Free chapter · Read without an account
Chapter 1
➰🗝️ ƘULLI A DUHU 🗝️➰
NA
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️
KARAMCI WRITER ASSOCIATION
(Karamci tusheñ mu'amala ta gari.)
Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai.
PAGE 1️⃣
Wangame ƙofar ƙatoton gate ɗin ƙayataccen gidan aka yi, wata farar mota ce ta fara sawo kai, kafin wasu baƙaƙen motoci guda huɗu su danno kai biye da ita a baya, a sukwane suka shiga cikin gidan.
Suna isa wajen parking, aka buɗe baƙaƙen motocin. Wasu manyan manyan ƙattai masu ji ƙarfi, sanye da baƙaƙen kaya, fuskar sam babu annuri, suka fito daga motar cikin hanzari suka zagaye farar motar. Ɗaya daga cikin su ya buɗe murfin motar.
A hankali wasu kyawawan ƙafafu suka bayyana, waɗanda ke sanye cikin takalmi ƙirar (Gucci Horsebit Loafers), kafin gangar jikin ta bayyana baki ɗaya.
Wani kyakkyawan mutum ne mai zubin fulani ya bayyana, sanye yake da White Luxury Tailored Three-Piece Suit, waɗanda suka yi matuƙar haska farar fatarsa. Fuskarsa babu yabo ba fallasa, ya fara takawa cikin isa da ƙasaita irin na wanda jin daɗi da kuɗi suka ratsa shi. Take manyan zaratan mazan suka take masa baya cikin hanzari.
Kai tsaye ya doshi katafaren mansion ɗin da ke gabansa, wanda ke ɗauke da bene hawa hawa har uku. Faɗar irin haɗuwa da tsaruwar ginin ma ɓata baki ne, a gefen ginin an tsara wasu sassa daban-daban masu kyau da tsari.
In ka kalli gidan, ko'ina zagaye yake da ma'aikata daban-daban, suna harkokin gabansu. Suna hango mai gidan nasu suka fara baro inda suke suna zuwa suna miƙo gaisuwa cikin girmamawa.
Kai kaɗai yake gyaɗa musu ba tare da ya furta komai ba, a haka har ya isa bakin ƙofar.
Ɗaya daga cikin mutanen da ke take masa baya ne ya yi saurin zuwa ya danna wani abu kamar remote, take ƙofar farlon ta buɗe.
Mutumin na zuwa bakin ƙofar, mutanen da ke biye da shi a baya suka dakata.
Koda ya sanya ƙafarsa a farlon kuwa, ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon sabuwar duniya.
Faɗar irin tsaruwa da haɗuwar farlon ma ɓata baki ne, kai tsaye za a iya kiransa da aljannar duniya.
Sai dai na barku ku hasaso irin haɗuwa da kyawun farlon, don in nace na rubuta muku sai mu cinye shafi guda tass.
Babu kowa a cikin farlon, sai wani irin ƙamshin ni'ima mai sanya nutsuwa da ke tashi. Kai tsaye ya doshi hanyar Upstairs, bai fi taku uku zuwa huɗu ba, muryar wata dattijiya ta ratsa kunnuwansa.
"Yallaɓai, barka da dawowa."
Dakatawa ya yi daga tafiyar da yake, ya juyo ya kai kallonsa gare ta. Tana tsaye a bakin ƙofar kitchen, kanta a sunkuye.
Dattijiwa ce mai kimanin shekaru 60, sanye cikin riga da zani na atamfa.
Kamar wanda ba ya son magana ya amsa da, "Barkammu dai Baba, fatan komai lafiya?"
Ta riga da ta san abin da yake nufi, hakan ya sa ta ɗan tako zuwa bakin benen cikin ladabi ta ce, "Babu wata matsala yallaɓai.
Jinjina kai ya yi, ba tare da ya furta komai ba ya juya zuwa saman.
Juyawa tsohuwar ta yi, ta koma kitchen.
A hankali ya tura ƙofar ɗakin, wanda ba a iya ganin komai sakamakon rashin hasken da ba a kunna ba.
A hankali ya kai hannu ya danna makunnin fitilar ɗakin dake manne a jikin bango, take ko'ina ya cika da haske.
