Free chapter · Read without an account

Kai ka jawa kanka Chapter 6

by Ikilima Adam · KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka 6

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah


Page 6


Rike hannun nusy t'ai zasu fita 'yariko hannun fatima yai mata mgn kamar Haka ina fatan kinji dadin daren jiya.



Murmushi ta sakar masa tareda kwace hannun ta 'tai gaba tawuce sashin umma.


Kiran aminu yai awaya yace Kai dan iska shawarar dakaban Akan fatima da khalid yana tafiya daidai ' aminu ya bushe da dariya yace angayamaka nidin Wasa ne , kaide ai shaani kawai amma kasan me?


Khalid yace A'a ina tausayin ka .


Saboda ace Macé iya Macé kamar fatima wadda ta hada komai da komai , ace zumar ta bakaine zaka lasa ba asshh ansha dakai.


Ranka Khalid yagama baci ,nan take yaji kishin sa ya taso daurewa yai yace to ai tsaron lalura so kake in barta wataran tabar gidan bansani 'gwara ayi tuwo n'a maina

Dan iska sai anjima

.


Fatima rike da hannun nusy sukai bangaren umma 'ta same ta zaune ,Aisha n'a gasa mata kumburin da fuskan yai .


Aisha ta kalli Fatima cikin sakin fuska tace anti inakwana '


Lfykalau alhmdulillah fatima ta bata amsa ya maijiki .

.

Dasauki 'anti harkun fito Kenan zakije Kai nusy boko.


Tace eh naga Time yakusa .gaban umma takaraso taduka ta gaisheta a ladabce '


Lfykalau alhmdulillah fatima naji sauki ' kallon nusy t'ai taji tausayin yarinyar n'a kamata' .


Sha kan nusy t'ai tareda masu fatan adawo lfy.


Hartakai bakin kofa 'aisha tace anti dan Allah in zakije dauko nusy boko zamuje tare saboda zanje siyayya supermarket aljazira .


Tom babu matsala indo Allah yakaimu.

Dan bata fuska Aisha t'ai tace nidai nace muku banson kunace min indo sunan fa 'tsoffafi ne '


Umma t'ai dariya tace saiki gayawa uban naki daya samiki 'sunan uwar sa.


Da dariya fatima tabar dakin dan bata fiye surutu ba.



Ahanzarce tadau mota 'mai gadi ya bude mata Gate 'bata zarce ko'ina ba , sai makaranta su ,nusy


Sauko daga mota t'ai tareda mata rakiya har kofar Shiga .


Mai gadin makarantar sai washe baki yake 'yace amma hajiya wannan diyar taki kuna kama sossai.


Nagode tacemishi ataikace tareda juya akalar motar ta '


Abunda ta hango a wani motar dake kusa dasu ya girgiza mata tunani .


Alhaji nura rufe idanun ta 'tai tare da kara bude su,kodai ba daidai take ganiba ,again dai shidin ta hango .


Cikin mota rungume da wata classemat din ta 'Alisa.



Innalilahi wa'inna ilai rajun tashiga maimaita wa 'tsayar da motar t'ai.


Yai daidai da fitan alhaji nura daga motar abokiyar alfashar sa.


Ahanzarce take tafiya harta tuntube babu Wanda taji taba tausayi lokaci daya 'sai inna Farida.


Alisa ! Alisa! Alisa.


Arazane ta juyo dan ganin wacce ke mata wannan uban Kira.


Kallon kallon suka fara yiwa juna.



Alisa zare idanun ta t'ai tace daman fatima kina kasar nan 'naji ance kinyi aure.


Daidaita nutsuwarta t'ai tace eh fa nayi aure , kefa kinyi aurenne tana tsareta da idanu.


Numfasawa t'ai tace 'aa aini aure ba yanzu ba dan saina gama da wancen dan iskan surukin sani yaro.



Kinsan me fatima ta girgiza Kai 'wlh wancen mutum nan da kike gani yana tafiya tana nuna wa fatima motar shi'''


Eh inajinki Alisa .


Numfasa tai tareda gyara tsayuwar ta jikin motar ta.



Yamin alkawarin ze aure ni kuma yace min beda mata, yabari nagama sakan kancewa dashi fatima,duk nakori masoya n'a , Wanda keso n'a da aure ,saida tafiya t'ai tafiya yace min , shifa beyarda dani ba .

