Free chapter · Read without an account
13
by Sadik Abubakar · SAHURA 💖
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
*SAHURA 13*
Ganin fitar Sahura daga dakin yasa Hafsat ta kara lamgabar da kanta jikin Umma tare da fara zayyano mata korafe-korafen karya da gaskiya, "Umma wallahi yau yaya Faruk da Sahura sun ci mutuncina sosai, sun wulakanta ni sun yi mini gori wai ni dakikiya ce ba ni da kokari ban taba cin kyautar komai ba, wai asarar kudi kawai ake yi, amma ita Sahura wai daga kai ta makarantar gas hi nan ta fara samun kyautuka. Kuma wallahi yaya Faruk har cewa ya yi wai ba ni da tarbiyya. kuma wai barci nake yi a aji."
Ta sake fashewa da wani sabon kukan, Umma ta rungume ta ta ce, "Su suka fadi hakan, har da shi Faruk din ake kiran ki dakikiya? Amma idan haka ne lallai Faruk ya cika shashasha! Ki yi shiru, daina kukan ki bar ni da su."
Hafsat ta mike zaune daga kan cinyar Umma, idanunta sun yi jajir sun kumbura saboda hawayen da take ta zubarwa ta ce, "Umma kuma ba ma wannan ba, wai yaya Faruk ne har da saya wa Sahura waya babba, ta ma fi tawa girma fa sosai, ni kuma babu abin da ya saya mini.
Umma ta ce, “Ki yi shiru ki daina kukan, kafin Sahura ta rike waya ke kika fara rikewa don haka kin fita ko bavta so. Kuma computer din ma ki kwantar da hankalinki yadda nasa Abbanki ya saya miki waya haka zan sashi ya saya miki laptop din ma. Yanzu ki tashi ki je ki wanke fuskarki ga abincin ku can ki ci.”’
Komawar Sahura falon ta iske Faruk shi kadai, Salim ya yi ficewarsa ta zauna kusa da Faruk din tare da sake yi masa godiya, “Yaya Faruk babu abin da zan ce da kai sai godiya, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi, Allah Ya kara arziki da budi, abin da kake nema duniya da lahira Allah Ya ba ka shi, na gode na gode na gode sosai Allah Ya tsare mana kai.”
Faruk ya saki wani murmushi ya ce, “Duk wannan addu'a ni kadai haka, sai kavce wani wanda ya ba ki duniya.”
“Abin da ka yi mini ai ya fi duniya ni a wajena, ka kauda mini da damuwa ta, ka dawo mini da farincikina, ka mantar dacni duk wani kunci na rayuwa, ka 'yantar da ni, ka dora ni a tafarkin da zan cim ma burin rayuwata kamar sauran 'ya'ya. Don haka dole in yi maka godiya tare da yi maka addu'a da dukkan wani lafazi da na san ana roka wa dan uwa alkairi a wajen Allah Subhanahu Wata'lah.”
Faruk kallonvta kawai yake fuskarsa cike da murmushi tare da yin nazarin hankalin yarinyar, ta burge shi sosai, tana da zurfin tunani da hankali.
Ya nisa ya ce, “Ai wannan hakkina ne, ya zama dole in kula dake kanwata, Allah Ya yi miki albarka. Ni zan fita kin ga ban yi sallar Azahar ba, ki kwashe kayan ki kai dakinku.”
“To shike nan yaya Faruk sai ka dawo.”
Yavyi ficewarsa, yayin da ita kuma ta kinkimi kyautukanta ta nufi dakin nasu wanda har yanzu Umma na ciki Hafsat na shirya mata karairayi. Tana shiga ta sauke kayan hannunta, ta dauki daya daga cikin kyautukan ta ce, “Sannu Hafsat, yaya kan naki? Ki karbi wannan ni ma na rike wannan ko?”
Hafsat tavyi shiru ba ta karba ba, ba kuma ta ce komai ba Umma take kallo kawai. Umman ce ta mayar wa da Sahura martani da cewa, “A'a ki rike kayanki, ya ya za ki ba wa dakikiya abin masu ilimi, ai ita dakikiya ce, ki rike kyautarki kawai ita kuma ta rike dakikancinta.”
Sahura ta zube gwiwowinta a kan carpet ta fara ba wa Umma hakuri, “Umma don Allah ki yi hakuri, ni ban yi wa Hafsat gorin komai ba, Hafsat ai 'yar uwata ce, idan na yi mata gori in ce na yi me? Shi ma yaya Faruk din ba wani abu ya ce mata ba, kawai dai fada ya yi mata akan ta kara dagewa da mayar da hankali a kan karatu.”
Da Hafsat ta ga za a ba ta daya daga cikin kyautukan, sai ta fara sakin ranta har tana cewa, “E Umma gaskiya ne abin da Sahura ta fada babu ruwanta, ba ita ba ce ta ce mini dakikiya, yaya Faruk ne.”
Ganin yadda Hafsat ta fara salubewa Umma gwiwa, yasa Umman ta mike tare da cewa, “Ku je can ku shawota ke da ita, tunda haka kika ce, kun fi kusa, Auyo da Hadeja." Ta fice ta bar su a dakin su biyu.”
Sahura ta mika wa Hafsat kyautar, babu kunya bare tsoron Allah ta sa hannu ta karbe, kafin wani lokaci yanayinta ya dawo daidai yadda take, ta saki jikinta tamkar ba yanzu ta gama sharar kuka ba. Sahura dariya ta yi ta ce, “Ba za ki sha maganin ciwon kan ba ne, kada fa ya hana ki barci da daddare?” Da zolaya Sahura ta fadi haka, yayin da Hafsat ta dan zumburo baki ta ce, “Ba na son tsokana.”
Sahura ta sake yin dariya ta dan bugi kafadar Hafsar sannan ta ce, “Oh! Ashe da ma ciwon kan na rashin samun kyauta ne?”
Hafsat ta sake zumburo baki gaba ta ce, “Ba za ki bari ko? Wallahi za mu yi rigima da ke.”
Sahura ta ce, “To shike nan, yanzu tashi mu je mu ci abinci ko!‘’
Abincin Hafsat ta dauko musu suka koma falo suna ci.
Bayan kwanaki biyu, ranar litinin ke nan, Faruk ya koma makarantar domin karbo wa Sahura kyautar computer kamar yadda a ka yi alkawari. Misalin karfe 10:00am na safe lokacin da ya fita kasuwa, sai ya biya ta can domin ya karba. Zuwansa keda wuya kuwa suka gaisa da Principal din, nan take ya dauko computer HP sabuwa dal! A kwalinta da jakarta ya mikawa Faruk, ya karba ya yi masa godiya, ya fito ya wuce kasuwa abinsa.
Da yammaci misalin karfe 5:30pm, Faruk ya dawo gida yana shiga falon Hafsat ce zaune kan kujera ta saka television gaba tana kallon shirin film din Jaruma a tashar Tauraro TV. Ganin sa da ta yi da computer, ya tabbatar mata laptop din da aka yi wa Sahura alkawari ce, nan take ta sake jin wani kishi a zuciyarta, amma sai ta danne domin an riga an gama harbo jirginta, ko Umma ma ba za ta sake sauraren ta ba.
“Ina Sahura take?” Faruk ya tambaye ta, Hafsat ta bashi amsa, “Suna kitchen tare da Umma suna aiki.”
Dakinsa ya wuce da laptop din sai da dare ya yi, an ci abinci an gama komai, ana zaune a falo ana hira, sai ya mike ya nufi dakinsa jim kadan sai ga shi da computer. Nan ya bude ya fito da ita ya hada komai ya jona ta a wuta sannan ya kunna ta, bayan ta gama booting ya dan bude programs tare da kunna 'yan wakoki da videos na gwaji, kallon sa kawai suke, da ya gama ya ce, “To ga shi wannan ita ce computer da aka yi wa Sahura alkawari.”
Umma ta ce, “Na gani, Allah Ya sanya alkairi.”
Ba karanin dadi Faruk ya ji ba ganin yadda Umman ta yi fatan alkairi ga abin da ya shafi Sahura a karon farko. Hafsat kuwa kwafa kawai take, ta rasa me za ta ce, zuciyar ta babu dadi. Kai su Hafsat da kishi ake, Allah Ya kyauta.
Nan Faruk ya juyo ga Sahura ya ce, “To ga laptop dinki nan kamar yadda aka yi miki alkawari sai a rika kula kada ta hana ki aikace-aikace.”
Sahura ta dan yi murmushi ta ce, “Ai ba tawa ba ce ni kadai, tamu ce ni da Hafsat, ba ni kadai na samu ba, duk abin da na samu ai namu ne mu biyu, Hafsat 'yar uwata ce tare za mu rika amfani da ita.”
Wannan magana ta Sahura ta taba zuciyar Umma sosai, tunani take tare da nazarin wai Sahura wace irin yarinya ce marar fishi haka, tana da kyan hali, bata da riko.
Kasancewar da ma suna yin darasin computer studies a makaranta, don haka ba sa bukatar sai an koya musu yadda za su sarrafa computer. Haka suka rika amfani da ita su biyu gwanin sha'awa. Hafsat ma ta fi Sahura morar computer din.