Free chapter · Read without an account
Page 7 & 8
TWIST OF FATE
(Karkatarwan Ƙaddara)
By
REAL ESHAA
Free Page 7&8
____________________________Cike da Mamaki Ummu tace"tsayuwar me kuke haka??,Murmushi Ainah ta ƙaƙalo da faɗin"Dama rakata zanyi ta gaishe da In-law ɗin ta.Kallon dressing dake jikinta Ummu tayi dogon wando ne blue da Kuma farin t-shirt me dogon hannu kanta sanye da blue hula fuskarta babu make-up tuno kalaman Mom da Granny yasa tace,"Kar ki kuskura ki fito se kin canza wannan kayan,Kai ta gyaɗa tana mamakin kalaman Ummu,Riƙe hannun Sajnah Ummu tayi suka fice, Ajiyar zuciya RK ya saki tare da fitowa daga cikin Siff ɗin.Harara Ainah ta zabga masa cike da tsiwa tace"Malam se kasamu damar fice mana daga ɗaki ko??.Wani irin kallo ya Mata batare da yace da ita Komai ba ya ki shingiɗa akan gadon,Wara manyan Idanunta tayi tace"Katashi ka fita mana aɗaki,Lumsassun Idanunsa ya lumshe,still yaƙi tanka mata, Azuciye tace"Bari na kira Granny ko Ummuna idan sun zo zaka fita tafaɗa tare da nufar ƙofa taku biyu yayi ya fisgota ta faɗa faffaɗan ƙirjinsa, hannu yasanya tare da damƙe sumar kanta dake cikin hula,Cikin husky voice yace"Ni tsaranki ne da zaki tsaya gaba kina mayar min da magana??.Manyan Idanunta ta zuba masa cikin rashin tsoro tace"Malam sakar min Kai tun kafin na maka Ihu! Murmushin gefen baki yayi wanda ya lotsar da dimple ɗin sa yace"Ai meyi baya faɗa just do it,ƙaramin bakinta ta buɗe da niyyan ihu cikin banzari ya Sanya lallausan tafin hannunsa ya toshe mata baki tare da mannata ajikin siff ya Mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa cikin ƙasa da murya yace"Meyesa ki ka fasa!?,Banza kallo ta watsa masa cike da Jarumta ta tattaro ƙarfinta tare da ingijesa anma ko ge zau beyi ba sema muskilin murmushi daya sakar mata."Afusace tace"dalla Malam matsamin ajiki,Yatsine fuska yayi tare da ingijeta daga jikinsa yana jifanta da wani irin kallo batare da yace"komai ba ya nufi window ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da buɗe siff doguwar riga fari me adon baƙi ajiki ta ɗauka ta Sanya,kana ta feshe jikinta da turarukan ta masu daɗin ƙamshi ƙaramin veil tasa ta rufe madedecin kanta Cikin takun ƙasaita ta nufi falon, Murmushi ta saki ganin yanda Ummi ta Rungume Sajnah ajikinta,Cikin ranta tace"Alhamduliilah Sajnah tayi dacen suruka,Akan RK ta sauƙe manyan Idanunta hakan yayi dede da lokacin daya ɗago kansa harara ta zabga masa kafin ta ɗauke Idanunta daga kansa,Zama tayi daga gefen Ummu Kallon Mom da Ummi tayi tace"Good afternoon Maa,Da Murmushi Ummi tace"Afternoon Ainah how are you?."Am fine ta amsa kana ta gaishe da Daddy da Uncle Jabeer,Se Misalin ƙarfe huɗu na yamma suka yi musu sallama har jikin motocin su sukayi musu rakiya cike da farin da mmutuntawa suka rabu.Misalin ƙarfe bakwai da rabi Ainah ta fito daga bedroom jikin ta sanye da wando hallways kalar light purple da riga fari me buɗaɗɗen hannu daga ƙasan sa