Nacemishi kamar ya ?


Shine yake cemin wai so yake ya tabbatar bantaba sanin da namiji ba inbahakaba baze aure ni ba.


Nashiga tashin hankali fa ' dan n'a mugun kamuwa da son shi a lokacin 'kullum maganar da yakemin Kenan in bashi kaina sbd ni yar jami'a ce beson ya aureni ban cika Macé ba' ya sakeni ba girman sa bane.

Harga Allah nadauka dagaske yakeyi saboda yanda yaketa 'kiran sunan Allah abaki' daga karshe n'a sallama mishi kaina.


Rintse idanun ta ,fatima t'ai tanamai tausayawa Alisa.


Alisa ta kara da cewa tunda yasamu ya kusanceni yace ai alhamdulillah ni kamila ce 'inyagama abunda yake ,ze turo manya ,Alhaji nura kullum sai ya maidani kaman. Karuwar sa babu rana ta banza da bezo ya daukeni munyi lalata ba 'tun inajin banson abun 'har abun yafaramin dadi.


Muna cikin Haka nasamu ,ciki ina fadamai yace indai bincika saida nai masa dagaske n'a nuna masa zankai karar sa ,kotu sannan yace saide azubar da cikin 'hawaye shar a idanunta .


Ya cire min ciki wajen sau uku 'na karshen ne likita ya tabbatar min da bazan kara haihuwa ba saboda yawan cire cikin yataba mahaifata .


N'a sanar dashi 'yace min aishi wannan ba matsala bane ba haihuwa bane gabansa ya kwantar min da hankali 'nima nacire wani tunani araina.


Kwasam rana daya nazo super market nagan shi da wata yar yarinya da bazata wuce 16yrs ba haka' rike da hannun sa



Yana da dariya suna hira' gabana ne ya tsananta bugawa nace to mezeyi da yar karama yarinya Haka dan sam ban lura da kamannin da sukeyi da itaba.


Gaban sa nasha nace 'ranka yadade kwana biyu Inna kiraka baka dagawa 'shan kunu yai kaman betaba dariya ba 'yace min baiwar Allah lfy kuwa.


Hankalina yai mugun tashi nace alh nura, nice kake cewa bakasanni ba.


Yarinyar da suke tare naga tanamun kallon tuhuma 'ta kalleshi tace daddy wai wacece wannan .


Bansanta ba, shine amsar da ya bata .


Tsaki taja yarinyar tace mun kawai kuga ya da uba suna tafiya kita bin mu' sorry daddy be bukatan Karin aure fuuu taja hannun dadyn ta suka bar wajen.


Wallahi fatima 'sati n'a biyu kwance ban lfy tun daga ranar ' nafara bincike akansa har nagono surukin SANi yaro ne.


Har kofar gidan sani yaro naje kwanaki nasa Aka kiramin shi.

Yana ganina ya razana 'daukata yai a motar sa 'mukabar unguwar ,cikin lallashina yaita yi yace wallahi Alisa inaso auren ki ,banso boye miki inada mata , nasan bazaa Bari inkara aure ba' nan naringa zagin sa macuci azzalumi 'wallahi sai Allah ya saka min .

Haka dai yake zuwa wajena tun banyarda harna soma biye masa kamar yau dinnan da kika ganmu 'nayi alkawarin saina ruguza masa rayuwar sa 'sai yazama abun tausayi.


Fatima numfasawa t'ai 'cikin kaduwa da zancen ta ' tace amma Alisa kin tafka babban kuskure koda yake ai yariga da yafaru .


Bangaren haihuwar da akace bazaki taba samu 'inshaAllah zan taimaka miki 'tareda dafata 'suna kallon juna ido cikin ido.


Alisa inason kimun alkawari bazaki kara kulashi ba, abunda yai miki tabbas zamu dau fansa 'inason kirike darajar ki 'na ya mace.

Kallon agogon hannunta t'ai ,tace Alisa zan tafi saboda surukata ba lafiya amma ai zamuyi waya.


Karanto mun lambar ki .


Bata number t'ai fatima t'ai save 'Alisa tace waini baki gayamin unguwar da kike aure ba.


Murmushi fatima t'ai 'tace ai dan sani yaro nake aure.

Wanne daga ciki .


Kinsan akwai Khalid izza


Yusuf mai gaskiya


Deen dan kanin sa ne akace amma yazama danshi tunda hannun sa yake.


Dariya fatima t'ai saida fararen hakoran ta 'suka bayyana tace.


Inaga izzah shine mijina .


Wow amma fa wlh kinyi saa wannan hadadden gayen ,mai kama da larabawa ,gashi ya hadu da Macé daidai class din sa irinki.


Uhmmm Fatima tace .


Nidai zantafi saimunyi waya sallama sukai Alisa taimata godiya sossai Akan shawarwarin data bata.


Shamsu n'a hango bakin Gate din makarantar nusy Wanda a kullum saiya zo yatsaya yai ta kallon yarinyar yana kuka 'ahaka yakoma gidan nasu.


Maryam' da Inna l'ami ne zaune suna dama fura da nono 'itakuma ummu 'tun dazu take fama da wutar gawayi yaki kamawa hayaki duk yacika wajen 'sai rurrufe idanun su sukeyi.


Maryam tace me zehana aba baba ado yasiyo mana kalanzir tahada mana wutar nan nidai wlh yunwa nakeji.


Inna l'ami tace naga ai wannan furan zedan rage mana yunwa shiyasa muke damawa .


To ai Maza a dama cewar ummu .


Shamsu ne yakaraso wajen yazauna dirshan 'cikin gajiya yace wlh yau ma dai wlh banyi nasarar sato yarinyar nan ba 'saboda marikiyarta inta kawota bata wuce wa 'sai taga shigarta Haka kuma intazo daukanta 'wallahi tana wajen Zaman jira fitowar ta .


Ummu tace shikenan anrabani da ya ta shamsu'cikin kuka take magana yau shekaru nawa Kenan da rabon in sa yata a idanu n'a.


Kiyi hakuri ummu duk tsanani yana tare da Sauki karki manta fa 'nima fa ubanta ne.


Amma nasan tana samun kulawa sossai agidan 'musamman inkikai duba da umma.


Mikewa tsaye ummu t'ai fuskarta alamun babu Wasa aciki take magana kamar Haka.


Sai yaushe zamu daina boye kanshi shekaru n'a shudewa kawai mu fito ,mu nuna wa duniya muna raye 'ace yata banda ikon ganinta iyayena ,ma Haka.


Dafata shamsu yai 'yace kiyi hakuri fitowar adaidai lokacin ne barazane ga rayuwar mu 'harda n'a iyayen mu 'na tabbatar bazaki so akanki akashe iyayenki ba' yana dubanta .


Girgiza kanta tai'


Yace pls dan Allah kidan kara hakuri komai yakusa zuwa karshe.


Inna l'ami 'tace nagama dama furar kuzo kusha amma dai yau da daddare nakeson kuban tarihin rayuwar ku 'tana bata rai .


Maryam ' da ummu suka kwabe baki 'ahhh sannu Inna l'ami ai mun gayamiki sai nusaiba tazo garemu zamu baki labari.


Shamsu yai dariya yace Inna karki damu anjima dakaina zan baki labarin 'asalin mu 'suwaye insha Allah Yauwwa yanzu naji magana amma wayannan masu bakin jemagu kullum sai Jamin rai suke.


Ummu da Maryam suka tafa hannu wai mune masu bakin jemagu mungode Inna kedai 'kira mana mijin ki 'yataimaka yasiyo mana kalanzir kinsan dai ba fita muke ba.


Kwafa t'ai tace kwaji dashi acici mala'ikun tauna.


.......


Direct fatima gida ta 'nufa a farfajiyar gidan ta hango Aisha da isma'il 'suna hango ta suka nufo ta.


Ismail yace inawuni anti ta amsa masa fuska asake lfylau alhamdulillah


Aisha tace harkin dawo eh nadan hadu da wata kawata ne acen shine muka dan tsaya firan yaushe gamo 'batareda ta tsaya ba tawuce ciki tabarsu..


Isma'il yace Aisha banta samun Macé da kesona irinki duba da irin yanayin gidan Ku matsayin ubanki akasar nan.


Amma kike min biyayya 'sanadin yi biyayya kikai accident hankalin Yan gidan mu 'duka yatashi bazan gaji da baki hakuri ba' sorry am sorry sauraniyan mata 'mahaifina sunce ana nema musu izini zasu zo 'neman auren ki.


