Free chapter 路 Read without an account
Chapter 2
馃専馃専CHANJIN BA ZATA馃専馃専
By
MARYAM IBRAHIM Litee
2
Ni ma na bita.
tana mamutse da ita suka shiga 蓷akin,
murna yaya Azima take sosai,
ita kuma ta fa蓷a kan Innarmu tana kuka.
Mutanen gidan ma kan ka ce me,
sun cika 蓷akin.
sai da aka natsa kowa ya kama gabansa sai mu ka蓷ai.
Labari ake ta bata na bayan bata,
zuwa can sai ta zura min ido,
"Wai Shuhainar Inna ce ta zama haka? "
Jawo ni ta yi, "Ba ki gane ni ba ko?
Na ce "Da dai a hanya na ha蓷u da ke zan rin茩a tunanin ina na san ki,
dan ko hotunanki da ke akwai ba haka kike ba".
瞥ar dariya ta yi
ni kuma mamakin irin kyan da ta 茩ara nake,
duk da dai dama mutane suna cewa ba me kyanta a 蓷akinmu,
gata doguwa ce ita, kuma bata da jiki,
amma tsananin jin dadi yasa fatarta ta murje ta yi lukwi-lukwi,
kyan fuskarta kuwa ya isa.
A 蓷akin da Yusuf ka蓷ai na ga take kama, dan dai shi ba fari ba ne,
Ita kuwa kalar jikinta wani yallow yallow ta koma dan tsananin kyan da tayi,
蓷akinmu kuwa tunda ta shigo tamkar kana a cikin birnin paris tushen turaren saboda tsabar kamshin da yake.
wani 茩an茩ararren less ne jikinta wanda kallo 蓷aya kai masa ya wadatar da kai gane ba na me 茩aramin karfi ba ne.
Yaya Azima ta dubi Yusuf
"Amma dai 蓷an 茦anina tafiyar nan ba yau ba ko?
Ya murmusa.
"Ga fa sister ta iso wane tafiya,
sai dai kuma lokaci yana kurewa".
"Amina ta nemi jin inda za su,
aka fa蓷a mata,
ta ce;
Jiya bayan mun isa Kaduna,
na tsaya na saya mata kayan daki.
Yusuf ya ce
"Kaduna kuka sauka?
Ta girgiza kai .
"Abuja muka sauka.
"Mun samu mahaifinshi ya gyara ma shi 蓷aya daga cikin gidajen shi.
Kwananmu biyu, jiya muka isa Kaduna ya ga wani dan uwan shi,
ni kuma sai nayi sayayyar,
anjima ka蓷an kayan za su iso,
har da kayan kitchen da na saya mata a Dubai, dan sai da muka biya ta can,
har da su kafet su zannuwan gado da labulayya duk an yi sayayyar su.
Yaya Azima ta 蓷aga hannu sama
Allah kai ne Almusawwiru Mun gode maka bisa ga wannan rufin asiri da kayi mana Allah ka 茩ara rufa mana.
Innarmu kuwa sai dai
muka ga ta fa蓷i tayi
sujjada,
kafin ta 蓷ago
tayi ta sa mana
albarka.
ta dubi Anty Amina
"An tsinke da labari ba'a tanbaye ki mijin
naki ba.
Gyara zama tayi
"Tare muke
sai dai ya ce ba zai shigo yanzu ba,
wai yanda nake 蓷okin nan suma mutanen gidan suna 蓷okin ganina,
sai dai idan sun dawo gidan abokin shi da muka zo tare,
Abokin nasa 蓷an katsina ne,
sunan shi Abdullahi"
Innarmu ta ce
"Na gane shi".
Daidai nan amarya ummu ta shigo da gudu, sai wurga ido take inda za ta ga Aminan
A guje ta fa蓷a mata
Innarmu ta rike ha蓳a
"Ke kam yau sai jikin ki ya yi ciwo
Muka yi dariya
Amina ta ce
"Yayanmu Ina yaran ki? "
na san kin tara su da yawa, wai Yusuf ya ce min uku ne.
Ummu ta yi karaf ta ce
Haka ne, khadija ce babba mai sunan mahaifiyarsa,
sai yakub
sai na bayanta khalid ".
Ta karbe shi a hannuna tana ma shi wasa
"Anjima salma ta dauko min su
in gan su, amma na sha sun kai hudu.
Azima ta ce
"Haba dai sai ka ce duk shekara ake haihuwar duka auren shekaru shida ke ba ga shi ko daya ba ki haiho mana kin taho mana da shi ba"
Murmushi tayi
"Karatu na ke, amma na yi ta 蓳ari"
Ummu ta ce
"Amma ba yanzu za ku koma ba ko? "
"Mun dawo kenan ai mun sha turai"
Ta kamo hannuna
Me za ki dafa mana da rana?
na san innarmu indai tana da budurwa to ta kan horar da ita aikin gida".
Na dubi Yusuf
Ga mai gidan nan,
bai riga ya bada ku蓷a蓷en cefanen ba. "
Tana 蓷an murmushi ta dube shi
"Ran maigida ya da蓷e Me za'a yi mana ne"?
Yana 拼ar dariya ya ce
"Ai ba茩in ne sun fi 茩arfin aljihuna, "
Yanda ya yi maganar shi ya ba kowa dariya
Jakarta ta hannu ta jawo,
Bandir ne na yan 蓷ari biyu wanda ban yi tunanin an zari wasu masu yawa ba ta mi茩a masa
"Ayo mana cefane"
Ya karba yana
"Yawwa ko ke fa".
Na mika hannu
"To bani tunda dama kowa ya san ni kake ba in lissafa sai in sawo"
Tsaye ya mike
"A'a wannan ya fi 茩arfin ki, da kaina zan sawo".
Yayammu ta murmusa
"Yusuf ho indai kudi ne".
Bai saurari komai ba ya fice.
"Anty Amina ta ci gaba da tanbayar abinda za'a bu茩ata na fannin bikin
yayarmu na gaya mata.
Sha 蓷aya Yusuf har ya kawo mun dora,
ni da ummu dan har zabi ya sawo,
muka shirya ma ba茩i lafiyayyar miya.
Zuwa sha biyu kayan amarya suka iso,
dama tun kan isowarsu, an gaya wa mutanen gidan su shirya.
A ( Area) za su zauna mijin ma'aikaci ne.
kaf mutanen gidan sun tafi,
Yayanmu ma ta tafi, sai yara,
mun gama girki, muka dauko kulolin ummu da take tarawa, muka Zazzuba abincin mijin Anty Amina da abokin shi.
Muna sallar azahar, muka ji sallamarsu. Amina ce a falon dan ta idar, Innar mu ta fara fita suka gaisa, tayi waje. kamar jira yake ta fita,
sai cewa yayi"
"Ke kuma fa lafiya kike kwance kasa?? Tace " sanyin kasan da蓷i yake min."
Yace" Tohm ban yarda ba tashi"
ta tashi, ta shirya masu abincin a gaban su, abokin shi na mata tsiya, wai har yanzu gajiyar ce bata wartsake ba.
Suna fira
ummu ta fara fita
ta gaishe su,
tayi waje.
Ni ma ban tsaya cire hijabin ba, na fito na gaishe su
na fita,
Ina mamakin kyau na mijin Anty Amina
Dogo ne fari, dirarren namiji mai cikar halitta,ga sajen shi wani irin dogon hanci gare shi da wasu kyawawan idanuwa masu jan hankali, farin yadi yasa bashi da nauyi sosai da farar hular da su kai matu茩ar tona asirin kyansa.
Da na fito na ce ma innarmu bari in je in ce ma kawata ( hafsat) ta kusa da gidanmu, ba zan samu zuwa makaranta da yamma ba.
Inna ta ce "Anya shuhaina, ba fa kije da safe ba,
yanzun ma ki ce ba za ki ba?? Nace" kin san dai innarmu bana fashi,
Allah ban gaji da ganin aunty Amina ba.
Na fice.
Da yamma bayan yaya Azima ta dawo. Amina ta umarce ni in ta jawo jakunkunan da ta zo dasu, nayi kamar yanda Ta ce.
Jakar farko amsa sunan innarmu,
dan haka ita ta aje mawa.
Sai taba Azima tata daya, ta yaranta daya.
Sai ummu wadda Yusuf
ya ce
"Kawai kin kama sawo ma wannan yarinyar kaya,
ba ki ga akwatunan da aka dankaro mata bane?
ta ce
Nasa daban, nawa daban,
matsayin shi daban,
na wa daban."
ummu ta fara masa gwalo
ya ce "Allah zan make ki"
Innarmu ta ce
"Ka rufa min asiri, ke kuma ki bari.
