Free chapter 路 Read without an account

Page 7

by Rahama muh'md Rufa'i Nalele 路 FITO NA FITO AKAN SOYAYYA TA

*Fito na fito*

*A KAN SOYAYYA TA*

Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE

Wattpad @rahamanalele

*Haske writer's association*


Shafi na bakwai, 07


Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk Wanda yamin hakan ya d'ora haramun tunda ba amincewa ta.


Sannan makaranta na, na baku dama zaku iya tura labarin nan duk Inda kukaga dama, Ku Kan na yarje muku Dan nasan karanwata ne kawai naku bazaku Dora min Shi dan kasuwanci ba, babu hakan a tsarina.




RaHinAT ta kasa cin abinci, akan maganganun da HaYdaR ya gaya Mata, dake suna daining ne duk sun had'u da iyayen nasu, ita da qanwar ta Ummi da Abbas Dan autansu, kowa na cin Amma banda ita sai juya lokalin take, Dadynta na hankalce da ita Yace, "RaHinAT Yaya dai, tunanin me kike yi?, Murmushin yaqe tayi Mai da cewa "Ba komai bane Dady ina tunanin Ya Aliyu ne, murmushi momynsu tayi da cewa Kar wannan ya dameki, gobe ma Dadyn ki zaije kadunan kuma can gidan marayun zai fara zuwa.

Yace "kwarai kuwa, kuma Insha Allah zamu samu labari me kyau da yardar Allah, Dan haka ki kwantar da hankalin ki, Cikin farin ciki tace "Yauwa, nagode sosai Dady..

Nan ta fara cin abincin, dan da gaske taji dad'in hakan..



SafiYAH ko bayan ta koma gida can wajen qarfe goman dare ta rubuta ma HaYdaR message kamar haka.

_Shine ko ka nemeni ko, bayan nace maka zamu had'u Ka gaya min kaji dad'in lemon juice d'ina amma sai kak'i nema na_


Dake wayar na hannunsa akan idansa sak'on ya shigo, Saiya bata amsa..


_Sorry na Shiga wani abu daban ne, ina tabbatar miki tunda nake ban tab'a Jin dad'in abin sha kamar naki ba, yayi dad'i sosai na kuma gode_


Tana ganin amsar tasa farin ciki ya lullub'e kawai saita kira sa.

Ba jan aji ya d'auka da rigata yin magana wajen cewa, "kina Sona da yawa.

Tace, "Ai kaima kasani, dama na kira ne na gaya maka na iya kalolin abin sha fiye da 15, kuma dukka zaka Sosu Insha Allah idan ina yi maka su, yace "Dole na godema Allah daya had'ani da wacce zata bani su.

 Tace "idan Ka tashi rokwan Shi ka qara da rokonsa ka Soni fiye da yanda nake Sanka, Ka zama ni nima na zama kai

Yace "Kuma ni da kaina, tace "eh mana, kawai Ka Amsa min.. yace "Tom naji, Allah na rokeka Ka saka min San SofiYYAH na Sona fiye da yanda take Sona..

Cikin Sauri tace "Amiin.. kana taci gaba da cewa, "Kana da kirki, na rok'eka yanzu Ka kuma aikata a yanzun

Yace "addu'a kika min shiyasa na aikata Kai tsaye, kinsan kema kin iya addu'a, tace "waya gaya ma, yace "Naji a jikina ne kawai idan kina San aikata wani Abu ko kina San wani Abu ya faru nan da nan kike rokan Allah da sunayen da ba'a dawo da addu'ar. Tace "tabbas duk rokwan da zanyima Allah bana rokwansa kai tsaye saina had'a da k'arfaffiyar addu'a ko kiransa da sunayensa kyawawa, wannan duk Momyna da Dadyna ne suka Koya min, tabbas babu wani sarki abayan Allah, Shi Shi kad'ai yake bashi da abokin tarayya, duk abin da Allah baiyi maka ba, toko wani bazai tab'a yi maka Shi ba, idan ko kaga wanin yayi maka to tabbas ALLAHN ne ya yarda da hakan, Allah dai ya qarama Annabi DARAJA..


Yace "Amiin wannan zancen naki gaskiya ne, naji farin ciki da kika kasance ahaka, zan amsa Kiran Dady yanzu dan naga Kiran nasa ya shigo.

Tace "ok, Bye kayi mafarkina, yace "ALLAH ya yarda. "Amiin tace ya kashe wayan.


Taji dad'in hirar data Shiga tsakaninsu yanzu, tana kuma fatan tasamu matsayi a zuciyarsa ta yanda zai dinga bama soyayyar tata kulawa, ya dinga bibiyarta kamar yanda take bibiyarsa a yanzu, tana fatan ya dinga kiranta suna Shan hira, tana ma kanta addu'ar hakan Allah ya amsa mata..




Washe gari ko ita da Momyn da Dadynta sukaje suka duba wannan mahaukaciyar, Dadynta ya d'auki nauyin komai nata, Dan baqaramin Shiga zuciyarsa tayi, haka ma Momyn nata, itama ta Shiga ranta sosai taji tausayinta..



HaYdaR ko yana room din Dadynsa suna sallama akan tafiyar tasu Kaduna, bayan sun gama sai Dadyn Ya kallesa dakyau tsaf ya fahimci HaYdaR zai iya Auran RaHinAT dinsa, Shi Yana ganin kodai ma itace wacce ta kirasa jiya suna breakfast, idan har itace tabbas zai iya Auranta, Sam baiyi mamakin tayaya ya samota ba, ya dai San ko abokan sa nanan zai iya Sasu su neman masa ita, qila ma ko tun yana England suka Sama mai ita, shine bayan sun fahimci juna a waya suka fara soyayya, shiyasa yanzu daya dawo yaga Yana dokin San zuwa ganinta..


Shi kuma har a zuciyarsa Yana matuqar San had'a jini da yaran, Yana San HaYdaR fiye da San da yakema ReeYAH da Usman, bai tab'a tunanin soyayyar da yake masan takai har haka ba... 


Cikin nutsuwa yace "Ina San Ka Auri ZuwaiReeYAH HaYdaR, ina San had'a auranka da ita.

Cikin fad'uwar gaba, HaYdaR ya kallesa da sauri cikin sanyin murya da rawarta yace, "Ka gama min komai Dady, Ka gama nuna min qauna, ban San dame San saka maka ba, Yace "Ka riketa ita da d'an uwan ta Usman Amana, shine abin da zakamin naji dad'in sa har cikin Kabari na.

  Hawaye ne ya zubo ma HaYdaR yace, "wallahi ka cika mahaifi Dady, Samun irinka awannan lokacin Yana da matuqar wahala, ina Sanka Dady fiye da son da nakema kaina, ina kuma qaunar ReeYA da Usman gani nake sune farin ciki na..

  Yace "Nasan kana da wacce kake so, wacce jiya ta kira ka muna breakfast, tabbas ita nake San Ka fara Aure Dan nasan qila ko itace RaHinAT dinka.

Yace "Dady ba RaHinAT bace, RaHinAT yanzu idan munje gidan marayun zanje nemanta, Gaskiya ne Dady ina fatan Auran RaHinAT..

Yace "toh ita wannan din wacece, yace "SafiYAH ce, yarinyar aunty Khadijan ka, Sam bansan Yarta bace, sai jiya da naje gaisheta naganta. 

Yace "toh HaYdaR Tayaya soyayya ta Shiga tsakaninku 


Nan HaYdaR ya kwashe komai daya faru tsakaninsa da SafiYYAH a supermarket ya gayama Dadyn, ya qara da cewa, "tabbas Dady SaffiYYAH na Sona, itace tayi save na number nata acikin wayata, wannan zaisa kowa idan yaga number nata a wayata zaiyi tunanin mun juma da juna, kuma gaskiya Dady Nima ta Fara kwanta min arai..

Cikin farin ciki yace "Na fahimta, kuma naji dad'in hakan, kuma bazan canja magana ta ba, tabbas ita zaka fara aura, daga ita sai RaHinAT, in yazo ZuwaiReeYAH ta biyo bayan su..

Ka gaya min zaka iya rikesu ko kuma kawai zaka Auri RaHinAT ta isheka, Ka gayamin gaskiya bazan takura ka ba, bana san kayi abin da baka so...

Cikin matuqar ladabi, yace Wallahi Dady dukka ina sansu idan har ka amince zaka d'aura min Aure dasu.

 Cikin farin ciki yace Naji dad'in wannan abu HaYdaR, Allah yayi muku albarka, yasa Ku gama da duniya lafiya, Allah kuma ya d'oraka akansu su, su soka su qaunace ka fiye da yanda Kai zaka sosu, ya kuma kareka daga shirrin su ta yanda bazasu tada maka da hankali ba..


"Amin yace Mai, daga haka sukayi sallama, daidai lokacin Laila ta shigo d'akin, itama yayi mata sallama daga haka ya fitto..


Anan falo ya tarar da Usman yace, "Sai mu tafi ko..

ReeYAH ce ta fitto daga room dinta tace "lalle Big Brother har zaka fitta ni bakayi sallama dani ba.

  Murmushi ya sakar Mata me wayayarwa, anan take yaji yarinyar ta kwanta Mai arai da tazama matar sa, nan yaji Yana Mata SO irin na MASOYA, Sam baiga aibun Yarinyar ba, shikam bazai tab'a qin jinin mahaifinta ba, koda ace ita kad'ai yace ya aura yabar SafiYAH da RaHinAT wallahi barinsu zaiyi bari na har abada..


Cikin murmushin yace da ita, "ai ko mun tafi dole zan tuna banyi sallama da qanwata ba, dole haka zan dawo nayi sallama da ita, bayan hakan na buqaci tayi mana addu'ar dawowa lafiya..

Usman yace "yanzu Yaya akan wannan saimu dawo? waro yayi da cemai, "kwarai, saboda tana da matuqar mahimmanci Usman, wai me yasa Ka raina ta ne, ina itace yayar ka, tace "Gaya Mai dai brother, Rigani fittowa duniya kawai yayi Amma bawai shekaru ba, ai Dady ya gaya min yana fittowa nima na sullub'a, kaga kenan ko minti d'aya bai ban ba, Usman ya Galla Mata harara, yace "Wallahi ko second ne na girmeki dole ki yarda da hakan dole ki daukeni a matsayin nine gaba dake, dole Kina ban girma na, tace "qarya ne bazan yarda da hakan ba, yace "kin San ALLAH saikin yarda da hakan, zatayi magana sai HaYdaR yace "Kunga Ku dakata, wai dama Usman shine Babba, ya fad'i hakan Yana me kallan ReeYAH, d'aga Mai Kai tayi alamar eh, sai yaci gaba da cewa, Tab dijan, ashe kece me laifi, gaskiya ya fad'a dole ki yarda shine Babba, dole ki dinga girmamasa a matsayinsa na Yayanki, ni bamma tab'a ganin mace me San girma irinki ba, bayan kinsan shine gaba dake Amma kike mai haka, yanzu ki bashi hakurin abubuwan da kikai masa da bana nan kuma daga yau ki dinga girmamasa a matsayinsa na Yayan ki..

Turo baki tayi gaba cikin sanyi tace "toh, kana ta kalli Usman din tace kayi hakuri.

Cikin farin ciki yace "Ya wucce Dan haka gaba kikiyaye, yanzu Yaya nake agunki, ki dinga girmama ni kamar yanda kikaji Yaya yace...

Shuru tayi..

HaYdaR yayi murmushi da cewa, "toh ReeYAH zamu tafi.

  Kallansa tayi da cewa, "toh ALLAH ya dawo daku lafiya, Ka kuma gaishe min da Aunty RaHinAT, "Amiin zataji..

Daga haka suka fitto.


Dake jirgi zasubi shiyasa Basu dad'e ba suka sauka, Ashe jirgin d'aya suka hau da Dadyn RaHinAT.

Dake Dadyn nata yaga HaYdaR jiya a companyn Dadyn nasa har sun gaisa dashi yay masa barka da dawowa, shiyasa yanzu suna sauka suka sake da hira, anan HaYdaR ya gane Dadyn RaHinAT din gidan marayun da zasu shima nan zashi, nan ya gaya mai shima can zasu je, haka suka had'u sukayi can kai tsaye gidan marayun.


Suna zuwa ko dama gidan marayun sun sheda Dadyn RaHinAT, HaYdaR ne dai basu ganesa ba, sanda Dadyn RaHinAT ya gama tambayar HaYdaR sukace mai ba labari, dan Wanda ya daukesa ya gaya musu ya turasa karatu England, Dan haka sai ya dawo zai nemesu..


Jiki a sanyaye Dadyn RaHinAT din ya fitto daga office din nasu, sai su HaYdaR suka Shiga, nan HaYdaR ya bayyana musu ko Shi wanene..

Nan farin ciki ya cika su, sukayi saurin tsayar da Dadyn RaHinAT, da nuna masa HaYdaR suna cewa Aliyun da yazo neman labari akansa to gashi nan.


Nan farin ciki ya kamasu dukkansu su biyun, Shi HaYdaR sai yanzu ma ya ganesa, tabbas shine Wanda ya d'auke masa RaHinAT dinsa..


Bayan HaYdaR ya gama da gidan marayun ya basu gudun mawar da yayi niya da Wanda Dadynsa ya basa ya basu, nan suka keb'e shida Dadyn RaHinAT, Inda Dadyn RaHinAT din ya basa labarin komai Dan gane da barinsu Kaduna...

 Nan ya zaro wayarsa ya nuna masa hotan RaHinAT din....

 Aiko wata muguwar fad'uwar gaba ce ta ziyarci ZUCIYAR HaYdaR, ganin RaHinAT qawarsu ReeYAH wacce ya kamata tana shan giya Ashe itace RaHinAT dinsa..

Nan yayi shuru da zubama wayar Ido kawai Yana kallan hotan...


Alhaji Zakkari wanda yake Dadyn nata yace, "ina qaunar RaHinAT HaYdaR, yarinyar bata da matsala, tunda muka raineta bamu tab'a kamata da aikata wani Abu mara kyau na Allah Wadai ba, da ace Abbas babban d'ana ne da tabbas shi zance ya Aure ta, to sai gashi yazo a qaninta na biyu, da zan iya rokar wata alfarma agunka da nace Ka Aure ta HaYdaR, Kai ne Wanda zakafi kowa riqeta bisa gaskiya da amana..


  Sauke ajiyar ZUCHIYA HaYdaR yayi da cewa, "Zan Auri RaHinAT Insha Allah Dady, Ka kwantar da hankalinka..

Yace "Alhamdulillah Ka tayani kai amanar nan lafiya, Allah yay muku albarka, nagode sosai da amincewar ka..

Murmushi kawai HaYdaR yayi mai..

 Ganin hakan yaci gaba da cewa ni zan duba abokaina anan, Dan haka zaku rigani tafiya, ma had'u kawai acan..

Yace "tom Dady amma Karka gayama RaHinAT nine Aliyun ta, Insha Allah zan gaya mata da kaina,

Murmushi yamai da cewa "Tom Amma Karka d'auki lokaci, dan zata tambayeni me ake ciki. Yace "toh Insha Allah bazan dauki lokaci ba..

Daga haka suka rabu.


Usman akwai wani abokinsa ishak da suke skull d'aya Wanda Shi dan Kadunan ne, jiya ma ya tawo Kadunan, kuma Yana da address din gidan nasu, Dan haka rokan Yayan nasa HaYdaR yayi Kan ya basa minti talatin zaije su dan gaisa, HaYdaR yace Mai toh ba damuwa..


Bayan ya tafi ne yake ta tambayar ma'aikatan gidan marayun wayanda suka taso tare a gidan, da yawansu wasu sunyi aure sun Auri Yan gidan, Amma babban abokinsa Yana nan Kaduna Yana aiki, kuma daya tambaya a wane company yake aiki nan suka gaya mai, farin ciki ko ya kamasa, Dan companyn Dadynsa ne Inda shima zai Fara aiki acan, haka ya dinga musu tambayoyi suna bashi amsa, a haka Usman ya dawo Shi da abokin nasa suka samesu, HaYdaR ya kalli abokin Usman din yaga sai murna yake yi da zuwan da Usman yayi masa, nan ya gane suna San junansu da abotar tasu, acikin ZUCIYARSA yayi musu addu'a Allah yasa mutuwa ce zata rabasu, Dan sun dace da abotar  


Nan ko sukama gidan marayun sallama, har airport abokin Usman din ya rakasu sukayi sallama, Basu ko dauki lokaci ba suka dawo Abuja...


Dadynsu ya kallesa yace "Da alama tafiya tayi kyau, HaYdaR yayi murmushi yace "Gaskiya Kam, dan RaHinAT ba wata bace bace Yarinyar da amininka Alhaji Zakkari yake rikewa. 

Murmushi Dadyn yayi da cewa "tabbas ya kirani d'azu ya gaya min komai, nayi kuma farin ciki sosai da hakan, Ka duba ikwan Allah duk sai suka kasance qawayen juna..

Murmushi HaYdaR yayi.

Dadyn yaci gaba da cewa "toh Allah ya baka ikwan rigesu da amana, yasa su alkairinka ne kaima alkairinsu ne, sannan ka shirya Auran nan da wasu watanni kad'an haka, duk zan tattauna da iyayen nasu, yanda mukayi zaka jini nan da kwana biyu, Allah yayi maka albarka.

"Amin yace a hankali Kana yaci gaba da fad'in, ina ganin Nan da kwana biyu zan fara zuwa office Dady, Dan sati biyu ko d'ayan ma yayi yawa , na Saba da aiki Idan ba damuwa zan fara zuwa gata Insha ALLAH, yace "Ba damuwa yanda kace, dama ina so Ka huta gajiya ne, Amma tunda kace haka Allah ya bada sa'a.

"Amiin Dadyna....


Koda ya Shiga room dinsa salla yayi Kana ya Shiga tunanin RaHinAT, dole ya nemeta ta Gaya Mai dalilinta nashan giya, dama Shi tunda ya ganta yaji fad'uwar gaba yasan akwai magana, Ashe HEENAT dinsa ce, wato kamar yanda tace mai, daga ALLAH sai Shi ne kawai suka San tana shan giya, bayan haka ko iyayenta ma basu sani ba..


ReeYAH ce ta Shiga falan nasa da sallama, hannun ta dauke da abincinsa, bayan ta ajiye tamai tamai sannu da dawowa zata fitta Saiya kira ta, bayan ta zauna kan kujera mecin mutum d'aya kallansa tayi Wanda Shi yana kwance ne kan kujera me cin mutum uku. Tace Yaya ya Aunty RaHinAT d'in. 


Murmushi yayi da cewa, "kinsan wacece RaHinAT d'in, tace "aa, yace qawarki ce RaHinAT...

  Waro ido tayi cikin sauri da tsoro tace "Kai haba Yaya, kuma zaka aureta ne?, Allah yasa baka Santa da Aure.

  Shuru yayi Mata da zuba mata Ido, ganin hakan tayi saurin cigaba da cewa, ko kana Santa da Auran ne, Yace "da matsala ne..

Cikin sanyin jiki tahau juya hanayenta tana cemai, "SafiYYA na Sanka Brother gashi kai da RaHinAT zaku so junanku daga dukkan alamu gashi su qawaye ne tayaya zasu iya rayuwa da miji guda d'aya tsakaninsu, bayan suna qawayen juna, ni na kasa fahimtar mezaije ya dawo..

  Kallan nata dai yake yi yanda take magana a sanyayen to ya zatayi idan taji itama zai Aure ya had'ata dasu..


  Ganin Yama ta shuru yasa ta qara tsaida idanta akansa taci gaba da cewa, kayi shuru sai kallona kake brother.

    Tashi yayi da bude wani qaramin akwatinsa ya d'auko wata fulawa me kyau, Kana yazo gabanta da jan senter teble ya zauna suna kallan juna kusa da kusa, Kana yace, nasan ayanzu kinsan ba Dady bane ya haifeni, kawai ya daukoni ne daga gidan Marayu domin Samun lada agun Allah..

D'aga mai Kai tayi jiki a sanyaye, ganin hakan zaiya miqa mata fulawar, da cewa, "Zaki AURE NI...

Kallansa tayi a furgice da cewa "Aure? Aure kuma Ya HaYdaR, yace "Yes Aure, Dady ya kirani d'azu ya gaya min cewa ya riga da ya yanke hukuncin d'aura mana Aure ni dake..

Cikin matuqar tsoro ta dafe girji tace "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, kuma ka yarda..

Yace "Yarda Kai, da gudu na yarda, duk duniya bazan tab'a qin zab'in Dady ba..

Tace "RaHinAT SafiYAH ya zakayi dasu, yace "kwantar da hankalinki mana, duk zan auresu ai, cikin tsoron dai tace "Ya Allah, tayaya zan iya Zama da mijin SafiYYA mijin RaHinAT...

Yace "ok yanzu na gane, wato bakya Sona..

Cikin wani hali tace, "wallahi ina Sanka Ya HaYdaR, Dan Allah Karka min mummunar fahimta, yace "ok, oya karb'i wannan fulawar soyayyar, Dan na yanke kice Amarya ta acikinsu, daga yau sunanki Kenan aguna.

Cikin tsoro ta karb'i fulawar Y'ar me kyau abin ta, Dan tayi mata kyau sosai, cikin sanyi ta kallesa taji gabanta ya fad'i, tace "kuma yanzu soyayya zamu fara ko..

Yace "idan kina Sona ba, nikam ina sanki sosai..

Tace Nima ina sanka, Amma Karka gayama RaHinAT da SafiYYA Dan Allah ni idan lokaci yayi zan gaya musu, yace "Nifa bazan iya b'oye soyayyarki ba, tace "yaushe Ka fara Sona har haka Ya HaYdaR..


Tashi yayi da komawa kujerar da yake Yana cewa, "Ada soyayyar qanwa nake miki, Amma ayau da Dady yayi min maganar Auranmu sai naji na gamsu ina Miki soyayya irin ta masoya, Dan Allah AMARYA TA, kar kice baki Sona..

Tashi tayi cikin damuwa, ji tayi kuka yazo mata, Amma haka ta maida shi, tace "Ya HaYdaR babu macen da zakace kana Sonta tace aa, sai dai in mara rabo ce, Nima ina sanka Ya HaYdaR, ina qaunarka, kuma zan Aure Ka, Kayi min 馃挴%..

Yace "toh Jin damuwar ta miye, me yasa jikin ki yin sanyi haka...

Hawaye ne ya zabo mata tace dashi, "kawai ina tunanin makomar soyayya ta ne, SafiYYA idan tana San abu ko a ina nunasa takeyi, bata da rufa rufa da iyakar gaskiyar ta take rayuwa da kowane irin abu, yayin da RaHinAT idan tana San abu sai tasan yanda tayi ta mallaki wannan abun ita kad'ai, ni kuma ban San kaina ba, ban San ya nake ba, Sam banda zab'i

Yace "badai ina sanki ba, toh kisa aranki AKAN SOYAYYA TA zaki San darajar chose..

Tace "Bana San na fara Sanka in Shiga d'aki ko toilet nayi kuka, Bana San na fara Sanka azo a kwace min Kai, nifa Bana San na fara Sanka nazo na rasaka, wallahi idan haka ta faru akwai babbar matsala, komai zai iya faru dani...


Tashi yayi yazo gabanta tare da zuba mata Ido, ya rigada ya gane yarinyar tana da tsoro, Shi kuma yasa aransa Indai da gaske zuciyarsa take Yana Santa irin son da yakema RaHinAT na Aure toko soyayyar tasa zata koyar da ita rashin tsuro..


  Ido cikin ido yace mata, "ina sanki... 

Daga zuciyarta amsar tazo mata batare data shirya ba tace, "ina Sanka Ya HaYdaR..

Murmushi ya sakar mata.. ita kuma hawaye ya zubo mata

karb'ar wayarta yayi ya d'auki numberr RaHinAT Kana ya bude mata kofa, ahankali ko taje ta wucce har ta fara yin nisa yace "kiyi mafarkina fa.

Juyowa tayi ya daga mata gira ahankali tace "insha Allah..

Daga haka tayi room dinta..

Tana Shiga hawaye yata ambaliya a fuskarta, batayi aune ba kuka ya kubce mata, Ashe dama kaddararsu haka zatazo musu, su Auri miji d'aya, ita Kam tayaya zata Fara da rawar kai irin na SafiYYA, tayaya zata iya da wayo irin na RaHinAT...



Shi ko Kiran wayar RaHinAT yayi.. lokacin tana kwance a gadon momynsu suna hira, taga kiran ya shigo, tace tana d'auka, yace "ina San magana dake, mu had'u a wajen shaqata na Reenas, HaYdaR ne Yayan ReeYAH..

  Nan tatashi da sauri tana cewa "tom karfe nawa, yace "nan da minti talatin, tace "ok tom sai nazo.. kashe wayar yayi, itako tsoran sa ne ya cika mata zuciya bata San ya tona mata asiri dan haka dole zataje ta gaya mai gaskiyar dalilin fara Shan giyar tata.. nan ta kalli Momyn nasu tace, "Momy zani wajen SafiYYA Dan zamu gidan wata qawarmu babbansu ya rasu ne.

Tace "Ayya Allah yaji qansa, ki gaishe min da Momyn ta, sannan karku jima kinga magriba ta kusa, tace "tom zataji Insha Allah zamu dawo da wurri.


Nan tayi room dinta ta canja Kaya kana ta dauki Y'ar pose dinta tama momyn nasu sallama, ummi tace zata rakata tace no ta zauna..

Nan ta hakura badan ranta yaso ba...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol