Free chapter 路 Read without an account
3
by Sadik Abubakar 路 SAHURA 馃挅
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
Shafi Na 3
"Umma wallahi wannan 'yar iskar ce ta daki Hafsat a ciki, har ta fadi wai don ta ce ta yi mata wanki, shi ne ni kuma na rama mata."
Muryar Salim ke nan wacce har yanzu ba ta da maraba da ta makakke. Hafsat kuwa kwantar da kai ta yi jikin Umman tana kukan shagwaba tare da cewa, "Umma wannan tsinanniyar yarinyar ta bar mana gidanmu kawai, ba ta da mutumci ta koma can kauyensu mu huta."
A yatsine Umma ta juya ta dubi Sahura wacce tuni lebe ya sumtume mata saboda dukan da Salim ya yi mata a bakin ta ce, "Kadan ki ka fara gani indai za ki rika yi musu abin da bai dace ba. Maza ki tashi daga nan ki je ki wanke wannan bakin jinin naki marar mutunci. Kuma wallahi idan kika kuskura kika fada wa wani abin da ya faru, ni da ke ne. Koda Faruk ya tambaye ki me ya same ki, ki ce masa bugewa kika yi da kofa."
Sai ta juya ga su Salim kuma ta ce, "Kun yi mini daidai duk lokacin da ta yi muku rashin mutumci ku yi mata duk abin da kuka gadama ni na saku."
Allah Sarki maraici ba dadi! Da kyar Sahura ta rarrafa toilet ta wanke fuskarta, jikinta har ya fara tsami saboda ta bugu sosai a hannunsu. Ga shi har yanzu jinin da ke zuba a goshin ta yaki tsayawa, falo ta dawo ta zauna tana goge jinin da zanenta, tana shasshekar kuka. Umma ce ta sake dawowa falon ta ce mata, "Maza kuma ki tashi ki je ki debi kayan hafsar ki wanke mata su tas!"
Haka nan Sahura ta mike da kyar ta kwashi kayan wanki ta nufi tsakar gida, ta fara wankin ke nan sai kanta ya fara mata wani azababben ciwo kamar zai fice daga jikinta. Tsugunnawa tavyi a daidai lokacin da Faruk yake shigowa gidan, ya gan ta a durkushe, "Ya ya aka yi Sahura?" Tambayar da ya yi mata ke nan, yayin da ta dago kai sai ya ga goshinta a fashe ga kuma lebenta ya kumbura suntum!
*"SubhanAllah!* Me ya same ki haka Sahura? Me ya faru?" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kanta.
Sake tambayar ta ya yi, "Wa ya yi miki haka? Ki yi magana mana."
Kokari ta yi ta dawo da muryar ta daidai domin ba ta son ya fuskanci akwai alamun kuka a tare da ita, muddin ya fahimci haka to zai yi abin da shi ma ransa zai baci a wajen Umma. Don haka sai ta maze ta ce, "Wallahi kofa ce ta buge ni, kuma kaina yana mini ciwo."
"To me yasa ba a aje Chemist ba an yi miki dressing a wajen, an dakatar da zubar jinin? Wannan kayan wankin waye kike wankewa? Wai shin Umma ba ta nan ne, ba ta san kin ji wannan ciwon ba ne?"
Ajiyar zuciya Sahura ta saki sannan ta ce, "Tana nan."
Girgiza kai kawai Faruk ya yi sannan ya ce, "To maza ki ajiye wannan wankin ki dauko hijabinki mu je Chemist a sa miki magani."
Bai gama rufe bakinsa ba sai ga Umma ta fito, harara me zafi ta aika masa tare da cewa, "Na ji duk abin da kake cewa, gwani dan na iya, sarkin tausayi, mu ba mu da tausayi sai kai ko? To babu inda za ta je, idan kika kuskura kika ajiye wannan wankin za ki ga abin da zan yi miki."
Wani irin kallo Faruk ya bi Umma da shi hade da tunanin shin wannan wane irin rashin tausayi ne da rashin imani haka? Ya ya za a yi yarinya ta ji ciwo haka jini na zuba ba ki kai ta Chemist ba, sannan ba ki bar ta ta huta ba sai ma wani aikin wahalar da kika sake ba ta. Kuma sannan ki ce ba za'a kai ta chemist ba? Sam ba zai yi yu ba, dole ne a kai ta ayi mata magani.
Faruk, a zuciyarsa yake wannan zance kafin daga bisani ya ce, "To Umma ya ya za a bar ta da jini yana zuba haka kuma ga shi bakinta ya kumbura, ya kamata a kai ta Chemist koda magani ne a ba ta sannan bai kamata ba a ce ta yi wannan wankin domin shi ma zai iya hana jinin tsayawa sakamakon sunkuyar da kanta da za ta rika yi. Ina ita Hafsat din take, ta fito ta wanke mana ba kayanta ba ne? Ke Sahura tashi mu tafi Chemist."
A fusace Umma ta juyo kansa tare da cewa, "Kai ka fita daga idona in rufe, idan kana son zamanka lafiya, to ka daina shiga al'amuran gidan nan game da yarinyar nan, wata ran sai na tsine maka. Ka ji na fada maka ko, ka tsaya iya matsayinka ba na son shisshigi."
"Umma tunda nake ban taba yin sa'in sa dake ba a kan wani abu, kuma ban taba daga murya ba a kanki, to amma ki sani lokaci ya yi da zan fada miki gaskiya. Abin da kike yi game da Sahura ba ya dacewa. Ya kamata ki sani ita ma fa 'ya ce kamar kowa kaddara ce ta sa ta rabu da iyayenta, ba ita ta zabi haka ba. Shin idan Hafsat ce ta je hannun wata matar ake mata ukuba irin yadda kike wa Sahura ranki zai miki dadi? Shin ba ki san cewa ya dace ki fifita Sahura a kan Hafsat ba? Sahura marainiya ce, *Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa ya yi gargadi akan kuntatawa maraya da cutar da shi, sannan kuma ya yi bushara ga duk wanda ya kula da maraya cewa za su shiga aljanna kafada da kafada da shi.* Umma ya dace ki sauya tunaninki akan yarinyar nan, ki kula da ita da rayuwarta, Allah zai tambaye ki duk yadda kika rike ta. Shin wai ma wane abu yarinyar nan take yi miki a gidan nan wanda ba daidai ba? Babu wani abin da kika taba cewa ta yi ta ce ba za ta yi ba, ko kuma ta yi miki ba daidai ba. Yarinya ce mai kyawun hali da tarbiyya. Yanzu ki duba wata ishara, ko za ki mutu baki isa ki aiki Hafsat ba sai idan ta yi niyya don radin kanta, shin wannan bai ishe ki ki yi tunani ba?"
Duk wannan zantukan da Faruk yake ba su sa Umma ta yi sanyi ba ko ta canja tunani, sai ma wata wulakantacciyar harara da take galla masa, ji take tamkar yana watsa mata garwashi a zuciya. Faruk bai sake magana ba ya wuce daki ya dauko wa Sahura hijabi ya ba ta ya ce ta saka ta tashi su tafi. A tsorace Sahura ta saka hijabin, ya ja hannunta suka fice.
*Whatsapp: ***