Free chapter · Read without an account
03
by Rahma Kabir · LUBABATU
QLUBABATU
03
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
_Daga fejin farko zuwa na biyu naga tsantsar kaunarku a gareni masoyana, lamura sunyi min yawa bazan iya bin comments dinku ina nuna godiyata ba, sai dai ga tarin godiya da jinjina a gareku bisa ga nuna kauna Allah ya saka da alkhairi ya biya muku dukkan bukatunki. Rahmarku ce, son so fisabilillahi_
*MAFARI... Waiwaye*
YOLA
Baihari local government
_Na kirkiri sunan Baihari a matsayin karamar hukuma tare da rigar ardo, duka kirkira nayi_
Karamar hukuma ce dake cikin garin Yola, wanda yake cike da tarin makiyaya fulanin asali sosai da al'adarsu, akwai wayewa ta yan boko masu riko da addini. A Baihari akwai kauyuka sosai a karkashinta wanda suke hade da hausawa da kuma wasu yarika daban daban, sai dai fulani sunfi yawa kasantuwar garin ya kafu dansu ne.
*Rigar Ardo*
Riga ce daya daga cikin kauyukan dake karkashin Baihari, yana da tarin tarihi wanda ya ginu tun zamani mai dogon zango, akwai matukar yalwar mutane da kuma arzikin makiyaya da manoma, hakan yasa rigar ya kara habaka sosai wanda kananun riga dake kewayensu suka maida rigar Ardo babban birninsu. Sai dai mutanen ciki akwai duhun kai ba suda wadataccen ilimin addini komai nasu sunfi sanya al'ada sama da addini, sannan boko bai je musu ba babu kuma wutar lantarki, suna da karancin rijiyoyi dole sai a rafi suke dibowa. Kadan ne suke iya fita suje cikin Baihari yin siyayya musamman wasu daga cikin masu siye da siyarwa da mata masu tallar nono, akwai wanda ma basu taba fita cikin birnin Adamawa ba.
Mahaifinmu Malam Adam ya kasance daya daga cikin mutanen wannan riga wanda nan ne asalinmu, ya kasance kuma babban makiyayi.
Tun ina yar shekara bakwai zuwa takwas na fahimci ni banda amfanin yin rayuwa a dorar duniya har kawo da nake shekara sha shida, kasantuwar na taso cikin wani irin ahali masu wuyar sha'ani da duhun kai wanda basu yadda da kaddara ba, ina samun tsangwama ta ko ina a cikin rigarmu ta Ardo, musamman mahaifina daya ke kyarana da nuna kyama a gareni, saboda yana ganin tunda aka haifeni na zame masa matsala kuma silar karayar arzikinsa, hakan yasa mutane da danginmu suke guduna saboda a ganinsu ni annoba ce, a gurin Ummanmu ce kawai nake jin dadi sai yar uwata Jidda. Umma ta yi ta yi da Baffa a kaini asibitin birni a dubani ko ciwon na can ne, amma fir yaki ya ce ciwon bana asibiti bane sai dai mu cigaba dana gargajiya.
Mu biyu rak suka haifa, sunan mahaifinmu Adamu, mahaifiyar mu Haajara, Naci sunan Kakata Lubabatu mahaifiyar Ummanmu, mun taso duk kakanninmu basa raye sun kwanta dama, auren hadi ne aka yiwa Ummanmu da Baffa, duk kuma haifaffun rigar Ardo ne, Baffa yana da kani guda Ibrahim yana zaune a cikin Baihari tare da matarsa guda daya mai suna Asma'u, 'ya'yansa uku, Muhammad sani, Hauwa'u itace tsarata sai takwaran Baffanmu Adam shine autansu. yana kasuwancin tumaki cikin rufin asirin Allah.
Adda Jidda ita ce babba sai kuma ni ke bi mata daga kaina Umma bata sake haihuwa ba duk da Baffanmu yaso ya samu yaro namiji amma saboda ni an haifeni da nakasu, sai ya roka Allah daya tsaida masa haihuwa in dai za a cigaba da ba shi irina to ya yafe, haka kuma Allah ya amsa adduarsa basu sake haihuwa ba har kawo girmanmu, duk da ya sake auren wata mai suna Aisha ko zai samu karuwar haihuwar namiji amma shuru kamar dan sanda yaci shirwa, zamansu bai dade ba ya rabu da ita. Adda Jidda ta taba aure sai dai bata kaiga Haihuwa ba mijinta ya rasu shekara uku kenan, akwai masu niman aurenta sosai amma ganin tana samawa Baffa kudi wajen tallar nono sai ya dinga jawa manemanta rai, har ya kaiga wasu sun hakura, masu naci ne dai suketa zarya da kara mita wajen ganin sun samu aurenta.
Tafiya nake da kyar ina sharce hawaye da hannun haguna cikin kunci saboda rashin jin dadi da bakar azama, bansan me ake kira da jin dadin rayuwa ba domin na taso cikin wani mawuyacin hali wanda nake kiransa da kaddararren al'amari. Ina dauke da tulu na wanda yake cike da ruwa, tunda na baro rafi nake tunanin yadda zan karasa gida, azabar da nake ji tamkar ana hura wuta a sassan jikina duk iya dauriyata sai da hawaye ya cigaba da zarya a kuncina sai dai ban iya fidda sautin kukana saboda tsantsar azaba, dole nake hutawa a duk taku goma da zanyi a haka harna fara hango cikin rigarmu, hakan yasa na fara jin dadi a raina ganin nayi rabi daga cikin tafiyata na zuwa gida, nan take na tuna da addu'ar da ummanmu ta koya min ayatul kursiyyu wanda ya daukeni kusan wata da watanni kafin na haddace shi, shima saboda ta dage min da na ci wajen maimaici, kuma ina ganin sauki a duk lokacin data karanta min. A hankali na soma karantawa cikin sanyin murya wanda yake tabbatar da zugin da nake ji, bansan kira'a ba amma ina sarrafa harshena cikin wani irin sigar tausayi, muryata zakwai kuma siririya hakan sai ya bada wani irin salo mai dadi, ni kaina ina jin dadin yadda nake karatun, hakan sai ya samar min da natsuwar ruhi ina jin zafin jikina yana sauka. Mun taso bamu san boko ba saboda baije cikin rigarmu ba, sai dai cikin Baihari ne ake yi shima ba kowa ba saboda Al'adar da muka fi rikewa tun kakanni, sai makarantar allo muke zuwa wanda karatun mata sai da daddare, ba wani karatun kirki ake mana ba saboda sai a kusa wata biyar ana maimaita sura daya, domin su kansu malaman suna bukatar karin karatun saboda duk tsafke ne da lalube suke, a gurin Ummanmu ne muke dan koyan karatun saboda ita gidansu malamai ne, kuma ba laifi tana da sani fiye da Baffansu.
A haka harna isa gida, ina shiga naji Baffa yana surfa masifa wanda nake da yakinin cewa akaina yake yi, ilai ina yin sallama ya waigo a fusace yana huci yace cikin tsawa.
Dan uwaki ina kika tsaya tun dazu ana jiranki ki kawo ruwa a daura sanwa amma shuru kamar an tsukaki
Idona ya kawo kwalla sai dai ban bari ya zuba ba na ce cikin rawar murya.
Baffa kafata ne ke tsananin ciwo ga zazzabi ya rufeni, da kyar na iya kawo kaina gida.
Rufemin maki shashasha ai nasan zancen kenan, tun jiya kika soma kiran ciwon kai nasan zaki kira min bala'i, yaushe na gama kashe kudin maganinki wajen malam Dauro ace abu yaki ci yaki cinyewa, kai ni dai da haihuwarki gwanda barinki wlh gwara ki mutu na huta da bakin ciki da kike jefani.
Ashsha malam wannan wani irin magana ce haka? Gaskiya ba kyau ya kamata kasan kaddara, baka san irin baiwar da Allah yayi mata ba nan gaba kila sai kaci arzikinta.
Cewar Ummanmu cike da takaicin maganganun Baffa.
Allah ya kyauta dan banga abin arziki a gun wannan yar ba mai mugun abu, yarinyar da tun da kika haifeta ta Zame min jafa'i kullun cikin asara, yan kadarorina duk sun kare wajen magani, Allah dai ya saka min dan wlh kin cusheni Lubabatu.
Ya kare maganar kamar zai fashe da kuka, wannan karan Umma tsaki kawai taja ta wuce madafa dan duba wutan sanwar data ke kokari hadawa, sai ya fice daga gidan rai bace, dai dai shigowar Jidda wacce ta dawo daga tallar nono, ta karaso inda nake tsaye jingine da bukkar dakinmu na kwana ta dafani.
Ki kara hakuri da halin Baffa ya daina damunki dan yaci ace yanzu kin saba, Allah dai ya yi miki arzikin da Baffa sai ya amfana da shi.
Kinci gidanku nace Jidda bana son irin wannan kalami da kike akan Baffanku.
Cewar Umma ta danno mata dakuwa daga nesa, Jidda ta kunshe dariyar data zo mata ta shige daki tasan tabbas dole sai Umma ta tanka mata in dai tayi zancen Baffa, duk da tasan gaskiya ta fada amma da yake uwa tagari ce kullun sai ta tsawatar.
Da yake na riga na saba da surutun Baffa sai abin bai min zafi ba na share hawayena na shiga daki danna huta, saboda Adda Jidda ta dawo zata yi duk aikin gidan.
____
Cikin dare azabar ciwo ya tasheni daga barci, tun ina dauriya ina danne kukana dan kar na tashi Adda Jidda har sai da ya fito ina rerashi cikin tsananin tausayin kaina, Jidda ta mike zaune ta tana kallona.
Jikin ne Kuma ya tashi Luba? Sauran sassaken maganin nan kuwa kina shansa? Ko naje na tashi su baffane?
A'a karki tashe su, ga sauran maganin can a kwano miko min nasha.
Allah ya yaye Miki wannan cuta ya baki lafiya.
Ameen. Na amsa cikin runtse ido yayin dana kurbi jikon magani, sam babu dadi a baki amma haka nake sha badan raina naso ba. A haka nayi ta murkususu har zuwa sallar Asuba, na tashi Jidda ta fita tsakar gida taci Karo da Umma tana alwala dan tuni Baffa ya tafi masallaci, tace Mata.
Umma jikin Lubabatu ya motsa cikin dare amma tasha magani, ban sani ba ko ta samu barci dan yanzu ma itace ta tasheni.
Subhanallahi, wannan ciwo na Lubabatu yana damuna, Allah ya yaye Mata bari Baffanku ya dawo sai na sanar masa anjima sai ya kira Mai magani yazo ya dubata.
Nikam Umma Ina ganin Mai zai hana mu dangana zuwa asibitu na birni, Allah sai nake ganin ciwonta kamar bana gida bane.
Jidda ko na yiwa Baffanku wannan zancen sai dai raina ya baci, muyi ta mata Addua Allah ya kawo mata karshen wahalarta.
Ameen ta amsa ta dauki buta ta shiga bayi Umma kuma ta wuce daki ta tada sallah.
---
Da gari ya waye sosai misalin karfe tara na safe, Umma ta sanar da Baffa yaje ya kira mai magani yazo ya dubani ya kara bada wani jikon yace shi Zan koma sha, ya amsa kudi kimanin dubu biyu ya tafi, Baffa ya yi ta sababi yace.
Insha Allah daga yau bazan sake kashe kudina akan Lubabatu ba, na yi iya yina, bazan cigaba da bata takiba bana ganin yabanya.
Malam lada kake samu, kayi kokari ka amsa kaddararmu.
Ai tuntuni na amsa amma zuwa yanzu na gaji. Ke kuma kiyi kokari ki saida nonon da aka daura miki dan yau ranyo aljuhuna yake ba ko sisi, da kudin cinikin da za kiyi shine zan siyawa garkena harawan abincinsu.
Baffa ya kare maganar ga Jidda ya fice yana goge bakinsa da tsinken askwaki, Jidda ta amsa da to ta dauki gammo Umma ta daura mata babbar kwaryan nono, ta bude maki tace min da karfi.
Lubabatu na tafi talla insha Allah in na saida kwaryar nono zan siya miki tsiren Habibu ki ci ki huce takaicin Baffanmu.
Ta fice abinta Umma tana yi mata sababi akan abinda take fada, Ina jinsu sai dai nayi dariya dan inda sabo na saba da rikicinsu.
*
Tunda jidda ta fita talla bata Dawo ba sai yamma, da yake cikin Baihari take zuwa tallar. Wani me mota mai suna Haruna ne ya dawo da ita cikin rigarmu saboda ya bukaci yana so ya yi tsaraba da nono ta tabbatar masa akwai a gida, jikin Baffa yana rawa ya yi masa kyakkyawar tarba, yasa aka dama masa fura da nono aka kai masa Haruna yaci ya koshi kana aka kawo masa kwaryar nono biyu daya bukata ya siya harda karin damin kudi ya yiwa baffa, ba karamin murna ya yi ba ya dinga sanya masa Albarka, ganin wannan karamci daya samu ya ce zai kara dawowa siyan nonon a tanadar masa nan da kwana biyu insha Allah zai zo, har mota baffa ya raka shi ya tafi. Haruna ya dinga kada kai yana fidda kayataccen murmushi mai sauti, ya furta a fili.
Tabbas wannan ita ce zabina, ina hango nasara a cikin tafiyar nan.
Sai ya duki sitiyarin mota ya kwashe da dariya, haka ya cigaba da tuki cikin tsananin murna kamar wanda aka yiwa kyautar kujerar makka, har ya isa cikin Baihari ana gabda magrib, ya tsaya wajen wasu gungun almajirai ya basu kyautar wannan nonon daya siya ya wuce cikin Yola dan yana so da sassafe yabi jirgin da zai kaishi Kano.
***** **** ******
Kaduna
Rahima tunda suka fito lectures suka wuce jikin wata bishiya suka zauna ita da kawarta Aliya, tana bata labarin saurayinta da suke charting cewar yace zasu hadu, ta kara da cewa.
Kina ganin wani irin tarba ya kamata nayiwa Hashim yace weekend zai zo, Kuma kin ga wannan ne farkon haduwata da shi.
Ki masa abinci mai dadi da drink, ai ina ga shikenan sai kiyi shiga mai kyau.
Ok zanyi nazarin abinda zan dafa masa, wlh duk na kosa mu hadu bansan ya aka yi na kamu da sonsa har haka ba.
Ni dai shawarar da zan baki shine kibi a hankali ki daina wannan rawar kan, namiji ba ayi masa haka, kija ajinki yadda ya kamata.
Hmmm naji amma ba wani aji da zanja tunda mun saba sosai a waya.
Aliya ta tabe baki ta mike tare da cewa.
In kin gama zuban tashi muje muci abinci dan yunwa na keji banyi wani kari me kyau ba.
Ok kawai Rahima tace ta mike suka wuce.
---
Sai yamma lis Rahima ta dawo ta samu Mami a falo tayi mata sannu da gida kana ta wuce sashin Umminsu dan ta bata labarin zuwan saurayinta. Ummi tana kwance bisa gado tana yin waya murya can kasa cike natsuwa.
Habba Hydar ya zakace haka na gaya maka ba kada wata matsala da Alhaji, wlh zai amince da zaman a gidanmu.
Hydar ya murmusa.
To shikenan tunda kince haka zanzo Nan da one week insha Allah sai ki shirya min tarba mai kyau ki kuma fadawa 'ya'yana ina bisa hanya.
Ya fada cike da tsakiyanci. Ummi ta tashi zaune cike da tsantsar farin ciki wanda ya bayyana karara a fuskarta tace cikin zukuwa.
Allhamdulillah nagode Hydar Allah ya kaimu wlh ka sani farin ciki sosai, duk na kosa na ganka na jima banyi ido hudu da kai ba tun a Germany fa kusan shekaru hudu.
Hydar ya yi dariya tare da sake jaddada mata lallai zai zo ta shirya masa kawai, a dai dai wannan lokacin Rahima ta shiga dakin, Ummi ta yi saurin sallama da shi ta kashe wayar, sai ta waigo wajen Rahima fuska daure.
Bana ce duk in zaki shigo min daki ba ki fara sallama har sai na baki izini ba kafin zaki shigo.
Ohhh kiyi hajuri Ummi wlh na sha'afa ne yanzu nake shigowa daga makaranta. Halan da Abba kike waya?
A'a uncle Hydar ne zai zo wanda ya jima baya kasar nan.
Wow ko wanda nake yawan samunki kina waya dashi?
Eh kanina dana fada muku gaba daya baya rayuwa a nan yana Germany.
Amma Ummi ai kince mana ke kadai iyayenki suka haifa.
Shi yaron wan Babana ne.
Wai Ummi yaushe zaki kaimu gun yan uwanki ne? Rabonmu dasu tun muna kanana.
To duk iyayen sun mutu sai mu 'ya'ya muka rage kuma kowa yanata kansa.
Amma Ummi ko yayane ai yaci ace ki kaimu
Ke na gaji da maganarki wuce kiban guri na kula ke sam surutu baya damunki. Wai mema ya kawoki nan?
Hmmm dama zan fada miki ne wannan mutumin da muka hadu a waya yace zai zo da weekend din nan.
Rahima! Bafa nason jaye jaye ki shiga hankalinki tom, kuma ki wuce ki ban wuri.
Kai Ummee
Nace ki tafi, Allah ya kawo shi lafiya.
Rahima ta amsa da Amin ta wuce tana tsalle kamar wata karamar yarinya, Sam bata kaunar a kushe mata abinda take so burinta kowa ya mara mata baya akan abinda take muradi. Kasantuwar yau tana cikin murna da zumudin zuwan Hashim yasa ta manta da batun Umar balle taje ta tsokaneshi fada suyi rikici.
----
Sara tana zaune a daki ta rafka tagumi tana saka da warwara har Ubaidu ya shigo ciki bata sani ba ya ajiye brief case dinta da key mota a center table ya isa inda ta zauna ya sakala hannunsa a wuyanta, ta yi saurin dagowa tare da sauke ajiyar zuciya.
Diamond tunanin me kike yi ne haka? Meye matsalar?
Tunanin rayuwa nake yi, dazun aka kirani kawata Kausar ta haihu baby boy shine naga dududu 9months kenan da bikin harta haihu, ni ko gashi shekara uku kenan shuru ko batan wata, gaskiya Diamond abin yana damuna ina so na haihu, pls ka yarda muje asibiti adubamu musan inda matsalar take.
Hmmm Sarah kenan, meyasa kike damun rayuwarki ne haka, bacin kinsan dukkan rabo na Allah ne, Ni Banga abin damuwa ba wlh saboda komai yana da lokacinsa ki fatan Allah ya kawo mana a lokaci mai albarka, bana so kina sanya damuwar abinda bake ce zaki maganinsa ba. Amma ko wani ya sauya miki ne a gidan nan saboda rashin Haihuwa?
A'a
Tace cikin sanyin murya.
To meyesa zaki sanya damuwa hakanan bacin komai yin Allah ne, Diamond ki natsu pls ni ba ki da matsala dani.
Shikenan ya wuce, ya aikin hop baka kwaso gajiya ba dan yau akwai tab'i ba dan kadan ba, zan lasheka kamar mayunwaciyar zaki.
Hahaha ai na fiki jin yunwa kedai akwai kidan dare da zai bata hankali masoya, ki shirya yin rawar da zaki bada gumi sosai.
Ta mike tana dariya tare da kama masa hannu.
Kullun a shirye nake da daukar haddar karatunka.
Nima shaida ne.
Ubaidu ya fada yana kanne mata ido daya tare da yalwataccen murmushi a fuskarsa, suka shige cikin bedroom suna hirarsu cikin nishadi.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
_________________
*Tallah*
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.