Free chapter · Read without an account
Page 25
*💫FORBIDDEN LOVE💫*
_Haramtacciyar soyayya_
2️⃣5️⃣
*Iya mata Banda Maza Dan Allah Dan annabi, idan kinsan bazaki comments ba karki shigo please, Banda tallah*. ***
A daya bangaren hajiya saleemeh ke gaban LEC A. M with so much tears tana fad'in “yanzu fisabilillahi abinda zakamin kenan , aduk zaman damukai dakai inada tabbacin bantaba munana ma ba Amma sakayyar da zakaimin kenan baban Yara , idan kamin haka hakika ka cutar Dani hakika ka zalinceni bazan iya yafema ba tabbas”yama rasa ta inda zai bullo Mata ta fahimce shi , sannan kuma harga Allah bayaso wani sa'bani yashiga tsakaninsa da iyalinsa bakuma yaso yaransa Susan meke faruwa, gurin zama yayi Mata nuni dashi , babu musu hajiya saleemeh ta zauna tana goge hawayen ta Dan jitake kirjinta har wani zafi yake d'auka , dubanta LEC A. M yayi ya sauke ajiyar zuciya had'e da fad'in “yanzu saleemeh mene matsalarki akan abinda nakeso fad'amin”dasauri ta katseshi da fad'in “mecece matsalata kake tambayar , kafi kowa sanin matsalar ni Banga dalilin da zakaso yarinyar nan ba , what's too special about her da har idonka ya rufe ka kasa sanin daidai da abinda yake ba daidai ba haba alhaji come back to your senses mana this is too much”daga Mata hannu sama yayi kafin yace“bafa abinda na tambayeki kenan ba saleemeh, this is between me and you”sannan yayi shiru Yana dubanta kafin ya dora da fad'in “you are asking mena gani akan Sabrine har nakesonta right? ”karayin shiru yayi na wasu minutes kafin ya Kara da fad'in “baki lura da Sabrine sosai ba saleemeh ki kalleta wallahi exactly like Fatima”da sauri hajiya saleemeh ta Mi'ke tana Dan dafe kirji tare da furta “fatima!! Kuma alhaji ”d'aga Mata Kai yayi alamar eh, wasu sabbin hawayenne suka zubo Mata ta dubeshi tare da fad'in “yanzu fisabilillahi alhaji akan tana kama da wannan me idon mayun shine zaka tada rigimar auren ta alhaji”wani irin bacin Raine ya ziyarci LEC A. M tare da nuna hajiya saleemeh danyatsa Yana fad'in “aduk abinda zaki furta kada ki kuskura ki aibata Fatima kinji na fad'a Miki , now get out of my side” yafada da wani irin fad'a har Saida hajiya saleemeh taji tsoro tana kallonsa,
“out!!! ” ya Kara fad'a cikin d'aga murya, cikin sanyin jiki hajiya saleemeh ta janye jiki tana mamakin yadda akai alhaji ya juye ya zama haka, cikin kuka ta juya tabar dakin, Afiya na ganin fitowar ta da kuka taji zuciyarta tayi zafi kawai ta juya tashige d'aki
Hajiya saleemeh nashiga d'aki tai ta sunturi ta kasa zaune ta kasa tsaye, samu tayi ta zauna gefen gado had'e da lalubo wayarta , contact d'inta tashiga tai typing hajiya zainab Amma Sam lambar Bata fito ba , tagama duba dubenta har Gmail Bata ganta ba , dafe Kai tayi had'e da furta innalillahi , shiru tayi nawasu Dan lokuta saikuma tayi dialing wata number ansa hajiya murja , ringing biyu tayi aka d'aga had'e da fad'in “hajiya Saleemeh manyan gari”cikin daure wa na Hana kanta kuka ta furta“murja Dan Allah temako zakimi ”
Dagacan wadda aka Kira da murja tace“dama tunda Naga kiranki nasan in kaji gudu da labari to inajinki wane temako”dasauri tace“dan Allah kituromin number d'in zainab”
“too ikon Allah zainab fa kikace , ”cikin 'kaguwa hajiya saleemeh tace“kinga Dan Allah nidai ki temakamin ki turomin” dagacan akai dariya had'e da fad'in “to zan duba Miki Allah yasa tana gari Dan zainab kafar yawo ce”da sauri hajiya saleemeh tace“nidai ki turo min ”
“zan turo Miki yanzu”tanajin hakan ta yanke wayar ta Matsu a turo Mata , kusan mintuna goma Sha biyar sannan wayar hajiya saleemeh ta fara ringing, da sauri ta d'aga had'e da fad'in “baki turomin bafa ”dagacan hajiya murjar ta furta“aikuwa nikam du na duba banganta ba wallahi bansan ya akai ba ”
“ innalillahi wainna ilaihirrajuun yanzu Dan Allah murja Ina zan Sami zainab koma number d'inta wallahi Ina cikin matsala” ta fad'a tana Mi'kewa daga kan bed d'in datake, hajiya murjarce dagacan tace“kinga kibani Nanda gobe inshallah zan Samo miki number d'inta amam gaskiya ayanzu bansan Ina take ba”da sauri hajiya saleemeh ta furta“yauwa hajiya murja nagode Allah yabar zumunci saina jiki”daga haka suka yanke wayar da fatan Allah yasa dai Sami hajiya zainab d'innan
Alhaji Hassan ne ya dubi matarsa wadda itama ta bashi hankalinta Dan abinda yake Shirin Gaya Mata tabbas me muhimmanci be
“Abinda na Tara gidan ABDURRASHID ya girmi tunanina can you imagine wai yarinya d'aya suke so shida Adnan gaba d'aya abin ya girmi tunanina”
“ikon Allah ”matar tasa ta furta cike da mamaki sannanta Dora da fad'in “yanzu shi tayaya zai so abinda dansa yake so fisabilillahi kayi hakuri Amma kaninnan naka baya kyautawa wallahi sam”tayi maganar cikin fushi da bacin Rai, murmushi alhaji hassana yayi kafin yace“nima hakan naji abinda kika hi yanzu bayin hajiya saleemeh ta shaida min abinda ya faru a waya, Amma kinsan me”girgida Kai tayi had'e da fad'in “saika fad'a”cikin murmushi yace“natambayeshi dalilin dayasa yakeson yarinyar Amma abinda yafadan sainaji Ina goyan bayansa”damamaki matar tasa tace“kaikuwa mezai fad'a maka da har zaka goyi bayansa fisabilliahi alhaji”wani Saban murmushi yayi tare da fad'in “kema kanki zaki ji dad'in abinda zan fad'a domin abdurrashid da kansa yake shaida min cewa yarinyar kama take mai da fatima ”cikin dafe kirji matar tasa tace“fatima kuma alhaji yanzu shi yafadi sunan Fatima da bakinsa ” cikin tsantsar farin ciki Alhaji Hassan yake maganar Dan iya fuskarsa zata tabbatar maka da hakan“wallahi abinda mukai dashi kenan shiyasa nafi goyan bayansa fiye da Adnan domin wata kila hakan da Allah yayi wata gaskiya ce take so ta bayyana”cikin d'aga hannu matar tasa tace“Allah na gode maka inshallah Allah zai fito da gaskiyar damuke jira shekara da shekaru hakika na goyi bayan abdurrashid sosai akan wannan Al amarin tabba alhaji kaiyafi dacewa kasami Adnan kabashi hakurin ya hakura da yarinyar ya barwa mahaifinsa”shiru yayi kafin yace “um um bahaka ne zai faru ba mudai zuba ido mucigaba da addua Allah zai kawo mafita”
“Amin ”matar tasa ta furta had'e da Mi'kewa tana Kara jinjina abin da alhaji Hassan ya sanar Mata
Kamar Wasa haka soyayya me karfi ta kullu tsakanin Sabrine da Adnan Amma ba tare da ita Sabrine ta sanda son Adnan take aganinta kawai Yana burgeta ta ne , and he's so nice, shine dalilin dayasa ma taji tana son dawowa school Dan harga Allah Tama manta relationship d'in dake tsakanin Adnan da LEC A. M gaba daya , Adnan ya mantar da ita komi , abin har mamaki yake bawa Granny especially taji ma Sabrine tace zata koma makaranta , abin yayiwa Granny dad'i sosai tayi adduar Allah yasa haka ne mafi alkhari tsakanin ta da Adnan Dan harga Allah Adnan yashiga zuciyar Granny sosai
Adaren ranar da Sabrine ta dawo school Bata sanarwa Adnan da wowarta ba dan tabbas da saiya zo, washegari da safe wurin karfe Tara na safe wayar Sabrine ta d'au ringing daidai lokacin tana wanka hakan yasa har Kiran ya katse , jin Kira ya sake shigowa yasa Latipha kallan wayar ganin an rubuta Adnan yasa Tai murmushi had'e d'aukan wayar Tai picking call d'in, cikin shagwaba Adnan yace“ Sabrine konayi Miki lefi ne pls am sorry amma karki hukunta ni ta hanyar 'kin d'aukan waya ta inba haka ba yanzu ki ganni a kaduna”ya Kare maganar da wata sexy voice , dariya Latipha Tayi tare da fad'in“ai bama saikasha wahalar zuwa kaduna ba kawai ka taho school”jin muryar Latipha Adnan yad'an zaro ido had'e da fad'in “latipha you mean sabriny ta dawo school”
“eh mana”latipha ta katse shi, sannan ta Dora da fad'in “ don't tell me Bata fad'a maka ta dawo ba”
“yeah is okay thanks for this wonderful news, idan ta fito kice Mata I will come anjima”
“yeah sure”ta fad'a tana kashe wayar daidai lokacin Sabrine ta fito daure da towel tana goge jikinta tace “who call? Granny d'itace ko”harararta Latipha tayi tare da fad'in “a'a wannan kam darling d'inki ne”
“darling ”Sabrine ta furta tana kallon Latipha
“idan baki yarda ba saiki duba ai”aikam da sauri Sabrine tazo ta kar'bi wayar hannun Latipha tana dubawa , “and yace he is coming anjima” Latipha Tayi maganar tana shigewa bandakin Dan itama wanka zatai suna da lecture
“what you mean kin fad'a masa na dawo”daga bandakin Latipha tace“an fad'a d'in anaso ana kaiwa kasuwa , idan LEC A. M d'in kikeso ai saiki bayani”
Dafe Kai Sabrine tayi had'e da fad'in nikam shurutunki Latipha wani sa'in beyi ba wallahi yanzu kinsa ni amatsala
Ta fad'a tana ajiye wayar tana d'auko Mai ta shafa,
Har suka gama shiryawa ita da Latipha Sabrine na mita akan Bata kyauta Mata ba itakuwa Latipha ko ajikinta dariya ma takeyi,ahanya ne Sabrine take tambayar Latipha meyasa ita Bata kula kowa Amma ita ta dage Dole saita saurari Adnan
Dariya Latipha Tayi kafin tacewa Sabrine
“sabrine kenan ,saboda banaso kishiga halin danashiga ss
Sabrine wallahi rayuwar nan kullum Kara tsada take samun miji nagari kullum wahala yake Sabrine wallahi ayanzu duk wacce tasamu miji indai me nagarta ne gwara tayi auren ,shine dalilin dayasa kikaga na takura Miki akan Adnan”dakatawa Sabrine Tai da tafiya tare da fad'in “latipha tell me what's too special da Adnan ke dashi”dafa kafad'ar Sabrine Tai tare da fad'in “wallahi Tako Ina Adnan mutumin kirji ne kodan yadda yake binki Sabrine zakisan hakan ki duba yadda yawan Yan Mata suke wadanda ko kansu zasu iya bashi Amma Dole ke yakeso, kuma Nina fad'a Miki zakizo ki bani labari for sure”tana fad'ar hakan ta kama hannun Sabrine suka karasa lecture hall d'insu,tun kafin su karasa shiga Sabrine ta hango LEC A.M takan iya ganin yadda du ya rame,jitai tausayinsa ya kamata , sa'banin yadda Sabrine Bata iya zama Abaya sai agaba ,Amma wannan Karan can baya ta nema ta zauna Dan sotake ta bawa kanta distance da LEC A.M ko hakan zai zama mafita gareshi ya Dena santa,
Yadda LEC A.M yaga Sabrine tayi hakan ya tabbatar masa cewa Sabrine gudunsa take ,gaba d'aya jiyayi ya kasa lecture d'in Amma haka ya tilastawa kansa yadinga Yi cikin salo yadda dalibai zasu game
Karfe biyu suka fito daga lecture d'in tacan kofar baya Sabrine ta fita tana jiran Latipha da fito,Amma tananan tsaye taga LEC A.M ya tun karo inda take tsaye zuciyarta ce ta fara dukan uku uku, kirjinta ya dinga bugawa da sauri ta juya ta fara tafiya ahankali kamar wadda kwai ya fashewa Amma ta tsinci muryar LEC A.M ya furta
“Sabrine ”tsayawa da tafiyar Sabrine Tai Amma ta kasa juyowa ,ahaka yazo ya sameta har gabanta yaja ya tsaya ,kanta a'kasa gaba daya takasa d'agowa hannunta har rawa take ta kasa holding littafan sosai……
*Marasa comments dakaina zanyi remove inshallah*