Free chapter · Read without an account

CHAPTER 11

by Aisha Adam · AKIDATA

           


           _*AƘIDA TA*_ 


PERFECT WRITERS ASSOCIATION 


(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) 


***


P. W. A


*Story and written by* 


_*AISHA HUMAIRA 

(Daddy's girl)*_ 


The experience writer of 

*ABDUL JALAL*

* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *

And now 

*AƘIDA TA *


I dedicated this book to my Mum 

(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum 


Special thanks to all members of my Association 

Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community. 


         


              PART1 

                 Page 11



Bin motar Yusuf yayi da kallo harta ƙure, sannan a sannu yaja ƙafar sa ya ci gaba da tafiya abubuwa daban daban na yawo a kwanyarsa. 


Maimakon ya tafi gida seya tsaya yayi sallar azahar ya wuce gurin aiki, office ɗin Abbas ya tafi yaje ya tarar da shi yana tsaka da wani aiki, Abbas na ganin Yusuf yai murmushi suka gaisa sannan yace  

"Yane mutmina? Akwai wani latest update ne?"


Yusuf ya ɗan ɓata rai yace "na baka abu kayi assisting ɗina kaƙi, seni nayi abuna bakomai nagode"


"wane abu kace inyi assisting ɗin naka naƙi?" Abbas ya tambaya


"Akan mahaifin yarinyar nan Nurat mana, Nace ka tayani bincike akansa amma ƙarshe ni nayi abina"


Dafe kai Abbas yayi yace "Sorry my man, wallahi aiki yayi min yawa na manta shaf"


"Shikenan amma ina tafe da Labari ne"


Abbas ya tattara hankalin sa yace "ina jinka, dama kamar kasan jiya Oga Suleiman yayi min maganarka"


Yusuf yace "Abbas ina kyautata zaton akwai sa hannun matar Mahaifin Widad a farmakin da'ake kai musu"


Abbas ya ture System ɗin gabanshi ya sake tattara hankalinsa yace "ta yaya kenan? Meka gano?"


Nan Yusuf ya gaya masa abubuwan da Su Hajiya Halima keyi, da kuma Yadda suka yi da Ramla"


Jinjina kai Abbas ya shiga yi yace "Lallai biri yayi kama da mutum, amma kaga Oga yana Abuja akan wani case, Amma idan hakane meye alaƙar iyalan Alhaji Nasir da Mahaifin Nurat?"


Yusuf yace "Abunda zan ɗora da bincike na akai kenan"


Waya ce ta fara ringing, Abbas da Yusuf suka shiga waige waigen wayar da take ringing ɗin, Abbas yace "kamar daga jikin ka ringing ɗin ke tashi fa"

Se yanzu Yusuf ya tuna an bashi sabuwar waya, hannu yasa ya ɗakko wayar ya ɗaga, suka gama magana Umma ce ta kira shi. 

ssebayan Yusuf ya gama Abbas yace  


"jar uba mutumina wannan latest phone ɗinfa? Miƙomin in ganta, yaushe ka siyi waya haka, kaida manyan wayoyi basu dame ka ba?"


Yusuf ya miƙa masa wayar yace "Widad ce ta aikeni na siyo mata wayoyi masu tsada guda biyu, ina kai mata ta bani wannan"


Abbas ya dinga jinjina kai yana jujjuya wayar yace "Lallai ka faso gari, amma kamata yayi ka siyar da ita kai sabgar gabanka da kuɗin"


"Idan kuma ta tambayeni wayar nace na siyar taji daɗin Yimin wulaƙanci ko?"


Abbas yace "A'a ba haka nake nufi ba, Ashe dai har yanzu halin nata na nan, ai kwanan nan Insha Allah zan ɓullo gurin naku"


"to nidai in kazo ka kula, karka sake ka gaya wa wani unguwar da nake, haka kurun sun matsa da son sanin daga inda nake zuwa, dan nima kaina ban yadda da mutanen gidan ba"


Abbas ya kwashe da dariya yace "ashe dai ta koya maka halin nata"


Alert ne ya shigo sabuwar wayar Yusuf dake hannun Abbas, zare ido Abbas yayi yace "Yusuf an turo maka kuɗi"


Yusuf yace "waye ze turomin kuɗi tsakiyar wata haka?"


"wallahi dagaske nake, dubu ɗari shida"


Miƙewa tsaye Yusuf yayi yace "ni a wa? Waze turomin kuɗi haka?tabbas anyi kuskuren lambar account"


Abbas yace "dakata, kuma ba uwaɗakinka bace?"


Shiru Yusuf yayi yace "to aini bata da Account number ɗina, sedai idan naje gobe in Allah ya kaimu in tambaye ta, Amma inma itace gaskiya kuskurene, Kaga Abbas se anjima akwai inda nake son zuwa"


Gaba ɗaya Yusuf ya ruɗe, mamaki ya cika zuciyarsa yafi tunanin ko Ramla ce, dan tana son ta siye shi yayi mata aikin data keso? Amma daga rabuwarsu ta ina zata samu Account number ɗinsa?. 


***********************


A mugun fusace Ramla ta koma gida, tana zuwa bata tsaya ko ina bs se ɗakin mahaifiyar su, taje ta tarar da ita suna magana da Amal.


"Mummy akwai matsala fa"


"matsalar me?"


"Mummy this guy is very rude, we have to exact power over him, how dare will he look into my eyes and tells me that he won't do what i ask him to do?" ta ƙarasa maganar tana ta gauraya Numfashi.


"Kinga nutsu kiyi min bayani ya kukayi dashi?"


Ramla ta warware mata komai, Amal tace "da anyi shawara dani da baza'a tun kare shi ba saboda nasan ba zeyi ba, Mutum ne me kafiya da dagewa akan gaskiyar sa"


Cikin fushi Ramla tace "A beg shut up Malama, wayafi kafiya talakan banza mara amfani, ni ya tsaya ya kalli cikin idanuna ya cimin mutunci, shikenan dani yake zancen wallahi se nasa zaman garin nan ya gagare shi banza da kansa kamar lemo"


Amal tace "Wai kansa kamar lemo, kekuma naki fa"?


"dan Allah kuyi min shiru karku yi min faɗa anan, mafita ya kamata munema ba surutu ba, sannan Amal wallahi idan baki kiyayeni akan yaron nan ba sena saɓa miki fiye da tunanin ki wallahi, bazan taɓa aurawa maƙasaƙancin mutum ɗana ba, dan haka ki shiga hankalin ki, zaƙewar da kike masa tayi yawa "


Zumɓura baki Amal tayi ta bar ɗakin.


"Mummy inaga mubi Amal a hankali, tabbas son gayen nan take, Amma cikin hikima zata iya samo mana abunda muke so, ki dena yawan hantarar ta a kansa, karta zo ta bijire mana daga baya fa"


"Bazan bari alaƙar tasu tayi nisa ba, saboda yaron kalar mayaudaran mazane, yana da mu'amala me kyau, daɗin Soyayya ze iya sa Amal ta tona komai, kin san bata da hankali, Amma zan sanar dake mataki na gaba da zan ɗauka.


**************************


Safa da marwa yake yana kaiwa yana komowa a cikin wani matsakaicin Office, yana ta sake nanata maganganun da Oga ya gaya masa game da poisoning ɗin Bala a prison, wani mutum ne yayi Sallama a office ɗin yace 

"Yallaɓai Hisham lafiya kake nemana?" 

Hisham yayi ajiyar zuciya yace "Oga Bukar ne ya bada wani aiki, kuma muddin aka samu kuskure bamuyi ba ze halaka mu" 


"Kamar Yaya? Wai shi meyasa be maida kisan kai komai ba saboda buƙatunsa? Wallahi nayi dana sanin sabga dashi" 


"Kwantar da hankalin ka Bashir, mu lallaɓa muyi masa wannan aikin bisa Yarjejeniyar shine na ƙarshe, idan ya cigaba da takuramu, semu ma mu ɗana masa tarko" 


Tsaki Bashir yayi yace "ina jinka, me kuma zamuyi masa?" 


"yace so yake ayi poisoning ɗin Bala, yadda ze fara rashin lafiya, da an kai shi Asibiti kuma zesa a ƙarasa shi, saboda Balan yayi barazanar tona Musu Asiri, sun barshi a gidan yari tsawon shekaru takwas, sunƙi fitar da shi" 


"wallahi Hashim mutanen nan basu da Imani, tsaf muma zasu iyayi mana abunda suka yi wa Bala, amma salin alin muyi abunda suke so, muna dafe kan madarar kawai zan ajiye aikin gidan nan in fece" 


Hisham yace "shikenan but you have to focus" 


Bashir ya jinjina kai ya fice daga office ɗin. 


*********************************

Dogayen kaya ne a jikin Yusuf, yayi kyau sosai ya shiga falon da sallama, ba'a amsa ba kasancewar ba kowa a ciki, ɓangaren Widad ya nufa kansa tsaye, yaje ƙofara falonta ya tsaya, tare da yin knocking. 


Ƙasa ƙasa ya jiyo muryar ta tace "Come in" da Sallama ya shiga falon, tana zaune tana shan tea, ya kalleta yace "barka da Safiya ranki ya daɗe" jinjina masa kai tayi ba tare da ta amsa ba, ta cigaba da abunda take ba tare da tace uffan ba. 


Haka ya shuɗe tsayin wasu lokuta yana zaune yana jiranta, ga shan tea ɗin take kamar tana shan magani. 


Yusuf ya gyara zama yace  

"Ranki ya daɗe jiya naga an turomin kuɗi a account ɗina masu yawan gaske, ban sani ba koke ce, shine nace bari in tambaye ki" 


"Kana expecting ɗin kuɗi daga gurin wani ne?" tai maganar tana ajiye cup ɗin hannunta


"A'a, bana yi" ya bata amsa


"Anyway salary ɗinka ne na 3 months da ban baka ba"


Zare ido Yusuf yayi yace  

"Amma sunyi yawa fa, ya zanyi da wannan maƙudan kuɗaɗen?"


"Zaka iya zubarwa, wannan kai ta shafa"


"A'a Madam, banyi aikin da zan karɓi wannan kuɗaɗen ba, sun yi yawa ban san....


"Kai ɗan Yimin shiru mana, idan ban manta ba kafin in ɗauke ka aiki na gaya maka salary ɗinka, kasan sunyi yawa meyasa kace zaka yi aikin? A beg keep this aside follow me"

Tayi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗin ta, jiki ba ƙwari Yusuf yabi bayan ta.


Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗakko wayar nan da tasa ya siyo, ta tako zuwa gaban Yusuf, sedai tana zuwa suka ji wani shock a tare, ƙamshin turaren da Yusuf yake yasha banban da wanda ta hana shi sakawa, amma muddin zata ji ƙamshi a jikin sa se wata kasala ta saukar mata.


Shikam Yusuf ƙirjin sa ne ya shiga bugawa da ƙarfi ba tare da yasan dalilin hakan ba.


Widad ta tattaro nutsuwar ta ta dube shi ta miƙa masa wayar, yasa hannu ya karɓa yana kallon ta, a hankali tace


"Yanzu misali a ce wannan wayar ranka ce, a ina zaka ɓoye ta?"


Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "zan mata kyakkyawan ɓoyewar da babu wanda ze san inda take se Allah"


"Good haka nake son ka ɓoye wannan wayar tamkar na baka ranka, duk kusancinka da mutum karka kuskura yasan da wannan wayar a tare da kai, karka yarda da kowa, wannan wayar tamkar na baka ranka ne!!! ka kula da ita"


A diririce Yusuf yace "Amma me yasa zan kula da ita haka? Ban gane tamkar kin bani raina ba"


Ɗan taɓe baki tayi ta juya tace "bashi da mahimmanci kaji wannan a yanzu, saboda sanin hakan a yanzu tamkar sake jefa rayuwar ka cikin hatsari ne, let me tell you something, don't trust anyone, i repeat myself don't trust anyone, jeka ƙarfe biyar zan fita yau"


Yusuf ya jinjina kai yace "Amma kuɗin nan da kika bani wallahi sunyi yawa"


Widad tace "You can go, na sallame ka"


Yusuf yace "Amma ban san yadda zanyi da wannan maƙudan kuɗin ba"


Ba tare da ta kula Yusuf ba ta shiga ƙoƙarin rage kayan jikin ta zata shiga wanka, ba shiri Yusuf ya juya da sauri ya bar ɗakin, yana mamakin wauta irin ta Widad. 


*********************************


Alhaji Musa ne zaune a falon sa, 'yarsa Nurat na kujerar dake facing ɗinsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunata. 


"Wallahi Nurat na rasa me zan miki in huce, da tuni harkar nan ta kankama, amma kikayi mana wauta da hauka, idan abun da muke nema ya samu, se kinfini mora" 


Murya na rawa da alama tana tsoron mahaifin nata tace  


"dan Allah kayi haƙuri, nima wani ne yace ze saceni idan ban nuna masa inda take ba" 


"waye shi ɗin?" ya tambaye ta a ɗan hasale


"Wallahi ban san waye ba, nima bata gayamin waye shi ba" 


"Ni zan gano ko waye inyi maganin sa, yanzu dole ki samo wata hanyar abunda zaki yi ta sake zuwa gidan nan" 


Saurin girgiza kai tayi tace "Ai kasan ba zata ƙara yadda dani ba, wallahi kome zanyi ba zata zo ba" 


A fusace yace "tashi ki bar nan, komai a kasa dake se kinyi wauta, ni nasan abunda zanyi" 


****************************


Album guda na hotunan Widad yake dasu a System ɗinsa, ji yake kamar ya janyo kwanakin da ze koma Nigeria, kallon hotunan ta kawai yake hakan ke ƙara samasa nishaɗi. 


Video call ya kira Mummy, Hajiya Halima na ganinsa tayi murmushi tace  

"'yan makaranta, lokaci ya kusa ko?" 


Anwar yace "Eh Mummy se missing ɗinku nake, ina su Ramla ne" 


"Suna nan gasu a kusa dani" 


"shine ba zasuzo mu gaisa ba, dama ba nemana suke ba" 


Amal tace "waze kira ka a kwashe masa kuɗi" 

Haka suka dinga video call suna hira da 'yan uwan sa, can yace "Mummy wai ina Widad ne? Naji ance tana Nigeria kuma tunda nake kira bana ganin ta" 


Tsaki Mummy tayi tace "Ban sani ba, ita ta haifeka koni? Idan bani kske nema ba shikenan, kullum baka da zance sena wanne banzar yarinyar?" 


"yi haƙuri Mumsy, Yadda mahaifinta ya riƙemu ai senake ganin kamar babu laifi dan na tambayi inda take" 


Ramla tace "Brother dan Allah karka ɓatawa mutane rai, waya ke maganar wannan mahaukaciyar" 


Anwar yace "ni a ganina, Widad rashin me janta a jiki da kuma depression yasa condition ɗinta ya zama complicated, amma... 


Cikin tsawa Hajiya Halima tace " Rufemin baki dan uban ka, kaga ka kiyaye ni ko in ɓata maka rai, in baka son ɓacin raina karka sake Yimin zancen yarinyar nan, ko dan kai kana can baka san irin zaman da muke a gidan nan ba" 


Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala, ana Wulaƙanta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta" 


Anwar yace "Amma Mummy.... 


A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai" 


Amal ta katse kiran. 


Anwar ya turawa Amal message 

"Amal ɗan turomin lambar Widad" 


Ta masa reply da "Taɓɗijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa" 


Jujjuya message ɗin ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin hakan. 


Yana wannan tunanin Fahad ya shigo ɗakin da sallama, ya kalli Anwar yace "Man what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba" 


Ɗan guntun tsaki Anwar yayi yace "Fahad, ni gaba ɗaya na kasa gane kan lamuran nan dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se taita faɗa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me lambar Widad balle ya bani" 

Fahad yace 

"Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta sam bata Yimin ba, nifa tun tana ƙarama yadda take wannan Share mutanen haushi take bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taɓun hankali "


Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ƙyaleni, baka san yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya ma in baka Ramla zaka iya riƙe ta kuwa? "


Fahad yayi murmushi yace 

"Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi" 


"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ƙagu kamar in janyo lokaci in koma gida, gashi seka rigani komawa Nigeria" 


"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan" 


Shiru Anwar yayi ya miƙe ya bar ɗakin, dan Fahad ya fara baƙanta masa rai. 


Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta ɗau wayar tasa a kunnen ta, shiru ta ɗanyi tace  

"Ok, thank you very much, send the address via my email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa. 


Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne meson tsafta sosai, baya son datti sam. 


Message ne ya shigo wayar Yusuf ya ɗaga ya duba. 


"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani" 


Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message ɗin daga Widad ne, 'Amma yaushe ta samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta ɗanji jiki. 

Guri ya samu ya tsaya yana jiran fitowar ta. 


Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya ɗaga kai ya kalli gate, ganin Widad ne yasa ƙirjin Yusuf bugawa da ƙarfi. 


Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi stocking ta saka beilt, ɗan ƙaramin baƙin veil ta ɗaure gashin kanta, dukda ƙasan gashin nata ya fito. 

Google glass ne a fuskar ta baƙi, ga takalmi me matuƙar tsini, se 'yar ƙaramar jakarta, gaba ɗaya bazaka ce idan Widad ta buɗe baki zata yi hausa ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito. 


Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka kurum yaji takaicin fitar Widad a haka. 


Ƙarasowa tayi ta miƙawa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya karɓa, ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba ɗaya ƙamshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace

"Ina zamu je?" shiru tayi na ɗan wani lokaci sannan ta miƙa masa wayarta, yasa hannu ya karɓa ya duba. 

Adress ɗin inda ze kaita ne, ya ɗago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ƙara yi masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar. 