Kallonsa ya kai kan haɗaɗɗen gadon alfarmar, tana kwance kamar yadda ya bar ta, jikinta lulluɓe da luntsumemen bargo mai laushi, fuskar nan ta yi fayau, kyawawan idanunta a rufe tana sauke numfashi a hankali.
Sai da ya fara cire suit ɗin jikinsa, ya riƙe ta a hannunsa kafin ya fara takawa zuwa gadon idanunsa a kan fuskarta.
Ajiye rigar ya yi a gefen gadon, kafin ya zauna ya kai hannu ya cire takalmin ƙafarsa da safar, ya hau gadon baki ɗaya.
Hannunsa ya kai a hankali ya yaye bargon da ke jikinta, ya matsa sosai haɗe da shigewa ciki ya rungume ta a hankali yana sauke numfashi ba tare da ya ɗauke idanunsa a kan kyakykyawar fuskarta ba. Ita kam ba ma ta san yana yi ba, barcinta take cikin kwanciyar hankali.
Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, ita tana barci shi kuma yana rungume da ita yana aikin kallonta tamkar ya samu TV. kafin ta fara motsa idanunta kaɗan-kaɗan. Jin ta rungume a jikin mutum yasa ta ware idanun baki ɗaya a kan kyakkyawar fuskarsa, ɗan zaro idanunta ta yi, cike da mamaki tana shirin magana ya riga ta.
"Barka da tashi sarauniyar da ke mulkin zuciyar bawan Allah."
Ya furta hakan cikin wata murya mai taushin gaske.
Sai da ta ɗan lumshe idanunta kafin ta ware su a cikin nasa ta saki ƙaramin murmushi mai sanyi, kafin ta buɗe bakinta
"Barka da dawowa mijin baiwar Allah."
Murmushi ya sake sakar mata, ya lallaɓa ya sauke kanta a ƙirjinsa ya kwantar da ita, kafin ya tashi zaune yana kallonta ya ce, "Ina fatan babu wani abu da ya damu gimbiya bayan tafiya ta?"
Lumshe idanunta ta yi daga kwancen da take alamar tabbatar masa da komai lafiya.
Murmushin jin daɗi ya saki,, ya kai hannu ya ɗan lakaci kumatun ta ya manna mata kiss a goshin ta.
Ya ɗago yana bin fuskarta da kallo "Kina jin yunwa?."
Da ido ta yi masa alama da "Eh."
Narke fuskarsa ya yi ya kai hannu ya kama kunnuwansa duka biyun ya marairaice "Ayi min afuwa, wani ɗan aiki ne ya riƙe ni sai yanzu na samu dawowa."
"Baka yi laifi ba."
Ta faɗa a tausashe."
Jinjina kai ya yi cikin kulawa sa hannu ya ɗago ta da dubara sakamakon yanayin jikinta da yake a sake baki ɗaya, da alamun bata da lafiyar da za ta iya motsawa.
Don ba ta motsa ba ko kaɗan har ya yi nasarar jingina ta da jikinsa, yana rungume da ita ya ce, "Wanka za mu fara ko abincin?."
Ƙara kwantar da kanta ta yi a ƙirjinsa.
"Mu fara wanka."
Ta furta a sanyaye.
Jinjina kai ya yi, ya kwantar da ita ya sauka a gadon, toilet ya nufa ya fara haɗa ruwan wanka mai ɗumi wanda ya zuba turarukan wanka masu daɗin ƙamshi, kafin ya ɗauko towel ya dawo kan gado. Cikin dubara ya juyata, sai da ya ɗaura mata towel ɗin sannan ya zare mata doguwar rigar jikinta, idanunta da suka cika da hawaye a kan kyakkyawar fuskarsa tana bin sa da wani irin kallo mai ƙunshe da tarin abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba.
A hankali ta buɗe bakinta.
"Nagode mijina."
Da sauri ya kai ɗaya hannunsa ya rufe bakinta, zuciyarsa cike da tausayinta ya girgiza mata kai cikin taushin murya.
"Babu wannan a tsakaninmu Sa'adah, don Allah kar ki ƙara."
Ba tare da ya ba ta damar magana ba, ya yunƙura ya cicciɓeta gaba ɗaya duk da kasancewarta mai ƙiba, ga kuma larurar da ta haddasa rashin motsa jikinta, bai damu da hakan ba ya fara takawa har sai da ya dangana da toilet.
Kai tsaye ya sauke ta a cikin kwamin wankan da ya haɗa ruwan a ciki, bin sa da kallo Sa'adah take, tana jin wata irin zazzafar so da ƙaunar wadda ke haɗe da tausayi mijin nata na sake ratsa zuciyarta.
Rage kayan jikinsa ya fara yi, shi ma ya shige cikin ruwan wanka, ita ya fara yi wa wanka kafin shi ma ya yi.
Yana gamawa ya ɗaura towel, ita kuma ya naɗe ta cikin rigar wanka tsaf ya sake cicciɓarta ya fito rungume da ita.
Keken guragun da ke a gefe ya nufa da ita, ya ajiyeta cikin dubara, sai da ya ga ta zauna da kyau, sannan ya tura keken zuwa gaban madubi.
Hair dryer ya ɗauka, ya shiga busar da sumar kanta, kafin ya gyara mata gashin tsaf ya tufke shi cikin tsari, tamkar dama can ya saba da hakan.
Daga nan ya shiga shafa mata mai, zuwa gyaran fuska da sanya mata turare, sai ga shi Sa'adah ta fito fesss ta yi wani irin kyau, in ba'a faɗa maka ba za ka rantse lafiyar ta ƙalau.
Wardrobe ya nufa, ya ɗauko wasu ƙananan kaya na shan iska, waɗanda ya san tana matuƙar so a rayuwarta.
Saboda Sa'adah ko lokacin tana da lafiya, ita ɗin ma'abociyar sanya ƙananan kaya ce, takan ce manyan kaya suna takura mata.
Da ido kawai Sa'adah ke kallonsa, har ya gama sanya mata kayan, kafin shi ma ya ɗauko nasa kayan shan iskar ya sanya.
Kallon agogon da ke manne a bangon ɗakin ya yi, ganin ƙarfe 12:30pm, hakan ya sa ya juyo ya kalli Sa'adah cike da kulawa ya ce, "Abincin ko?"
Jinjina masa kai ta yi, tana ɗan shagwaɓe fuskarta alamar tana jin yunwar.
Cikin hanzari ya dawo kusa da ita ya fara tura keken zuwa bakin ƙofar, wani ɗan ƙaramin corridor ya bi da ita, sai ga su sun bayyana a wani haɗaɗɗen farlo wanda ya gaji da kyau, ya ninka farlon farko kyau da komai.
A tsakiyar farlon ya dakatar da tura keken, kafin ya taka zuwa jikin window ɗin ya ɗage labulayen baki ɗaya ta yadda za su iya hango tarin ma'aikatan da ke zirga-zirga a farfajiyar gidan. Ƙara matsar da keken nata ya yi zuwa jikin dining table, ya zauna a kujerar da ke kusa da ita, ya juya ya nufi hanyar barin farlon.
Da ido Sa'adah ta bishi tana ƙara jin tausayin mijin nata na ratsa zuciyar ta.
Shi kam Kamal yana kai tsaye ya sauka zuwa ƙasa, a kitchen ta tarar da Baba tsaye tana jera kulolin abinci a wani babban faranti.
Tana ganinsa cikin ladabi ta sunkuyar da kai ta ce "Yallaɓai barka da sakkowa."
Jinjina mata kai ya yi "Yawwa Baba." Ya amsa a
taƙaice.
"Yallaɓai sama za'a kai ko anan za'a ajiye."
Baba ta tambaya tana nuna masa abincin da ta jera.
Hannu ya miƙa mata "Babu buƙatar hakan, daga yau in kin kammala ki ajiye a farlon ƙasa in na zo zan ɗauka. Babu buƙatar ki sake hawa sama."
Cike da mamakin maganar tasa Baba ta ɗauki babban farantin ta miƙa masa.
Yasa hannu ya karɓa ya juya, bayansa ta bi da kallo zuciyarta cike da saƙe-saƙe.
Saman Kamal ya koma, ajiye abincin ya yi a dining ɗin.
Ya ja kujera ya zauna yana bin Sa'adah da murmushi ya shiga zuba musu abincin, cike da soyayya ya fara amfani da hannunsa yana ɗiba yana ba ta, har sai da ya ga ta kauda kanta alamar ta ƙoshi, ya tsiyaya mata ruwa a glass cup ya bata. Cikin kulawa ya yago tissue Paper ya goge mata baki.
Sannan ya ja plate ɗin shi ya fara ci cike da natsuwa.
Sai da ya ƙoshi ya ture plate ɗin, yana shirin kwashe kwanukan ne ya ji muryar Sa'adah "Me zai hana ka sake nemo wata ƴar aikin, ko dan irin wannan ayyukan suna yi maka yawa."
Dakatawa ya yi ya ajiye abubuwan dake hannunsa ya ɗora hannuwansa akan teburin yana kallon ta "Sa'adah, a halin yanzu bana jin zan sake ɗaukar wulaƙanci daga koma waye akan ki, bare kuma ƴan aiki.
Da wani ya wulaƙanta min ke gwara na kashe duk wasu harkokina na tsaya na kula dake, ba zan yarda na ƙara kuskuren dana aikata a baya ba."
Buɗe baki Sa'adah ta yi tana shirin magana, da sauri Kamal ya ɗaga mata hannu muryarsa na fita da ɗan zafi ya ce "Na roƙe ki, kar ki sake tada maganar nan don Allah."
Ba don ran Sa'adah ya so ba, ta jinjina masa kai tana kallon yadda ya kwashe komai ya gyare wajen tsaf zuciyarta cike da tausayin shi, akan irin hidimar da ya ke yi mata dare da rana.
Dawowa ya yi, ya ja keken guragun da Sa'adah ke kai ya matsar da shi cikin windon farlon sosai, ta yadda suke iya hango komai da ke gudana a cikin gidan da yadda ma'aikata ke zirga-zirgar su cike da himma.
Tsugunnawa Kamal ya yi a gefen keken Sa'adah ya ɗora hannunsa guda a cinyarta, yana murmushi yana kallon fuskarta.
Yana iya hango ƙauna da begen da ke ƙunshe a kallon da take yi wa mutanen dake farfajiyar gidan, ɗan kauda kansa ya yi yana jin wani abu na motsawa a zuciyarsa.
"Kina son sauka ƙasan ne?"
Ya jefa mata tambayar haɗe da maida kansa zuwa inda take kallon wani ma'aikaci dake bawa fulawowi ruwa.
A bazata tambayar ta zo wa Sa'adah, hakan ya sa ta yi saurin juyo da kanta ta kallesa, bisa ga mamakinta sai ta ga shi ma inda take kallo ya ke kallo da kyakkyawan murmushi bisa fuskarsa.
"Ƙwarai ina nufin kina son sauka ƙasa ki ga yanayin gidan?"
Ya faɗi hakan haɗe da ɗauke kansa ya juyo ya fuskance ta baki ɗaya.
Lokaci guda idanun Sa'adah suka cika da hawaye, a hankali ta maida kanta ta kwantar a jikin keken ta lumshe idanunta, hakan ya ba wa hawayen da take riƙewa damar zubowa.
Ganin hawayen ta ba ƙaramin tada masa hankali ya yi ba, cikin sauri ya miƙe zagaya ya durƙusa a gabanta, fuskarsa cike da damuwa ya riƙo hannayenta yana ɗan matsawa a hankali.
"Kuka kuma Sa'adah?"
Kasa ɗagowa ta yi ta kallesa, sai hawayen da ke sintiri a fuskarta tamkar an buɗe famfo.
"Haba Sa'adah, ya ya kike so na yi? Kin fi kowa sanin yadda kukanki ke ƙona min zuciya, ki yi haƙuri ki manta da komai mu rungumi ƙaddarar mu, in sha Allahu watarana sai labari."
Ya ɗan dakata yana sauke numfashi da sauri da sauri.
Jin ya yi shiru ne ya sa Sa'adah dakatawa da kukan da take, ta ɗago ta kallesa sai ta ga shi ma ita yake kallo, ɗan kauda kanta ta yi haɗe da runtse idanunta ta buɗe su kafin ta fara magana cikin raunin murya.
"Ya Kamal na gaji, na gaji, zuciyata ta yi rauni, a kullum ina kallon kaina a matsayin matsala wa rayuwarka, na zame maka wani nauyi mai girma a gare ka Ya Kam..."
Da sauri Kamal ya sanya hannu ya rufe bakinta yana girgiza mata kai, hawayen tausayin matar tasa na zuba a idanunsa, an rasa wanda zai yi magana a cikin su, ba ka jin komai sai shashshekar kukan Sa'adah.
Cikin taushin murya Kamal ya fara magana.
"Haba Sa'adah, waye ya faɗa miki ke ɗin matsala ce a gare ni? Ki sani matsayin ki bai taɓa canjawa a gare ni ba, a kullum addu'a nake akan Allah ya ba ki lafiya, ya kuma ba ni ikon kulawa da ke da riƙe amanarki har ƙarshen rayuwarmu."
Murmushi mai ciwo Sa'adah ta saki, tana ƙoƙarin danne abin da ke taso mata.
"Me yasa ba za ka amince ka maida ni gaban su Ummah dan su kula dani ba kamar yadda suka buƙata? Nauyin ya yi maka yawa Ya Kamal, yakamata ka duba ka maida ni gida don iyayena su kula dani, ba za ka iya ba kai kaɗai. Bai kamata ace babban mutum kamar ka bai yana ɗawaniya da ni haka ba, yanzu lokaci ne da ya kamata ace kana jin daɗin rayuwarka, na yi na yi akan ka ƙara aure nan ma ka ce min a'a, bayan kasan Hajiyarka bata da burin da ya wuce taga jikanta a duniya."
Ta ɗan tsagaita da maganar tana kallon yadda ya zuba mata ido tamkar zai haɗiye ta.
"Wato ina magana ka maida ni kamar wata TV kana kallona ko?"
Ta faɗi hakan da muryar kuka cikin shagwaɓa da raunin murya.
Murmushi mai laushi Kamal ya saki, wanda ya ƙara bayyana zallar kyawunsa, kafin ya ɗage kafaɗarsa ya ƙara matsawa ya haɗe gwiwarsa da tata idanunsa akan fuskar ta
"Ni gaba ɗaya ma ban fahimci abubuwan da kike cewa ba Sa'adah. Fuskar ki kaɗai in na kalla na saka ni na manta komai a duniyar nan, ina jin wani musulmin daɗi da nishaɗi na mamaye ni." Ya ɗan dakata haɗe da kai hannuwansa duka biyun ya riƙo fuskarta yana ɗan shafa kumatun ta, ya cigaba da magana "Bare in na tuna ke ɗin tawa ce nakan ji kaina a matsayin mai sa'a a rayuwata, Sa'adah ki sani duk duniya babu macen da zan iya aura na haɗa soyayyar ki da tata, in kuwa na sake na yi hakan ina mai tabbatar miki da ba zan iya yin adalci a tsakanin ku ba, ba zan iya bata lokacina ba koda kuwa minti ɗaya ne daga rayuwata da sunan soyayya. Saboda haka ki rufe babin nan kawai ki cigaba da haƙuri da soyayyar da nake miki har zuwa lokacin da Allah zai kawo ƙarshen ciwon ki, in sha Allahu na san za mu yi farin ciki Sa'adah."
"Ammah Ya Kamal na san wane ne kai, shin haka za ka cigaba da zama dani bana amfana maka ko......"Sake rufe mata baki ya yi yana girgiza mata kai, duk yadda Sa'adah ta so yin magana, Kamal ya hana ta furta komai. Bisa dole ta ja bakinta ta yi shiru, zuciyarta cike da tausayin mijin nata na irin ɗawaniya da wahalar da yake yi a kanta a matsayinta na mai larurar da ba ta iya ko ɗaga hannunta,bare ta amfana masa ta hanyar mu'amalar aure, bayan kanta da take iya motsawa da bakinta da take magana da shi, babu wani abu da ke motsi a jikinta, takan ji tausayin mijin na ta musamman da ta san shi ɗin mai yawan buƙata ne.
Wannan larurar tata yau tsawon shekaru biyu kenan, kuma Kamal bai taɓa nuna gajiyawa ko kyamar ta ba, hidima yake mata da kuɗinsa da ƙarfin sa, a duk inda yake baya yarda ya shafe awa uku bai waiwayo gida ba, duk da tarin dukiya da kuɗin da Allah ya ba shi, hakan bai sa ya ƙara aure ba duk da yana shan faɗa daga mahaifiyarsa da 'yan uwansa a kan hakan, sai dai ya toshe kunnuwansa, yakan ce Sa'adah matarsa ce, shi ya ga zai iya zama da ita a yadda take.
Cikin dubara Kamal ya shiga jan Sa'adah da hira, har ya yi nasarar kauda mata tunanin da ke damunta. Sai ga Sa'adah ta sake har da su dariya sakamakon labaran ban dariyar da ya dinga kawo mata.
Kiran sallar azahar da ya ratso kunnuwansu daga cikin masallacin da ke bakin gate, shi ya sanya Kamal ya tura keken nata zuwa toilet ɗin da ke farlon, don dama duk lokacin da yake gida a wannan farlon suke wuni, ko sallah baya yarda ya fita zuwa masallaci duk da a cikin gidan yake, yakan tsaya ya ja su sallah duk da Sa'adah tana yin ta ne daga kan keken, tunda ba iya motsawa take ba, takan ayyana komai a zuciyarta kamar yadda addini ya koyar ga mara lafiya irin ta.
KATSINA
"Zahra! Zahra!! Zahra!!!"
Wata mace kakkaura baƙa mai zubin samudawa ke furta sunan, tana tsaye a ƙofar ɗan ƙaramin ɗakin jar ƙasar wanda ko fulasta babu, sai wani ɗan ƙaramin ƙyauren langa-langa wanda yake daf da ɓallewa, da wani yololon tsumman labule wanda saboda tsabar wahala har ya fara yayyagewa.
Wata kyakkyawar budurwa ce fara tas, ta buɗe labulen ta fito jikinta na rawa don amsa kiran mahaifiyar tata.
Matar na ganinta ta ƙanƙance ido tana bin jikinta da kallo, baki a buɗe. Sunkuyar da kai yarinyar ta yi tana ɗan jan wuyan rigar makarantar da ke jikinta.
Ta riga da ta san abin da zai biyo baya, amma ba ta da wani zaɓi ne da ya wuce ta yi hakan, don a zahirin gaskiya in ta ci gaba da biyewa uwarta, ta san sai dai ta tashi babu wan ba ƙanin.
Tsawar da Saude ta daka mata ne ya sa ta yi firgigit ta ɗago.
"Ya ina magana kin sanya ni gaba kin faɗa tunanin naki na jaraba? To in kin gama ki wuce ki sanya hijabi ki zo ki je wajen Bala mai shago ki ce ya auna min waken awara kwano goma, in na juya muka siyar zan kawo masa kuɗin sai na sake amsar wani."
Rau-rau Zahra ta yi da ido, ta ɗago ta kalli mahaifiyarta, duk da irin shakkarta da take, haka ta buɗe baki murya na rawa ta ce.
"Babarmu, bai kamata ki ƙara cin bashin Bala ba, kina ganin wancan karon yadda kuka ƙare da shi. Da ace juyawa za mu yi ta hanyar sana'a da sauƙi, amma kullum sai dai ki ciyo bashin mutane ki karyar da farashin ki siyar, ki ƙara ciyo wani. Haba Babarmu ki duba kullum..."
Tun da ta fara magana Saude ta ƙanƙance idanunta tana kallon ta, tana ji tamkar ta fusgota ta yi ta jigba tsabar takaici. Kasa jure maganganun 'yar tata ta yi, hakan ya sa ta daka mata wata uwar tsawa cikin masifar da ke cinta ta fara magana bakinta har kumfa yake tsabar masifar dake cinta
"Ke wace ce da za ki sanya ni gaba kina faɗa min magana haka Zahra, dan ubanki ba don bashin da nake ci ba, za ki girma haka har ki yi wayon da za ki tsaya gabana kina faɗa min magana."
Ta dakata tare da nuna Zahra da jikinta ke rawa da hannu
"Ki wuce ki amsa min ko ranki ya ɓaci, mara zuciya wadda ta gaji tsiya da talauci daga faƙirin ubanta, inda yana wadatamu ai da ban ci bashin kowa ba na zauna lafiya."
Jiki na rawa Zahra ta koma ɗaki tana jin wani ɗaci da ƙuna a zuciyarta, wasu zafafan hawaye suka fara sintiri a bisa kumatunta.
Hijabinta ta ɗauka har ƙasa ta zumbula a kan uniform ɗin makarantar bokon da ke jikinta, ta fito daga ɗakin.
Saude na ganinta ta ɗaga murya
"Sauran in kin je ki tsaya a bakin shagon kar ki shiga, wallahi in kika bari na biyo bayan ki ba za ta yi miki kyau ba."
Ba tare da Zahra ta ce komai ba, ta juya ta nufi ƙofar fita daga ɗan ƙaramin gidan nasu.
Tun da Zahra ta fita ƙofar gidan nasu ta sunkuyar da kanta, sakamakon hango cambar da ke gaban gidansu cike da tarin mazajen unguwar a zaman tsurku da gulma, waɗanda a kullum safiyar duniya sai sun zauna har zuwa lokacin da wasu daga cikin su za su tafi kasuwa, wajen yakan rage ƴan tsiraru waɗanda ake kira da ƴan zaman kashe wando.
Aikuwa tana zuwa daidai inda suke, ta ji sun yi tsit alamar ita suke kallo.
Wani irin haushi da takaici ne ya turniƙe Zahra, har ta sha kwanar kantin Bala tana jin idanunsu na yawo a jikinta. A zuciyarta ta ce, _Mutane ba su da aiki sai sa ido da aibata 'ya'yan wasu._
Koda ta isa ƙofar shagon Bala, ta tarar da kantin a cike da masu siyayyar safe, hakan ya sa ta raɓe a gefe ta kasa shiga har sai da ta ga ya rage wata yarinya a ciki, sannan ta shiga ta tsaya a kusa da yarinyar cikin ladabi ta ce.
"Bala ina kwana?"
Sai da Bala ya lissafa canjin yarinyar ya miƙa mata, kafin ya juyo ya kalli Zahra ransa a haɗe ya ce.
"Lafiya ƙalau."
Jikin Zahra a sanyaye da yanayin nasa ta ɗan gyara tsayuwarta.
"Dama Babarmu ce ta aiko ni, ta ce ka auna min waken awara mudu goma, in muka juya za ta kawo maka kuɗin."
A GIDAN SAUDE
Saude na ganin fitar Zahra, ta yi sauri ta shige wani ɗaki da ke kusa da wanda Zahra ta fito.
Dama gidan duka ɗakuna biyu ne sai ɗan zagayen da aka yi da langa-langa, nan ne banɗakinsu wanda babu rufi, ko arziƙin kitchen ba su da shi sai wata tsohuwar rijiya da ke a tsakiyar gidan, wadda a yanzu ba a ɗiban ruwa, bola ma suke zubawa a ciki.
Babu komai a ɗakin sai wani ɗan ƙaramin gado na katako mai farin painti, sai wata ƴar yololuwar katifa wadda gaba ɗaya ta siɗe dake kan gadon. Tsakar ɗakin babu sumunti, sai wani buhu da aka shimfiɗa saman shi duk ƙasa da ƙura.
Kai tsaye Saude ta nufi gadon ta tsugunna ta jawo wata ƙaramar ƙwarya wadda ke rufe da wani jan tsumma.
Zama ta yi dirshan a tsakiyar ɗakin, kafin ta buɗe ƙwaryar dake cike da wasu manyan layu da wasu tarkace masu kama dana tsafi, sai wani ruwa mai launin ja dake cike a wata ƙaramar farar kwalba.
Hannu ta kai ta ɗauki wata laya ta sanya a bakinta, ta buɗe kwalbar nan ta karɓi ruwan dake wani irin tashin wari da hamami a bakinta.
Miƙewa ta yi tsaye ta fara zagaya ƙwaryar tana wasu irin sambatu marasa daɗin ji, kafin ta kalli gabas ta kira sunan Bala da ƙarfi sau uku, haka ta dinga juyawa gabas da yamma kudu da arewa tana kiran sunan Bala mai shago, a ƙarshe ta tsugunna ta ɗauki ƙwaryar tana jujjuyata, tana wata irin dariya tana ce wa "Bala ka aunawa Zahra waken suya kwano goma kamar yadda na buƙata." Sau uku ta ambaci hakan, kafin ta sauke ƙwaryar ta cire layar bakinta idanunta sun kaɗa sun yi jajir, ta maida komai yadda ya ke ta rufe ƙwaryar ta maida ƙasan gadon, sannan ta koma bakin gado ta zauna tana sakin wani mugun murmushi.
*Me ku ke tunanin zai faru?🤔 Ku dai ku cigaba da bibiyar.......*
*🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*
***