Free chapter · Read without an account
Chapter 1
*KARYAYYEN ALƘAWARI*
(THE BROKEN COVENANT)
BY
Fatima Isa Manu
( Sahiba )
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
بسم الله الرحمن الرحيم
SHIMFIƊA…
Kano State, Nigeria..
Kano ta Dabo cigari, gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fi ka.
Kanawa sun kasance masana noma da sana'o'in hannu kamar rini, jima (sarrafa fata), ƙira, da saƙa. Ciniki a lokacin ana yin sa ne ta hanyar furfure (kasuwancin canjin kaya da kaya) kafin a shigo da amfani da kuɗi. A ƙarni na 15, shahararren Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya kafa Kasuwar Kurmi. Wannan kasuwa ta zama matattarar fatake da ayarin raƙuma (Trans-Saharan Trade) daga kasashen Larabawa kamar Libya, Tunisiya, da Maroko. A zamanin Sarki Yakubu (1453), fatake Larabawa na farko daga Tripoli suka zo Kano, kuma saboda jikinsu mai haske, Kanawa suka sa musu suna "Turawa", wanda hakan ya assasa unguwar Dandalin Turawa da ke cikin birnin Kano har yau.
Kafin zuwan Musulunci, tarihin Kano ya ginu ne a kan tsubbu, asiri, da tsafi. Mutumin farko da ya fara zama a Kano shi ne Barbushe, wani ƙatoton mafarauci da ke zaune a Dutsen Dala.
Barbushe babban boka ne mai tsaron gunki mai suna Tsumburbura. Shi kadai ke da ikon shiga kurmin gunkin don yin tsafi da duba asiri, inda yake bayyana wa mutane abubuwan da za su faru a nan gaba (kamar yaƙi ko fari).
Bayan zuwan addinin Islama a ƙarni na 14 a lokacin Sarki Yaji I, asirin tsafi ya juye zuwa harkar sirruka na addini, inda garin ya shahara da malamai masana ilimin lissafi, duba, da rubutun shaida (allo). Wannan ya sa Kano ta zama babban birni na neman kariya ta asiri da addu'o'i ga sarakuna da 'yan kasuwa.
Soyayya da rayuwar nishaɗi a Kano tana da alaƙa mai ƙarfi da sarauta, kuɗi, da adon mata.
Sarki Muhammadu Rumfa shi ne sarki na farko a tarihin Kano da ya gina babban fada (Gidan Rumfa), kuma tarihi ya nuna cewa ya auri ko ya tara mata kimanin guda 1,000 a fadar sa. Wannan ya nuna yadda soyayya da sha'awar mata suka kasance babban al'amari a fadar sarauta. A fannin samari da 'yan mata, soyayyar Kano ta ginu ne a kan kunya da ladabi. Samari kan je "zance" da daddare, inda yarinya ke fitowa tare da ƙanwarta ko ƙaramin yaro (mai tsegumi). Ana nuna soyayya ta hanyar kyautar kayan alatu, turare, da kuɗaɗen goron sallah. Idan ana maganar soyayya, mata Kanawa sun shahara tun asali da karkata ga gyaran jiki, saƙar gashi, sanya sarƙoƙi (kamar yadda mata ke rataya tsofaffin kuɗi a wuya don jan hankalin masoya), da amfani da lalle. Kuɗaɗen da 'yan kasuwa ke samu, kusan gabaɗaya suna narka su ne wajen faranta wa matansu ko masoyansu rai.
TSOKACI…
Tabbas wani lokacin nauyin baki shi ke jawo mana mu rasa abu mafi muhimmanci a rayuwarmu, ba tare da mun ankara ba.
A wani lokacin kaddara ce take nemo mu ba tare da mun farga ba, kuma dole mu amshe ta a hannu bibbiyu dan ta zama kaddararmu kuma ba’a canja kaddara, a wannan karan Nameer ne ya je inda kaddaransa take ya jawo shi ba tare da ya farga ba, Samira kuma ta amsa hannun biyu ta yanda batayi zato ba.
BAN HAKURI…
Wannan littafin da gaske ya faru, idan yayi dai-dai da rayuwarka/ki akasi ne ayi hakuri, ban amince a daura shi a youtube ba tare da amincewata ba, sannan gajeran labari ne.
*PAGE 📄 1.*
Sanye take da hijab maroon color wanda ya haska ƙyaƙƙyawan fatan ta, kallo daya zaka mata ka gane bafulatana ce duba da yanayinta, fara ce doguwa tsiririya, idan ka kalli fuskarta yana ɗauke da manya idanunwa masu ratsin baƙi, hancinta gajere amma yana da kyau, sai pink lips nata da yake dai-dai da hancinta, tana da dimple na hagu.
A hankali ta d’ago da kanta ta sauk’e idanunta akan K’awarta, kamar bazata yi magana ba ta motsa ƙaramin bakinta, “ Nafisa mu koma hostel din ni nagaji, sai 2-4 muke da Pratical na Malam Hamisun,”
Nafisa ta gyara tsayuwarta tana cewa, “ Sorry dear bari a kawo handout din sai mu tafi,” Tana gama faɗa wani ƙyaƙƙyawan matashi saurayi ya iso hannunsa rike da taƙarda yana mik’a musu.
“ Muktar tun dazu kai fa muke jira,” Cewan Nafisa bayan ta amsa.
Ya shafa kansa yana satan kallon inda Samira take ya ce, “ Samira ko magana babu?”
Ɗauke kanta tayi daga garesu ta soma tafiya, Nafisa ta ce, “ Ka ga kar tayi fushi dani, sai anjima bye,”
Yayi murmushi kawai ya juya ya koma cikin hostel din maza, yana shiga suka ci karo da shi yana daka masa harara, “ Nameer handout kawai na bata fa, ba wani hira muka yi ba,”
“ Na maka magana ne ko na tambaye ka? Makiri baka da gaskiya,” Cewan ƙyaƙƙyawan saurayin,
“ Wai na fara kare kaina da wuri ne,” Sannan ya ƙarasa ya hau kan katifarsa ya zauna.
Nameer ya koma ya zauna ya dafe kai, sai sannan na ƙare masa kallo, chocolate color ne, dogo mai faffadan kirji, sannan yana da jiki amma na gym ne, idan aka koma fuskarsa kuwa nan zaka gane cewa Allah ya zuba halilta, sajensa ya kwanta luf luf, yana da hanci da ƙaramin baki, idanunsa fari mai ɗauke da brown, gashin kansa ya ƙwanta alamun yana shan gyara.
Muktar ya juyo ya gansa yana cewa, “ Boye boyen nan bashi da amfani ko kadan Nameer, is better ka sameta ka faɗa mata kana sonta,”
Ya sauke numfashi a gajarce, “ Ba yanzu ba tukun,”
Ko da suka shiga hostel room 17 ne nasu, hakan yasa suka wuce upstairs direct suka shiga.
Wurgar da jakan hannunta tayi sannan ta nufi toilet tana fama masifa, “ Kema kamar mayya dole sai kin ari handout, common handouts bazaki iya muje ki siya ba, idan ma baki da kudi ne ni zan siya miki, “ Ta dan sauke numfashi ta cigaba da fad’in, “ Amma ya zama na karshe karki kuma sake aran handout a wurin maza bana so Nafisah,”
“ Test fa muke dashi anjima taya bazan ara ba Samira? bayan kinsan malamin bashi da kirki akan abu kadan sai ya baka carryover,”
“ Ke kika sani kuma” Ta ƙarashe tana fitowa daga toilet din bayan ta ɗauro alwala, sallaya ta shimfiɗa ta saita alkibula ta tada kabbara.
Rama sallan azahar tayi sannan ta zauna ta soma karatun test da za suyi anjima.
Ƙarfe uku da talatin da bakwai suka iso bakin hall da za’ayi test din, maza sun cika bakin k’ofan sai hayaniya akeyi, ta turo baki tana kallon Nafisa.
Nameer da ke chan gefe yana surutu shi da tawagarsa ne ya hango ta, kallon Mansoor yayi yana nuna masa bakin k’ofan tare da furta, “ A cewa Rijalun din chan su bace daga hanya kafin na iso”
“ Angama Oga” Ya nufi wajen yana fitoo, duk suka juya suna kallon shi, wani daga cikin su ya ce, “ Ya da fitoo a class fa kamar arne?”
“ Anyi din kana da ja ne?” Ya matso dab dashi kamar zai kai masa duka.
Baya guy din yayi yana kallon inda Samira take sannan ya ce, “ Da sai kace min jela ka biyo ai, dama ba’a raba bunsuru da aku…” Bai kai ga gama maganar ba yaji saukar naushi a bakinsa, ihu ya saka yana d’aka tsalle yayi baya, take bakinsa ya soma zubar da jini kamar fomfo.
Nameer ya komar da Mansoor baya yana fad’in, “ Hakoran naka zun zube ko da saura? ko dai rawa yake yi?”
Dariya Mansoor ya masa yana cewa, “ Hala dai sai an kai shi clinic duba da yanda hokaran ke rawa”
Samira tabi gefe ta wuce bata ko kalli inda suke ba, Mansoor ya matso gurin Nafisa yana cewa, “ Ƙawar nan taki akwai jan aji”
Harara ta watsa masa ta wuce ta gefen shi bata ce komai ba.
Juyawa Nameer yayi yana kama hannun Mansoor suka koma wajen zaman su, hall sai hayaniya akeyi akan abun da Nameer yai wa Sadiq, shigowan lecturer da wasu malaman ne yasa akayi shuru.
Sai da ya kira attendance sannan aka shirya kowa da wajen da ya kamata, kafin ya rubuta 10 questions yace answer 7, 1 hours test. duk kowa ya dukufa kan rubutu amma ban da Nameer, hankalinsa yana kan Samira yana duba masu kallon ta, idanunsa ya sauk’a akan Dr mujahid da sai kallon ta yake yi.
Taune bakinsa yayi da karfi wanda ya saka ya fara jini, yana jin zugi a zuciyarsa kamar wanda ake hura wuta, ya damke biro da karfi har sai da ya karya.
Duk abunda ke faru akan idanun Malam Hamisu, dan gyaran murya yayi ya ce, “ Remain 20 minutes “
Lumshe ido Nameer yayi ya juya ya kalli biron, ya dubi Mansoor da ke gefen shi ya ce ya basa biro daya, bayan ya amsa ne ya shiga rubutu bai d’ago ba sai da ya kammala tas.
Malam Hamisu ya ce, “ Summit “ Duk suka yi summiting kowa ya fice.
Ana fitowa Nameer ya tsaya a bakin k’ofan kansa a k’asa ya zuba hannu a wando, Mansoor yana kallon shi ya hadiye miyu yana matsawa gefe, har zai masa magana sai ya fasa chan dai ya daure ya ce, “ Boo mu tafi”
“ Sai na raunata mutumin nan zan bar nan wajen, sai na illata shi..
*Unguwar Rimi*_____
Kaf unguwar babu gidan da ya kai gidan Malam Audu tara yara, matansa hudu Baba ladi, Asabe, Rabi da Zuwaira, ko wacce yaranta sun kai bakwai, Rabi ce kawai take da yara uku mata, sai kuma sauran yaran da iyayensu sun fita.
A gidan kowace mace ita ke nemowa kanta abinci ita da yaranta, kuma dole ne idan aka dafa a bawa Malam Audu a cewarsa ai shi ya ajiye su.
Idan an samu da rana to babu na dare, haka kuma idan an samu na dare babu na rana, yaran duk sun bokare ko wacce ta fita neman na kanta, k’ananan kuma an daura musu talla.
Idan aka cire yaran Rabi sauran duk zaman kansu suke da yawon ta zubar.
Yaran Baba Ladi sune Mubarak, Aisha, Halima, Murja, Yakubu, ilyasu, sai Lawandi.
Asabe kuma Jamila, Muhammad, Faruk, Musa, Auwalu, Karima, da furera.
Sai Rabi yaranta uku, Samira, Na’ima da Khairat.
Zuwaira ce Amarya ita yaranta biyar, Audu, Hadiza, Falmata, Nusaiba sai Ishaq.
Rabi ta zabi suyan kosai a bakin k’ofa, a cewarta yaranta mata ne bazasu je yawon karuwanci ba, gwara ita tayi talla, da kudin kosai take biyawa yaranta kudin makaranta, wanda yanzu Samira tana nursing HNDn shi wannan shekaran zata gama, sai Na’ima da take ajin karshe a secondary, Khairat kuma tana jss 2. kaf gidan kuma sune kawai suke makaranta sauran duk Allah baku mu samu ne.
D’akuna guda shida ne a gidan, ko wace mata d’akinta daya yara mata ma nasu daya haka ma maza, haka za’a taru manya da k’ananan a kwanta, da mazan suka kalli abun ba mai bullewa bane suka bar gidan da kwana sai jifa jifa suke shigowa, haka idan ranan kwanan daya daga cikin matan yayi yaran zasu fita.
Yau ma kamar dai kullum Malam ne zaune a tsakiyar gidan ya shimfid’a taburmansa yana faman tsinewa yaran gidan, “ Da haihuwar yara irin su Jamila gwara tafiya tsirara, shegu yan iska yan hau, a ce duk yawon da kuke yi ban taba kallon wata daya daga cikinku an saukar da ita a mota ba sai dai a keke, yan iska mahaukatan banza”
Asabe tana goge hakoranta da ashuwaki ta ce, “ Kai kuwa malam ban da mutuwar zuciya kalan naka har kana da bakin magana, nan fa idan an kawo tsire ko balangu ka tsikara hannu kaci”
“ Yi min gori Asabe, na gagara da gidana ko?”
Zuwaira ta cafke da cewa, “ Malam to karya aka maka ne? nan a wajena idan Hadiza ta kawo kankaran madaran kake lashewa har hana yaran kake yi ka shanye, zuciyarka ka bawa kare ya lashe shi tas”
Cike da balbalin bala’i Malam ya shiga fad’in, “ Ashir naku, masu bak’ak’en bakuna, yara dai yarana ne, idan ma gori zaku min sai ku bi a hankali, ban da nima Allah ya rufe min ido ina ni ina auranki Asabe? fuska kamar takashin biri”
Yaran da suke zaune daga gefe suna wasa suka kwashe da dariya, Asabe ta wurga musu dutsi akayi rashin sa’a ya buge kan Lawandi yaron Baba Ladi, ihu yaron ya saka ya shiga birgima a k’asa yana fad’in an rusa masa kai.
Baba Ladi ta fito daga cikin d’aka tana fad’in, “ Idan na yarda in mutu, ni za’a saka asara, rashin lafiya ga ciwo, asibiti da nisa magani tsada, bai yuwa wallahi ki tsaya nima na rama”
Asabe ta mike tana daure dankwali a kwankwaso ta ce, “ Ki rama fa? to Ladi zo ki rama mugani” Ta dunkule hannu.
Malam ya ce, “ Kuyi wallahi, wacce ta fasa dama tsoro take ji”
Baba Ladi tayo kan Asabe ba shiri aka shiga kokawa, ihu yaran gidan suke yi ana tsalle, Zuwaira ta ja hannun yaranta k’anana zuwa d’aki ta tura kofanta.
Daga waje Rabi da ke suya taji hayaniya da ihun yara suna wakar, ‘A chasu kai kai a chasu, a chasu ba mai raba ku tunda kuna da gajeran wando,’
Ta furta, “ Inna’illahi wa’inna ilaihi raji’un!!” Ta bi mutanen wajen da kallo sannan ta kalli Khairat ta ce, “ Zo ki cigaba da suyan ina zuwa” Ta shiga ciki da sauri.
D’aukan tabarya Asabe tayi da niyar bugawa Baba Ladi akayi rashin sa’a sai kan Malam.
Azabebben ihu Malam ya saki yana dafe goshinsa da lokaci guda ta kumbura ta fara digar jini, Rabi ta saki salati tana kama baki, yaran kowa yayi shuru kamar wanda mutuwa taci su, Asabe ta kalli Baba Ladi ta kalli Malam.
Mutanen da suke waje dan siyan kosai suka shigo da gudu jin ihun Malam yana wayyo goshinsa.
Wani daga cikin mutanen mai suna Hashimu ya ce, “ Subhanallah, a kai shi kemis mana”
“ Babu inda zanje wallahi, ban da ko sisi, gwara a jik’amin hararrabi na sha, Asabe yau kwanan gidan ubanki zakiyi, bazaku kasheni ba…
😹😹😹😹😹😹😹😹😹😹😹😹
SAHIBA✍🏻
***