Yana cikin tuƙi wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen ɗin wayar, ya ɗaga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace 

"Umman Yusuf"


"Ɗan gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe, nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"


Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace  

"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner me kyau"


Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaɓa yake yi kamar yaro ƙarami, Widad kuwa ƙura masa ido tayi ko ƙiftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas ɗin idonta take kallon sa amma yadda yake wayar da Mahaifiyar sa ba ƙaramin birge ta yayi ba.


A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shauƙin da ƙaunar na iyaye, inama Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daɗi'

Ba tayi aune ba taji hawayen da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass ɗin fuskarta tayi tana goge hawayen idon ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace 

"lafiya dai?"

"Lafiya cigaba da tuƙinka, ina so muje gurin nan kafin 5"

Ya jinjina kai ya ci gaba da tuƙin, wani katafaren hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai mafi akasari kallo ɗaya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin shigar dake jikin su.


Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buɗe motar ta tsaya tana ƙarewa harabar hotel ɗin kallo.

Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace "wait for me here" 

ta sa kai da nufin shiga cikin hotel ɗin, da yawa mazan dake gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haɗu iya haɗuwa, wani takaici ne ya kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurɓataccen gurin.

Bin bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace  

"I said you should wait me inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because of me"

Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya riƙo Widad gaba ɗaya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace

"Guri irin wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"

Nutsuwa Widad tayi seda ya gama tsaf sannan tace  

"Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani Malam kana ɓatamin lokaci ni"


A hankali Yusuf yace "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ƙare miki kallo a haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"


Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ƙara shiga rayuwa ta, na gaya maks"


Ta juya ta shiga Hotel ɗin da sauri, wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya koma mota ya zauna yana tunani a ransa

'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka da ita ne?'

Wata zuciyar ta tambaye shi. 


Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya zauna akan motar yana ƙurawa hanyar da Widad tabi ido. 

Ba tsammani ya hangota tana fitowa, sedai fuskarta ɗauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ƙoƙarin tsaida ita yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige. 

Yusuf ya zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba ɗaya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi "Are you ok?" 


"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale


"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta ɗauke kanta tace  

"drive very fast please" gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ƙara gudu, kuma still bata dena kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar ɓacin rai da damuwa. 

Guri Yusuf ya samu yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta ɗakko wayar ta, ta ɗan daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "Hello Daddy" 


Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace "please Daddy I want Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama ask him to set up my visa" 


Shiru ta ɗanyi sannan tace "Daddy don't take it for granted please, i can't define what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma" 


"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da kai? Karo na biyu ina neman abu kana ƙin Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon Ƙwaƙwalwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ƙasa ta cigaba da kuka. 


Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai buƙatar yasan me taje yi Hotel. 


"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na" 


"Bazan iya tuƙin ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa ɗauke da damuwa 


A hankali ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano gaskiyar abunda ya faɗa 


"to meye haɗinka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi abunda ke gabanka"


A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tuƙi, sedai gaba ɗaya hankalin sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.


Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa, duk yadda yayi ƙoƙarin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.


Dafe kai Yusuf yayi yace "Subhanallah"


A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haɗa baki da kai zaka kashe ni ko? Dama na sani"


Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa masa mota se an biya shi.


Yusuf ya buɗe motar ya fita jiki ba ƙwari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in, Yusuf yace  

"Dan Allah kayi haƙuri, birki ne ya ƙwacemin, kuma kaga traffic ta tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi haƙuri"


"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai kaɗai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"


Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan haƙuri, dukda zagin da yakewa Yusuf amma haƙuri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota a zaune.


Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka haƙuri nake kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka huce" 


Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan da nan temper ɗinsa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya dena cewa komai.


Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena sa an sauke maka wannan rashin ɗa'ar taka mara tarbiyya kawai"


"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya kana ɗaga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"


Gaba ɗaya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.


Mutumin ya kalli Widad yace 

"Lallai ka ɗakko karuwa a mota, dole ka ɗagamin murya danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"

Ya ciro wayarsa yana waya. 


Yusuf a harzuƙe zeyi magana Widad ta ɗaga masa hannu alamar yayi shiru.

Ta ɗakko wayar ta tayi 'yan taɓe taɓe. 


Mutane suka ja gefe suna son ganin ƙarshen dramar, mintuna kaɗan sega motar 'yan sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace "gashi nan shine, ku kama shi shida wannan koɗaɗiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"


Tuni ɗaya daga ɗan sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me ɗan sandan ya jiyo bindiga a jikin Yusuf!!!


Ayshercool

*** 


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol