Free chapter · Read without an account
Page 11
by Sadiya Auwal · KAICO NAH
🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......
🏵🏵🏵
...11....
Yazeed ne ko kuma nace Mutari😂,yayi saurin dakatar da innan ta hanyar cewa,
"Haba inna daga dawowar mutum har kin fara surutu,ki bari mana gari ya waye,ga wannan dan allah kiyi shiru"
Yafada yana mika mata wani kudi a hannun ta,karba tayi kareda kalmashewa a jikin janinta kafin tace,
"Oh nina ce ai babu komai a kunkumika,yanzundai ku shiga ku kwanta saida safe,amma duk da haka inna ji shiru zaku jini sarai"
Daga haka tayi hanyar dakinta yaran suka bita yuuuu ta rufo kofar.
Bayan sun tafine mutari ya juya yana kallon sumayyah wanda tayi suman tsaye tun dazu sai yanzu daja dogon numfashi mai tsayi.
Shima daga kallon bai sake cewa komai ba sai wucewa dayayi hanyar wani daki itama ta bishi.
Shima dakim babu maraba da kadan yafi wanda innan take cikin fasali.
Fito da wani dan makulli yayi ya bude tareda kunna kai,da sauri ya fito yana tari saboda kurar da take dakin.
Tsayawa sukayi suna tunanin mafita,ganin babu yasashi tafiya bangaren inna ya dauko musu tsintsiya suka hau gyaran dakin a daren,duk da bai wani fita ba amma dai sun samu dan inda zasu kwanta dai.
Haka kowa yadan dora kansa ya kwanta babu mai cewa wani uffan,kowa yana tunanin mai kuma gobe zata zo dashi tunda yau kam ta kare.
.....hmmm.....Wanda yayi bacci dai yayi kawai.
Gwaff gwaff sukaji ana buga kofar dakin nasu da safe,sumayya ce ta tashi ta bude dakin suka hada ido da wata kazamar yarinya dukun dukun da ita hancinta fall majina,dagajewa sumayya yellown hakorinta tayi tareda cewa,
"Baba ya tahine?,dama tuwonku na kawomuku"
Kallon hannun yarinyar tayi wanda take dauke da wata langa irin fararennan da ake jeren kauye dahi,kwanon yasha lamba kaman wanda aka bubbugashi akan kwalta.
Karbar kwanon sumayyah tayi hannunta yana rawa tayi cikin dakin bata cewa yarinyar komai ba.
A jiyewa tayi a bakin gadon karfen da Mutari yake kwance,daga idonta tayi tana kallon saman dakin,wanda ana kallon rufin dakin saboda babu cilin,tunowa tayi jiya da kwana tayi tanajin karar beraye suna tsere a saman kaman zasu fado kanta.
Mutari ne wanda shima tun buga kofar ya tashi yana kallon yanda sumayya take kallon saman dakin kaman yanzu dazo duniyar,dan shi kansa yasan batasan da irin wannan rayuwar ba said yanzu.
Uhuhm yayi gyaran murya wanda hakan yasata dawowa da kallonta gareshi.
Kallo daya tayi masa ta dauke kanta zuwa kallon wani waje daban.
"Uhm wata yarinya ta kawo abinci tana neman ka,amma ta tafi"
"Naji ta ai dije ce,itace Y'a ta biyu bayan yayan ta Isah"
"Y'ay'anka kuma,dama kana da y'ay'a kenan,ka taba aure a baya?"
"Eh amma na rabu da matar,shine bayan mun rabu na barwa inna su na tafi cikin gari,anan muka hadu da Alhaji Sulaiman nafara masa driver,koh shekara ban yi ba muka saba da Abdurrahim dansa,hakanne yasa ma alhaji yakara min matsayin aiki zuwa drivern company nsa,har yazamana idan wasu manya suka zo nike daukan motarsu zuwa wanki da kuma shan mai idan zasu dade a garin.
KO motar dakika ganni da ita ma ranar haduwarmu ta wanice daya bani na kaita service,gidan man kuma dama sun sanni ina kawo motocin company,kasancewar gidan man Alhaji Sulaiman ne shiyasa bana bin layi a wajen.
Ke kuma ganin abinda ya ja hankalinki kenan yasa ni ma na biye miki muka fara soyayya,ganin kin dage sai munyi aurene yasa na nemi taimakon Abdurrahim har ya shawo kan hajiya saratu itama ta amince ta shiga maganar.
Kaya kuma da mayukan danake shafawa duk a kudin danake cafkowa ne idan babu wanda yake kusa,musamman lokacin da Alhaji yayi tafiyar nan na debi kudi dayawa har hajiya Saratu ta gane,dan dama abokantakar mu da danta ba so takeba.
Tayi niyyar maganane Alhaji yayi hatsarinnan,nasan kuma mutane suna rabuwa zata dau hukunci akaina,shiyasa kika ga na cikawa wandona iska na dawo gida,dan nasan koda tasan inda nake bazata biyoni ba tunda na gudu,amma idan na tsaya to mai rabamu da ita sai Alkali.
Kinji abinda naasan zan sanar dake kenan,labarin gidannan kuwa zaki gani dakanki idan kina cikinsa yau da kullum"
Duk abinda Mutari yake cewa sumayyah tanajinsa har yakai karshe,batace komai ba,babu abinda take sai zubar da hawayen takici da dana sani,wai wannan mitumin ta aura har take zaman aure dashi,wai shine wanda zuciyarta take mutuwar so,saboda takaici ma ko tambayar sa ya akayi ya sanja suna batayi ba,dan tasan ya akayi kawai,mutumin dayayi haka menene kuma idan an fada mata yayi bazata yadda ba,ai ita kawai ta cuci kanta ta kar kanta da kanta kawai.kaico da halin da ta jefa kanta a ciki,ta aikata abin danasani da nadama marar amfani.
"Wai tunanin mai kike haka harda hawaye,hmmm zama ki daina,kidawo hankalin ki dauki dumame kici tun kafin yunwa ta tambayeki"
Kallon kwanon tuwon tayi tareda budewa,wata koriyar miya idonta yayi arba da ita kaman fitsari,ga wani yankan tuwo manya manya guda biyu.
Saurin rufe kwanon tayi tareda tambayar mutari,
"Wannan din menene haka a cikin nan din?"
"Oh tambaya kike,abinci ne mana ina zaki ci kici dan wlh haka ne gatanki idan kuwa na haka ba keda sake ganin abinci mai garanti to sai dare "
Yana gama fadan haka yasakai ya bar dakin.maganganunsa ne suke yawo mata akai,na cewa bazata ga abinci ba sai dare.
Sake Bude kwanon tayi tareda saka hannun ta a hankali ta yanko lomar tuwon,bakinta ta kaita kaman mai tsoron ci.
Runtse idonta tayi tareda saurin tofa ta cikin kwanon jin yanda ajino moto da kuma warin daddawa suka gauraye cikin bakinta.
Dauko kwanon tayi tareda fito dashi waje,da gudu yaran suka taho tareda wafce kawanon suka dasa masa wawa kamar karnuka.
Ita dai zuba musu ido tayi tana ganin ikon Allah,wai wannan abinda tasaka a bakinta shi suke wa wannan kokuwar zasu ci"
Maganar inna ce ta katseta wanda hakan yasa ta bata hankalinta,
"Ina kwana inna"
Sumayyah tayi saurin tsugunnawa tareda gaisheta,dan ita haka kawai matar take bata tsoro,gata fiyat kaman tsohuwar fatalwa dan rama,kai kace idan akayi wata kyakykyawar iska faduwa zatayi.
"Lafiya ya kwanan bskunta,ina shi mutarin ya tafi?"
Tunani tayi sumayya a ranta,wato fita yayi ko uwarsa bai gaishe ba da safe?.
"Uhm inna ya fita ai tun dazu"
"Hmm dama nasan ai za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,zaije ya karar da dan kudin hannusa a wajen mai shayi ko,sai yarasa na kashewa yazo yana min muzurai kaman dan fulani shanu sun kare.
Maza kedin tashi ki hadamin kwanukan nan ki wanke min,kafin na zo na dora ruwan awarar rana nima,yau nina rasa ya akayi ma na makara a tashi wlh"
Har ta shige daki bata daina magana ba kaman rediyo,ita dai sumayya tanajinta har wuce kafin ta tashi ta nufi inda taga an tara kwanuka.
Wasu dozen din kudajene suka tashi a wajen lokacin da ta isa wajen,ita abinma tsoro yabata dan saida ya ja baya da sauri.
Kokarin amai ta farayi lokacin data kula tsabar kazantar wajenne yasa suka zo wajen.
Haka tana toshe hanci tana komai ta hada ruwa ta fara wanke kwanukan,dan ta kula ba iya ya jiya ne ba ma harda kwana da kwanaki a wajen.
Da haka da kyar da sidin goshi sumayyah ta samu ta tashi daga wajen zuciyarta tana tashi.
Har tayi hanyar daki taji muryar innan tana magana daga can wani waje a gefen gidan.
"Keh y'ar nan ina kike ne wai,in kin gama wanke wanken kizo ki tayani diban itacenan zuwa wajen hura wuta"
Haka sumayyah ta fasa komawa dakin ta tafi wajen innan,shikansa wajen da itacen yake banda wari babu abinda yake,haka suka debo zuwa inda za'a hura murhun.
Sunayi inna tana mita da haka ta gama hada wutar ta dora ruwan awarar.
Sallamar wata budurwa sukaji tashigo gidan dauke da wani babban botiki akanta na kokon safe.
"Oh ni diyar tasi'u,yanzu tallen da kika fita tun duru duru shine sai yanzu kika dawo shema'u?"
"Kai inna miye haka ne ko yaushe na fita ma zan dawone ban siyar ba kome ?"
Tana cikin maganar ne inna tashiga daki dakko wani abu,shema'u tana ganin haka tayi saurin ciro kudin tareda zarar wani ta soke a mararta.
Duk abinda take sumayya tana kallonta,da suka hada idone shema'u ta gallawa sumayyah harara,itama dayake teruwar ce ruwane tadoki babban zakara ta mayarwa da shema'u hararar har ta fi tata ma.
Suna cikin hakanne inna ta fito da kullin tsamiyar kanti a hannunta zata sakawa ruwan awararta.
Mika mata kudin shema'u tayi tareda cewa,
"Gashi inna cinikin da akayi,duka na siyar naira dari biyar ta bata a wajen siyarwar"
"Kai ma'u har naira dari biyar dui kina kallon ina haka,to wannan ribar mai zamu samu ma"
"Haba inna zamu samu mana,naga wani lokacin har kudi nake kawomiki ya hawo,sannan......."
"Kinga ya is a haka naji"
"Inna wannan din wacece ne naga tana tayaki aiki?"
"Matar mutari ce,wai anan zasu zauna yanzu"
"Anan kuma,sanda ya samu kudin bamu sani ba shine zai kawo mana matarsa cabdijan,hmmm kowa xai rike kansa kenan"
"Kinga kiyimin shiru kar ya shigo yanzu ya jiki yamiki shegen duka ki kasa fitamin talllan awara,dan kin sanshi ba imani ne dashi ba,zuciyace dashi sai kace ta kafiran farko"
"Yasan a inda yake zuciyar ai,sai wajen mugunta,idan wajen nemane ko mace nan ta ganshi"
"Ma'u bazakimin shiru ba koh,kurufamin asiri nace miki,kar yanzu ku debi yan kallo,a hanyarki ta dawowa kinga dauda kuwa?"
"Ahah ban Ganshi ba,shima wani dan kwayar,jiya dawowa ta dai naganshi shida abokansa da karfe sha biyun dare wai sannan zasu tafi yin patrol na wata anguwa"
"Hmm haka dai ya kare shikuma"
Har ma'u ta tafi ta dawo da sauri tareda kaiwa bakinta wajen kunnen inna,duk da haka sumayyah tanajinsu wanda suka zama mata tamkar television tana kallon drama.
"Inna Ni kinga jikin mutari kuwa yanda ya koma,yazama ja kaman jabiya ,dama gashi shikadai yake kama da baba irin jikin fulani,mukuwa gashi nan munyi kamarki .........uhm gamunan dai"
"Duka inna tayi saurin kaiwa shema'u tareda kunduma mata ashar,dan ina kana so kaga bacin ran innan to kace mata baban su shema'u yafita kyau.
Itadai hanyar dakin su tayi tanayiwa innan dariya,dan daga ganin shema'u kaga yar duniya lamba daya.
Har suka gama aikin awarar sumayyah tana mamakin abinda tagani a wannan gida mai cike da hauma hauma.
Suna gama dafa awarar inna ta dauko kwanon suya ta zuba mai aka hau suya.
Ita kuma shema'u sannan ta yi wanka zata fita da awarar zuwa waje.
Bayan an gamane inna ta dauko wani murfin kwano da zubawa sumayya awarar batafi guda uku na ta bawa yaro yakai mata daki.
Sumayyah tana kwance a kan gadon dakin sai ganin yaro tayi ta dan murfi an saka awara guda uku wai itace rabonta,ita da take tunanin za'a saka mata a kwano dayawa,gashi tun safe take aiki yunwa ta addabe ta kaman mai azumi.
Dan tsabar takaici sumayyah bata san lokacin data saki ihu ba hawaye yana zuba sharrrrrrr.
Gashi mutari tunda ya fita da safe bata kara ganin keyar saba.
________team din sumayyah ina kuke,ku kawo abinci fah mutuniyar ku tanajin yunwa😂🤣😂🤣😂.