Free chapter · Read without an account

Part 9 & 10

by Aishatu Abdullahi Idris · Twist of fate

TWIST OF FATE

(Karkatarwan Ƙaddara)






By

REAL ESHAA





Free Page 9&10


___________________________"Ohhhhh Ainah kede ba zaki canza ba yanzu meye abin wannan raki?,Tura madedecin bakinta tayi cike da Shagwaɓa tace"da zafi Dada,Taɓe baki Dada tayi ta nufi frigt batare da tace"komai ba ƙanƙara ta ɗauko ta ajiye masa, Clamly RK ya sauƙe zazzafafar ajiyar zuciya tare da janye ta daga jikinsa,Ya Kai towel ɗin bakinta,Hannunsa ta riƙe kamar za tayi kuka tace"Please live it it's hurt me, Lumshe Idanunsa yayi tare da ajiye bowl ɗin agefe, fisgota jikinsa yayi tare da matse hannunta yakai towel ɗin bakinta ya goge jinin tare da matsa Mata kana ya ɗauki ƙanƙara ya manna mata,Ƙaramin kuka ta saki da faɗin"My hand,Da sauri ya kalli hannun se kuma ya ɗagota daga jikinsa ya riƙe hannun yaja.Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da Kai hannuta ta ɗauki bowl ɗin ta ajiye akan cinyarta tare da Sanya towel ɗin ta goge masa bakinsa hannunta ya riƙe Yana kallon ƙwayar Idanunta yace"thanks,Miƙewa tayi batare da tace"Komai ba tashiga bedroom dake falon Seda ta ɓacewa kallon sa Kafin ya lumshe Idanunsa.Ba daɗewa Dada ta fito hannunta ɗauke da ƙaramin plate ta ajiye akan dining Kallon RK tayi tace"Abdulrahman zo kaci abinci,Ba musu ya Miƙe dan yunwa yake ji yanufi dining. Murmushi Dada ta sakar masa da faɗin"Bari na kira Ainah tayi serving ɗin ka,Kai ya gyaɗa sannan ta juyawa ta shiga ɗakin da Ainah take,zaune ta hangota abakin gado tana shafa lotion,"Sannu kifi Sarkin wanka Dada tayi maganan tana Zama akusa da ita," 'Bata fuska tayi da faɗin"Wallahi duk jikina ciwo suke min,"Dole jiki yayi ciwo ai, Allah yatsare gaba,"Ameen ta amsa tana godewa Allah da RK yaje akan lokaci da batasan meze faruba,"Kiyi sauri ki shirya se Kiyi servin ɗin Abdulrahman abinci Muryan Dada ya katse mata tunani,Kai kawai ta gyaɗa sannan Dada ta fice,Ahankali ta buɗe siff Lallausan Murmushi ta saki ganin sabbin kaya aciki ko bata tambaya ba tasan Dada ce ta shirya mata,Cikin ranta ta furta I love you my Dada.Rigar bacci da tsawonsa be wuce gwiwartaba fari soll yana da duhu da hannun spaghetti ta Sanya da hulan net kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.Anutse RK da kansa ke sun kuye aƙasa ya ɗago Jin sanyayyan ƙamshi daya ratsa masa hanci atake tsikar jikinsa ya tashi kallo ɗaya yamata ya ɗauke kansa,Cikin takun ƙasaita ta zauna akujeran dake facing ɗinsa tayi serving ɗinsu,Wayarsa dake aljihu ya hau ruri Ahankali yasanya hannu ya cire tare da sanyawa akunnensa yace"Sajnatyyyyyy,daga ɗaya ɓangaren ƙayataccen murmushi Sajnah ta saki tace"Barka da wannan lokaci Yaya RK,"Barkan kide,ya faɗa Ahankali,Shiru ne ya biyo baya na wasu sekonni se kuma tace"kaci abin kuwa?,Kai ya gyaɗa kamar tana gabansa,yace"yan zu nake ci,Cikin ƙasa da murya tace"Ina matuƙar ƙaunar ka Yaya RK ka kulamin da kanka, Lallausan tafin hannunsa yasa ya shafa tulin sumar kansa da faɗin""Thanks for your care daga haka ya katse kiran.Taɓe Baki yayi ganin Ainah Bata wajen anutse ya cigaba da cin abinci bayan ya kammala ya miƙe ya koma falon ya zauna,Dada ce ta fito kallonsa tayi da faɗin"Abdulrahman taso kayi bacci, Murmushi yayi tare da miƙewa dan shi kansa yasan baze iya kwana akan kushin ba,Tura ƙofar Dada tayi ta shiga ɗakin babu haske da yawa sanyayyan ƙamshin roomfreshner da ƙamshin tularen ta tare da sanyin AC ne ya fara amsa musu sallamar, wuta me Haske Dada ta kunne kasancewar deam night ne,Ƙudundune ya hangota acikin Fargo tana sauƙe numfashi,ƙarasawa bakin gafon Dada tayi tare da soma tashinta anma ko alamar motsawa ba tayi ba janye duvert ɗin Dada tayi tare da janyo hannunta cikin ɗaga murya tace"Narasa Ina Kika gado wannan baccin jaraba mutum ayita tashin sa baze tashiba.Manyan Idanunta dake cike da bacci ta buɗe Cikin magagin bacci tace"Ina zaki kaini Dadaaaa?,Tana riƙe da hannunta tace" ɗakina zamuje ki kwana se kibarwa Abdulrahman wannan,Fin cike hannunta m tayi ta faɗa kan gadon,Goshi Dada ta dafe tare da sake janyo hannunta suka fice tana tirjewa,juyawa yayi ya rufe ƙofar bayan fitarsu faɗawa kan gadon yayi Ahankali ya lumshe Idanunsa tare da kafa hancinsa akan pillow Yana sakin ajiyar zuciya da haka bacci ya ɗauke sa...