"ta ce "To."
shima Jaka guda aka ba shi
wadda ya ja ta zai waje da ita.
Azima ta ri茩e
Ta ce "
"Allah yadda kaga na kowa,
sai an ga naka".
Dolensa ya bude,
yadiddika ne
na maza masu matu茩ar kyau
da tsada,
sai shaddodi da takalma
da agoguna har da su turare.
Salma ma Jakarta daban ,
aka ba innarmu,
jakar innarmu atomfofi ne masu asalin tsada
hada mai (golding) da kuma lesussuka
da hijabai
da takalma flat,
haka na Azima.
Na ummu kayan barci ne dasu turaren wuta.
Nawa riguna ne dogaye da kuma riga da sket da takalma da hijabai (jilbab)
ta dube ni.
"Yusuf yace min ba ki sa gyale."
Na gyada kai,
Yusuf ya ce"
"Ai kin da蓳a a 茩as!
wannan da ki ke gani.
ya nunani da hannu,
"da ni kika ba su
da sunyi min rana,
dan kalarsu zan nema.
Amma kin ga wannan
yadda kika ganta haka
da hijabin nan,
to kullum a haka take. "
Azima Ta ce
"Allah dai wadaran babban kwabo".
Yusuf dai sai ya ja jakar shi ya yi waje.
Ta cire sar茩a da dan-kunnen dake jikinta. Ta mi茩a wa Yayanmu,
dan tun zuwan ta Yayanmu ta yaba kyansu.
Saura jakunkuna uku
, ta tura ma innarmu,
"Ga shi nan
abinda ya kama mutanen gidan nan,
zuwa abokan arzikinki ki ba kowa,
na hajiya ma suna nan ciki."
nan muka yi ta godiya.
Innarmu wadda tunda
aka fara bu蓷e kayan take kame da baki,
ta ce
"Hala dai tun randa ku ka sauka garin,
kika fara sayen wa蓷annan uban kaya?
tayi 拼ar dariya
"Haba dai na jima tukuna"
"Ummu ta ce "Uhm!
Anty Amina ta ta dube ta
"Yi maganarki.
"Ta ce naga kin ba Yayanmu
takalma da agogo da turare,
kince na babansu khaleed ne,
shi ne .....
Sai kuma ta 茩ara shiru
ta ce
"Da kin je direct!
Yusuf ya harare ta
"Mara kunya,
ita nufin ta ba'a ba nata mijin ba."
ai kuwa a guje ta bar dakin.
Da daddare sallar isha'i kawai nayi na hau gado.
Aunty Amina ta
ce"
Ba dai barci za kiyi ba??
Na ce "Hutawa zanyi, idan kuma barcin ya zo tom duk daya."
Ta ce
"Ke baki da saurayi ne?
Ummu da ke ta kwalliyar tafiya wajen angonta,ta ta蓳e baki
"Wannan, ai ta dai yi aikin gida,
amma duk wanda ya zo , ya ma gaji ya kama kansa,
bata sauraron kowa.
innarmu tana ganin
ta fara kuka, idan aka aiko kiranta,
za ta ce a rabu da ita akwai sauran time.
"Amina tayi 'yar dariya,
ita kuma ta fice.
Innarmu tana tsakar gida inda mutanen gidan ke shan iska.
Aminar ma ta fita tsakar gida,
shigowar ta naji tana magana.
"Inah ka bar Abdullahin??
Ya ce
"Zan zo wajen matata kuma sai na 蓷akko shi?
daidai yana zama wata carpet data shimfida masa,
ta ce
"Amma dai gari ya gari ka dauko shi?
Ya ce
"kin manta jihar shi ce nan,
yanzu haka ya isa katsina."
Ta ce
"Ka hana in maka girki, to me kaci?
Ledar dake hannunsa ya mi茩a mata.
Cire wa su mama leda guda,
ki aje mana guda.
Suna ci tana jan shi da fira,
wanda dama magana bata dame shi ba,
ban san lokacin da suka tashi ba
na dai farka naga innar
mu da amina suna ta fira, ba alamar barci,
Aunty ummu ce kusa da ni,
itama barcin take.
Da asuba tunda nayi sallah na kwanta,
Ina karanta addu'oi'n da ke cikin (hisnul Muslim).
Sai da 7:00 tayi,
na dora koko,
Yusuf ya kawo kosai ( Enough) har da bread.
Innarmu ce ta dubi Amina data shigo lokacin tayo brush,
ta ce
"Zaki iya shan kokon kuwa?
dan murmushi tayi
"Ka ji innarmu,
ke ki ka sha, 'yan'uwana suka sha,
sai ni ce ba zan iya ba,
Shuhaina zubo min."
na ce
"To".
sallamar da aka yi a bakin kofa ne
ya samu saurarawa.
Na san ba ni kadai na shiga mamaki ba,
kuma ba sallamar na ke mamaki ba, me muryar,
watau baba ya'u,
Kanin mahaifinmu shi ke bi masa,
dan sanin da nayi masa
baya hulda da mahaifiyarmu,
tun auren su Azima
daya kawo wani tsohon mai kudi,
ta ce bata san shi, Sai ya ce innarmu ke zuga ta,
tun daga nan bai kuma sake bi takan mu ba,
balle abinda ya shafe mu.
wai tunda an nuna masa iyakar shi,
alhali lokacin da babanmu ke raye, yana cikin wadanda suka fi kowa cin moriyar shi.
Wai yau shi ne har dakinmu,
Fakare na yi, in ji da wadda ya zo.
Bayan sun gama gaisawa da innarmu,
muka gaishe shi
"Ashe Amina kin zo?
Ta ce "Eh baba."
Ya ce
"Ai jiya ban shigo gidan da wuri ba,
don na je mani.
Da na dawo kuma na tsaya hira a layin barankaci."
Ta ce
"Mun same ku lafiya?
"Lafiya kalau,
ya mai gidan da iyayen shi?
"Ta ce "Duk suna Lafiya,
tare ma muka zo".
To to madallah
ai ladi ta bani tsaraba, har da ita dani da yara duka.
"Ta ce
"Ai ba komai Baba.
Ta sa, ummu ta miko mata jakarta ta hannu,
ta amsa ta zaro Bandir 蓷in 拼an Dari biyu
ta mi茩a ma baba,
"Ga shi ba yawa baba, ayi cefane."
Godiya ya shiga yi
har yana 拼ar 茩walla,
wai ya tuna dan-uwan shi mahaifinmu.
Ni ko dariya nake a zuciyata,
ina cewa
"ku蓷i masu gidan rana,
ba wuya sun ru蓷a mutum.
Allah ya dora mu kan kudi,
kowa san su yake
kamar me,
dan idan baka da su, sai kaga karan rogo ma ya fi ka amfani.
Sai na tuna wani malaminmu
da ke mana karatun tauhidi a islamiya
inda yake ce mana yana daga cikin hikimar
Allah ta'ala da ya turo kowane manzo
zuwa ga mutanen sa da mu'ujiza
ga abinda manzon ya zo da shi,
kuma mu'ujizar manzon
tayi dai-dai da abinda mutanen sa suke akai,
dan mutanen su gaskata mu'ujizarsa.
Dan bijiro da imaninsu da cewa
lallai wannan daga Allah ta'ala yake.
Kamar Annabi musa
(A.S) mafi yawanci a zamanin sa sihiri ne,
kuma suna gasgata masu sihiri,
sai Allah ya aiko shi da mu'ujizar data ru蓷a duk masu sihiri,
kamar kuma Annabi isa( A. S).
Allah ya aiko shi ne a zamanin likitanci da ma'abota ilimin 蓷abi'a
Sai ya zo masu da mu'ujizar data dace da wannan,
ya kasance
yana warkar da makafi da kutare
da tayar da matattu da izinin Allah.
Amma manzonmu Annabi Muhammad (S.A. W)
an aiko shi a lokacin fasaha da balaga ta magana,
sai ya zo masu da mu'ujiza dawwamamma, ita ce Al-kur'ani.
Sai malamin namu ya ce
"Da ace a yanzu za'a sake turo Annabi, da me kudi za'a turo,
dan mutanen yanzu ba abinda suka fi ganin kimar shi irin naira".
To haka dai baba ya gama matse-matsen shi, ya tafi.
Ni kuma na tashi na gyara dakin.
Ummu ta kwashe wanke wanke za tayi.