KARYAYYEN ALKAWARIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

KARYAYYEN ALKAWARI

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

writer

More from @sayheba

Sample · Chapter 1

*KARYAYYEN ALƘAWARI*   (THE BROKEN COVENANT)  BYFatima Isa Manu( Sahiba )💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️(J.W.A) ‎بسم الله الرحمن الرحيم SHIMFIƊA…Kano State, Nigeria..Kano ta Dabo cigari, gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fi ka.Kanawa sun kasance masana noma da sana'o'in hannu kamar rini, jima (sarrafa fata), ƙira, da saƙa. Ciniki a lokacin ana yin sa ne ta hanyar furfure (kasuwancin canjin kaya da kaya) kafin a shigo da amfani da kuɗi. A ƙarni na 15, shahararren Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya kafa Kasuwar Kurmi. Wannan kasuwa ta zama matattarar fatake da ayarin raƙuma (Trans-Saharan Trade) daga kasashen Larabawa kamar Libya, Tunisiya, da Maroko. A zamanin Sarki Yakubu (1453), fatake Larabawa na farko daga Tripoli suka zo Kano, kuma saboda jikinsu mai haske, Kanawa suka sa musu suna "Turawa", wanda hakan ya assasa unguwar Dandalin Turawa da ke cikin birnin Kano har yau.Kafin zuwan Musulunci, tarihin Kano ya ginu ne a kan tsubbu, asiri, da tsafi. Mutumin farko da ya fara zama a Kano shi ne Barbushe, wani ƙatoton mafarauci da ke zaune a Dutsen Dala.Barbushe babban boka ne mai tsaron gunki mai suna Tsumburbura. Shi kadai ke da ikon shiga kurmin gunkin don yin tsafi da duba asiri, inda yake bayyana wa mutane abubuwan da za su faru a nan gaba (kamar yaƙi ko fari).Bayan zuwan addinin Islama a ƙarni na 14 a lokacin Sarki Yaji I, asirin tsafi ya juye zuwa harkar sirruka na addini, inda garin ya shahara da malamai masana ilimin lissafi, duba, da rubutun shaida (allo). Wannan ya sa Kano ta zama babban birni na neman kariya ta asiri da addu'o'i ga sarakuna da 'yan kasuwa.Soyayya da rayuwar nishaɗi a Kano tana da alaƙa mai ƙarfi da sarauta, kuɗi, da adon mata.Sarki Muhammadu Rumfa shi ne sarki na farko a tarihin Kano da ya gina babban fada (Gidan Rumfa), kuma tarihi ya nuna cewa ya auri ko ya tara mata kimanin guda 1,000 a fadar sa. Wannan ya nuna yadda soyayya da sha'awar mata suka kasance babban al'amari a fadar sarauta. A fannin samari da 'yan mata, soyayyar Kano ta ginu ne a kan kunya da ladabi. Samari kan je "zance" da daddare, inda yarinya ke fitowa tare da ƙanwarta ko ƙaramin yaro (mai tsegumi). Ana nuna soyayya ta hanyar kyautar kayan alatu, turare, da kuɗaɗen goron sallah. Idan ana maganar soyayya, mata Kanawa sun shahara tun asali da karkata ga gyaran jiki, saƙar gashi, sanya sarƙoƙi (kamar yadda mata ke rataya tsofaffin kuɗi a wuya don jan hankalin masoya), da amfani da lalle. Kuɗaɗen da 'yan kasuwa ke samu, kusan gabaɗaya suna narka su ne wajen faranta wa matansu ko masoyansu rai.TSOKACI…Tabbas wani lokacin nauyin baki shi ke jawo mana mu rasa abu mafi muhimmanci a rayuwarmu, ba tare da mun ankara ba.A wani lokacin kaddara ce take nemo mu ba tare da mun farga ba, k...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play