Free chapter 路 Read without an account

7

by Sadik Abubakar 路 SAHURA 馃挅

Sadik Abubakar

Lafazi Writers

Wattpad @sadikgg

*SAHURA 07*

Kama hannunsa ta yi ta girgiza sannan ya yi juyi hade da mika, "Kai do Allah ka tashi haka gari ya waye tun tuni, ka tashi ka yi sallah ka zo ka yi breakfast." Nan ya yunkura idanunsa da kyar suke budewa.

Juyowar da Umma za ta yi kofar dakin, idon ta a kan kwalbar syrup din nan, "Inna lillahi Wa Inna ilaihir raji'un!''

Ta fada daidai lokacin da ta dafe kirjinta fuskarta ta sauya lokaci guda sannan ta ci gaba da cewa, "Salim abin da ake fada mini a kanka ashe gaskiya ne? Yanzu rayuwar da za ka jefa kanka ke nan, shan miyagun kwayoyi, me ya hada ka da wannan maganin?"

"Haba Umma don Allah, me yasa kike fadar haka, wai me nake yi ne? WaLlahi kawai Yaya Faruk ne ya samin ido, yau ne fa kawai na sha wannan maganin saboda na gaji ina son in yi barci sosai."

Umma ta ce, "Gajiyar uban me ka yi, aikin me kake yi da za ka gaji? Me ka nema a gidan nan ka rasa? To ka saurare ni sosai, wallahi a wannan zuwan da Abbanku ya yi bayan Faruk ya fada masa duk rashin mutumcin da kake, cewa ya yi zai kai ka a sa maka mari, ni ce na ba shi hakuri. Amma waLlahi muddin ka sake komawa wannan shaye-shayen zan cire hannuna daga maganarka, zan kyale shi ya yi maka duk irin hukuncin da ya gadama, babu ruwana da kai."

"Umma ki yi hakuri shike nan na daina, ba zan sake ba."

Umma ta ce, "To shike nan ka tashi ka je ka yi sallah ka zo ka yi breakfast, ga abincin ka can a kan tebur."

Bayan kwanaki biyu ke nan da kai wa Baba Abu korafin Umma, sai ta shirya tun da safe tayo wa gidan tsinke domin ta zo ta ji ba'asin da yasa Umman take abubuwan da ba su kamata ba. Misalin karfe goma na safe 10:00am ta iso gidan.

Kai tsaye ta shiga ta yi sallama, Sahura ce a tsakar gidan tana wanke-wanke, ta ajiye da sauri ta mike cikin fara'a da murna ta tarbi Baba Abu, "Sannu da zuwa Baba."

Baba Abu da fara'arta ita ma ta amsa wa Sahura, "Yawwa Sahura sannu da kokari, ina mutanen gidan?"

Sahura ta ce, "Suna falo ki karasa."Kafin ta gama rufe bakinta tuni Hafsat ta jiyo muryar Baba Abun, a guje ta fito daga falon ta zo ta rungume ta tana fadin, "Oyoyo oyoyo" Ta ja ta suka yi falo. Umma ce zaune a kan kujera, mikewa tsaye ta yi ta tarbi Baba.

Wani mamaki da tunani Umma ta tafi na dan wani kankanen lokaci dangane da zuwan mahaifiyar tata a irin wannan lokacin haka. Anya lafiya kuwa? To me ke faruwa kuma Baba da safe haka, ba ma za ta aiko Halifa ba da kan ta?

Wannan tunani da kuma yadda Baba Abun ta sauya fuska dai ldai lokacin da suka hada ido, yasa ta dan sha jinin jikinta, amma sai ta kanne kawai ta ce, "Sannu da zuwa, da safe haka kike tafe, in ce ko dai lafiya?"

Baba Abu ba ta ba wa Umma amsa ba, sai ta zauna bisa kujera, ita ma Umman kan kujerar ta koma ta zauna tare da umartar Hafsat da ta kawo wa Baba ruwa da lemo, ta kuma zubo mata abinci. Nan take Hafsat ta make ta nufi kitchen. Kafin Hafsat ta dawo, Umma ta zame daga kan kujera tare da risinawa, ta gai da Baba cikin ladabi da girmamawa, "Ina kwana ina gajiya, ya kuke ya gidan."

Baba Abu wacce ta dan hade rai ta amsa mata, "Lafiya lau."

Umma ta ci gaba da cewa, "Ya ya sahu kuma, kina fama da kafa, ai da kin aiko Halifa ma, in ce dai lafiya ko?"

Baba Abu ta ce, "Ai sakon ya fi karfin aike."

Komowar Hafsat daga kitchen ta katse wa Baba Abu martanin da ta fara mayarwa. Farantai biyu ne cike, daya na abinci daya kuma kayan ruwa da lemuka ne, ta aje gaban Baba Abu ta ce, "'Yar tsohuwa ga abinci nan ki ci ki koshi kin ji na san kin sha tafiya, ki huta." Wata harara Umma ta aika mata wacce ta katse mata tsokanar da take wa kakar tata, sai ta mike ta nufi dakinsu.

Falon ya yi shiru na wasu 'yan dakiku kafin daga bisani Baba Abu ta ce, "Saratu me yasa har kullum ke ba za ki girma ba ne? Ace har kawo yanzu ba ki san Annabi ya faku ba, ba za ki iya magance matsala ba idan ta taso miki, ko kuma in ce ma ke ce da kanki kike kirkiro wa kanki matsalar."

"Baba to me kuma aka ce na yi yanzu, wani abin ne ya faru kuma? WaLlahi mutane dai ba sa kyautawa, gulma da munafurci sun yi yawa, wani ne ya ce miki na yi wani abin?"

Baba Abu ranta a bace ta ce, "Saratu ina guje miki fishin Ubangiji, biLlahillazi idan ba ki sauya halinki da mu'amalarki ba a kan yaran nan, za ki hallaka kanki. Faruk ne ya kai mini korafin kin daina masa magana kuma idan ya gaishe ki ba kya amsawa a kan ya nusar dake wani kuskure da kike aikatawa bisa amanar marainiyar yarinyar nan. Shin yanzu ba abin ki yi farin ciki ba ne tare da godewa Allah, da ya baki yaro nutsatstse wanda zai ga kin yi abin da bai dace ba ya nusar dake? Amma saboda sakarci sai ki dora wa yaro karan tsana? To ina so ki saurare ni sosai da kunnen basira, kar in sake ji, kar in sake gani. Yaron nan yana da kyakyawan hali, ki hada kai da shi, hatta Salim da ke rashin jin nan da kin ba wa Farukun dama da goyon baya, da ya ladaftar da shi, dan uban shi tunda ba shi ya haifi kansa ba. Sannan kuma dangane da ita Sahura, daga yau din nan, ke daga yanzu ma ina son ki dauke ta tamkar ke kika tsugunna kika haife ta. Duk abin da za ki so ya samu Hafsatu, to ki so wa Sahura shi fiye da Hafsatun, hakazalika duk wani abu da kike gudun ya samu Hafsatu, to ki kare wa Sahura shi da dukkan karfinki da iyawarki. Ba na son na sake jin wani abin cutarwa ya sake taba wannan yarinya, ki hada kansu gabadaya, Allah Ya shiryar miki da su, Allah Ya yi miki albarka."

Umma, wacce kanta yake kasa tun lokacin da Baba ta fara fada, sai yanzu ta dago kai tare da sakin ajiyar zuciya sannan ta ce, "Shike nan Baba na ji kuma In Sha Allahu zan kiyaye, ki ci abincin kada ya yi sanyi. Ki yi hakuri hakan ba za ta sake faruwa ba, na gode."

Baba Abu ta dan yatsini abincin sama-sama, ta sha ruwa. Suka dan taba wata hirar daban. Sai misalin karfe sha-biyu 12:00pm na rana sannan ta yi shirin komawa. Umma ta yo mata rakiya har bakin titi, ta tare mata Dan Sahu shata, ta biya shi har gida ya kawo ta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol