Free chapter 路 Read without an account

18

by Bilqeesa Ibraheem Musa 路 AUREN KADDARA KO BIYAYYA?

Dad yadawo gida ya sanarwa mom yanda sukayi dasu umma, 

Mom tace alhaji aida bakace musu hakaba.

To bilkisu ya kike so nace musu lokaci yayi dazan daina barin su yaya suna danne hak'in iyalina, dan bazai yuwwuba ace ni bani da 'yanci iyalinama basuda shi,

 "Mom tace to shikenan ALLAH ya zab'a abinda yafi alkairi"

  "Dad yace amin"

"Mom tace to masu kai amaryafa sun shirya dannaga abokan angon harsun iso, dad yace nagansu awaje harma mun gaisa, ai kawai abasu amarya sutafi, tunda bakunce can zasu kwana da k'awayentaba??

  "Mom tace eh"

"To sai ku had'asu da manya uku suje su kwana can"

To shikenan alhaji mom tafad'a tana nufar hanya.


Ankai amarya d'akin mijinta kowa yaga gidan saiya rud'e da kyansa. To shima dai ango anan ya kwana ab'angarensa, washe gari akayi walima 'yan yola suka wuce gida, suka bar amarya na kwasar kuka, danma su kairat da kausar suna gidan tare da ita har dare, saida suka gyara mata ko ina sannan, mom ta aiko musu direba da abinci mai kyau da dad'i, yatafi da 'yan biyu gida, suka bar Munneerah na ta kuka.


Dady yana gidan har wajan k'arfe tara yana sak'a da warwara akan amaryar tasa, ak'arahe ya mik'e yay wanka yashirya cikin fararen kayan barci gajeren wando da riga mara nauyi, ya bud'e jikinsa da turare mai k'amahi, sannan ya kwashi wayoyinsa da jakkar aikinsa ya nufi d'akin amaryar tasa.


Itako Munneerah tunda su 'yan biyu auka tafi tayi zaman awa d'aya tana kuka, dataga ba mai lallashin ta, tamik'e tai shirin barci takulle d'akin ta kwanta, wai dan kar dady yashigo.


Ya iso ya tab'a kofar arufe yay d'an tsaki wai wannan yarinyar shi take rufema k'ofa dan ta rainasa, da har yayi niyyar komawa b'angaren sa ya kwanta abinsa, sai yatuna nasihar iyayansa, dan haka yazube kayan dake hannunsa saman kujeran dake kusa da k'ofar bedroom d'inta yafita ya koma b 'angaren sa ya d'akko wani key d'in yadawo..


 yasa key d'in ya bud'e d'akin, ya kwashi kayansa yay ciki.

Ta mik'e zumbur zaune tana kallonsa cikin mamaki, kallo d'aya yay mata ya kauda kai, kujerar dake d'akin yanufa ya zube kayansa bisa tebir d'in gaban kujeran ya zauna.


Ya kalli Munneerah dake ta faman kallonsa, sai kuma ya mik'e ya nufi wajan gadon, shima yana kallon ta, ya kauda kai, kinci abinci ya fad'a yana bud'e kulolin dake gefenta??

   "Tace na k'oshi"

"Ya d'aure fuska mekika ci??

 "Ba komai"

Oya sakko kici abinci kafin na b'ata miki rai.

Ganin ya tamke fuska yasata sakkowa da sauri, dan dady yanada kwarjini sosai duk fitsarar ka in ya had'e fuska sai kaji shakkarsa.


Ya kalle ta tana cikin doguwar riga ta barci, amma bata kai k'asa ba,tayi mata kyau sosai, ya zauna bakin gadon, ita kuma ta zauna k'asa tana zuba masa abincin, ta gama ta jawo wani filet d'in zata zuba, yace karki zuba wannan ma ya ishemu.


Ya sakko ya zauna saman kafet d'in, ya fara cin abincin, itako ta kasa ci sai wasa take da zoben hannunta.

Ya d'an buga cokalin ajikin filet d'in, ta d'ago tana kallonsa,bana son yawan magana fa kici abinci,ba yanda zatayi dole ta d'auki cokali tafara ci, bai kuma bi takanta ba ya ci abincinsa da dukkan kayan abincin ya mik'e ya koma saman kujera, ya bud'e jakkar aikinsa, ya d'akko wasu book's yana dubawa.

Ta d'an ci abincin ta tattare kayan takai kichin,

Ta dawo ta haye gado ta kwanta, shikam yanata bin cikensa har wajan kar fe 2:pm sannan ya mik'e yaje kan gadon daga gefenta ya kwanta yay addu'a sai barci.


 da asuba dady ya tashi, sai da ya tada ita sannan yafice yaje b'angaren sa yay alwala yasaka jallabiya ya nufi masallaci, koda ya dawo b'angarensa ya wuce yay kwanciyar sa.


Munneerah ko da ta idar da sallah saita d'akko AL'KUR'ANI ta hau karatu, dan bata iya barcin safe ba,sai da agogo ya nuna 7:am sannan tai addu'a, ta tashi ta gyara d'akinta fes ta had'a masa book's d'insa da wayoyinsa waje d'aya ta adana masa, ta wanke bayinta, ta dawo falo ma ta gyara ta bad'e gidan da k'amshi, mai dad'i.


Kichin ta nufa tana nazarin mizata fara dafawa yau amatsayin ta na amarya,馃 can tai murmushi da alama ta tuna,dan haka ta hau aikin girki.


Sai wajan karfe 08:30 am, ta kammala, tajere k'ayataccen break d'inta, a inda aka tanada dan cin abinci, 

Bayan ta gama ta nufi d'aki dan yin wanka.


Wajan k'arfe 8:30am shima dady ya tashi, yay wanka, ya shirya cikin jar shadda d'inkin zamani yayi kyau sosai sumarnan da sajensa sunsha gyara sai walkiyar mai sukeyi, yasaka turarensa mai dad'in k'amshi,

Ya fito hannunsa rik'e da farara riga da likitoci kesakawa.

Kaitsaye b'angaren Munneerah yanufa......鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.