Free chapter · Read without an account

Page 23 & 24

by Aishatu Abdullahi Idris · Twist of fate

TWIST OF FATE

 (Karkatarwan Ƙaddara)







 By

REAL ESHAA





 Free Page 23&24


________________________________Afusace Granny tace"Wannan wani irin Shashanci da rashin hankali ne?,Ashe Abdul baka da hankali ina maka kallon nutsetstse mutum me hankali da kamala Ashe ba haka kake ba"?.Shiru RK yayi duk se yaji ya muzanta me Granny take nufi dashi?,Kallon fasiƙi ko me take masa Innalillahi wa'inna ilahai rajiu'n ya faɗa aƙasan ransa."Murya na rawa Ainah tace"What do you mean Granny?,Did you suspecting us?".Wani shegen kallo Granny ta watsa mata cikin fushi da ɓacin rai tace"Uwarki nake ba zarginki ba in banda tijara da rashin kunya ni zaki yiwa silly question bayan abinda idanuna suka gane min?".Miƙewa Ainah tayi duk da yanda cikinta ke murɗa mata be hanata faɗin"Enough Granny Ina ce ga Sister Sajnah Meyesa idan wani abu zamuyi baza mu keɓe mu aikataba se agabanta,bayaga haka Abdul Sister Sajnah zata aura shin wace alaƙa ce zata shiga tsakaninmu"?.Hawayen da suka gagara tsayawa Sajnah ta sharesa cikin sanyin murya tace"Granny is not what you think?,Kinfi kowa sanin halayyar sister Ainah batason ayi Mata injection, time da taga ya RK ze Mata shine tayi yunƙurin gudu by mistake ya RK ya faɗa kanta ta ƙarashe tana fashewa da kuka me gunji.Duk Ido suka zuba Mata ganin yanda take kuka tamkar ranta ze fita.Da sauri Ummu da Abbey suka ƙarasa bedroom ɗin jin sautin kukan Sajnah,riƙe kafaɗar Sajnah Ummu tayi da faɗin"What's wrong with you Sajnah"??,Cikin sheshsheƙan Kukan data kasa tsayarwa tace"Ummu sister Ainah Bata da lafiya ina tausaya mata ciwon ya sameta babu mutum akusa da ita bakiga halin da muka sameta ba badan Allah ya kawo muba bamu san halin da zata kasance ba".Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe tace"Stop crying Daughter,Dada mukaje dubawa munacan Ummin Abdul ta kira ta sanar mana anma lafiya muka tafi muka barta,Ƙarasawa bakin gadon Abbey yayi ya riƙe hannun Ainah da faɗin"Sorry Aintah Allah yabaki lafiya"Ameen ta amsa tana wasa da yatsun hannunta",Tsaki Granny taja tare da Jan hannun Sajnah suka fice tana ƙananun magana,Da kallo suka bisu Kai Ummu ta girgiza da faɗin"Allah yaƙara sauƙi sannan ta fice, Miƙewa Abbey yayi sakamokon wayarsa da aka kira, Ahankali RK ya ƙaraso kusa da ita tare da dur ƙusawa agabanta Lallausan tafin hannunsa yasa ya ɗago fuskarta tare da ƙura mata lumsassun Idanunsa cikin sanyin murya yace"Am sorry Ainah" Murmushi ta ƙaƙalo wanda be wuce saman laɓɓantaba tare da miƙewa tace"Kai zan bawa haƙuri Abdul akan abinda Granny tayi maka.Miƙewa yayi ya ƙaraso daf da ita har seda ta matsa jin yanda kusancinsu yayi yawa,Cikin tsira mata idanu yace"Akwai magana me muhimmanci da nake so mu tattaunawa dake,Kai ta gyaɗa tana wasa da yatsun hannunta,Dede setin ya Kai bakinsa da faɗin"...Gyaran murya da Ummu tayi yasa sukayi saurin juyawa,Da sauri Ainah ta matsa daga jikinsa tare da Zama agefen gadon tana dafe gefen cikinta,Lumshe idanu RK yayi yace"Se anjima Ummu zan wuce, Murmushi tayi da faɗin"Mungode kagaishe da Hafsat da Hajara."Insha Allah za suji ya faɗa yana ficewa".Ƙasa da Kai Ainah tayi ganin kallon tuhuma da Ummu ke jifanta dashi rufe ƙofa Ummu tayi ta dawo ta zauna kusa da Ainah tafin hannunta ta riƙe acikin nata babu walwala atare da ita tace"Meye alaƙar ki da Abdul!??",Arazane ta ɗago fuskarta da hawaye ya bushe cikin rawan murya tace"Ummuna me kike nufi??,Kina nufin zargin mu kike da Abdul??,Ummuna shine fa mijin da Sister Sajnah zata Aura"!.Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe tace"Banason matsala Ainah na lura da kallon da Mama ke muku,sannan yanda Abdul ke rawan jiki akanki dole yasa zargi azuciyoyin mutane that's Why kikaji na tambayeki,Taɓe baki Ainah tayi da faɗin"Inda sabo yaci ace mun saba da tsauraran hallayar Granny."Ajiyar zuciya Ummu ta saki da faɗin"koma menene Kiyi baya da Abdul.Ya mutse fuska tayi tare da miƙewa tashiga toilet ba tare da tace"Komai da Ummu ba...

Suna shiga ɗaki Sajnah ta faɗa kan gado tare da fashewa da wani irin kuka me gunji,Da sauri Granny ta dafa kafaɗarta kamar za tayi kuka tace"Meyafaru Sajnah?",Bata jira jin abinda zatace ba tace"kema kinga abinda hango ko?tabbas zargina ze zama gaskiya akwai alaƙa tsakaninsu.Miƙewa Sajnah tayi tare da share hawayen fuskarta tace"A'a Granny ba Abinda kike tunani bane sam bana zargina Sister Ainah ko ya RK,tashare hawayen da suka gagara tsayawa afuskar tace"Banason ganin sister Ainah cikin halin damuwa bazan iya juran hakan ba wannan dalilin kesani kuka.Murmushi Granny tayi tace"shikenan Allah yabata lafiya ta faɗa tare da shigewa bedroom.Pop Sajnah ta tsirawa idanu hawaye na zuba daga Idanunta...

Ahankali ya fito daga motar bayan yayi parking tamkar Wanda aka zarewa laka haka yake tafiya bakinsa ɗauke da sallama yashiga falon,Anutse ya sake maimaita sallamar but still Babu Wanda ya amsa masa se ido da suka zuba masa, mamaki ne ya kamasa ganin baki ɗaya family ns sa zaune.Ɗauke kansa yayi tare da nufar Up-stair,Cikin tsawa Ummi tace"Dakata Abdul!,Cak ya tsaya batare daya juya ba,ƙarasawa kusa dashi tayi tare da juyo da fuskarsa cikin tsaresa da Ido tace"Abdul meye alaƙar dske tsakanin ka da Ainah??,Shiru yayi tare da Sunkuyar da kansa ƙasa.Afusace ta sake ɗago da fuskarsa dake ƙasa tace"Ba magana nake ba kayimin banza!!??. Still kansa aƙasa yace"Nothing Ummi,Afusace ta kuma faɗin"Abdul ka bani amsa kafin na ɓata maka rai,"Da ƙyar ya danne abinda ke taso masa da faɗin"She's My Freind,Abotace Kawai atsakaninmu.Wani irin kallo suke binsa dashi sam basu yadda da abinda ya faɗa ba,Lumshe idanu RK yayi yana jin yanda bugun zuciyar sa ke ƙaruwa.Cikin wani irin fushi Ummi tace"Ƙarya kake Abdul??,Ka faɗamin gaskiya."Murmushin da yafi kuka ciwo yayi da faɗin"Gaskiya ɗayace Ummi babu wata alaƙa atsakanina da Ainah face abota...Kai ta girgiza da faɗin"ban yadda da abinda ka faɗa ba sam babu gaskiya acikin kalamanka,Durƙusawa yayi akan gwiwoyinsa tare da riƙe hannunta yace"Ummi ki yadda dani babu wata alaƙa atsakanina da Ainah face"Abota wacce Sajnah ta ƙulla.Afusace Mom tace"ƙarya kake Abdul Sajnah ba zata amince kayi abota da wancan gantalalliya,tubabbiyar yarinyar da batasan kunya ba bare Kuma ace kamun kai da kawai ba.Hannu RK ya ɗaga mata da faɗin ya Isa Mom kidena aibanta Ainah koma ya take 'yar uwar matar da zan Aura ce.Tsawa Ummi ta buga masa cikin rawan murya tace"Abdulrahman akan wata banzar yarinya mara kamun Kai kake mana rashin kunya?.Wani irin tashi jijiyoyin kansa sukayi Idanunsa suka kaɗa sukayi jawur dasu shin da cewa yayi yana son Ainah wani irin hukuncin zasu ɗauka akansa,Kuka Faruk ya fashe dashi tare da zama kusa dashi cikin yanayin maganarsa yace"Oooo Stop shouting at him Ummi zanyi magana dashi ya dena Abota da Ainah because she's bad girl.Kallon Dady Ummi tayi cikin muryan kuka tace"Kayiwa ɗanka magana Daddy me Abdulrahman ke nufi damu sam ban yadda abota ce atsakaninsa da Ainah ba nafi kowa sanin halayyarsa?.Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe da tunda aka fara magana bece komai ba Anutse ysce"Abdul,Juyawa RK yayi tare da zubawa mahaifina nasa Ido amma be amsa.Cikin tsaresa da ido yace"Ina so kasan cewa baka isa ka maidamu ƙananun mutane ba idan ma akwai wani abu aranka is better is cire tun kafin lokaci yaƙure maka,Be jira jin abinda zeceba ya juya yabar falon.Miƙewa Mom tayi tare da zabga masa harara kana tabar falon Ahankali duk suka watse ya rage se shi kaɗai.Ya daɗe azaune yana tunanin mafita kafin ya Miƙe ya nufi Bedroom ɗin Ummi,Bakinsa ɗauke da sallama yashiga,kallo ɗaya ta masa ta kawar da kanta,Asanyaye ya ƙarasa tare da ɗaura kansa akan cinyarta ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro,Ɗago kansa tayi da faɗin"Menene??,Hannunta ya damƙe acikin nasa yace"Ummi ki gafarceni nasan zakiji ba daɗi amma sam zuciyata batason Sajnah Ummi Ainah zuciyata keda burin kasancewa da ita amatsayin matar Aure...Ture kansa tayi daga jikinta cikin wani irin fushi dabe san tana dashiba ta nunasa da yatsa da faɗin"Abdulrahman koda zaka mutu babu aure bazan bari ka auri Ainah ba domin ba itace zaɓina ba sannan bata da qualities da zata kasance amatsayin surukar wannan gidan!.Tunda ya fara magana yake girgizi kai hannunta data fisge ya sake riƙewa da faɗin"Ummi ki fahimceni wallahi rasa Ainah tamkar rasa wani jigone acikin rayuwata... Bata bari ya ƙarasaba ta kifa masa Lafiyayyan mari cikin tsananin fushi da ɓacin rai tace"Abdul muddin Ni na tsugunna na haifeka wallahi baza ka taɓa auren wannan yarinyar amatsayin matar aurenka ba,Kuncinsa ya dafe yana kallonta da rinannun idanunsa ze sake magana...Ta ɗaga masa hannu da faɗin"ya isa haka wallahi koda wasa naji kafitar da maganar waje sena mugun saɓa maka taƙarashe da nuna masa hanyar fita...Tamkar mashayi haka ya fice yana haɗa hanya kai tsaye bathroom ya shiga kansa ya sakarwa shawer ya daɗe yana sakarwa kansa ruwan sanyi anma zuciyarsa ta gagara sanyi wani irin zafi yakeji azuciyarsa,da ƙyar yafita Agurguje ya shirya Cikin jeans sky blue da riga baƙi an rubuta Never Give Up da manyan baƙi jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshinsa duk da kasancewar fuskarsa babu walwala hakan be hana ainihin kyawunsa fita ba.Wayoyinsa ya ɗauka da key motarsa ya fita sashen Ummi ya nufa har ya murɗa handle ƙofar ze shiga ya tsaya yayi jim kome ya tuna yafasa ya juya kai tsaye inda suke parking motsrsu yafita motar Ummi yashiga yabar gidan kai tsaye hospital ya nufa.....Tunda ya fita Ummi ke kai komo acikin ɗakin,kallo ɗaya zaka mata ka hango tsantsar tashin hankali kwance afuskarta,tayi zaton ze dawo ya bata haƙuri se taga saɓanin haka, wannan abinda yayi ya tabbatar mata da cewa da gaske yake...

Yana parking Motar ya fito percien da Norse se gaishesa suke,yau Koda ɗaga hannun ne ya kasa,A corridor da zesa dashi da office ɗinsa yaci karo da Ramat,da sauri ta Shari gabansa ganin yana ƙoƙarin ratsata ya wuce,Tafin hannunsa ta riƙe cikin muryan kuka tace"Am sorry Dr am very sorry about what happened Please forgive me Dr Lucky told me to Stop away from you but I can't you are My love",ta ƙarashe Cikin matsanancin kuka!!.Janye hannun sa daga Cikin nata yayi babu walwala atare dashi yace"It's Ok".Ɗago kanta tayi da faɗin"Ka yafemin?,Kai ya gyaɗa batare da yace"Komai ba yasan zafin so da halin da mutum ke shiga wannan dalilin yasa be kyaretaba.Ds gudu ta juya tabar wajen ranta fess,Office ɗin yashiga tare da Zama Akan kujera ya lumshe Idanunsa duk da aikin da yake gabansa baya Jin ze iya komai damuwar dake ransa baze barshi ya iya aikata komai ba.Dafa Kafaɗasa Dr Lucky yayi yace"What are you thinking freind".Lumsaasun Idanunsa ya lumshe tare da ciza ƙasan laɓɓansa yace"It's family matter".Kai Dr Lucky ya gyaɗa tare da zama agefensa,Yace"Just Pray friend".Murmushi RK ya ƙaƙalo da faɗin"I will By the Grace of God!...

Wayarsa dake kan table ne ya katse tattaunawan nasu,Ahankali yasanya hannu ya ɗauka Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da amsa sallama.Daga ɗaya bangaren Sajnah tace"Am Sorry ya RK time da ka kira bana kusa Ahankali yace"What's wrong with you??, Murmushi tayi tace"Nothing daga bacci na tashi,"Ok ya jikin Ainah??"Shiru tayi na wasu secon Kafin tace"Da sauƙi!."Ok zan zo letter idan na tashi daga aiki take care of yourself."Insha Allah Ilove you,"Ok bye yace"tare da katse Kiran,Da kallo tabi wayar tare da Rungume Wayar aƙirjinta tana sauƙe ajiyar zuciya son RK ajinin jikinta yake.

Zama Ummu tayi agefen Ainah tare da miƙa mata coffee dake hannunta, Manyan Idanunta ta lumshe da faɗin"No Ummu banaso!.Ɓata fuska Ummu tayi tace"Maza ki karɓa Kisha tun safe rabonki da wani abu ko kin taɓa ganin anyi jinya babu abinci?".Marerece fuska tayi da faɗin"To ina Sister Sajnah ta dama min Custard?.Ɗauke Kai Ummu tayi da faɗin"Itama Bata Jin daɗi bari na haɗa Miki ta faɗa tare da miƙewa.Anutse Ainah ta miƙe tashiga toilet ruwan zafi sosai tayi wanka dashi sannan ta fito Ahankali ta zauna ta shafa lotion kana ta miƙe Dubai abaya pinch color me adon farin stone ta ɗauka ta sanya tana ƙoƙarin yafa mayafi wayarta ta hau ruri, Ahankali ta koma bakin gadon ta zauna Jin yanda ƙafafunta ke rawa,Ganin number ba Suna yasa batayi picking ba har kiran ya katse,sake Kira akayi akaro na biyu,Ya mutse fuska tayi tare da picking Cikin muryanta da be fita sosai tayi sallama.Daga ɗaya ɓangaren lumsassun Idanunsa ya lumshe Yana Jin yanda suwwan muryanta ke bin duk wani ɓango da tsokan dake jikinsa,Ciro wayar daga kunnenta tayi Jin shiru still taga Yana kan network, Ahankali tace"dawa nake magana iskar me zafi RK ya furzar daga bakinsa da faɗin,Ya jiki Ainatyyyyyy??"Da sauri ta runtse Idanunta tare da dafe setin zuciyarta dake bugawa da mugun sauri.Ahankali tace"Da sauƙi"Murmushi yayi tare da lumshe lumsassun Idanunsa yace"What are you doing now??,"Nothing tace"dashi"Kinci abinci?,Kai ta girgiza alamar a'a."Meyesa? Asanyaye tace"Kawai banso ne,ɓata fuska yayi kamar tana gabansa yace"But kinsan in Baki ciba ba Zaki ji karfin jikin kiba?.Madedecin bakinta ta tura batare da tace Komai ba, Murmushi yayi yace"Zaki tura baki da kyau idan na kamaki!.Manyan Idanunta ta Wara with so much surprise tace taya akayi yasan haka.Dariya yayi yace"kidena tunani da yawa kinga baki da lafiya".Tura Baki tayi tace"Kana abu kamar kana aiki da iska, Murmushi yayi yace"Anjima Zanzo duba jikin ki be jira Jin abinda zata ceba ya katse Kiran yana sakin murmushi.Hararan wayar tayi tare da tura Baki,tace"Troblem maker,Mug ɗin dake ɗauke da Custard Ummu ta ajiye Mata kana ta juya ta fice, Murmushi ta saki ganin custard vanilla ne gashi yasha madara Ahankali tasa cokali tashiga sha,tass ta shanye sosai takeson Custard,Ganin har anyi maghriba Sajnah Bata shigo sashen suba yasa ta kirats awaya ringing daya Sajnah ta ɗauka.Ajiyar zuciya Ainah ta saki tace"Sister Sajnah through out banganki ba".Murmushi Sajnah tayi da faɗin"Wallahi banjin daɗi ne anma zan shigo,Cike da damuwa Ainah tace"Allah yabaki lafiya sannan ta katse Kiran.

Ainah na ajiye wayar wani Kiran ya sake shigowa screen ɗin ta kurawa ido ganin number dake yawo yasa tayi mamakin Kiran seda yankusa katsewa tayi picking,Cikin yanayin muryanta da be fita sosai tace"Assalamu alaikum", Murmushi RK yayi yace"Ainatyyyyyy come out,Miƙewa tayi daga kishingiɗar da tayi da mamaki tace"Zuwa kayi ne?"Eh yace"ataƙaice",

Ok am coming ta faɗa tare da katse Kiran kana ta miƙe,Jikinta ta feshe da turarukanta masu daɗin ƙamshi ba tayi wani make-up ba anma tayi kyau naban mamaki, Ahankali ta fita falo bedroom ɗin Ummu ta nufa bakinta ɗauke da sallama sallah Isha taga tanayi juyawa tayi ta fice...Cak ta tsaya tana bin coumpound ɗin da kallo ganin babu alamarsa awajen.Jikin gate ta ƙarasa ta buɗe gaba da gidan su ta hango motarsa yayi parking anutse tanufe sa.Tun time data fito ya ƙura Mata idanu yana Kallon yanda take tafiya cike tantsantsar nutsuwa da ƙasaita,lumsassun Idanunsa ya zubawa shape ɗin kugunta daya baje acikin rigar zuwa fuskarta dake ɗauke da dara daran idanu,madedecin bakinta da yayi pinch color ya tattare ya ƙarewa kallo aƙasan ransa ya furta(Masha Allahu la quwwata Illah billa)Knowking glass da tayi yasa shi sauƙe gauron numfashi tare da buɗe Mata gaban motar,Ƙin shigata tayi tasa kanta acikin glass ɗin da faɗin"Barka da zuwa.Kawar da Kai gefe yayi yace"Kishigo Mana,Yamutsa fuska tayi tace"No basena shigaba nan ma is ok, Lumsassun Idanunsa ya lumshe da faɗin"But magana me muhimmanci zamu tattauna akai,Batace komai ba ta buɗe motar tashiga tana yamutsa fuska,"Ina sister Sajnah?", Lumshe Ido yayi yace"ke zan tambaya ai".Tsayayyun Idanunta ta zuba masa batare da tace"komai ba ta lura da yanda yake lumshe ido idan yana magana hakan ya zame masa jiki...Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da juyawa ya fuskanceta."Ainah ya Kira sunanta babu alamar wasa atare dashi, Ahankali ta ɗago kanta tare da zuba manyan Idanunta Acikin nasa, Ahankali tayi kasa da kanta tace"Na'am.Zazzafar Ajiyar zuciya ya sauƙe da faɗin"komai Kika gani acikin rayuwa muƙaddarine ko wani bawa da kalar yanda ƙaddara ke zuwan masa me daɗi ko akasin haka ya zama dole bawa ya amshi ƙaddara ayanda tazo masa,Ko bahaka bane?.Kai ta gyaɗa alamar hakane,"Good yace"Sannan ya cigaba da faɗin"Alokacin da iyayena suka zaɓa min 'yar Uwarki amatsayin matar Aure tabbas naso na daure in hana zuciyata bin ƙudurin ganin na cika musu muradin sede kash!,Na gagara hakan domin kullum zuciyata takan bijiro min da sabon soyayyar abinda take muradi da ƙulafaci akullum burin zuciyata na bata abinda take buƙata duk da kuwa Ina hango babban ƙakubale akan hakan.Ajiyar zuciya ta saki tare da katsesa ta hanyar faɗin"Ni ban fahimci abinda kake nufiba baya ga haka sister Sajnah ce ta dace da kasanarwa da damuwarka bani ba domin itace ke Shirin Zama Mata Kuma abokiyar Rayuwar ka.Kai ya girgiza Ahankali ya kamo tafin hannunta acikin nasa yace"Nasani anma ayanzu bani da wacce zan faɗawa matsala ta sannan na samu maslaha sama dake,Yayi ƙoƙarin danne abinda ke taso masa da faɗin"Ainah Koɗan babu ƙaunar 'yar Uwarki acikin zuciyata,hasalima ban taɓa ɗaukarta amatsayin masoyiyaba face yar uwa tun daga yarinta zuciyata ke kallon Ainah amatsayin ƙanwa,Amma Azahiriin gaskiya da Akwai wacce zuciyata ke da muradin kasancewa da ita amatsayin matar Aurena.Da sauri Ainah ta janye hannunta daga nasa tana wara manyan Idanunta akansa with so much surprise tace"What do you mean?Abdulllll ta Wani irin ja sunan da ƙarfi."Calm down please Ainah ya faɗa yana riƙe hannunta ganin yanda ta zzazzaro idanu.Kasa cewa Komai tayi se Ido data zuba masa tana jiran Jin abinda zece.Kamar Wanda aka fisgo maganan daga bakinsa yace"Ilove you Ainatyyyyyy I really love you you are my dream girl kin daɗe acikin zuciyata kullum da matsananciyar ƙaunarki nake tashi...Azabure Ainah ta fisge hannunta daga nasa cikin tsananin tashin hankali da ruɗu tace".....








 AYI SHEARING SABODA ALLAH MASOYA




 Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani....





               ESHA CE🤙🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol