Free chapter · Read without an account

10

by Rahma Kabir · KAZAMIN TABO

ƘAZAMIN TABO


10


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir.



Anas sun koma asibiti an karasa yin binciken da ake masa, suka daura shi akan magani tare da tabbatarwa Abba insha Allah jinsa zai dawo daram kamar da, suka dawo gida Abba ya sauke shi a kofar gate sai ya wuce asibiti shi kuma Anas ya shiga gida. 


Abba ya samu Dr . Abdul ya gwada masa BP dinsa kuma ya hau dari da tamanin, dole yasa Dr. Abdul ya daura shi akan maganin hawan jini da zaisa jininsa ya sauka, sannan ya ba shi wasu shawarwari wanda zasu taimaka masa wajen jininsa kar ya rika hawa, sai ya sallame shi ya tafi. 


Abba yana fita ya wuce kasuwa a can dinma kwanciya yayi ya kasa yin komai, mamakin abinda Momy ta yi dazun ya dame shi, a ganinsa ya dace ace ta fada masa abinda Nabeel yayi, tunda ta tabbatar dai ba zai kuma yiwa 'ya' yansa mugun hukunci ba, kuma yana da hakki ta fada mishi matsayinsa na mahaifinsa, yadda take son boye maganar ya daure masa kai, sai wani tunani ya fado masa yayi guntun murmushi tare da gasgata cewar dole zata boye mi shi. A haka ya yini sai dare ya dawo gida. 



*******


Bayan wata guda 


Anas ya yi ta shan maganinsa har lamarin ya yi sauki, sai dai kuma ya koma yana ji kadan can kasa, sai an matso sosai kusa da kunnensa anyi magana da karfi kafin zai ji, a zuwa lokacin har muryarsa ya sauya zuwa na bebe, da karfi yake magana sannan da sauri, duk da sunata zarya asibiti amma abin bai sauya zani ba, daga karshe likita ya tabbatar musu cewar sunyi iya yinsu akan lamarin, iya abinda za su iya yi kenan dan Anas ya riga ya nakasa ya zama bebe, dan haka suyi hakuri su dauki dangana, in ba haka ba sai dai suyi ta yawo asibiti suna kashe kudi a banza. A ranar da likita yayi musu wannan bayanin Abba ya girgiza wanda yasa jininsa sai da ya kara hawa, jinya sosai yayi harda kwanciya asibiti, sai da yayi kwana biyar kafin aka sallamo shi ya cigaba da jinya a gida, da kyar ya samu kansa ya dawo hayyacinsa, kakus ta dage da bashi baki da shawarwari gami da tsananta addu'a, haka ma bangaren momy tayi iya yinta, a haka har Abba ya dangana ya fauwala wa Allah, sai dai duk in ya tuna shi ne silar sanya Anas a wannan yanayi sai ya ji babu dadi, ya riga yayi masa Kazamin tabon da har Abada ba zasu mance ba, inda ana maida hannun agogo baya tabbas da ya sake wannan kaddara mai cike da bakin ciki da alhini, sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dole su hadu su dangana tare da yin hakuri.



_____



KANO


Karfin addu'ar da Khadija take yi a zuciyarta yasa ta samu salama daga halin da sake ciki, ta yunkura da kyar ta ja jikinta a tiles zuwa bakin gadon ta tsuguna akan guiwarta ta mike tare da ambaton sunan Allah, sai aniyar zuciya take yi ga wani kullin abu daya tsaya mata a zuciya wanda da zata samu damar yin kuka da kila zata samu rangwame daga kunan da yake mata, ta sanya hannun damanta a hancin Amira taji shuru babu numfashi, sai ta daura kannunta duka a gefen zuciyarta ta ji yana harbawa a hankali, sai ta sauke gauron numfashi kafin ta mike ta shiga toilet da jan kafa, ta hada ruwa mai zafi a baho ta fito ta dauki Amira cikin karfin hali ta kaita toilet din ta sanya ta a cikin ruwan data hada, nan take Amira ta sauke numfashi da karfi, sai Mami ta yi kokarin zame mata riga ta shiga watsa bata ruwan a jiki da furkarta tana matsa jikin musamman cinyoyinta, sannan ta sanya hannu a kasan Amiran ta shiga wankowa, sai a lokacin ta ji hawaye yana bin kuncinta, Amira ma saboda zafi da radadin da taji a kasanta, yasa ta farka tare da rike hannun Mamin tana cewa cikin dishewar murwa idonta rufe. 


Da zafi zan mutu. 


Mami ta ji kuka me sauti ya turnukota sai ta yi sauri ta danne shi tana fidda kwalla me yaji, haka ta cigaba da wanketa a hankali harta gama mata wankan, sannan ta cireta ta rufa mata towel ta fito da ita ta kwantar a gefen gadon in da jinin be bata ba, Amira tuni barci ya kara daukarta domin jikinta ya kara laushi ga kuma yadda taji dadin wankar kamar ya sauke mata wani gajiya ne, Mami ta koma bayin ta hada nata ruwan wankan tayi, ta fito ta sanya wani bakar doguwar riga da hijab ta shinfida sallaya ta zauna a kai ta shiga gabatar da nafila a zaune, domin kafafunta ba zasu iya daukarta ba saboda wankan da tayi ya kara kashe mata jiki, ta jima a zaune har kusan karfe daya kafin ta idar ta kwanta akan daddumar ba jimawa barci ya dauketa. 


Abba kuwa da rarrafe ya isa gadonsa ya hau ya kwanta, jikinsa yayi masa mugun sanyi ya kasa yin wanka, tsananin damuwa ya dabaibaye zuciyarsa, tsoro da fargaban hukuncin da Khadija zata dauka akansa yake, yana tsoron ta fallasa kazamin tabon da ya yiwa 'yarsa, yana tsoron da wani ido zai kalli danginsa da mutanen gari, yana tsoron asirinsa ya tonu tare da kunyar fita cikin mutane harya hada ido dasu, ya tabbatar da cewa wannan bakin fantin daya gogawa kansa sai ya yi silar fasa aurensa da Bilkisu, da tunani barkatai barci ya dauke shi cike da tunanin makomar rayuwarsa nan gaba.


Kiran sallar farko ya farkar da Mami ta mike cikin nauyin jiki idanunta duk sun kummbura saboda kukan da ta yi, ta isa jikin Waldrop din kayanta ta sauke akwatin trolley dinta guda biyu ta shiga jera kayanta da suke walddrop a ciki, sai da ta kwashe kusan fin rafin kayanta, kafin ta hada da mayafanta da hijabai sai ta rufe su, ta dauko wani bakar jaka na matafiya ta jera jakukunanta da takalma a ciki har guda hudu, sannan ta kwashe gwala gwalanta a wani karamin jaka ta sanya a ciki, ta dauki bakar leda ta zuba kudadenta da suke dakin a ciki harda wanda Abba ya bata jiya duk ta hada ta daure ta sanya cikin jakar, saita koma dakin Amira ta hada kayanta a babban trolley kadan ta bari, ta kwashe harda yan kunyayenta da su gyalenta harda hijabai, takardunta na makaranta ne kadai bata dauka ba domin babu wani amfani da za suyi mata har sai sun dawo, ta fito da trolley din falo ta koma dakinta ta ajiya kayan da zata sanya mata, ta dauki key din sabon motar da Abba ya bata ta ja trolley din kayanta ta fita dasu zuwa falo, haka ta fice dasu daya bayan daya cikin wannan daren, ta bude boot din motar ta jera kayanta aciki sai ta bude back seat ta sanya kayan Amira a ciki, sannan taje gaban motar ta kwantar da seat din gefen driver sai ta dawo ciki, ta kwashe duk wasu abubuwan amfaninta ta adana su sannan ta sanyawa Amira kaya riga da siket na atamfa, ta sanya mata hula akai sai ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, lokacin anata kiran sallah sai ta gabatar da nafila kafin tayi sallar asubahi ta yi addu'a ta mike, ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar rigar atamfa sai ta daura daukwalinta ta yafa gyale ta wuce dakin Nura, ta shiga ta zauna gefen gado ta dafa kansa tana cewa tare da fitar hawaye. 


Zanyi kewarka Nura sosai amma nan da wani lokaci zan dawo insha Allah, da zarar Amira ta samu lafiya sannan na samu natsuwa sosai azuciyata.


Sai ta yi masa addu'a ta shafa masa a kai ta mike da sauri jin an fara shiga masallaci, ta fito ta isa dakinta ta dauki Amira sannan ta fito ta kaita mota ta sanya a seat din data kwantar, ta koma ciki ta dauko wayoyinta da kuma key din shagonta hade dana mota ta fito, ta shiga motar ta sanya key ta kunna kafin tayi hon me gadi da sauri ya fito daga dakinsa, yana hango motar yayi saurin bude gate ta fice abinta, yana yi mata sai ta dawo bata tanka shi ba, yabi bayan motar da mamaki domin tunda yake bai taba ganin ta fita a irin wannan lokacin ba, ya rufe gate ya dauki butarsa dan yayi alwala.


Mami ta tsaya a shagonta dake bakin titin layin, ta bude tare da kwashe kudin dake drower, sannan ta bude fridge ta kwashe sauran drink din da suke ciki guda goda sha uku ta zuba su a seat din baya kafin ta koma ta dauko kudin ta fito ta rufe shagon ta dawo cikin mota, sai ta turawa yarinyar dake tsare mata shagon text kamar haka. 


Sadiya da fatan kin tashi lafiya, wani tafiya ta gaggawa ta ta so min dan haka na rufe shago karki bude har sai in na dawo na nimeki, sannan zan tura miki salary dinki na wannan watan ta account. Nagode. 


Tana gama tura mata, sai ta zuba kudin a ma'ajiyar mota, sai ta kunna motar ta yi gaba.


Abba kuwa karan hon din motarta ne ya tashe shi daga barci yayi saurin sakowa daga gado jin an tayar da sallah amasallaci, ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa ya fito ya sanya jallabiya ya gabatar da sallarsa a daki, bayan ya idar ya koma gado ya kwanta ya shiga tunanin inda Khadija zata je da asuban nan, hankalinsa yayi mugun tashi tsoronsa karta je gidansu ta fada abinda ya aikata, da sauri ya sauko daga gadon kamar an tsikare shi, ya shiga zaga dakin yana jero addu'a akan Allah yasa ba gida ta tafi ba, sai da ya gaji da yawo kafin ya koma ya kwanta a haka barci ya kuma daukarsa. 


Da gari ya waye sosai Nura ya farka barci ya fito falo ya ga ba kowa sai ya wuce dakin Amira, ya samu bata ciki sai ya shiga dakin Mami itama bata nan sai ya wuce dakin Abban su ya murda yaji a rufe, sai ya buga nan take Abban ya farka ya zo kofar dakin ya bude murya yana cewa. 


Waye ne?


A tsorace yake gudun kar ya bude yaga khadija ce, yaji muryar Nura yana cewa shi ne sai ya sauke gauron numfashi ya bude yana cewa. 


Nura sai yanzu ka tashi? 


Eh yau Amira bata tashe ba na duba ta a daki bata nan, kuma har yau Mami bata dawo ba. 


Ok Mami ta dawo jiya ta kai Amira asibiti, yanzu jeka shirya da sauri ka karya saina saukeka a makaranta dan yau school bus dinku ta wuce ka. 


Da to ya wuce, ya koma dakinsa ya shiga wanka Abba kuma ya wuce dakin Mami ya samu a bude yake, sai ya shiga idonsa ya sauka akan gadon wanda jini ya bata zanin, sai yayi saurin runtse ido ya bude tare da naushin iska zuciyarsa cike da nadamar abinda ya aikata, sai ya isa gadon ya cire zanin gadon ya dukunkune shi ya shiga niman leda amma be gani ba, a haka ya fahimci cewar babu trolley din dake kan Waldrop din dakin, ya isa Waldrop da sauri ya bude, sai yaga duk ta kwashe kayanta kadan suka rage, ya zaro ido waje cike da tsoro yana cewa. 


Ina kuma khadija ta nufa? Kar dai ace gida ta tafi. 


Sai ya fito da sauri ya nufi dakin Amira, yaga itama babu kayanta, sai ya fito falo jiki a sanyaye ya zauna rike da zanin gadon cike da tsantsar damuwa, tashin hankalinsa kar ace Khadija gida ta tafi, a haka ya zurfafa tunaninsa akan niman mafita, Nura ya fito cikin shiri ya cewa Abban ya gama, sai ya mike jiki ba kwari ya shiga kitchen ya dauko bakar leda ya sanya zanin gadon sai ya fito ya dauki key mota da wayarsa suka wuce.


Abba yana sauke Nura ya kira Alh. Abba a waya ya tambaye shi inda yake, ya tabbatar masa da yana gida sai ya kashe wayar, yana tunanin gwara yaje ya fada masa abinda ya faru, saboda shi ne kadai amininsa wanda ya yarda da shi da zai iya fada masa matsalarsa, wata kila ya sama masa mafita, burinsa dai bai wuce ace asirinsa ya rufu ba,ko ta halin ƙaƙa, saboda yana gudun shan kunyar duniya, a hanya ya tsaya ya yarda zanin gadon a wani rafi kafin ya wuce gidan Alh. Abba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol