Free chapter · Read without an account

Chapter 2

by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN

*đź’«MATAR SALMAN đź’«* 


➡PART ONE
PAGE 2

🌹 _LABARINA_ 🌹


 *RUMAISA IBRAHIM* cikakken sunana kenan! Na taso a kauyen Gano Jahar Kano. mahaifiyata sunanta Amina. Na tasone cikin kulawa da samun kyakkyawar tarbiyya daga mahaifiyata, idan ka ganni bazaka ce a kauye nake ba saboda yadda Mamana take kula dani sosai, kasancewar ta mace mai zafin nema, na tashi naga tana sana'a sosai kusan duk abinda ake so a kauyenmu tana kawo wa na amfanin yau da kullum.

Ta na shiga birnin kano duk sati sati don haka ko wani zuwa sai ta saya min kaya masu kyau irin na 'yan birni.

Ta sakani a makaranta da islamiyya. Allo kuwa tun ina primary na sauke. Ya zamanto a kauyen duk inda na shiga bina ake da kallo wasu na sha'awata wasu ko bakin ciki sukeyi dani.

Tun ina karama wasu lokuta na kanga Mama na tana kebe kanta a daki tayita kuka in na tambayeta tace min kanta ke ciwo. Har yanzu da na girma shekarata  goma sha shidda ina SS2.

Watarana mun taso daga makaranta ina ta sauri in dawo gida don makarantan akwai nisa da gida sosai. Jinayi ana kiran sunana a nan na juya da sauri don inga waye sai naga ashe Bello ne É—an makwaftanmu, ya nace min kullum sai ya aika a kirani gashi mama tace kada in kuskura koda wasa in saurari wani a kauyen nan don bata so.

Ina cikin wnn tunani ya karaso yana murmushi yace ”har kun taso ne?”

Fuskata ba fara'a nace ”eh mun taso.”

Yace ”Rumaisa baki ga sakona bane?”

Nace ”na gani mn.”

Yace ”amma baki ce komi ba.”

Shiru nayi sannan nace ”Ni fa Mama ta hanani kula kowa tace karatu zan yi kuma sai na gama Jami'a.”

Dariya yayi sannan yace ”jami'a a kauyen nan ne har zaki yi jami'a? Hmm kinga Rumaisa bari in gaya miki gaskia aure shine ya kamaceki yanzu  ba wani boko ba, tunda Allah yasa kin sauke Qur'ani ki amince in rufa miki asiri in aureki ba sai an tsaya tone tone ba, watakila shiyasa mahaifiyarki take tsoro yasa tace makaranta zakiyi, ni ba ruwana da asalinki haka nake son ki.”

Jikina ya mutu tunda ya fara maganan, domin gaskia ni bansan  waye BABANA ba. Wani bai taba zuwa wai dangin Babana ba, kai harma Mama ban san kowa nata ba.
Hawayene ya zubo min da na tuna kusan kullum na kanga Mama a damuwa in ta kebe ita daya.

Gaba daya na manta da wani Bello da sauri na barshi a gurin yana ta kwalan kira nayi banza dashi.

Tafiya sauri sauri nake har na isa gida ina haki Mama tana ganina tace ”Ke lafiya na ganki haka waya koroki?”

Na girgiza kai nace ”babu na shige ciki na kwanta.”

Shiru shiru taga ban fito na nemi abinci ba, don haka ta shigo É—akin ta zauna kusa dani tace ”Rumaisa me nene yake damunki  kin shigo cikin yanayin damuwa ko abinci baki nema ba?”
 Na girgiza kai nace" bab.......

Ta katseni da sauri ta ce ”Akwai abinda kike boye min, Rumaisa bakida kowa a garin nan sai ni don haka dole ne ki fada min damuwarki.”

Na mike na zauna sannan na kalleta nace ”Mama tambaya zan miki zaki ban amsa?”

Ta ce ”In har na sani me zai hana na baki amsa?”

Nayi ajiyar zuciya nace ”Mama WAYE MAHAIFINA?”

Nan da nan naga fuskarta ta sauya ta mike rai bace tace  ”Uban wa ya saki kizo ki min wannan tambayar fada min.”

Tsoro ya rufeni ganin yadda ta fusata.

Tsawa ta daka min  ”Nace uban wa yasa ki zo ki min wannan tambayar?”

Na kara rikicewa da kyar bakina ya iya fadan ”Bello ne dama yace........”

Na fada mata komi.

Ta gyada kai tace ”Ohh wato har yanzu baki rabu da Bello ba ko? ba na fada miki cewa bazakiyi aure ba sai kin gama Jami'a? To bari kiji ko kin gama ma ba'a kauyen nan zakiyi aure ba, don haka ko da wasa kar na kara jin ko ganinki da Bello kai kowa ma indai anan kauyen ne, don haka ki kama kanki.”

Tunda ta fara magana nake ba ta hakuri nidai.

Tace ”tashi ki fita kije ki debi abinci kici.”

Ina cin abinci naga ta dauki hijabinta ta yi waje rai bace.

Daga wannan rana na shiga damuwa ba abinda nake son illa in san wacece ni. Uwa uba kuma gidansu Bello yan'uwansa sun sakoni a gaba tunda Mama taje ta fadawa mahaifiyarsu maganganu akaina, ya kasance duk inda suka ganni sai sun zageni hade da yi min gorin asali.

Na shiga damuwa sosai har ya kasa boyuwa kana ganina ko baka sanni ba kasan ina cikin damuwa.

Yau bayan na taso daga islamiya don yanzu banda kawaye ma duk sun juyan baya ni kaɗai nake tafiyata.”

Kannen bello suka tareni a hanya zainab da Kulu. Na kallesu nace ”Lafiya?”

Kulu ta harareni tace ”kudaden da yayanmu ya kashe miki zaki tattara ki bamu.”

Cike da mamaki nace ”wane kudade kuma?ni Bello bai taba bani ko sisi ba....”

Zainab ta katseni da fadin ”karya kikeyi shegiya munafuka dole ne kawai ki fito da kudin nan ki bamu ehe!”

Kulu ta karba tace "duk karuwancin da akace mamanki takeyi a birni ta dawo da lodi lodin kaya da kudi bai isheku ba sai kin kara dana ya Bello......”

Raina ya bala'in baci na kallesu nace ”gaskia Kulu abinda kuke min ya isheni don kun fara wuce gona da iri, zaku min komi in shanye amma banda naganar zagin mahaifiyata.”

Zainab tace an zageta sai me? Waye ita a garin nan banda karuwa, idan karya muke mata gaya mana waye ubanki?”

Kulu ta karba ”tace tunda muka taso a garin nan bamu taba jin wanda yace ya sanku ba.......”

A fusace na É—auketa da mari. Nan da nan muka kaure da kokuwa. Dama hakan suke so don haushina da sukeji .

Nan aka taru a wurin ana rabamu sai zagina suke suna cewa Mama na karuwa ce.

Da kuka na bar wurin Allah Allah nake na isa gida don wlh hada kayana zan yi in bar garin nan in shiga duniya neman asalina.

Horn din mota nakeji tun dazu a kunne na wanda ya ki karewa nan da nan na birkice na rasa ina zan yi. Kawai na tsaya cak! Idona rufe ina sauraren ta inda motar zai kwasheni.

Saɓanin hakan sai na ji takun mutum ya na zuwa inda nake kamshin turarene mai dadi ya daki hancina da sauri na bude idona
Rass!  Naji zuciyata ya tsinke da ganin wanda ke gabana!
Wani matashin saurayi ne  kyakkyawan gaske kuma É—an birni sai kun ganshi in tsaya kwatancen kyaunshi bata lokaci ne. Kawai dai ya hadu ga kwarjini.

Sai dai na lura kamar ransa a bace yake don wani irin kallo yake min kaman zai dauke fuskata da mari.

Sai lokacin na gane a tsakiyar hanyar wucewar mota nake ta tafiya gashi sun ta min hon amma ko a jikina don ma mota basu cika shiga layin sosai ba ko adaidata sai dai su sauke mutum a can babban hanya basa shiga saboda gargada da yashi.
Shine ya sauko ransa a bace.

”Wannan wane irin rashin hankaline haka?”

Ya fada a fusace yana kallona sannan yaci gaba da fadin

”Dallah tashi a hanya zamu wuce ƴar kauye kawai.”

Ba tare da na damu da abinda ya fada ba don ba shine a gabana ba na tsallaka gefe naci gaba da tafiya na.

 Fizge motar yayi da karfi ya bade ni da kura ya wuce sai lokacin na lura ashe su biyu ne ma Hmm. Nayi gaba kadan sai naga motar sun paka shi sun fito suna zaune a kai, taÉ“e baki nayi nace a zuciyata duk uban saurin nan naka dama nan zaku tsaya ashe, ba sama zaku tashi ba.

Har zan wucesu sai ɗayan yace min ”Malama don Allah muna da tambaya ne”

 Tsayawa nayi nace "to Allah sa na sani.”

Fuskarsa dauke da fara'a yace "ke kuwa 'yar kauyen nan ne?”

Nace ”Eh ka tambayi abinda zaka tambaya  don sauri nake in isa gida.”

Murmushi yayi ya kalli ɗan'uwansa da ya kame ko kallonmu bayayi yana latsa wayarsa.”
Yace ”kaji ai 'yar kauyen ne.”

Ba tare da ya dago ba yace ”to ka tambayeta kawai mana.”

Mai fara'an ya juyo gareni yace ”ya sunanki?”

Cike da mamaki nace "Tambayar taku kenan?”

Wani shegen kallo na farkon ya jefa min sannan ya kara tamke fuska yana kallon wayarsa, ɗan uwan nasa yayi murmushi yace ”A'ah ba shikenan ba akwai wata mata da mukazo nema a kauyen nan ne.”

Nace ”wace mata kenan meye sunanta?”

Yace " sunanta Amina kuma tana da 'ya Rumaisa ko Rumasa'u na ɗan manta dai.”

Bansan lokacinda nayi murmushi ba don tuni jikina ya bani wannan 'yan'uwana ne.”

Shi ma murmushi ya min. Ba ɓata lokaci nace ”Gidan na can gaba muje nima can zani.”

Yace ”Kai gaskiya naji daɗi da bamu wahala ba, in ba damuwa zo muje a mota mana.”

Na girgiza kai nace ”A'ah ni bana shiga motan da bansan masushi ba.”

Dariya yayi yace ”Gaskiarki kar a sace ki to muje a kafa shi ya biyo mu a mota”

Ya juya ya kalli danuwansa yace "To oga munyi gaba ka biyo mu a mota.”

Ko dagowa baiyi ba bare a sa ran amsa daga gareshi. Muka jera dashi sai tadi yake min gashi da abun dariya.

Nace ”wai wancan me motar ɗan'uwanka ne kuwa?”

Yayi dariya yace ”Ɗan uwana ne ba kya ganin kamanni?”

Nace ”hakane kam, sai dai naga shi baya fara'a ko an bata mishi rai ne?”

Yace "ke rabu dashi miskilancine zalla ba wani abu ba.”

Na juya baya har lokacin yana zaune kan motar yana kallon wayarshi

Mun isa kofar gida na kalleshi Nace ”To bari na shiga me zance da ita?”

Yace ”kice mata baki daga birni.”

Nace ”to.”

Na shiga ciki da sallama can ɗaki mama ta amsa min na sameta a dakin Nace ”Mama kinyi baki sunce daga birni suke.”

Da mamaki tace ”baki daga birni kuma to ina suke?”

Nace ”maza ne su biyu inaga ma kamar 'yan biyu ne fa sunzo da mota.”

Ta danyi shiru daga bisani tace ”to saka musu tabarma a waje kije kice su iso.”

Nace ”to.”

Bayan na shimfida tabarma na je na samesu ashe har miskilin ya karaso na kalli dayan Nace ” ta ce bismillah Ku iso ciki.”

Na wuce gaba suna biye dani a baya har ciki na nuna musu tabarma suka zauna. Mama ta fito daga daki duk ta bisu da kallon rashin Sani suma kallonta suke.

Ta yi musu sannu da zuwa ta zauna a kujera suka fara gaisawa. Sannan shiru ya biyo baya......Mama ne ta yanke shirun da fadin  ”Sai dai ban ganeku ba kuyi hakuri don Allah.”

Mai fara'an yayi murmushi yace ”Eh bazaki gane mu gaskia amma mu ɗin.......”

Mama ta katse su da fadin ” Ku tsaya in canka.”

Murmushi ta yi ta mike ta karaso inda suke ta kallesu cike da fara'a tace ” *SALMAN*  da  *SALIM* ne.”

Ta nuna miskilin tace Kaine ”Salman.”

Sannan dayan kuma tace Kai kuma babu tambaya Salim ne.”

Murmushi  wanda ta kira da Salim din yayi yace "hakane Goggo Amina mune.”

Mama cike da farin ciki ta zauna tana fadin ”Allahu Akbar kune kuka zama samari haka?”

Ta kalli Salman tace ”Salman ina Innarku?ina Yaya na?”

Kanshi a sunkuye yace  ”Duk suna nan laifya Goggo Amina don sun san ma zamu zo nemanki.”

Ta danyi jim cikeda mamaki sannan tace ” Allah sarki.”

Sannan ta kalli Salim tace ”Salim ya Aunty Zuwaira da Yaya Kasim kannenka nawa yanzu?”

Ya na murmushi yace ” Suna lafiya, kannena su biyu ne Fa'iza ne sai Hakim.”

Tace ”Allah sarki Salman kaifa?”

Yace ”Su hudu ne duk mata Sadiya da Raihana, sai Sakina da Zainab yaran Mama.”

Mama cike da fara'a tace ”Masha Allah gida ya cika Alhamdulillah Allah yayi albarka.”

Suka amsa da ameen sannan suka danyi shiru Salman ya ɗago ya ɗan kalleta yace ”Goggo ina yarinyarki ta girma sosai ko?”

Mama tayi dariya tace ”Ta girma fa, yanzu sai a fara shirin bikinku dama kai nace zan baiwa lokacin cika alkawari yayi.”

Ta karasa maganar da dariya, shi ma ya ɗan murmusa ya sunkuyar da kai. Salim yayi dariya yace ”Goggo kin ganshi wai bayaso to ki bani kawai ni in ta girma muyi aure.”

Mama tasa dariya tace ”wane girma kuma ta kusa gama secondary”

Cike da mamaki suka dago suna kallonta tace ”To ai itace ta muku jagora kuka shigo tare Rumaisa ba.”

Salim yayi saurin fadin ”Itace dama ta girma haka, kai masha Allah Goggo kyakkyawa kuwa da ita. Kai Bros kazo kauyen nan da sa'a, kawai kayi serious ka ji in kuma bakayi ni dai ayi dani Goggo.”

Harararsa Salman yayi bai ce komi ba. Mama dai dariya take musu 
Sannan ta kwala min kira tana "Rumaisa ki fito ki gaida Yayyun naki ki kawo musu ruwa.”

Bata san duk abinda suke ina tsaye a window gabadaya murna kamar ya kasheni ba,  da sauri na saka hijabina na fita duk ido suka sa min kunya kamar na nitse.

Na wuce na dauko jug din roba na saka musu  ruwa a randa na kawo musu da cups sannan na saka musu.

Mama ta kalleni tace ”Rumaisa wannan yayyunki ne Salman da Salim yaran yayyuna biyu Wanda muke ciki daya, Wato Yah Muhammad babban Yayanmu mahaifin shi Salman, Sai mahaifin Salim Yah Kasim, sai ni ƴar autarsu, uwa daya uba daya, mu uku Allah ya ba iyayenmu kuma duk sun rasu.”

Murmushi nayi na kalli Yah Salim sannan na kalli Yah Salman abin mamaki sai naga yana kallona muna hada ido sai ya ɗan saki fuska yace " kanwata kiyi hakuri da abinda ya faru dazu.”

Kaina na sunkuyar sai na tsinci kaina ina matukar jin kunyarsa nace "babu komi laifina ne.”

Mama tace ”ta yi muku rashin kunya ko? ”

Yayi saurin faÉ—in  ”Aah Goggo Amina nine na mata laifi.”

Anan suka dinga min tambayoyi akan makaranta ina amsawa Mama kam bata sa mana baki ba ta tafi ta hura wuta ta dora tuwo don tuni nayi miya dama.”

Magriba yayi na kawo musu ruwa a buta sukayi alwala na fita na nuna musu masallaci suka tafi.

 Bayan sun idar da sallar magriba suka dawo na kawo musu abinci sunci kuwa sosai. Bayan sun gama Mama tace in tattara kwanuka bayan na kai tace in tafi daki in dau  torch light in yi karatuna.”

Anan na barsu suna hira har karfe takwas sannan sukayi mata sallama. Mama ta kira ni tace inje muyi sallama dasu suna waje.”

Tuni har sun fita Salim ya shiga mota yana waya Salman ne ke tsaye. Na ɗan russuna nace ”Yaya ku gaida gida mun gode da ziyara, Allah ya kiyaye hanya.”

Na juya zan tafi naji yace ”Zo Rumaisa.”

Na juya cike da mamaki na tafi gunsa.

Ya numfasa yana kallona yace "zamu dawo nan da one week me kike bukata a birni inzo miki dashi?”

Na girgiza kai ina jin kunyarshi nace ”babu komi Yaya na gode da kulawarka.”

Bai ce komi ba yasa hannu a aljihunsa ya ciro kudi bansan ko nawa ba ya mika min Na girgiza kai nace "Aah Yaya na gode ka barshi.”

Ya ɓata rai yace ”Karɓi in baki son bacin raina, ko rokona kikayi.”

Dole na karba nayi godiya ya Salim ma ya fito mukayi sallama sannan suka tafi.

Bayan nayi sallar isha ne na fadawa Mama abinda su Kulu da Zainab suka min.

Sosai ran mama ya baci tace ”babu komi  zan kai karasu gun mai anguwa don a sawatar nasan uwarsu ce ke zugasu.”

Duk yadda naso Mama ta ban labarin 'yan'uwanta sai kauce min take har na hakura kawai.

Amma abin na damun raina duk da ma yau naga 'yanuwana kam, Amma ina son sanin Mahaifina da danginsa.


 *RUMAISA SALMAN BY MAMAN KAUTHAR*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol