Free chapter · Read without an account
Introduction
UQUBA CHAPTER 2
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWAN GAMJI......
Washe gari da safe baffa da kansa yayimata wanka ya bata madara ta sha sannan ya bawa Ajimal renon ta Domin lokacin Ajimal ya kai shekaru sha takwas a duniya '
naja 'atu Kuma shekarar ta biyu.
Baffa na fita Amo batayi qasa a guiwa ba ta d'auki mayafin ta ta nufi gidan babbar aminiyar ta salame "
Kai tsaye suka shige cikin d'aki '
Amo ta kwashe labarin komai ta fad'awa salame,
Game da maganar tsinto yarinyar da baffa yayi,,
Ta qara da cewa...
Ai ba hauka nakeyi ba wallahi bazan iya renon y'ar wasu ba '
Nawan ma kawai dan sun zamamin dole ne abarni da iya su sun isheni,,
Haba salame Da wanne zanji?
Naji da talaucin malam ne ko naji da riqon yara na kokuwa naji da renon waccar shegiyar y'ar tsanar?
Ta qarasa maganar tana riqe ha'bar ta had'e da ta'be baki.
Se da salame ta d'an numfasa sannan tace"
Amma Amina bakida wayo wallahi,
Ai ko baki kar'bi yarinyar nan dan Allah ba kya kar'beta ko dan gudun maganar mutane,,
Kinsan fah yanzu an dena kiwon dabba mutum ake kiwo '
Kowa ya shiga gidan yaga malam ko Ajimal suna renon jaririya ke za a fara zagi ace bakida tausayi kinqi ka'bar jaririya.
Da mamaki Amo ta kalleta tace '
Yanzu salame kece kike magana akan tausayi?
Yaushe kika fara tausayin y'a y'an wasu kuma?
Kin manta murjanatu y'ar marigayiya indo abokiyar zamanki irin wahalar da ta sha a hannunki?
Kode bakiji labarin da na baki da kyau bane?
Yarinya ce fah aka kawo ta akace na riqe ta Kuma bansan kowa nata ba "
Wani shu umin dariya salame tayi sannan ta kalli Amo tace,
Sarai na fahimci labarin Kuma na gane me kike nufi '
Sannan Kuma nid'in ce de da kika sani kirarina yana nan"
Turnuqu fad'an ibilisai yaro be ganiba balle ya raba,
Jani muje ko daban daban ma dawo Mugu shi yasan makwancin mugu '
To amma meyasa kika ce na kar'bi wannan tsintacciyar yarinyar?
Amo ta fad'a fuskarta d'auke da mamakin kalaman salame '
Sosai salame tayi dariya sannan tace,
Saboda ta hakane kad'ai zaki iya jifan tsun tsu biyu da dutsi d'aya,,
Ke ban ganeba kin qara sakani a duhu...
Bari nayimiki gwari gwari yadda zaki gane.
Amo tayi saurin gyara zaman ta tace,
Ina sauraronki fayyacemin yadda zan gane"
Dariya salame ta sakeyi irin dariyar nan na qeta Sannan tace ,
Qin kar'ba yarinyar nan ze saka kowa ya dinga yimiki kallon muguwar mace marar imani"
Amma idan kika kar'beta za a dinga kallonki a matsayin mace me kirki da tausayi,
Ko shi kansa malam se kinfi samun abunda kikeso a gurin sa,,
Sannan Kuma yarinyar nan macece '
Da zarar ta fara tasawa zaki iya jaura da ita,
Ki dinga kasamata talla kullum,,
Sannan kuma ki dinga 'bata ta a idon malam da na mutane,
Hakan ze saka mutane su dinga yimata kallon shed'aniyar yarinya marar tarbiyya "
Ke kuma kowa ze dinga tausayamiki da tunanin yarinyar tana cutar da ke Itada y'a mace ce,
Duk rintsi bazata ta'ba kaucewa umarninki kokuma ta gujewa inda ta tashi ba,
Domin koda ta tafi batada inda zataje dole seta dawo gareku "
Zaki huta da duk wasu ayyukan gida da sauransu,,
Ita zata dinga yimiki komai.
Karki bari a sakata a makarantar boko ko ta Arabic'
Tunda Naja 'atu y'ar kice yazama dole ta huta a gidan ubanta,
Ita zaki saka a makarantar boko se itakuma wannan tsintacciyar ta dinga kula da aikin gidan,
Duk wanda yayi magana se kice itace taqi makarantar da kanta '
Babu yadda bakiyi ba kema tafi qarfin ki ne shiyasa kika haqura kika kyaleta.
Tunda mace ce idan kikaso hatta za'bin mijin da zata aura kece kikeda wuqa da nama se wanda kikaso zata aura "
Kinga seki za'ba mata wanda kikaga dama ko ya yake ki turata kawai ki huta,
Amo wacce tunda salame ta fara magana ta kasa kunne tana sauraronta had'e da jinjina kai tana jin jina irin wautar da taso tayi na qin kar'bar yarinyar '
" Tace "
Kinga kuma fah kinyi gaskiya salame '
Tirqashi se yanzu na gane irin girmar wauta da asarar da naso na tafkawa kaina,
Amma yanzu tunda kin dawo da ni kan hanya' bari na koma na kar'beta,,
Idan malam ma yazo zancemasa na canza shawara zan kar'be ta.
Dariya salame tayi tace '
Yauwa to ko ke fah ana nunamiki annabi kina rintse Ido "
Haka sukayi sallama ta koma gida cike da farin ciki tana jujjuya maganganun salame a kwakwalwar ta ,,
Baffa yayi mamakin ganin jaririyar a hannun ta da ya dawo,
Gefen taburmar da take zaune riqe da jaririyar ya samu ya zauna sannan ya fara magana cikin mamaki '
Aminatu kince ke bazaki iya riqe wannan jaririyar ba,
To menene kuma yasa kika canza ra ayin ki lokaci guda '
Take Amo ta fashe da kukan qarya wanda tun da wuri take rihazal d'in shi ,,
Sannan cikin kuka ta fara cewa '
Wallahi malam yarinyar ne tausayi take bani na kasa nitsuwa,
Allah sarki yarinya abun tausayi an kama an yasar da ita a bola tamkar ba y'ar adam ba Allah ya isan ta kuma se Allah ya saka mata '
Jiyan ma tsoro ne ya hanani kar'bar ta saboda yadda na ganta nayi tunanin ba mutum bace "
Amma wallahi ina sonta zan had'a ta da Naja 'atu su zama kamar nice na haifesu duka ,
Insha Allah malam bazan dinga nuna bam banci a tsakaninsu ba.
Sosai baffa yaji dad'in maganganun ta haka ya dinga sakawa Amo albarka '
Amo kuwa taci gaba da kula da jaririyar da temakon Ajimal "
Baffa yanajin dad'in hakan sosai,
Sede bayan shekara 5 komai ya canza 'Amo ta dena kulawa da Rafi 'a,,
Kullum tana cikin dukanta da zaginta da aibata ta ,,
se ya zamana gurin Ajimal kawai take zuwa ta samu sassauci '
Domin Naja 'atu ma babu abunda ta rage daga cikin halin Amo"
Duk wasu munanan halayen Amo Naja 'atu ta d'aukosu tun tana qaramar ta.
Ko kad'an bata qaunar Rafi 'a domin kullum Amo tana fad'a musu cewar,
Rafi 'a y'ar tsintuwa ce basuda wata alaqa da ita.
Bayan shekara goma Amo ta qara matsawa Rafi 'a sosai '
Kullum tana cikin duka zagi hantara tsangwama,
Kullum Rafi 'a tana cikin kuka ga yunwa da wahala "
Domin ko abinci Amo bata bata sede idan baffa ya dawo daga kasuwa ya kawomata rogo ko dankali d'an hausa ,
Haka zataci yana shaqeta wani lokacin idan ta gama ci ya qulle mata ciki tayita birgima '
Amma hakan baze hanataci ba idan an kawo gobe "
Domin batada za'bi idan bata ci ba yunwa zatayimata illa.
Gashi ini takeyi a gurin talle,
Da safe koko da qosai da rana shinkafa da wake da dare kuma tayi tuyan awara ,,
Hakan be hana a sakata ayyukan gida ba "
Kullum kafin asuba ta gama yi za a tasheta ta tafi d'iban ruwa a rijiya.
duk tsananin sanyi da akeyi bata ta'ba fashin d'iban ruwan ba koda kuwa batada lafiya '
Tana kammala d'iban ruwa zata kama share gida ,
Seta gama sharan sannan ta d'aura musu abun karyawa tayi wanke wanke"
Haka tana gani za a cinye abincin ita ko loma baza a bataba ,
Se wataran ne idan Ajimal yana gida idan aka raba abincin seya d'auki nasa ya kai d'akin sa ya kirata da niyyar yimasa gyaran d'aki '
Idan taje seya bata yayita lallashinta yana kwantar mata da hankali,,
Yana nunamata tayi haquri komi me wucewa ne.
Duk randa baffa yayimata magana akan abunda takeyiwa Rafi 'a haka zata zageshi tass"
tayimasa wankin babban bargo kamar d'an ta,
Shikuwa baffa baida bakin magana yana shakkarta sosai domin Amo kwararriya ce wajen bin bokaye da malaman tsubbu '
Haka de da kissa da munafurci da bin bokaye Amo tayi nasarar shiga tsakanin baffa da Rafi 'a"
Domin a yanzu ko rogon ma ba kullum yake kawomata ba,
Duk randa be kawoba haka zata kwana ido biyu babu bacci cikinta yanayimata qugi saboda yunwa.
Wani lokacin idan yunwar ta dameta sosai haka zata tashi cikin dare ta hura wuta ta tasa ruwan zafi ta dinga sha a haka ,,
Ga babban abunda yafi yimata ciwo '
Kullum Amo a cikin yimata gori take akan ita y'ar tsintuwa ce,
Waya sanima ko cikin shege akayi da aka haifeta akaje aka jefar"
Wannan abun yafi komai yimata ciwo a zuciya.
Idan Amo ta yimata gori akan asali tanayin kuka sosai da nadamar kasancewarta a raye,,
Meyasa iyayenta sukaje suka aikata son ransu ita take fuskantar hukuncin?
Meyasa suka kasa haquri da rayuwa har suka bari zuciyarsu tafi qarfinsu?
Da sukasan sunajin kunyar duniya meyasa suka bari suka haifeta?
Idan har bazasu iya riqetaba meyasa basu kasheta tun ranar aihuwar taba?
Wai shin su wanene ma iyayenta?
Su d'in sun kasance musulmai ne kokuma sunada wani addini ne daba?
Kullum idan tayi wannan tunanin se taji cewar Amo tanada hujjar fad'an komai a kanta '
Domin ita kanta batasan wacece ita ba.