Washe gari bayan sun kammala breakfast RK ya kalli Dada yace"Ni zan wuce Murmushi tayi tace"My regards to Your family."Insha Allah yace"tare da Ficewa,Hararan Ainah Dada tayi tace"Ba zaki rakashi ba mutum ya sadaukar da ransa akan ki anma ko Allah yatsare ba zaki masa ba,Tura madedecin bakin tayi tare da miƙewa ta buɗe ƙofar ta fita ga mamakinta se tagansa tsaye ajikin ƙofar,Tsayawa tayi akusa dashi tace"Nagode Allah yasaka da alkhairi,Ƙayataccen murmushi ya sakar mata da faɗin"You are highly welcome,Har jikin mota ta rakasa ya Shiga yaja,hannu ta ɗaga masa har ya fice.A dining ta samu Dada zama tayi agedenta,Da sauri ta ɗaga kanta Jin abinda Dada tace"Tsareta da Ido Dada tayi tace"Kinyi shiru Murmushi tayi tace"Ba abinda ke tsakanin mu dashi hasalima babu wata jituwa atsakanin mu ko jiya da Kika ganmu atare Allah ne ya jefosa anma ba tafiyarmu ɗaya ba.Hannunta Dada ta riƙe tace"Meye ra'ayin ki Akan sa??, Taɓe baki tayi tace"Ni bani da wani ra'ayi akan sa domin shi mutum ne me girman Kai da izzah ba shida haƙuri ko Mutunci aduk sanda aka taɓa shi Yana ji dakai sannan shi mutum me tsananin son kanshi, alokata da dama yasha faɗa da mutane Koda kuwa sun fisa Akan ƙaramin abu yana amfani da suna da kuma kimar da mahaifinsa keda shi Agaskiya be ɗauko halin mahaifiyarsa ko mahaifinsa ba yafi ɗauko halayyar matar uncle ɗin sa halinsa ɗaya ke birgine shine tausayi da kuma Jin ƙishirwa adaren jiya daya temakeni hakan ya tabbatar min da ze iya temakon kowa koda kuwa babu jituwa atsakanin su... Ajiyar zuciya Dada ta sauƙe da faɗin"me Kika fahimta acikin halayyar sa da kika faɗa,Taɓe baki Ainah tayi da faɗin"Ayan da na faɗa Miki halayyarsa ahaka na fahimta.Tafin hannunta Dada ta riƙe acikin nata da fadin"acikin maganan ki na fahimci abubuwa da dama na farko Abdulrahman mutum ne me tsananin tausayi sannan yana da haƙuri, anma idan aka taɓa shi baze bari ba sannan mutanen da suka fishi yake tanka musu basu kama girmansu bane,kada ki manta Abdulrahman mutum ne me sakin fuska sann... Katseta Dada tayi ta hanyar cewa shikenan abar maganan haka please duk ma me yakawo wannan maganan?,"Ni Wallahi bansan me Sajnah ta gani atare dashi ba da har ta amince masa!."Shiru Dada tayi se kuma tace"Soyayya suke da Sajnah??,Taɓe baki Ainah tayi tace"Jiya da rana aka zo tambayar masa.Ajiyar zuciya Dada ta sauƙe tare da faɗin"Allah ya Sanya alkhairi"Ameen ta amsa...Koda RK ya isa gida direct sashen sa ya wuce Cikin mintuna kaɗan ya shirya tare da feshe jikin sa da turaruka masu daɗin ƙamshi labcoat ɗin sa yasan ya tare da ɗaukar breafcase ɗinsa ya fita kan dining ya zauna coffee kaɗai ya zuba a mug yasha ya fice kasancewar babu kowa a falon,motar sa ya Shiga tare da yi Mata key yabar gidan,Ƙira an Sheik Ishaq ibn Abdallah ya kunna yana bi har ya isa tangamemen hospital ɗin da yake aiki,Cike da girmamawa Norse da perciens ke gaishesa, hannu kawai yake ɗaga musu har ya isa office ɗinsa.Zama yayi akujeran sa tare da lumshe Idanunsa yana tunani,Wayar sa data karaɗe office ɗin da suwwa ya Ciro daga aljihunsa kobe duba ba yasan me Kiran kasancewar ringing ɗin ta na dabanne cike da girmamawa yace"Good morning Ummi,"Ba tare data amsa gaisuwar saba tace"Ina ka kwana jiya Abdul?,Sannan nayi ta try number ka is not reachable and ka dawo gida baka nemeni ba Afusace ta ƙarashe maganan.Asanyaye yace"Am sorry Ummi yanzu zan fara aiki idan na dawo zan miki bayani but please Kar kiyi fushi dani... Ajiyar zuciya ta sauƙe tace"Ok take care of yourself."Insha Allah yace"tare da katse kiran.Kallon Faruk Ummi tayi ta sakar masa da murmushi da faɗin"What do you want?Ganin yanda ya tsareta da ido, Hannunta ya riƙe yace"Oooo I want to see Sajnah, Murmushi Ummi tayi tace"Kar ka damu zata zo soon,Kuka ya fashe dashi yace"No Ummi I want to see her soon.Mom dake sauƙa daga step tace"Meyefaru Faruk?,Miƙewa yayi ya fara bubbuga ƙafarsa tare da hargitsa tulin sumar kansa daya sha gyara yawu na zuba ta gefen bakin sa,dafe Kai Ummi tayi.Durƙusawa Mom tayi agefensa tace"Stop crying son and tell me what do you want!.