Free chapter 路 Read without an account

02

by Rahma Kabir 路 LUBABATU

LUBABATU


02


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir


EWF.



Baba dama ina so Lubabatu ta zama makofin Jidda ce in ba alkawarin wani akanta.


Yayi maganar cikin jan fasali da sunne kai a kasa tsabar biyayya.


Au to to wannan tunani naka yayi matukar kyau, Kuma koda akwai maganar wani ai dole a jiye shi gefe a dauki naka tunda kai mun sanka kuma ka cancanci a baka. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kasan dai Lubabatu tana dauke da lalura zaka iya da ita kuwa?


Baba nasan da haka, domin in baka manta ba nine nayi silar da aka gano abinda ke damunta, dan haka aurenta kamar jahadi ne, sai dai zan so kafin a yanke maganar a ji ta bakin Lubabatun


Rabu da ita in dai mu mun yarda bata isa tace a'a ba, domin a musulunce ni keda hakkin zaba mata miji kuma kai kayi min tunda tuwo na mai na za ayi, sannan kusan taimaka mata zaka yi saboda lalurar da take fama da ita.


To shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairinsa.


Ameen, Ina ga kafin ka tafi za a tsaida kwanakin biki kawai tunda abu na gida ne, sadaki ka bayar ko nawa ne Albarka kawai muke bukata.


Nagode Allah ya saka da Alkhairi


Baba ya amsa da amin tare da sanya masa albarka. Haka Haruna ya sauke masa yan dubu dubu bandir uku ya kama dubu dari uku kenan.


Ga wannan dubu dari na sadakin, sauran kuma ayi hidimar biki dasu.


Yauwa Allah ya yi Albarka. Na tsaida bikin ranar sadakar arba'in din Jidda, ana gamawa sai a daura aure, insha Allah zan sanar da yan uwa kaima sai kayi kokari ka sanar da manyanka. Sannan batun kayan dakin Jidda ka barsu kawai a matsayin na Lubabatu sauran abinda ya dace ka saida sai ka kawo mana kudin.


To insha Allah ba damuwa Allah ya kara girma. Ni zan tafi sai ana gobe addu'ar arba'in din Zan zo.


Masha Allah Allah ya yi maka Albarka ya tsare hanya.


Haruna ya amsa da Amin yana godiya, har waje Baba ya rakashi ya hau a taxi ya wuce da shi filin jirgi zuwa kaduna.


Baba ya shiga gida cike da fara'a fuskarsa, Umma dake zaune bisa tabarma a baranda ta bishi da kallon mamaki harya zauna kusa da ita ta ce cikin zakuwa.


Malam rabon da in ganka a irin wannan yanayin tun kafin rasuwar Jidda, lafiya kake ta fara'a haka kamar anyi maka kyautar hajji.


Baba ya dire mata kudi a gabanta.


Amina Allah ya kawo min karshen wahalata, wannan kudin da kika gani na auren Lubabatu ne.


Ban gane ba, me kake nufi? Mu da muke cikin alhinin rashin Jidda me zai kawo maganar auren Lubabatu kuma?


Haruna dai shine mijin domin ya bukaci da a bashi aurenta.


Haba Malam ni kam ina ganin a bar wannan maganar, dan bai kamata a tauyeta ba.


Wlh karki sake ki kawo min gargada a wannan auren, ko kin manta ita Lubabatun matsala ce ke gareta, ba tada wani mashinshini daya ce yana sonta saboda lalurar ta, ina ganin ai Huruna kamar taimakonmu zai yi dan haka in ba zaki fadi alkhairi akan wannan maganar ba to gwara kiyi shuru kawai.


Hmmm shikenan Allah ya zaba abinda yake Alkhairi.


Yama zaba insha Allah, daga ni har ke saukinmu ne yazo wahalarmu ya kare. Tashi ki kiramin ita na sanar mata.


To kawai Umma tace ta wuce dakin lubabatu ta sameta kwance cikin rufa da alama sanyi take ji, ta sanar da ita kiran mahaifinta sai ta dawo ta zauna kusa da Baba. Cikin kaduwar sanyi Lubabatu ta isa barandar ta zauna ta gaishe da Baba ya amsa kana ya daura da cewa.


To Lubabatu Allah ya kawo lokacin da zamu rabu dake, domin na karbi kudin aurenki zaki zama makofin Jidda a gurin Haruna.


A gigice Luba ta dago kai tana kallon Baba cike da mamaki bata taba zaton abinda zai gaya Mata ba kenan, nan take taji zufa ya rufeta babu zazzabin ya tafi, ta ce cikin muryar kuka.


Amma Baba yaushe anty Jidda ta rasu da har za a kawo wannan zancen. Gaskiya bana son sa.


Da ki so da karki so aure kamar an daura, na kira ki ne dan ki sani saboda ba yardanki nake nima ba, wato kina mana bakin cikin dan Alkhairan da yake mana ya yanke ko, bacin aurenki da shi wani jari ne a garemu da saukin matsalar lalurarki. Dan haka kije ki fara shiri insha Allah ranar addu'ar arba'in din Jidda za a daura.


Lubabatu ta rushe da matsanancin kuka ta mike da kyar ta isa daki, Umma ta bita da kallon tausayi har sai da kwalla ya saukar mata a kunci, ba tada yadda zata yi domin in Malam ya yanke magana babu wanda ya isa ya ja da shi, amma da ta hana wannan auren. Lubabatu tana shiga daki ta tsaya a jikin bango tana rusa kuka tare da tuno da maganganun da tayi da Jidda, bata gama fita daga radadin rashinta ba gashi Baba ya bijiro mata da wannan lamari mai wuyar fassara.


Shikenan na shiga uku ni Lubabatu, ban san wani irin azal ke bibiye da rayuwata ba, tun ina karama ta zuwa yanzu bansan meye jin dadin rayuwa ba, na taso cikin azaba, kyara, tsangwama. Sannan a lokacin da nake hangen zan dandani zumar rayuwa sai gashi zai yanke. Ta yaya zanyi rayuwa da mutumin da ya yi rayuwa da yayata, mutumin da ko amafarki ban kawo zan zauna da shi ba balle so ya shigo ciki, ni kam banda sa'a a rayuwata.


Sai ta rushe da sabon kuka har ana jiyo sautinsa a tsakar gida, Umma ta shige daki ta shiga matsar kwalla itama, tsananin tausayin kanta dana 'yarta ya kamata, shiko Baba yayi ficewarsa waje ya soma labartawa mutane zancen auren Lubabatu. Yanzu ita kenan ta rage musu, sai Allah ya dauke me lafiyar ya bar musu mai lalura, inda Malam yana da hankali wannan kadai ya ishe shi ishara akan irin abinda yakewa Lubabatu, amma sam bai gani ba son duniya ya rufe masa ido.


***** *** *****


Kaduna


Tun da yamma Rahima take ta tunanin yadda zata gano abinda Umar ke shiryawa da Jamila har zuwa dare tana saka da warwara, gaba daya ta hana kanta sukuni saboda tsabar sharri dake cinta a zuciya, d'an uwanta ne uwa d'aya uba d'aya amma ta tashi da ganin kyashinsa a zuciya kullun burinta ya yi kuskure ta samu abin fad'a ko wanda zata rika tsokanarsa, kuma Allah yana yawan bata dama akansa, sai dai bangaren Umar duk da mugun nufinta a kansa shi kuma Allah ya sanya masa son 'yar uwarsa ko da zata kuskure masa ba zai hana ya raga mata ba.


Dare yayi sosai misalin karfe d'ayan dare, ta yi nisa wajen hirar banza da saurayinta Hashim, sai da ta samu gamsuwa sosai da hirar da suke kafin hankalinta ya dawo jikinta ta duba lokaci a wayarta taga karfe daya, ta yi sallama da shi ta mike zaune tana jan tsaki.


Na bata lokaci na abanza ni banyi karatun text din da muke da shi gobe ba. Ko da yake nasan Aliya ta yi banda matsala zata taimaka min.


Sai ta mike ta fito falo domin ta dauki ruwa tasha saboda k'ishi dake damunta, ta fito kenan taji alamar bude kofar falonsu da sauri ta boye a bayan kujera tare da dafe kirjinta cike da jin tsoro, Umar ya shigo da Jamila rike da hannunta a hankali cikin sanda har suka ratsa falon suka yi hanyar dakinsa, cike da mamaki da al'ajabi Rahima ta dago kai a hankali ta bisu da kallo, yanzu dai ta gama yarda da zargin da take akansu, dan haka dole ne ta nuna musu ta gansu, sai ta mike wuf tabi bayansu lokacin da ta isa sashinsa ta samu har sun shige ya rufe kofar, ta saki murmushin mugunta tace a ranta.


