ƘULLI A DUHUFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

ƘULLI A DUHU

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

➰🗝️ ƘULLI A DUHU 🗝️➰NA🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️KARAMCI WRITER ASSOCIATION(Karamci tusheñ mu'amala ta gari.)Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai.PAGE 1️⃣Wangame ƙofar ƙatoton gate ɗin ƙayataccen gidan aka yi,  wata farar mota ce ta fara sawo kai, kafin wasu baƙaƙen motoci guda huɗu su danno kai biye da ita a baya, a sukwane suka shiga cikin gidan.Suna isa wajen parking, aka buɗe baƙaƙen motocin. Wasu manyan manyan ƙattai masu ji ƙarfi, sanye da baƙaƙen kaya, fuskar sam babu annuri, suka fito daga motar cikin hanzari suka zagaye farar motar. Ɗaya daga cikin su ya buɗe murfin motar.A hankali wasu kyawawan ƙafafu suka bayyana, waɗanda ke sanye cikin takalmi ƙirar (Gucci Horsebit Loafers), kafin gangar jikin ta bayyana baki ɗaya.Wani kyakkyawan mutum ne mai zubin fulani ya bayyana, sanye yake da White Luxury Tailored Three-Piece Suit, waɗanda suka yi matuƙar haska farar fatarsa. Fuskarsa babu yabo ba fallasa, ya fara takawa cikin isa da ƙasaita irin na wanda jin daɗi da kuɗi suka ratsa shi. Take manyan zaratan mazan suka take masa baya cikin hanzari.Kai tsaye ya doshi katafaren mansion ɗin da ke gabansa, wanda ke ɗauke da bene hawa hawa har uku. Faɗar irin haɗuwa da tsaruwar ginin ma ɓata baki ne, a gefen ginin an tsara wasu sassa daban-daban masu kyau da tsari.In ka kalli gidan, ko'ina zagaye yake da ma'aikata daban-daban, suna harkokin gabansu. Suna hango mai gidan nasu suka fara baro inda suke suna zuwa suna miƙo gaisuwa cikin girmamawa.Kai kaɗai yake gyaɗa musu ba tare da ya furta komai ba, a haka har ya isa bakin ƙofar.Ɗaya daga cikin mutanen da ke take masa baya ne ya yi saurin zuwa ya danna wani abu kamar remote, take ƙofar farlon ta buɗe.Mutumin na zuwa bakin ƙofar, mutanen da ke biye da shi a baya suka dakata.Koda ya sanya ƙafarsa a farlon kuwa, ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon sabuwar duniya.Faɗar irin tsaruwa da haɗuwar farlon ma ɓata baki ne, kai tsaye za a iya kiransa da aljannar duniya.Sai dai na barku ku hasaso irin haɗuwa da kyawun farlon, don in nace na rubuta muku sai mu cinye shafi guda tass.Babu kowa a cikin farlon, sai wani irin ƙamshin ni'ima mai sanya nutsuwa da ke tashi. Kai tsaye ya doshi hanyar Upstairs, bai fi taku uku zuwa huɗu ba, muryar wata dattijiya ta ratsa kunnuwansa."Yallaɓai, barka da dawowa."Dakatawa ya yi daga tafiyar da yake, ya juyo ya kai kallonsa gare ta. Tana tsaye a bakin ƙofar kitchen, kanta a sunkuye.Dattijiwa ce mai kimanin shekaru 60, sanye cikin riga da zani na atamfa.Kamar wanda ba ya son magana ya amsa da, "Barkammu dai Baba, fatan komai lafiya?"Ta riga da ta san abin da yake nufi, hakan ya sa ta ɗan tako zuwa bakin benen cikin ladabi ta ce, "Babu wata matsala yallaɓai.Jinjina kai ya yi, ba tare da ya furta komai ba ya juya zuwa saman.Juyawa tsohuwar ta yi, ta koma kitchen.A ha...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play