta shanye shayin nan tas.
Ta buɗe littafin rubutun ta.
Ta daga biro ta soma rubutu.
"Tambaya ta farko. Me ya faru da Flight 217 a wancan daren bayan tashinsa?"
Ya kalli ƙasa na tsawon sakanni, sanann yace "Ba jirgin ba ne matsalar."
Rania ta tsaya da rubutu tace "Me kake nufi?"
Ya numfasa.
"Mutanen da suke bayan jirgin ne matsalar."
Rania ta kalli Hamza.
Hamza ya kalli dattijon.
Idris ya ƙara da cewa.
"Idan kina son sanin gaskiyar ki fara da mutumin da ya ƙi sanya hannu."
Rania ta tsaya cak.
"Waye mutumin da ya ƙi sanya hannu?"
"Captain Zayd."
Rania ta lumshe idanu na ɗan lokaci.
Ashe sunan da ta fara gani a takardun ba kawai sunan tsohon matuƙin jirgi ba ne.Amma har yanzu ba ta san dalilin da ya sa wannan sunan zai zama farkon hanyar zuwa gaskiyar da take nema ba.
Ta cigaba da rubutu.
"Captain Zayd ya ƙi sanya hannu a kan me?"
Ya miƙa hannu ya ɗauki gilashin da ke gaban sa,ya sha ruwa kadan.
"Wannan wata tambaya ce da na dauki shekaru ina son mantawa da ita."
"Amma ba ka manta ba?"
"A'a."
Rania ta jingina da kujera.
"Me ya faru?"
Dattijon ya yi shiru na ɗan lokaci.
"Ranar kafin jirgin ya tashi, an kawo takardar tabbatar da cewa an kammala gyarn jirgin."
"Eh."
"Amma?"
Idris ya sauke numfashi.
"Captain Zayd bai yarda da ita ba."
Rania ta fara rubutu.
"Me ya sa?"
"Ya ce akwai abin da bai kamata a bari a yi watsi da shi ba."
"Me?"
Idris ya girgiza kai.
"Ban san cikakken bayani ba."
Rania ta ɗaga kai.
"Ka kasance ma'aikacin kula da jiragen. Ta yaya ba ka sani ba?"
"Saboda ba duk abinda ke faruwa a wurin aiki ake gayawa kowa ba."
Wannan amsar ta sa Rania ta dakata.
Ta rubuta a gefen shafinta.
"To waye ya sani?"
"Ban sani ba."
"Shin Captain Zayd ya ƙi sanya hannu ne kawai?"
"Eh."
"Me ya faru bayan ya ƙi?"
Idris ya kalli ƙasa.
"Washegari aka maye gurbin wani ma'aikacin."
Idris bai amsa ba.
Rania ta maimaita.
"Wane?"
Ya ɗago kansa.
"Ni."
Rania ta yi shiru.
"An Kore ka?"
"Ba a kore ni kai tsaye ba. An ce in huta na wani lokaci."
"Ba tare da dalili ba?"
"Dalilin da suka bayar shi ne rashin biyayya."
Rania ta ɗan yi murmuhshi mara daɗi.
"Rashin biyayya?"
"Eh."
"Saboda ka goyi bayan Captain Zayd?"
Idris ya gyaɗa kai a hankali."
Rania ta rufe littafin ta.
"Bayan haka fa?"
"Bayan haka sai hatsarin ya faru."
Falon ya yi tsit.
Hamza da ke zaune ya jefa ta shi tambayar.
"Shin ka taɓa magana da hukumar bincike?"
Idris ya kalle shi.
"Na yi."
"Me suka tambaye ka?"
"Abin da na sani."
"Ka gaya musu?"
"Na gaya musu gaskiya."
Rania ta tambaya.
Ya yi murmuhshi cike da takaici.
"Ba duk gaskiyar da ke faɗa ake son ji ba."
Rania ta ji wani abu ya soki zuciyrta.
Ta buɗe littafinta ta sake rubutu.
ZAYD REFUSED TO SIGN.
IDRIS WAS REMOVED.
THEN THE CRASH HAPPENED.
Ta ɗaga kai.
"Mallam Idris,ina takardar da Captain Zayd ya ƙi sanya hannu?"
Idris ya kalle ta na dogon lokaci.
"Ban sani ba."
"Amma ka taɓa ganinta?"
"Eh."
"Ina take?"
Ya miƙe.
"Ki jira ni."
Ya shiga wani daki a bayan falon.
Rania ta kalli Hamza.
"Ka lura?"
"Da me?"
"Yana ɓoye wani abu."
Hamza ya yi murmuhshi.
"Ni ma na lura."
"Amma yana jin tsoro."
"Wataƙila yana da dalili."
Kafin Rania ta amsa, Idris ya dawo.
A hannunsa akwai wani ƙaramin akwati.
Ya zauna.
Ya buɗe shi.
Wasu tsofaffin takardu ne ya fitar da guda ɗaya.
"Ba zan baki wannan ba."
Ta ɗaga girar ta.
"Me yasa?"
"Amma zan iya bari ki gani."
Ya shimfiɗa takardar a gabanta.
Takardar ta tsufa,gafenta ya fara yin rawaya.
Rania ta karanta layukan farko.
Sai ta tsaya.
A ƙasan takardar akwai sa hannu.
Captain Zayd Sulaiman. Abinda ya ɗauki hankalinta shi ne a gefen sa hannun akwai jan alama.
REJECTED.
Rania ta kalli Idris.
"Me ya sa aka ƙi wannan takardar?"
Idris ya rufe akwatin.
"Wannan.."
Ya yi shiru.
"Shi ne abin da ban taɓa samun amsa a kansa ba."
Rania ta ɗaga kanta.
"Ki kula da wanda kike tambaya."
"Me kake nufi?"
"Saboda ba kowa ne zai amsa miki tambayar ki don gaskiya ba."
Rania ta ɗauki jakarta.
Ta san hirar ta ƙare.