Anzo dai dai wajen yasin na kara samun wata hanyar cin kaniyarka.


Sai ta tsaya a bakin kofar ta soma bugawa a hankali, dai dai lokacin Umar yana kissing Jamila har sun fara shiga wata duniyar, jin buga kofa yasa suka saki juna a zabure, Jamila ta mike tare da boyewa a gefen Waldrop ta manne da bango kamar taza shige ciki, shiko gogan da kyar ya hadiye miyau ya mike a sukwane ya iso kafar tare da tattaro kwarun guiwa yadda zai kare kansa domin duk a zatonsu wani daga cikin iyayen gidan ne ya gansu. Umar ya bude kofar sai ya ciki Karo da Rahima tana jifansa da shu'umin dariya, yaja dogon tsaki tare da daure fuska.


Mayya uban meya kawoki nan a wannan daren?


Chargern wayarka zan gwada a nawa in ya yi sai ka aramin zuwa safiya zan dawo maka da shi.


Ina taki changern? Sannan ma uban me kike yi har tsawon wannan lokacin baki barci ba?


Abinda kake yi shi nake yi.


What!


Ya fada a tsawace sai tayi saurin wayencewa.


Kai Yaya Umar kwallon tv fa nake nufi.


Ok kawai ya ce tare da cewa ta jirashi ya miko mata chargar, ya juya yana kofarin rufe kofar ta tura da karfi ta shige tare da cewa.


Nace maka zan gwada a nan in ya yi sai na tafi da shi.


A fusace ya hankadata har tana bige kai da kofar.


Fita min a daki na fasa bada chagern tunda bakya jin magana, nasha gargadinki cewar dakina sirrina ne, dan haka wuce ki bani waje.


Shine zaka tureni na bige to Allah ya isana, kuma duk abinda kake boyewa a dakin na sani, saina tona maka asiri na fadawa su Ummi cewar Jamila Mai aiki a dakinka take kwana.


Sai ta juya a fusace zata fita, Umar ya riko hannunta da sauri cike da tashin hankali ya samo bata hakuri, Jamila dake boye a dakin itama ta fito tana yi mata magiya, da kyar suka tsawo kanta ta hakura tare da alkawarin zai bata dubu talatin na toshiyar baki, sannan suka yi agreement cewar maganar ta mutu, Rahima ta wuce daki cike da farin ciki, zata cigaba da amfani da wannan sabuwar damar data samu tana tatsar kudi a gurinsa. Umar ya rufe dakin ya dawo ya zauna cike da takaici yasan ya jawowa kansa karin damuwa saboda yasan halin Rahima ba zata taba barinsa ya zauna lafiya ba duk da yana kyautata zaton ba zata fada ba sai dai yasan zai sha wuyarta sosai, a wannan daren dai su Umar basu samu jin dadin da suka saba samu ba saboda a cikin dari dari suka kwana cike da zullumi.


______


Ummee.


Yau ita ce da girki ta isa dakin Abba ta sameshi zaune yana duba system ta zauna nesa da shi fuska a dukunkune, ya dago ya kalleta baice mata komai ba ya cigaba da aikinsa, sai da suka dauki kusan minti ashirin a haka kafin ya ajiye aikin da yake yi ya mike ya zame jallabiyarsa ya hau kan gado yana cewa.


In kin gama abinda kike yi ki ka she mana wuta ina jiranki.


Ummi ta ja guntun tsaki tace a ranta.


Sai kace wani abun arziki zai tabuka.


Ta mike ta kashe wuta ta hau gadon gefenta ranta yana yi Mata kuna, Allah ya gani bata kaunar Abba yanzu duba da yadda cutan sugar da hawan jini ya nakarkasa mazakutansa, minti biyu da soma sex sai yayi realising, shiyasa Ummi take takaicinsa banda yana da kudi da tuni ta rabu da shi ta sake wani auren, amma a haka take maleji saboda tana tasan kudi a jikinsa sannan ma ita ke juya akalarsa sai yadda take so yake yi a gidan, saboda tuni ta kama zuciyarsa a hannu da asiri ta gama da shi, shiyasa take kawal-walniyarta son ranta ba matsi ko takura, 'ya'yanta kuma sune 'yan gaban goshinsa kishiyarta kuma ta zama hoto sai dai ta yi komai cikin umarninta. Ta yi nisa a cikin tunani Abba ya daura hannunsa kan wuyanta yana zagayewa da sauri ta sauke ajiyar zuciya ta waigo ta kalleshi, ya sakar mata murmushi.


Tunanin me kike yi? Bacin kina tare dani.


Hmmm ina tunanin yadda zaka jagwalgwalani ne ka barni da ciwon mara, gaskiya Alhaji ni yau ba ni da ra'ayin komai.


Au haka kika ce?


Eh saboda nasan gajiyar dani kawai zaka yi kuma ba biyan bukata.


Shikenan yi barcin ki amma zanje na rage gajiyata a wajen Atika.


Amma kasan girki nane ko


Eh sau nawa ina baki girkinta, ya kamata ki ji tausayina tunda kince ba zaki bani ba.


Ummi taja guntun tsaki cike da takaici.


Shikenan na amince akan ka kaimin kwanana wajen wata, sai dai wlh dole ka tsaya ka gamsar dani bayan ka samu naka gamsuwar.


An gama hajiyata.


Sai ya mike cike dazakuwa dan yasan d'and'anon hajiya na musamman ne Yana mugun samun gamsuwa fiye da Uwar gidansa wacce sai su kwashe wata uku babu mu'amalar aure daya shiga tsakaninsu tsabar rashin jin dadin juna da basa ji, wani lokacin ma har ciwo yake jiwa Mami saboda rashin ruwan ni'ima, sai ta yi jinyar kwana biyu shiyasa sam bata kaunar ya kusantace ta sakarwa Ummi shi gaba daya, iyakarta da shi girki ne kawai a ranar kwananta sai dare ya kwana dakin Ummi, tun abin yana yi mata zafi har ya zame mata jiki ta saki akalarsu ta cigaba da harkanta, iyaka in abu ya mata zafi sai dai tayi kuka tace Akwai Allah kuma zai saka mata, bata iya rama fada shiyasa Ummi ta yi mugun rainata ta kwace girman gaba daya sai abin da take so zai gudana a gidan.


Haka Abba ya kusanci Ummi cike da jin haushinsa, ya gama jagwalgwalata ya barta kwance da ciwon mara, ta mike cikin kunan zuciya ta shige bayi tare da sakarwa kanta shawa, ta jima a haka kafin daga bisani ta fito ta maida kayan barcinta ta wuce dakinta, Abba Yana yi mata magana ta yi banza da shi ta wuce ya girgiza kai yana murmushi.


Nasan zaki huce zuwa safiya kuma ko dan bukatar kudi zaki dawo ki sameni.


Sai ya mike ya isa toilet yayi wankar tsarki ya dawo ya kwanta, ba jimawa barci ya dauke shi. Ummi kuwa sai juyi take a gado da kyar barci ya dauke ta.


***


Da safe


Rahima ta kammala shirin makaranta ta fito ta karya kana ta wuce dakin Umar dan ta fara kuntata masa, ta riga ta san su Ummi basu tashi ba shiyasa ta yi gaba abinta. Ta shiga buga masa kofa cikin nauyin barci yaji ya farka, ya mike da kyar ya iso kofa ya bude, ganin Rahima ce ya sashi yin tsaki.


Amma wlh kina takuramin, haba Rahima meye matsalarki da ni ne?.


Hahaha makaranta zaka kaini shine nazo na tashe ka


Ta yi maganar cikin dariya. Ya galla mata harara.


Kije driver ya kaiki mana ko dama nine nake kaiki?


A'a kawai dai yau ina so yayana ya kaini a mashin dinsa roba roba, daga nan na had'aka da kawayena ku gaisa.


To ba zani ba.


Ya fada tare da banko kofarsa ya wuce ya kwanta, Rahima ta daure fuska ta shiga dakin.


Allah kai zaka kaini ko na tona maka asiri.


Kai innalillahi... Haba Rahima Dan Allah ki tafi mana ba nace zan baki 30k ba, pls ki rabu dani


Hmmm ni dai kawai ka kaini a zauna lafiya.


To naji, yanzu jirani nayi wanka da sallah sai in kaiki shekenan?


Hmmm bazan iya jiraba, ina ga dai kafi so na tona komai, Bari naje na samu Abba. 


Sai ta fita da sauri tana cewa Ummi da karfi. A sikwane Umar ya rarimo rigarsa da makullun mashin ya biyo bayanta yana kwala mata kira, a falo ya ganta ta zauna ya galla mata harara ya yi waje, Rahima ta mike tana taunar cingom tare da murmushin mugunta sai ta bi bayansa, cike da kunar rai Umar ya kaita makaranta kamar zai yi kuka dan takaici ita Kuma murna fal cikinta dan ta kuntata masa.


******* ***. *******


*Yola*


Da yamma Umma ta samu Lubabatu a daki ta zauna gefen katifarta ta ce ta tashi ta zauna suyi magana, babu musu ta zauna tana sauraren abinda zata ce Mata.


Lubabatu Ina so ki dauki dangana game da aurenki da Haruna, haka Allah ya kaddara mana wanda ba muda tsumi ba muda dubara, ki saki ranki ki cigaba da walwala, ki roki Allah ya zaba miki mafi Alkhairi insha Allah ba zaki nadama ba.


Hawaye ya gangarowa Lubabatu a kunci tasa hannu ta share tare da daidaita natsuwarta kana ta soma magana.


Umma zanzo ace wani mijin Baffa ya zaba min ba Haruna ba, ta yaya Zan auri mijin yayata? Sannan ma ban gama sabo da rasuwarta ba sai a bijiro min da wannan maganar, ina zan saka raina fisabilillahi, wlh Umma lamarin yamin nauyi da yawa a zuciyata.


Hakanan zaki daure kiyi hakuri, nima inda so samu ne wlh bana son auren nan, amma kinsan halin Malam in ya kafe akan abu tofa baya sauyawa, ki sanyawa zucirarki salama ki amsa kaddararki insha Allah zaki ci ribar hakan.


Shikenan Umma Allah ya tabbatar min da Alkhairi ya jikan anty Jidda.


Amin ya rabbi haka nake sonki da dauriya ki cigaba da addu'a insha Allah nasarar biyayyarki yana gaba.


Nsgode Umma da karamin karfin guiwa, ki cigaba da yi min addu'a Allah ya cika min burina.


Ameen, Luba kullun kina cikin addu'a ta ba dare ba rana, insha Allah zan ta yi miki har iya tsawon rayuwata.


Lubabatu ta matsa ta rungume Umma ta saki siririn kuka wanda yake fitowa daga bangon zuciyarta, a duniyar nan ba tada kamar Umma domin itace kawai take damuwa da duk matsalarta sai kuma Jidda wacce Allah ya yiwa rasuwa, sabanin Baffansu da duk ya daura mata karan tsana akan wani dalilinsa mara tushe.


#Rahmace

#MamanSultan

#share

#comments

#vote

 


      _____________________


   *TALLA*


*Mg's herbal whitening black soap*


Idan akaji gangami to tabbas akwai labari. Ina Amare, Uwargida kai har ma da 'Yan mata masu tasowa, hakika mata da kwalliya aka sanmu, shin kuna so ku kara kyau fatarku tayi luwai luwai ki zama 'yan caras kamar madubi?


To ga dama ta samu, mun zo muku da Sabulun Mg's a kan farashi mai sauki, duk wacce ba tayi anfani da sabulun nan ba an barta a baya, domin duk masu korafin cewar sabulan gyaran jiki basa Aiki to ina so ku cire Mg's a ciki domin shi kankat ne wajen mai da tsohuwa yarinya. Ko yaushe Mg's sai sambarka dan haka ku hanzarta ku samu naku, siyan na gari maida kudi gida, Mg's sabulu ne daya tamkar da dubu.


Masu bukatar fatarku tayi haske to Sabulun Mg's herbal whitening black soap ya waratar daku, jikin ku zai yi kyau da sheki da kamshi. Kayanmu baya bleaching organic ne, zai fiddo muku da ainahin natural beauty dinki ne, dan haka duk wanda ya gwada shi ne zai bada labari. Amare da sauran Mata kuyi kokari ku mallaki Mg's domin ba ruwanku da zuwa a dirje muku jiki zaku ga yanda fatarku zata dinga walwali. Ina masu.


Pimples 

Tabo(spot)

Sunburn

Nankanwa

Dama duk wani matsalar fata kuyi kokari ku nemi soap din Mg's, insha Allah before 2weeks zai share muku hawaye, ku zama abun kwatance. 


You have to try it and see for yourself 100% tested and trusted.


Soap price: 3k

Location: Kaduna

Muna turawa ko ina, amma delivery is not free


Mai so kindly WhatsApp message to *** or

Call ***


_Note: Babu in da zaku sami mg's herbal whitening black soap sai a number din nan, now Akwaisu available_


we can't wait to be a part of your beauty story馃槏

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.