atsuke yake,tayi stoking da farin belt kanta yane da ƙaramin veil light purple hannunta na maƙale da hangbag irin na 'yan Mata me kyan gaske Ahankali jikinta ke fitar da fitinannen ƙamshi me sanyi.Anutse ta Rungume Ummu dake tsaye jikin frigt tare da bata peck a kuncinta,"Ashagwaɓe tace"Ummuna zan tafi,Ɓata fuska Ummu tayi tare da janye ta daga jikinta tace"Meyesa bakyajin magana Ainah tun wuri baki jeba se yanzu da dare yayi bayan kinsan Abbey ki beson fitan dare baya ga haka kinsan High-tension be da kyau Koda ace rana ne bare Kuma dare so please ki haƙura.Rau-rau tayi da manyan Idanunta kamar za tayi kuka tace"Please Ummuna Insha Allah ba abinda ze faru.Ummu zata sake magana tace"please Ummuna Dan Allah kibarni naje I miss My Dada."Ok karki daɗe please idan Kuma kinga dare yayi ki kwana acan idan yaso gobe seki dawo."Cike da farin ciki tasake bawa Ummu peck ahannunta tace"Thanks Sannan ta fice,Da Sajnah dake ƙoƙarin zuwa sashen nasu taci karo Murmushi Sajnah tayi tace"Sister Ainah Ina zuwa kikayi irin wannan adon ba neman escort,"Fari Ainah tayi da Ido da cewa zo muje ki rakani gidan Dada I miss her.Wara madedetan Idanunta Sajnah tayi tace"Wace unguwar zani a wannan Daren ai sede ince Allah ya kiyaye.Taɓe baki Ainah tayi tace"Sarkin tsoro to aise Kiyi zamanki, Murmushi Sajnah tayi tare da faɗin"Inde akan wannan unguwar ce ki kirani da ko wane suna na amince ta faɗa tana shigewa.Seda ta fita juntion Kafin ta samu adedeta,Cikin harshen turanci tasanar da shi inda ze kaita,ɗan Jim yayi se Kuma yace"anma bazan Shiga dake ciki ba,Kai ta gyaɗa tare da faɗin"ba damuwa, sannan ta Shiga.Adede inda sukayi ze sauƙeta ya tsaya fita tayi tare da ciro masa kuɗinsa ta bashi lokacin gari ya fara duhu ga hadari anutse take tafiya kamar daga sama taga anshari gabanta,Ayatsine ta ɗago kanta tare da watsa masa mugun kallo ta kauce,Sake taran gabanta yayi yace"Fine girl how are you??,Kallon ɗan iskan askin dada dake kansa da Kuma shigar dake jikinsa tayi,Ahasale ta sake ratsawa gefensa zata wuce batare data tanka Shiba, Unexpect taji sau'kan hannunsa a ƙugunta, Azuciye ta ɗaga hannu ta yarfa masa mari,Kafin ta sauƙe hannunta taga wasu manyan samari Wanda aƙalla sun kai biyar suka kewayeta,Cikin hargagi ɗaya daga Cikin su yace"How dare you slapt our boss.Da ƙyar ta haɗiye wani mugun yawu daya tsaya Mata a maƙogoro, Murmushi gayen data mara yayi yace"I will teach you lesson that you will never forget,ya Faɗi haka tare da janye veil dake kanta.Wani irin tsoro da fargabane ya shigeta arayuwar ta batason abinda ze taɓa mata mutuncin ta komai ƙanƙantar sa tanaso taje gidan mijinta amatsayin cikakkiyar mace Mai daraja.Tunanin ta ne ya katse alokacin da taji hannunsa akan belt dake ƙugunta, Zazzafafan ajiyar zuciya ta sauƙe tare da tattaro ragowar jarumtakarta ta ingijesa daga jikinta hangbag ɗinta ta ɗaga tare da buga masa agoshi Kafin ya ɗago kansa ta ruga da gudu"Cikin tsawa Boss ɗin yace"Catch her.Jin haka yasa tashiga gudu da iya ƙarfinta,Waigawa tayi taga sun kusa cimmata mata,Atsorace ta Cigaba da gudun tana waigensu wani irin tuntuɓe tayi atake ta zube awajen goshinta ya bugu da dutse,Ahankali ta buɗe idanunta da taji sunyi mata mugun nauyi ta sauƙe akan samarin dake kewaye da ita, Lumshe Idanunta tayi Hawaye suka zubo mata,Cikin tafiyar tantirai Boss ya ƙaraso kusa da ita tare da tsugunnawa akanta hannun ya sanya ya ɗago kanta tare da matso da fuskarta daf tasa da sauri ta juyar da kanta ganin abinda yake ƙoƙarin yi,Sake juyo da kanta yayi Yana jifanta da mugun kallo,Yawun dake bakinta ta tattaro ta watsa masa afuska, Afusace ya ɗaga hannu tare da kife ta da mari kana da ƙarfin gaske ya fincike Belt dake ɗaure aƙugunta,ya ranƙofa kanta,Runtse Idanunta tayi tare da karanto duk wata addu'a data zo bakinta,Haske ne ya gauraye mata idanu kamar me tsoron wani abu ta buɗe idanunta da taji sunyi mata mugun nauyi,Ahasale boss da tawagar sa suka juya ganin wanda ke haske musu ido,batare da tsoro ko fargababa mamallakin motar ya dumfaro kansu tare da danna hong da ƙarfin gaske,Yana zuwa inda suke yayi parking Cikin han zari suka kewaye motar Zama ya gyara tare da gyara zaman farin eyeglass dake Idanunsa amugun fusace,Boss ya umarce tawagar sa dasu buɗe motar,Hannu ɗaya daga Cikin samarin yasa ya buɗe, Cike da mamaki suka juya ganin wanda ya buɗe motar ya baje alasa sakamakon wani bahagon naushi da mamallakin motar ya sakar masa,Azabure suka yo kansa cike da izzah mamallakin motar ya zuro ƙafafunsa haɗaɗɗen agogon azurfan dake hannunsa ya murza tare da dun ƙule hannunsa ya zabga musu naushi rufuwa sukayi akansa tare da riƙe hannunsa kansa Boss ya nufa tare da dunƙule Hannu ya zabga masa naushi agefen bakinsa atake wajen ya fashe,duka Boss yashiga Kai masa tako Ina agaba ɗaya ilahirin jikinsa, Miƙewa Ainah tayi cikin tsananin tausayin mutumin daya ɗauki kasada adomin ya tamaketa wani irin shock ne ya ziyarceta ganin fuskar da ko amafarki ba tayi tsammani ze iya temakon taba,Ihu ta buga asanda taga Boss ya zaro wuƙa Ze caka masa Cikin ƙarfin da batasan tana dashi ba ta ingijesa wuƙar ya faɗi,Ganin hankalin gayun yayi kan Boss ɗin su yasa RK shammatar su tare da dukan su tako Ina Cikin ƙaramin lokaci ya galabaitar dasu.Da sauri ya fisgi hannun Ainah ya sata a mota ganin yana ƙoƙarin yin rivears ne yasa tace"Gidan Dada zani ba musu yagyara motar tare da fusgar motar da gudu ganin yanda Boss suka biyu su,Suna Isa ƙofar gidan Dada ya danna hong leƙawa gate man yayi Ainah tayi saurin sauƙe glass din motar kasancewar me duhu ce,ganin ta yasa gate man din yayi murmushi tare da komawa ciki ya buɗe Musu gate suka shiga.Babban coumpound ne dake ɗauke da manyan sashe huɗu yayi se flowers da suka kewaye ko wani sashe se kuma parking space me ɗauke da motoci daga gefe akwai manyan tanks na ruwa,Anutse ta sanya ƙafafunta da taji sunyi mata mugun tsami awaje,Runtse Idanunta tayi tare da komawa Cikin motar ta zauna tana sakin Ajiyar zuciya.Ɗan taɓe baki yayi ganin yanda take narkewa,Buɗe motan yayi ya fita cak ya tsaya Jin ana knoking ɗin gate,Leƙawa mai gadin yayi ganin wa anda ke tsaye ya sashi ƙaƙalo murmushi da faɗin"How may I help you Sir,"Cikin harshen turanci Boss yace"akwai motar data shigo nan gidan??,Kai gate man ya girgiza alamar a'a,"Are you sure Boss ya faɗa yana ƙoƙarin leƙawa,Da sauri gate man yace"Yes Sir am very sure Juyawa Boss yayi suka bar wajen...Ajiyar zuciya Ainah ta saki Cikin sauri ta buɗe motar ta fita tare da Jan hannun RK zuwa sashen Dada Suna zuwa tayi knowing,daga ciki akace"Who's that??"Nice Dada cewar Ainah.Buɗe ƙofar akayi,Kallon mamaki Dattijuwar matar tayi ɓakace doguwa kallon ɗaya zaka mata kasan lokacin ƙuruciya ta zuba kyau... Maganan dake bakinta ne ya maƙale ganin Babu ɗan kwali akan Ainah ga gefen bakinta dake fashe kallonta tamayar kan RK da shima gefen bakin sa ke kumbure da Kuma yanda jikinsa yake buɗuɗu."Subhanallah Meyesa meku haka tayi maganan cikin yanayin razana??,"Murmushi Ainah tayi da faɗin"Nothing Dada calm down ta faɗa tare da Zama Akan kushin bayan ta Shiga.Biyo ta Dada tayi tace"Ku faɗa min Meyafaru daku??, Murmushi RK yayi da faɗin"Nothing Dada,Zama tayi akusa dashi tace"Just tell me true I know unguwarmu Bata da kyau Meyafaru da ku??."Ajiyar zuciya ya saki ganin yanda ta damu yasa shi faɗin"Ba abin damuwa bane nan yashiga zayyane mata,"Salati ta Sanya Cikin faɗa tace"Ainah Meyesa bakya Jin maganane so nawa nake faɗa Miki kidena zuwa unguwar nan idan dare yayi??.Tura madedecin bakinta tayi tace"I miss you so much that's why ta fada tare da shigewa bedroom.Miƙewa RK yayi yace"Dada zan tafi,"Kai Dada ta girgiza cike da ƙaunarsa tace"Haba me gida mu kwana idan yaso gobe seka koma,Kai ya girgiza da faɗin"a'a Dada d...Da sauri tace"Dan Allah Kar kayi musu Kaga yanayin unguwar tamu ba kyau Kuma mutanen zasu iya dakon ka."Kai ya gyaɗa badan ranshi yaso ba sedan baya son musu,Futowa Ainah tayi hannunta riƙe da ƙaramin bol dake ɗauke da ruwan zafi da kuma ƙaramin towel Zama tayi akusa da RK Ahankali ya ɗago Idanunsa dake alumshe ya zubasu akan kyakyawan fuskarta,Idanunsa ya sauƙe adede gefen bakin ta dake fashe,Towel ɗin ya karɓa daga hannunta tare da tsomawa acikin ruwan ɗumin hannu yasa ya dafe goshinta tare da Kai towel ɗin kan bakinta,Runtse Idanunta tayi tare da riƙe tafin hannunsa Jin yanda zafi ya ratsata.Lumsassun Idanunsa ya zuba mata da faɗin"Ki tsaya mana,Baki ta tura cike da tsiwa tace"Nide banso ka barni,Kafin ta ƙarasa maganan yafisgota jikinsa,Wara Ido Dada tayi da shigowar ta kenan cike da Mamaki tace"...
AYI SHEARING SABODA ALLAH
Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah ka Kai Haske kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka rigamu gidan Gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...
ESHAA CE