Free chapter · Read without an account
Rayuwar Indo a Kyauyen su
Tsaye nake bakin titi Ina jeran napep dan gaba ɗaya Rana ta ishe Ni duk nabi Na jigirce da ɗauda ga kuma ƙaurin talauci , gaba ɗaya abin duniya ya mani katutu dan nida mahaifiyata bamu da mai taimaka mana hakan yasa mahaifiyata take aiki dare da Rana dan ganin bamu kwana da yunwa ba , Na gaji da jira dan Inda a ƙasa Na tafi da yanzu Na kusa zuwa gida dan nafi minti ashirin Anan , kallo Na maida a kan hannu Na da duk yabi ya lalace da ƙaushi Na kalli shohuwar naira ashirin din da ummata ta bani kafin Na baro gida , Ina sane da mai abin hawa bai ɗauke niba a naira ashirin saboda yadda man fetur yayi tashin Goran zabuwa a halin yanzu, dama kuma Ina sane da hakan amma shegen taurin kai irin nawa bazai bari ba , dan nasan danaje gida idan nayi mutunci shine Na wurga masa naira goma dan Na ajeye raguwar gomar nasai sundilken gidan Abu yar cakusa , idan kuma yan rashin mutunci ne akai Na koda sama da ƙasa zata haɗe bazan baɗa wannan kuɗin ba sai dai mai abin hawa yayi man Allah ya Isa A haka duk yanzu masu abin hawa sun fara ganeni shiyasa duk Wanda Na tsayar baya tsayawa dan haka kawai Na kama hanyar tafiya gida.
Wata dattijuwa ce wacca bazata wuce shekara 41 a duniya ba amma duk wahala ta gama jeme ta duk ta kode , Zaune take akan kujera tana ƙankare ƙamzo a tukunya , waƙar barmani chuge take rerawa ta gwarne iKON Allah , daga kanta tayi domin ji datayi anyi kwallo da butikin da ta gama wanki dashi yanzu , ko kanta bata ɗago ba dan tasan ko wacece ta fara cewa “ Indo wai sai yaushe zakiyi hankali ne ki rinka yin sallama idan zaki shigo gida ba ” ta faɗa tana soke yan kuɗaɗen ta a haɓar wani koɗaɗɗan zanin ta .
Kallon ta nayi Na sumɓuro baki waje Na cewa “ yo ke babalmu wannan wani irin Abu ne daga higowal mutum gida he a fara mihi faɗa ” Na faɗa Ina mata yan zabure zabure kamar zan bugeta .
“aa iyeh kai abin nan da ban mamaki yake ” ta faɗa tana kama haɓar ta dan mamaki , sannan ta ɗura da “tohm buganni uwata , nace buganni uwata Indo , wai Indo wai har lalacewar taki takai haka Indo tohm gaskiya da change wannan lamarin naki , gaskiya dama Afashe tana birni sai ki ƙoma wajen ta ƙila acen kinyi hankali Indo ” ta faɗa tana Ida kai tukunyar ta wajen wanke wanke .
Saurin washe baki Na nayi danjin ance za'a kaini gidan Afshe a birni “da gaske babalmu zaki kaini birni wajen afhe , ahe zan je birni Naga mutanen cikin kallo ” Na faɗa Ina ƙara rungume babalmu .
Saurin zanye ta take daga jikin ta dan kada ta Ida ɓalla mata ɗan guntin ƙasusuwan ta da suka rage tana cewa “dan Allah Indo kiyi hkr kaɗa ki karya , dan allah ki sauka” ta faɗa tana sauke ta .
“wai da gaske zanje wajen afhe a binni ” Na faɗa .
“Ehh mn me zai hn ” ta faɗa .
“ kuma zanga mutanen kallo ”? .
“wannan Na kaɗai ban saniba , gsky idan kika takura man da tmby alquran babu Inda zakije gara ma ki kama bakin ki ” ta faɗa tana nuna mata alamun tayi shuru......
Fanan_A.A