Ƙin tan kata yayi ya cigaba da hargitsa tulin sumar kansa yana kuka,Waya Ummi ta ɗauka tare dailing number Granny ringing ɗaya Granny ta ɗauka tare da sallama,Daga ɗaya ɓangaren cike da ladabi Ummi ta gaishe ta,Amsawa Granny tayi da faɗin"Yasu Abdulrahman da Omar Faruk?l Duk suna lafiya ko,?"Lafiya su kalau yanzu ma Faruk ke rigima wai se Sajnah tazo gashi kuma drive ya fita bare na sashi ya kawosa.Murmushi Granny tayi tace"Badamuwa bari na kirata asashen mahaifinta se tazo."Godiya Ummi ta mata sannan suka katse wayar, Miƙewa Granny tayi tare da zuwa sashen Ummu bakinta ɗauke da sallama,Ummu dake gyara bedroom ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tace"Mama sannu da zuwa,"Yawwa aiki kike??,Kai Ummu ta gyaɗa tace"wani abu kike buƙata, Still fuskarta da Murmushi tace"Yanzu Fatima ta kirani awaya Wai Omar Faruk nata rigama se Sajnah taje shine nace"yanzu zan turata."Ok tana sama Bari na kirata,Hawa stair Ummu tayi ba daɗewa suka fito da Sajnah dake sanye Cikin doguwar rigar atamfa kanta yane da veil medium size.Kuɗin transport Ummu ta bata har gate Granny ta rakata abakin hanya ta tari adedeta, Tafiyar minti ashirin ya kaita unguwar Napep na parking ta fita ta basa kuɗin sa tare da Shiga ciki,tana tura ƙofar falon Idanunta suka sauƙa Akan Faruk daya har gitsa ilahirin falon,Da sauri ta tsugunna akusa dashi tare da riƙe hannunsa tace"Mekakeyi haka friend kana so ka jiwa kanka ciwo ne??Fisge hannunsa yayi cikin rawan murya yace"leave me alone as from today you are not my friend you don't care about me.Toshe bakinta tayi tare da fashewa da kuka tace"Am sorry Friend i promise ba zan ƙara barin kaba.Miƙewa yayi da gudu ya hau stair Mom zata bishi Ummi ta riƙe hannunta tace"Don't worry Sajnah zata kula dashi.Asanyaye Sajnah ta miƙe tabi bayansa Luckly abuɗe yabar ƙofar akan gado ta hangosa hannunsa riƙe da hoto Idanunsa sun kaɗa sunyi jawur alaman ɓacin rai da damuwa,Ƙarasawa tayi ta da kafaɗarsa tare da leƙa hoton da sauri ya noye hoton abayan sa tare da bige hannunta cikin tsawa kamar ba Shiba yace"I say leave me alone,Zama tayi abakin gadon ta fashe da kuka,Ahankali ya matso kusa da ita yace",stop craying??"Cikin sheshsheƙa tace"Um,um kana Kori na and I want to see that picture,Kai ya girgiza yace"that's is my secret,Ta gujeni tabar rayuwata If kema Zaki barni you can go babu damuwa zan rayu ni kaɗai.Kallon sa tayi cike da tausayin sa se Kuma ta fisge hoton abayansa wani razanannen ihu ya saki Wanda seda Baki daya gidan ya amsa, shake wuyanta yayi tare da manna kanta da jikin siff,Cikin tsananin tashin hankali Mom da Ummi suka nufi ɗakin zuciyoyin su na bugawa...


Kuyi haƙuri kwana biyu biki muke shiyasa kukaji shiru🙏🏻





AYI SHEARING SABODA ALLAH



Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah ka Kai Haske kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka rigamu gidan Gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani...





ESHAA CE🤙

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol