Free chapter ยท Read without an account

chapter one

by Zainab Yerima ยท MURADIN RAI

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*MURADIN RAI*๐Ÿฆ‹๐Ÿฆ‹๐Ÿฆ‹๐Ÿฆ‹๐Ÿฆ‹


_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*_


wannan littafin sadaukarwa ne ga *MARDIYYA LUMANA*


Labarin nan kirkirarren labari ne, bashi da halaka da rayuwar kowa, na kirkireshi duba da irin abubuwan da suke faruwa yanzu tsakanin samari da en mata.


*GARGAD'I*

*Ban yadda wani ko wata yayi/tayi amfani da wani sashi na labarin nan ba tare da izini na ba*


*GODIYA TA MUSAMMAN*


*Inason in mika godiya ta ga mutanen da sukebani kwarin gwiwa wajen yin Rubutu, kuma dalilin su nakejin inshaa Allah zan cigaba da wannan haraka ta rubuta.*

_Ummie mum benaxir (maman muhsin)_

_Nussaiba Mas'ud (mum Anisah)_

_Fatima kole (maman Iman)_

_Fatima auwal(fati giant)_

_Jamila corper (kanoconnect friend)_

_Mukhtar writer._


_wannan page din sadaukarwa ne ga Zeety (AZ) novels group, inajin dadin hadin kan da kuke bani a kowane lokaci, kuma kullum kuna rainah๐Ÿฅฐ... Allah ya barmu tare ya kuma had'amu ranan gobe kiyama Amin._



*wattpad @Zeety-AZ*

karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad ๐Ÿ‘†๐Ÿป



1๐Ÿ“š




A tsakiyar gado suke zaune su biyu, pillow ta d'aura akan cinyan ta sannan ta zuba uban tagumi, a hankali zeezee ta sauke mata hannu tace, haba kawata meyasa kikeson sawa kanki damuwa ne, nifa a iya sanina shine kinason Hasib kuma soyayyan da kike mishi ne ma yajawo wannan aurenโ€ฆ sexxy eyes dinta ta sauke akan zeezee sannan ta cije leben kasan bakin ta, a hankali Mardiyya ta zuro kafanta daga kan gadon ta sauka a hankali, jikin window taje ta zuge labule sannan tad'an tura glass d'in window gefe, lumshe idon ta tayi tare da fesar da wani iska me d'umi daga bakinta, a fusace zeezee ta tashi tace basai kin raina min hankali ba , bari nima in tafi gidan mu, tana maganan ne tareda sauka akan gadon, ji tayi mardiyya ta rike mata hannu amma ba tare da ta juyo ba, leka fuskanta ta tayi, hawaye tagani wani na koran wani, kunkumi zeezee ta kama sannan tace nashiga uku ni zainab, haba Mardiyya yanzu kuma meye na kuka? Kinga matukar bankai matsayin da zaki gayamin damuwan ki ba kibarni kawai in wuce gida, don na lura bakida niyyan magana, daganan tacire hannu ta acikin na mardiyya, ta fita a fusace.


ita kuma kukane yaci karfin ta takasa hanata tafiya, kan gado tafada tafashe da wani marayan kuka me sosa zuciya.



**Mardiyya da zeezee kawaye ne sosai wanda suka tashi tare, akwai shakuwa da fahimta sosai a tsakanin su, saidai duk da sun kasance kusan tare suka tashi amma akwai banbancin d'abiโ€™u a tattare dasu, Mardiyya batada magana kuma yarinya ce me zurfin ciki, zeezee kuma tanada surutu sosai, wani lokacin idan tadamu mardiyya da surutu saidai kawai ta rufe idonta don ba kullum kanta yake jure surutun zeezee ba, ita kuma zeezee hakan yakan b'ata mata rai a take sai tace zata tafi, nan zasu hau rikici saboda duk yadda zeezeen tadame ta bata kuma son abunda zai raba su.


Mardiyya ita kad'ai maman ta ta aifa ta rasu, baban ta ya sake aure kuma antyn ta ta riketa tsakani da Allah tamkar ita ta aife ta, tanada kanne guda uku wayanda baban su ne daya.


Mardiyya wankan tarwada ce don baza a taba sata a sahun bakake ba saboda bakinta me haske ne, wani lokacin ma zamu iya cemata fara, tsayinta daidai ne, tana cikin mata masu matsakaicin tsayi, batada kiba kuma ba siririya bace, sannan tanada structure me d'aukan hankali, tun bama idan tana tafiya ba, tanada sexy eyes masu kashe jikin duk wani me kallon ta, tanada dogon fuska me d'auke da dogon hanci tareda dan karamin bakiโ€ฆ tanada sassanyan kyau me d'aukan hankali gashi batada hayaniya komai nata ta acikin nutsuwa takeyin shi, batada wata kawar data wuce zeezee.**



Waya yakeyi a lokacin daya juyawa hayaniyan mutanen dasuke NYSC secretariat baya, dogon saurayi ne fari sol saje ne a kwance a gefen fuskan shi,daga yanayin shigan shi zakasan bakaramin dan gaye bane me kuma tsafta, white boot ne a kafanshi, sai wondon Nysc da farin shirt ajikin shi sai farin glass siriri daya manna a idon shi, a hankali yace ok mum ba damuwa tunda hakan kikeso zanje gidan uncle hanif d'in in zauna kituromin address d'in don bazan gane ba, to tace daga bangaren ta sannan tace ko kaifa Abbas, kawun ka in yaji kayi service a kano kuma kama gida nima bazai barni ba, kullum dama yanamin mitan bana son turaku anayin zumunci kaga yanzu tunda dama yafaru sai kaje, no problem mum, ya fad'a tareda mata sallama sannan yakashe wayan.


hannun shi yasa a waist tareda fura wani iska a bakin shi, sam shi baiso haka ba, baiso ace zai zauna a wani gida ba, bayason takurawa kowa kuma shima bayason kowa ya takura mishi, amma sam mum d'in shi takasa ganewa, a hankali yace gaskiya inaga dole nayi relocating na koma Abuja, tun yanzu yafarajin hayaniyan kano ya mishi yawa sannan gashi ana kokarin kaishi gidan mutane kamar wani karamin yaro, hannu shi yasa a goshi,ya taro naman goshin shi sannan yashafe fuskanshi, wayan shi ya zaro sannan yakira abokin shi Nabil wanda suka hadu a nysc camp, Nabil idan kagama ina jiran ka a mota, baijira me zaice ba ya kashe wayan sannan ya bud'e motan shi yashiga.


Glass din motan nabil ya buga mishi, unlock ya danna nabil ya bud'e yashiga, shigan shi yana daidai da isowan text d'in mum, bud'ewa yayi yaga address d'in hotoro ne waje college of agric, d'ago kanshi yayi yacewa nabil daga nan yanzu ta ina zan bi yakaini hotoro wajen college of agric? D'an shuru yayi tare da kankace ido sannan yace ohh nagane tawajen Ahmed musa sport center, sabuwar kwaltan nan, kaikaicewa yayi sannan yacewa Abbas me zakayi acan? D'an b'ata rai yayi sannan yace gidan brother mumcy ne wai can takeson nazauna, dan murmushi nabil yayi sannan yace to ai daga wajen babu wani nisa meyawa zuwa wajen PPA ka, saboda office d'in FIRS yanakan zaria road ne, da sauri Abbas yace yauwa ya kuka karene sunyi posting d'in ka inda kakeson kuwa?


Hannu shi yad'an ware sannan yace eh sun kaini kedco amma branch d'insu na zoo road, yad'anyi nisa da anguwan mu amma dai badamuwa. 


Motan ya tayar yana cewa yanzu dai zaka rakani hotoro idan mukaje na ajiye kayana sai inkai ka gida inga anguwan ku, badamuwa nabil yace, haka sukaci gaba da tafiya motan tsit kowa da irin abunda yake sakawa,Abbas jiyake kamar bazai iya zaman kano ba saboda tun yanzu garin ya isheshi, sai sakawa yakeyi da warewa, shiko nabil duk tunanin yadda zaina tashi daga en kaba yaje zoo road yakeyi, kuma ya isa kafun karfen takwas ga kuma cacan kudin abun hawa, saboda shi Nabil ba dan masu kudi bane karfin hali ne, karatun shi ma shi yad'auki nauyin kanshi, shiyasa yanzu ma yadage yasamu waje mekyau yayi service ko zai samu yatara wani abu bayan service yafara business saboda yadda aiki yazamo a kasan nan. 


Haka sukayita tafiya yana nuna mishi inda zaibi har suka isa wajen, daganan yakira number uncle d'inshi, ya karisa mishi kwatancen, suna isa gate din gidan sukayi horn, hannu shi yasa a habarshi yana dan cije leben shi tareda tunanin zaman dazaiyi a kano, ta cikin mirror ya hango wasu en mata sunfito a daidai gidan setin bayan su, sanye take da doguwar riga er dubai, iskane ya dan yaye gyalenta dasauri ta kamoshi, wajen wani mota yaga sun nufaโ€ฆ


kamar wacce aka kira juyowa tayi tana kallon motan su Abbas wannan ne yabashi daman ganin kyakkyawar fuskanta, take yaji kamar bugun zuciyan shi na karuwa da sauri ya kauda idon shi akanta, harma an bud'e musu gate bai sani ba, da sauri yashigar da motan shi ciki, zeezee ce tad'an zungure ta tare da cewa kinsan su ne? d'an gyara tsayuwan tayi tace wallahi hankali na ma ba a kansu yake ba, karisawa wajen su Hasib sukayi, kara tamke fuskan shi yayi, zeezee ce tace lafiya dai Malam Hasib naga kabata rai kaida yakamata ka ganmu kayi farin ciki, ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace ai zuwan mu bashida wani amfani tunda gama kallon wayanda kuke muradi, faisal muje ko, kafun faisal d'in yayi magana ma yafigi motan shi a guje yabarsu da kuraโ€ฆ....


*ZEETY DELIGHT*๐Ÿ’–


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol