Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Asmeetah Writer · WASAN ƘADDARA 1

╔══════════════════════╗
        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝

_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_

> ✍️ BY ASMEETAH WRITER

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

🌟 Under:

THE SHIDORIA WRITERS TEAM

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 CHAPTER ___17 and 18

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━


Janar Zarkhan ya dawo gida da yammacin ranar, kuma nan take ya sami labarin dukan da Arman ya raba wa ƙannensa a kan bidiyon da suka ɗora a intanet. Saɓanin yadda Hajiya Mairos ke tunanin Janar ɗin zai yi fushi da abin da babban ɗan na su ya aikata, sai goyon bayan Arman ya bayyana fili. Ya nuna cewa abin da Arman ya yi daidai ne, domin yaran sun cika rashin ji da shishshigi a kan abin da bai shafar su ba..

A babban falon gidan, Ahan, Elham, da Nana duk suna zaune jiki a sanyaye, yayin da Hajiya Mairos ke zaune ranta a ɓace tana kallon Janar dake cire safar hannunsa...
Janar ya gyara zamansa, ya duba yaran da kyau sannan ya furta,

 "To, kun dai san halin ɗan uwan naku, ba ya son shishshigi ko kaɗan, amma saboda rashin ji, dole sai kun shiga shirginsa... Yanzu dai kam, ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka."

Ahan dake zaune yana ta faman shan ƙamshi, fuskarsa cike da takaici da ɓacin ran dorinar da aka shimfiɗa masa a jiki, ya taɓe baki ya ce,

 "Dad, ruwa cikin cokali kam ai ko rabin sumar kaina ba zai ratsa ba."

Janar ya bishi da wani kallo, ya ce, 
"Ai daman mai hankali aka ce..."

Elham dake gefe tana matsa kunkuminta da aka buga a ƙasi, ta yi raɗa a hankali tana cewa,

 "Cabbb... ashe kowa ba shi da hankali indai cikin cokali ne zai isa wanka..."

Hajiya Mairos ta ji motsin bakinta, ta juyo da sauri ta kalle ta, "Me kika ce?"

Elham ta firgita, ta yi gaggawar wayancewa da wani murmushin dole, ta ce,
 "Ba komai Mom, kawai dai dukan da na sha ɗazu nake mita a kansa."

Nana dake zaune a gefe, ta gyara zama ta ce,

 "Allah fa daman Yaya Arman yana jin haushinsu, ba wai iya kan bidiyon da suka yi jiya da daddare ba ne kawai."

Elham ta juyo a fusace tana kallon ta, ta ce

"To munafuka, baƙar algunguma. Wa ya ce miki hakan? Wa ya baki ikon sa baki a zancenmu?"

Nana ta ci gaba da magana da sauri, "Eh mana...Damben nan da kika sha ke da wata yarinya a school ranar Laraba, duk Yaya ya sani. Kuma haka ranar kika yi transfer kuɗi da kanki daga bankin Mommy zuwa bankinki ba tare da kowa ya sani ba, kika goge transaction alert ɗin a wayar Mommy. Daga baya da aka kama ki, sai Mommy ta gaya wa Yaya Arman amma bai ɗauki hukunci a ranar ba. Still kuma kika gudu daga makaranta ke da ƙawayenki kuka tafi gidan party ranar juma'a duk Yaya ya sani. Sai da ya gama tara muku lafukan gaba ɗaya, shi yasa yau ya ɗauki hukunci..."

Elham ta ji bakinta ya mutu, ta tsuke baki ta kasa cewa uffan, domin duka abubuwan da Nana ta lissafo gaskiya ne...
Nana ba ta tsaya a nan ba, ta juya kan Ahan dake ta faman shan ƙamshi, ta ce, 
"Kai kuma Yaya Ahan, yawan ɗaukar ƴan mata a motarka kuyita yawo da su a gari kai da abokanka, har da kaiwa dare da kake yi a gidan party, duk Yaya ya sani..."

Nana zata ci gaba da fallasa sauran asirin, Ahan ya zabura ya daka mata wata uwar tsawa dake nuna tsantsar tsoron kar ta faɗi sauran,

 "Kiyi min shiru munafuka!!! Kada na sake jin muryarki a falon nan"

Janar Zarkhan da Hajiya Mairos duk suna zaune suna kallon yaran nasu..
Hajiya Mairos ta gyaɗa kai cikin takaicin halayensu, ta kalle su gaba ɗaya ta ce, 

"To ni yanzu ma na daina jin tausayinku gaba ɗaya. Allah yasa yazo ya ɗora da dukan naku munafukan yara..."

Janar ya yi murmushin fakaice na jin daɗi a ransa. Ya san halin Arman sarai tun yana yaro, baya gaggawar yanke hukunci a kan laifi guda, tara musu yake yi, ranar da kuka cika buta kuma, zai nuna muku cewa shi namijin duniya ne...

★★★

A babban ofishinsa mai cike da sanyin kwandishan da kamshin turaren wuta na alfarma, Doctor Arman yana zaune a kan kujerarsa ta juyawa. Gaba ɗaya hankalinsa yana kan wasu takardu da yake dubawa, fuskarsa ɗaure kamar koyaushe.
Knocking aka yi a hankali, sannan Isah, wanda yake babban yaron aikinsa ne a ɓangaren bincike da tsaro, ya tura ƙofar ya shigo domin dama Arman ɗin ne ya aika a ƙira shi...

Isah ya tsaya cikin girmamawa, "Gani Oga."

Arman bai ɗago kai daga kan file ɗin da yake dubawa ba, ya shafe kusan mintuna biyu shiru kafin can ya numfasa, ya gyara zaman gilashin idonsa, sannan ya ce da shi, 

"Ka san gidansu yarinyar nan?"

Isah ya ɗan sosa ƙeyarsa, ya ce,
 "A'a gaskiya sir, ban san takaimaiman gidan ba sai dai a nema... Amma dai a cikin ɗan binciken da na yi, na ji cewa a unguwar Rigasa take da zama."

Arman ya jinjina kai. Ya miƙa hannu cikin drower ɗinsa, ya ɗauko wani katon ambulan mai nauyin gaske wanda ke shaƙe da damin kuɗaɗe na dubu-dubu, sannan ya sa wata takarda a ciki wacce ya rubuta kalmar ban hakuri (apologize letter). Ya ɗora ambulan ɗin a kan teburin gaban Isah.

"Ka ɗauka. Ka je unguwar Rigasa ka nemi gidansu yarinyar, maza-maza ka bata wannan saƙon a hannunta."

Isah ya kalli girman ambulan ɗin, ya yi saurin gyaɗa kai, "Okay sir, an gama... but..." Sai ya tsaya yana ɗan fargaba..

Arman ya ɗago da idanuwansa dake cire kwarjini, ya dube shi kai tsaye, "But what?"

Isah ya ɗan sunkuya, "But gaskiya babu mai ko ɗigo ɗaya a cikin motata a yanzu haka sir, ban san ko zan iya ƙarasawa can ba."

Arman ya kauda idonsa ya mayar kan wani file ɗin daban dake gaban sa, ya ce cikin muryarsa ta ko-in-kula, "Ka tafi kawai. Zan yi maka transfer ɗin kuɗin yanzu."

Cikin tsananin murna da fara'a Isah ya ɗauki saƙon ya fice daga ofishin da sauri. Yana tafiya yana murna domin ya san halin ogansa sarai, idan har Arman ya ce zai yi maka transfer na kuɗin mai, to kuwa kuɗin sun fi ƙarfin mai na sati ɗaya, kyauta ce mai tsoka wacce baya taɓa bada kaɗan.

★★★

Tafiyar kusan sa’a guda ta kawo Isah cikin kuryar unguwar Rigasa. Saboda yadda layukan unguwar suke a cushe, sai da ya dinga tsayawa yana tambayar mutane kafin aka kwatanta masa gidan su Amira.. Cikin ikon Allah kuma, a daidai lokacin Malam da Kaka ba sa nan a gidan, sun fita harkokinsu.
Yaron da aka sanya ya ƙira Amira ya dawo ya sanar da shi "tana zuwa.."

Uma ta cire hannunta daga ruwan wanke-wanke, ta kalli Amira cikin mamaki,

 "Kun yi alƙawari da wani ne zai zo miki yau?"

Amira ta zaro idanu cikin gaggawa, "Ni kuwa Uma? A’a wallahi! Sam ban taɓa fita hira ba, kuma ni ba ni da wani saurayi."

Uma ta ɗan yi murmushi tana kallon ƴar tata, 

"To meye a ciki idan saurayi ne ya zo miki? Ai kin kai aure Amira, shekaru goma sha tara ai ba nan ba ne. Matan da kuka fito tare duk suna gidajen aurensu."

Amira ta langwaɓar da kai cikin shagwaba, 

"A’a Uma, ni karatu zan yi. Sai na karanci likita, na samu aiki tukunna na fara zancen soyayya."

Uma ta jinjina kai, "Allah ya bamu iko to. Amma dai tunda an ce baƙo ne, tashi maza ki wanke jikinki." 
Ta tura Amira, ta sa ta wanke jikinta sannan ta sanya mata hijabi mai kyau kafin ta fita..

Amira tana tura tsohon ƙyauren gidan ta fito, tana ganin wata danƙareriyar mota a fake a ƙofar gidan, sai da gabanta ya yanke ya faɗi. Ba ta taɓa tsammanin mai mota zai zo gurin ta ba, musamman a wannan lokacin da take cikin kunci..

Isah ya turo ƙofar motar ya fito, ya karɓe ta da fara'a, "Sannunki Malama Amira... Kin yi mamakin gani na ko?"

Amira ta kasa magana, sai dai kawai ta jinjina kanta..

Isah ya yi murmushi, "Ki kwantar da hankalinki, ba sace ki zan yi ba. Matso nan gaba kaɗan."

 Ya soma jan ta da wasu surutai domin ta saki jikinta..

A daidai wannan lokacin kuwa, Khadijah ta dawo daga ɗiban ruwa, ɗauke da bokiti a kanta, ta gibta ta gefen motar ta shiga gidan..

 Tana ajiye bokitin, Uma ta taya ta sauƙe wa.
Khadijah ta ja numfashi tana kallon mahaifiyarta, "Uma, yau ɗin mai mota ne a ƙofar gidan nan, wai gurin Aunty Amee ya zo?"

Uma ta zabura, gabanta ya faɗi, "Mai mota kuma?! Ya zo gurin Amira?"

"Daman ba ki san ta fita ba ne?" Khadijah ta tambaya tana zaro ido.

Uma cikin damuwa ta ce, "Na sani... na ɗauka wani ƙaramin mutum ne na unguwa, amma kuma mai mota?"

Nan take ran Uma ya ɓaci, tunawa da irin wulaƙanci da muzancin da masu kuɗi suka yi wa ɗiyarta a gaban makaranta... Cikin fushi ta ce a ranta,

 “Yanzu abun yana so ya zama gaskiya kenan? Daga batun jaka yanzu kuma za a fara biyo ta har gida? Meye damuwarsu da za su dinga shiga rayuwar yarinya? Meye na biyo ta har gida? To gaskiya ba zai yiwu ba.”

Uma ta shiga ɗaki da sauri, ta ɗauko hijabinta ta zura, ta yi hanyar waje fuskarta babu fara'a..

A daidai wannan lokacin kuwa a waje, Isah ya gama sanar da Amira saƙon ogansa Doctor Arman. Ya zura hannu ya miƙa mata ƙaton envelop ɗin kuɗin da takardar apologize letter ɗin..

Amira ta yi sololo da idanu tana kallon saƙon, tun da ta fito bayan gaisuwa ta kasa cewa uffan saboda tsabar fargaba..
Garin haka sai ga Uma ta fito ta sha gabansu. Isah ya gyara tsayuwa ya gaishe ta cikin ladabi.

Uma ta amsa fuskarta a ɗaure, ta ce,
 "Meye ne ya kawo ka gidan nan?"

Isah ya natsu, ya bayyana mata dukan saƙon da ke tafe da shi na ban haƙuri daga Doctor Arman..

Uma ta girgiza kai, "Ka je ka ce da shi ya yi haƙuri, amma babu wani abu nashi da za mu karɓa... Kuma ka ce da shi, don Allah, don ƙaunarsa da iyayensa, ya ɗauke idonsa a kan ɗiyata, su kyale mu mu rayu cikin talaucinmu."

Isah ya yi saurin cewa, "A’a Mommy, daman babu wata alaƙa tsakaninsa da ita, kuma ba wai nemanta yake ba. Ya turo ni ne kawai don a ba ku haƙuri a kan abin da ya faru na rashin mutuncin da aka yi mata."

Uma ta ɗan sauƙo, "Ayyah... mun gode sosai. Wallahi mun yafe duniya da lahira. Don Allah ka tafi kar mutane na unguwa su ƙara ganinku su fassara wani abu daban kuma."

Isah ya sake miƙa envelop ɗin, yana so lallai su karɓi kuɗin, amma sam Uma ta ƙi barin Amira ta saka hannu ta karɓa. Ganin za a ɓata lokaci, Isah ya matso ya manna wa Amira envelop ɗin kuɗin da takardar a hannunta da ƙarfi..

Uma ta harzuƙa, ta fizge kuɗin ta datsa wa Isah a ƙirji, sannan ta hankaɗa Amira tana jan hannunta suka koma cikin gida. Ɓacin rai da sauri ya sa ba su ankara cewa farar takardar letter ɗin ta suɓuce ta faɗi a ƙasa ba..

Isah ya tsaya yana kallon ƙofar da aka rufe, ya taɓe baki ya ce,

 "Wallahi kun yi wa kanku... Ko ba komai ai kowa ya san kuna da buƙatu a gidan nan, da kun karɓi kuɗin nan zai muku amfani." Haka ya gama surutunsa na takaici, ya shige motarsa ya fice daga unguwar..

Khadijah dake tsaye a bakin ƙofar gidan tana leƙen abin da ke faruwa, duk ranta ya ɓaci da ganin yadda Uma ta ƙi karɓan kuɗin.. Daga ganin kaurin ambulan ɗin, ta san kuɗin sunada yawa, domin za su kai naira dubu ɗari biyar...

Tana juyawa zata koma ciki, sai idonta ya kai kan farar takardar dake ajiye a ƙasa cikin ƙura. Ta leƙa ta tabbatar Uma ba ta kallo, ta tsuguna da sauri ta ɗauke takardar ta ɓoye ta a jikinta, sannan ta shige cikin gida..

Tana shiga ɗaki ta sami Amira zaune, Khadijah ta matso cikin sanɗa, ta ɗuko takardar ta miƙa mata a ɓoye, ta ce,

 "Aunty Amee, gashi... takardar ce ta faɗi a waje na tsinto miki, kar Uma ta gani."

Amira ta karɓi takardar tana kallonta, zuciyarta na dukan uku-uku..

Amira ta matse takardar da kyau a tafukan hannunta, jikinta na ɓari saboda tsoron kar Uma ta shigo ta same ta da ita. Ta kalli sashen da Uma take tana aikin gyaran ɗaki, sannan ta yi saurin daidaita muryarta ta ce, 

"Uma, zan shiga banɗaki."

"To, sai kin gaya mun Amira?," Uma ta amsa ba tare da ta zargi komai ba..

Amira ta faɗa banɗakin da sauri, ta tura tsohuwar ƙofar ta saka sakata.. Duka hankalinta ya karkata ne a kan farar takardar hannunta..
Cikin sanɗa ta baje takardar dake naɗe, wacce ke fitar da wani ƙamshin turaren maza na alfarma, wanda ko a mafarki Amira ba ta taɓa jin irinsa ba..

 Rubutun jiki na hausa ne, an tsara shi da kyau cikin takaitattun kalamai na isa da kuma girmamawa.. 

Amira ta zuba wa rubutun ido, ta fara karantawa a hankali cikin ranta...

Da farko, ina mai miƙa maki gaisuwa da fatan alheri. Na rubuta wannan takardan ne ba domin komai ba, sai don na sauƙe nauyin dake kaina a matsayina na musulmi kuma mutum mai daraja.
Abin da ya faru a makarantarku, babban kuskure ne da rashin hankali na matar dake da alaƙa da ni... Ƙage da ƙazafin da aka yi maki, duka na san ba gaskiya ba ne. Na san ba ki san kowa a ahalinmu ba, kuma jakarki ta tsinci kanta ne a motata ta hanyar tsautsayi.
Nayi matukar baƙin cikin ganin yadda aka ci mutuncinki aka tozarta ki a gaban mutane a kan abin da baki sani ba. Saboda haka, na aiko maki da wannan dan takaitaccen saƙon na ban hakuri.
Kada ki damu da maganganun mutane, kowa ya san ke ɗin ta musamman ce... Saƙon kuɗin da aka miƙa maki kuma, ba wai na siyan mutuncinki ba ne, tallafi ne na musamman don share maki hawaye da kuma taimaka maki a kan matakin karatunki na gaba.
Ina maki fatan alheri a rayuwa...

Amira ta gama karanta wasiƙar, ta tsaya tana kallon takardar. Wani irin nauyayyen numfashi ya suɓuce mata, ta dafe ƙirjinta dake dukan tara-tara..
Mamaki daban, fargaba daban. Ba ta taɓa tsammanin babban mutum wanda labarinsa da kwarjininsa ke cika gari zai iya aiko mata da wasiƙar ban haƙuri har cikin gidansu ba. Kalamansa sun dake ta, sun sanyaya mata takaici da raɗaɗin da take ji a zuciyarta tun ranar..

"Ashe ya san ba ni da laifi..." ta furta a hankali muryarta na rawa, yayin da hawaye masu ɗumi suka wanke mata fuska, suka ɗiga a jikin takardar. Ta ji wani sanyi a ranta domin sanin cewa mutumin da aka haɗa ta da shi bai yarda da ƙazafin da aka yi mata ba.
Ta naɗe takardar da sauri ta ɓoye ta a cikin rigan bra ɗinta, ta wanke fuskarta da ruwan butan da ta shigo da shi, sannan ta buɗe ƙofar ta fito, fuskarta ɗauke da wani sabon yanayi wanda ita kanta ba zata iya fassara shi ba...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol