Free chapter · Read without an account
Chapter 7
*🌈😂 KWAILA CE😂🌈*
*PAGE SEVEN*
_Idan anga errors matsalar keyboard ne😂_
"Gemu??"
Sunan da Zannur ya faɗa a ransa kenan yana ƙara ware manyan idanunsa akan ta,
Wanda yake ƙara hango Zallar kamar dake kwance tsakaninta da his Sunainerh ɗinsa.
Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali tare da Lumshe idanunsa yana jin wani abu mai kama da fargaba na ratsa masa zuciya.
Mene yasa take kama da Sunainerh matarsa wacce ya rabu da ita a lokacin da yafi buƙatar ta??? Tabbas wannan zai iya cewa Sunainerh ce, amma mene ya sanya ta zama haka?
Sunainerh classes lady ce, tana da tsayi da jiki and baƙa ce like Salame,
Amma mene yasa komai nasu ya zama ɗaya ne???
Yayi tambayar a zuciyarsa yana mai fesar da iska daga cikin bakinsa.
Salame ganin kallon da yake mata ne yasa tayi dariya har sai da dimples ɗinta suka loma kafin ta nuna sa da hannu tace.
"Wallahi Malam gemun nan kamar na ɗan taure, kai amma dai inyamurai ne suka haifeka ko? Haba ko inci kalli fuskar ka kamar an silala karas"
Ta faɗa tare da kwashe wa da wata dariyar har tana sakin tusa.
Da sauri Zannur ya runtse idanunsa yana jin zucyarsa na harbawa da ƙarfi cikin zucyarsa yace.
"Ya Rabbi, komai iri ɗaya, smile, dimples, teeths gave everything irin na My Sunainerh, Uhm!"
Ya faɗa a ransa yana mai cije lips ɗinsa, a hankali ya sauke heart berth, ganin yadda yarinya take zautar masa da tunani ne yasa ya shareta tare da juyawa yaci gaba da handwriting ɗin da yake, inda yake masu Spelling na kalmomi.
A hankali Salame ta miƙe tsaye ta shiga tafiya saɗaf saɗaf kamar ɓarauniya, cikin sanɗa ta ƙarasa bayan Zannur kafin a hankali ta miƙa hannunta ji kake caraf ta damƙe gemun Zannur.
Da wani irin sauri Zannur ya runtse idanunsa idanunsa saboda har tsakiyar kansa sai da yaji zafin fisgar gemun nasa da tayi.
"Ihuuuuu laushi, wallahi daɗin taɓa wa"
Ta faɗa tana ƙara matse gemun Zannur a hannunta.
Zafin da yayi masa yawa ne kuma ya sanya shi yadda allin hannunsa.
Da wani irin sauri ya juya tare dasa hannu ya kwashe Salame da wani irin gigitaccen mari.
Idanunsa har wani ruwan bala'i suke kawowa, jikinsa ya ɗauki rawa, saboda a all his life ɗin sa babu wanda ya taɓa yi masa haka sai ita.
Cikin jin bugun haushin yarinyar ya kalleta tare da faɗin.
"Stupid gal, mumu, empty head da idanu irin na Aljanu"
Salame kam yau duk rashin kunyar ta sai da tayi shiru ta zubawa Zannur idanu, a ranta take ayyana irin abinda zatai masa.
Lokaci guda kuma idanunta yayi jajirrr, Jikinta ya shiga rawa Banda kallon Zannur babu abinda take.
Siririn tsaki Zannur yaja yana mai sanya hannunsa tare da kaɗe gemun nasa, kai tsaye kuma waje yayi yana faɗin..
"Mayya"
Ya faɗa yana sauke Ajjiyar zuciya, ga wani irin halbawa da zuciyarsa ke masa, har yanzu mamaki da kuma ta'ajjuji bai sake sa ba.
Yana fita wajan famfo ya nufa ya wanke hannunsa da fuskarsa tass, wacce Lokaci guda tayi jajurr saboda damuwa da kuma baƙin cikin abinda Salame tayi masa.
Yana gama wanke fuska ya nufi cikin office yana tafe yana sauke tagwayen ajjiyar zuciya idanunsa yayi jajurr saboda rashin sabo da hayaniya, ga kuma yunwar dake damunsa har yanzu bai saki ransa yaci abincin garin yadda ya kamata ba.
Yana fita Salame ta kwanta a wajan tana birgima tare da ihu kafin a hankali ta saki fitsari tana faɗin.
"Wallahi ƙarya kake, duk gidan mu babu mayo, to ba gwamma maita ba da inyamurin mutum fuska kamar an silala karas, Wayyoooo Allah na shiga uku na lalace ya kashe min ɗan ciki na"
Ta ƙare maganar tana riƙe ciki tare da sakin wani gigitaccen ihu na zallar makirci.
Haka tai ta ihu har aka tashi tare da ɗaukan Al'ƙawarin rama abinda Zannur yayi mata.
A hanya kowa duk wanda ta gani sai ta tsokane sa, idan abinci ne kowa sai ta kwasa ta ɗiba da gudu.
Misalin 5 na yamma
Zannur ne zaune a shagonsa yana sanye da wata jersey tank top mai kyau wacce take ɗauke da hula,
Sai white bluetooth dake maƙala a kunansa, a hankali ya dannawa Ummi vedio call.
Cikin Sa'a ringing ɗin farko ta ɗaga a hankali ta sauke idanunta akan fuskar Zannur wacce lokacin guda kuma ta faɗa.
Cikin damuwa da kuma son ɗan nata da yayi mata yawa a zuciya tace.
"Babana yaya akai ne? Meke damunka? Baka cin abinci ko?"
Girgiza mata kai yayi yana ɗan ware idanunsa kafin ya buɗe bakinsa yace.
"Ummi naga My Sunainerh"
Da sauri Ummi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirji tace.
"Sunainerh?? Babana kana da hankali kowa? A ina za kaga Sunainerh??? Macan data ɓata a Cairo mene zai kawo ta nan?"
Ta faɗi hakan cike da kiɗima, kwaɓe fuska Zannur yayi kafin yace.
"Allah Ummi believe me naga My Sunainerh I saw her"
Ya faɗa idanunsa na tara ruwa, saboda ji yake son matar nasa ya dawo masa Sabo, tunda ya rabu da ita har yanzu bai samu kansa dai-dai ba, he's nothing without her gaba ɗaya rayuwar babu daɗi, he can't live without her amma idan ƙaddarar sa ne haka dole ya rayu babu Sunainerh, amma a karo na biyu ba zai saken da zai rabo da ita ba.
Girgiza kai Ummi tayi idanunta na kawo ruwa lokaci guda kafin tace.
"You're crazy Babana, how can that happen????? Eheee?"
Ta faɗa Muryarta na rawa kamar zata saki Kuka, Abba dake gefenta ne ya sanya hannunsa ya amshi wayar hannunta.
Kafin ya kalli ɗan nasa yace.
"Babanmu me kake cewa? What are you saying? Da gaske kaga Sunainerh? When? And a ina ka ganta explain to me"
Ya faɗa a nutse tare da sanya hannunsa ya jawo Ummi jikinsa ya bata hug side saboda yadda yaga hawaye na zuba a idanunta.
Zannur Ajjiyar zuciya ya sauke saboda bazai iya bayanin abinda yake ransa ba, ba lallai su fahimci halin da yake ciki ba.
Cikin nutsuwa Zannur ya faɗawa Abban nasa komai kafin ya ɗura da faɗin.
"Abba bari kaga picture ɗin da nayi mata, wallahi Itace My Sunainerh believe ni ban haukace ba, and Tayaya zan zama crazy akan village gal ɗin da ban sani ba, Tabbas Sunainerh ce wani abu ne wanda ban san ko mene ba ya sauya min ita"
Ya faɗa yana latsa ɗaya wayar nasa, nan take ya nuna masu picture ɗin Salame, wata iriyar zabura Ummi tayi shi kansa Abba idanunsa wanda yake iri guda dana Zannur ya ware, tsananin kamannin Salame da Sunainerh har ya ɓaci.
Ajjiyar zuciya Abba ya sauke cikin samun nutsuwa yace.
"Babana akwai ruwa kusa dakai??"
Kai kawai Zannur ya ɗaga masa dan baya jin zai iya magana.
"Ohhhyahhh drink"
Bottle of water ɗin ya ɗauka tare da ɓalle murfin ya manna a bakinsa a hankali kuma ya fara shan ruwa yana sha yana sauke ajjiyar,yana gamawa ya ajjiye gorar ruwan a hankali kuma yace.
"Abba na sha"
Jinjina kai Abba yayi kafin yace.
"How do you feel??"
Yana langwaɓar da kansa gefe guda yace.
"Better Abba,amma zuciya na ciwo i love my wife Abba, i love her to the rest of my lifeeeee"
Abba ne ya ɗan gyara tsaiwarsa yace.
"Wannan ba Sunainerh bace, kama ce kawai tayi yawa, kamar da idan ba Identical twins, babu yadda za'ai a samu Zallar kama tsakanin Sunainerh da wannan Yarinyar, something is feshin Babana, amma kada ka damu kanka wannan yarinyar babu tawadar Allah a fuskarta amma Sunainerh nada ita, amma a kwai mafita"
Da sauri Zannur yace.
"Amma ta mece gaya min please"
Murmushi Abba yayi yace "If you really love your wife then you can love this gal ma ai, go to her BI ABINDA ZUCIYA KESO shine samun nutsuwa, love her my friend koda ta kasance *TSINTACCIYA*(new novel Kada ko bari ya huce ku 300 kacal) ce bawa zuciyarka abinda take so shine samun sauƙi, amma kaje kayi tunani zan kiraka gobe bye friend"
A hankali Zannur ya buɗe bakinsa yace.
"Ok bye friend love you"
Yana faɗin hakan ya kashe wayar a hankali ya miƙe tsaye ya fita daga shagon domin yin wanka.
Yana fitowa Salame na kawo kai sam bai lura da ita ba hakan yasa cikin nutsuwa ya shiga Banɗakin ya kulle.
Salame ce ta kalli Saude cikin raɗa tace.
"Aikin Lada ya samu Saude zo muje"
Saude da bata Fahimci komai ba tace.
"Ina zamu kuma bayan gidan Mai gari Inna ta aike mu"
"Uhm ranar ramuwa ce tazo ai kinga can wajan"
Ta faɗa tana nuna mata wajan wasu tarin ƙadangaro da suke cin abinci ya wancin su kuma jan gwalagwada ne kafin tace.
"Guda biyar zamu kwasu ki ɗauki biyu na ɗauki uku"
Jinjina kai Saude tayi kafin tace "Amma mene zaki dasu??"
Dariya Salame tayi sosai kafin tace "wallahi kamar yadda ya sani fitsari shima yau sai yayi😂😂.
Wallahi idan ba share ba comments na daina team Zannur kuna ina???? Yau ka shiga uku🤚🏾😂✋🏾