Ranan jumaa nan take annurin dake kan fuskar Aisha yadauke , hawaye take shar idanunta.


Mamaki ne yakama Ismail yace maganganuna Sun bata miki rai ne 'ta girgiza kai alamun 'aa


Dakyar ta iya furtawa Allah yakaimu zan sanar 'nizan shige kaine ke ciwo.


Subuhanallah shine baki gayamin ba masoyiya muje inkaiki pharmacy .



Aa kabar shi inada magunguna aciki zansha daga Haka ta fice tabar shi nan 'yana ganin tawuce cike da tausayin ta da sonta dake karara ruruwa acikin zuciyar shi yaja motar sa yabar gidan.



Kowa n'a falo zaune 'har umma da sumayya ta taimaka 'mata takawo ta falon .


Inna Farida tace ke indo lafiyar ki 'kike kuka Haka 'kowa gidan yakai Duban sa akanta.


Bakomai tabasu amsa tareda wucewa side dinta.


Inna Farida tace nidai Allah yanunamin auren nan naku 'aisha keda sumayya .


Sumayya tace au hardani nidai bankai aure ba tana turo baki gaba.


Fatima ta amshi zancen da cewa au baki Kai aure ba ko?


Kai ta gyada mata 'tace Toni zankira yusuf in sanar masa indai yasamu wata a maiduguri yai auren sa.


Gab gab gab Haka sumayya taji zancen ya Doki zuciyar ta 'tace uhmmm anti Fatima karmuyi Haka dake kinfa san halin sa .miskilin mutum ne saiya dauka serieuse kike .


Au daman nacemiki da Wasa zan mai magana kedai kice inkira shi kisha mamaki.


Afuwan anti babba tashi t'ai tareda rufe idanun ta 'tai hanyar dakin su .


Fatima dawo ga dubanta Akan Inna l'ami d umma dasuke hira t'ai.


Gabadaya jikinta yagama yin sanyi 'tausayin Inna l'ami ne kawai yacika mata zuciyarta dayan bangaren kuma tausayin Alisa takeji ' murmushi t'ai da ita kadai tasan ma'anar shi tace azuciyar ta 'inshaAllah ni fatima saina koya maka hankali nura.


Mike wa 'tai tace umma zanje indan kwanta 'balaraba n'a kitchen tana dafa mana abinci kafun ta gama zan fito.


Da to suka bita.itako t'ai hanyar dakin su.


Inna l'ami ta fuskan ci 'umma tace meze Hana kikai nusaiba 'koda sau daya ne taga mahaifiyar ta.


Numfasawa t'ai tace wallahi burina Kenan kinsan maigidan nan bé 'barina fita kwata kwata be yarda dani ba 'dole inzan fita sai anhadani da boduygad kema kinsan haka'


Eh nasani 'amma dai ...


Sallamar Deeen ne yakatse mu firan oyoyo Dana saiyanzu kafito tun safe .


Eh wlh ban dan jin dadine.


Idanu umma ta zaro.shine babu Wanda kagayawa .


No karku damu 'ainasha magani 'shafa cikinsa yai tareda zama kan dinner table 'pls umma yunwa nake ji.


Inna Farida zuba masa idanu t'ai 'talura a Yan kwanankin nan beda nutsuwa gashi harya dan rame .


Murmushi t'ai tace wai deen wannan ramar dakai fa .


Kwarewa yai .

Suka hada baki wajen cemasa sannu .

Yaww a yabasu amsa.


Yace Inna nifa bawani rama 'to kumin aure indai kunason inyi kiba.


Umma da Inna l'ami suka kalli juna 'sukai dariya lallaima yaron kace wani Abu. To ina Yan matan naka da kuke tsarawa karyan aure kaida abokin ka.


Turo baki yai kaman zeyi kuka.


Nifa banda lokacin kulasu Yan matan Sun cika iyayin tsiya .


Balaraba ce dauke da dan maidaidai cin tray hannun ta 'indomi ta dafa masa 'kancewa umma t'ai mata magana.


Tana ajiye wa ta fice daga falon tareda yiwa su umma sannu da hutawa.


Kallon abincin yake ransa abace 'yace wannan ai abincin carton ne zaa dafa min yana kokarin tashi.


Caraf 'inna l'ami tarike hannun sa tace Allah baba n'a saikaci 'kenan mu carton ne da muke ci.


Muryan abba suka biyo yana dariya yace haba Dana kadaure Kaci koda kadan ne ai da safe ba abincin carton akaci ba.


Shagwabe fuska yai ' abba saboda Kai zanci abinci nan .to nagode Dana Allah yaimaka Albarka.


Kallon umma yai yaga ta kauda kan ta gefe.


Inna Farida ta gaishe shi aladabe ya amsa mata fuska asake'tareda bin hanyar fita.


Kome ya manta yadawo yace hajiya hassana yajikin naki' dasauki ta amsa masa ciki ciki.


Saina dawo tareda fita daga gidan.


..




11h ne yabuga 'fatima a hanzarce tashiga toilet takarayin wanka 'materiel ta saka mai dankaren kyau yasha adon stone.


Murza hoda t'ai cikin sassarfa ta sauko kasa 'direct dakin aisha 'ta nufa.


Iske ta t'ai zaune tace pls Maza taso muje kinsan banason inyi latti wajen dauko nusy '


To muje anti 'aisha tabata amsa tareda dauko gyalenta.



Daf da fita falon bata ankare ba ,saidai taji ta fada jikin mutum.


Ya salam ya furta zazzare idanu take tace ayyya sorry Deen yi hakuri ban lura ba.


Karkidamu damu ina zaku je ne Haka?

Zamu je dauko nusy daga nan supermarket zamu siyayya .

Adawo lafiya yabata amsa.


Inda t'ai gaba suka fice itada Aisha.


Deen n'a kallon su har sukabar gidan .


Tunani yakeyi barkatai Akan ta' to ita wannan yarinyar bata iya gane yanayin jikin mijin ta ne '


Barin wani tunani t'ai tareda shida daga ciki.



Fatima t'ai parking gaban makaranta tana jiran atashe su.


Shamsu dake gefe c'en yace kash yauma dai tarigani zuwa.


Wai ita bata latti ne'?yake tambayar kansa


Hango Aisha dayai tareda ita yasa shi soma boye kansa dan tabbas in taganshi zata gane shi.


Aguje fatima taje ta rungumi nusy tanajin son yarinyar acikin ranta.


Mama keda anti aisha kuka zo


Eh tare mukazo Maza shiga mota .


Suna barin makarantar hanyarsu ta zuwa super market 'aisha ta hango wasu yan shaye shaye Sun bugu.


Caraf idanunta yasauka Akan mummunan fuskan da bazata taba manta dashi ba.


Cikin razana da kuka daya tahoma mata tace anty fatima ki tsya kitsaya nace.


Cak fatima taja Burki 'tana kallon ta 'hannun take mata tareda nuna mata Mazan dake c'en gefen titi.


Tace shine .


Shine wa ...fadamin Aisha inajin ki.


Wannan shine mutumin da yai min fyade bakin ta ,n'a rawa cikin kakkarwa .


fatima ta kalli inda Aisha ke nuna mata 'eh ba shakkah watau ma giya yakesha 'hankalin sa kwance 'fiddo wayarta 'aisha kinada nombar sojan nan Ahmed yake ko faruk ? Cikin kuka' Aisha tace Ahmad sunan sa eh inada lambar sa.


Mika mata wayar fatima 'tai tana sa mata nombar takirashi.


Ina wuni inafatan kagane 'me mgana dagacen bangaren yace gaskiya banganeki ba.


Sunana fatima Khalid sani yaro.


Murmushi yai 'yace ranki yadade inawuni dafatan me jiki taji sauki alhmdulillah tabashi amsa 'muna nan tare da ita ahanyar mu ,ta zuwa super market 'mugaka dan iskan nan dayai mata fyaden ,yadawo kasar ne da Dukan alamu 'saboda yanda akai neman ,duniya baa ganshi ba.


Ahmad cikin kaduwa yace kujirani nan inda kuke 'ku gayamin inda zan sameku.


Kasa me mu kan titin makaranta subulus salam zaka ga n'a paka mota ta agefe Daya.


Ok gamunan nan tafe tareda katse Kiran.


Direct Kiran yusuf yai ya sanar masa' yusuf saida ya zubda hawayen farin ciki dan ganin ze hukunta me laifi.


Yace inason 'kaida yaranka kudau mota uku ,kuma kowanne dauke da bindigogi 'case dinnan baa katsina zaai ba..


Direct zaku zo mun dashi maiduguri 'dan yanada cikin ikona .


inshAllah ranka yadade kajira isowar mu.


.........motoci ajere n'a Yan sanda duk kowace motar cike da sojoji jin ance musu umarni ne daga Yusuf jikin su ,Nata Bari 'babu wata lokaci suka bar Barack dinsu .



.....fatima tace Aisha kuka bashi bane maganin damuwar ki'tun ranar da akai miki wannan aika aikan wallahi banda sukuni banason kiyi aure kisamu matsala daga wajen mijin ki 'amma akwai Kaka ta wacce ta haifi mahaifiyata ,zankaiki wajen ta nasan bazata rasa baki abubuwan da zasu kare martabarki koda anyi aurenki inshAllah.


Murmushi Aisha t'ai taji dadin zancen fatima ,rungume ta ,t'ai tanajin kaunar matar yayan ta.


Nagode anti Fatima tun lokacin da wannan abun yafaru dani kin bani kulawa ,fiye da misali



Aa Aisha banmiki komai ba hakkina n'a sauke amatsayin n'a kanwar mijina .



. wayar fatima ne yasoma ring azaton ta soja Ahmed ne 'saitaga khalid ,a tsorace ta daga .


Ke ina kika shiga ne daga dauko nusy shiru baki dawo ba.


Rasa me zata cemasa t'ai 'yasa ta katse wayar .


.......leka bakin titi take tana daga cikin motar ta 'hango motocin sojoji ne yasa ta 'fahimtar sune.


Ahankali ta sauke kafafun ta daga cikin motar ta' glass din ta tadauko tasaka ,tareda nufar inda mashayan suke .


Aisha sai binta da ido take tana fadin gaskiya matar yaya akwai iya taku komai Nata Akan tsari takeyin sa.



Sannun ku ! maganar dasukaji taimusu, Wanda yai wa aisha fyaden , dariya yasoma yace au kaga wannan fa ,wlh zaai da ita , dan ni wlh dan inyi fyade yanzu n'a gwammace mace tabani inci ta dadi ,sauran suka bushe da dariya ,kaide kace bawani sweet gareshi ba fyaden 'yace eh sossai ma .

Duk firan da suke fatima tana record awayarta ,


Murmushi t'ai tace daman shiyasa nakawo kaina ,amma kafun nan inason ka kalli gefen ka.


Dukansu waigowa sukai ganin sojoji Sun musu rumfa ,Sun saita bindigogi su kowanne su fuska da fask mark .


Azabure suka Mike zasu gudu 'carak suka riko su tareda nuna musu duk Wanda yai musu gardama yanzu ze bakunci lahira.


Cikin kaduwa yace wai laifin me mukai muku ne.


Fatima tace Aisha tazo nan ,saigata tazo nuna ta da yatsa t'ai tace ina fatan kasan wannan yarinyar .


Gabansa ne ya tsananta bugawa innalilahi wa'inna ilai rajun yaketa furtawa '


Gaskiya bansan ta .

Tass yaji saukan maruka daga soja Ahmed tareda Bada umarnin asa musu ankwa .


Mota suka jefa su, nan take unguwar yacika da Yan kallo ,kasancewa ma'aikata ne yasa aketa babu hanya suna wuce wa.

Direct maiduguri suka nufa .


Indo ta rungumi fatima tace ganin wannan rana yadan rage kashi goma cikin dari abunda yake damu n'a.


Karki damu kinga mubar zancen zuwa super market ,anjima Ku shirya keda deen yakai ki .


Kinga yayan ki yakirani bansan amsar da zanbashi yasa n'a katse wayar .


Cikin gamsuwa da bayanan ta 'suka bar wajen direct 'gida suka nufa.


Nusy dake bayan mota 'tace mama wai wayannan sojoji ne 'me sukazo yi ne?


Murmushi fatima t'ai tace barayi suka kama 'sannan in dadyn ki ya tambayeki ina muka tsaya kice masa ,muna makaranta Ku kinji ko.


Gyada mata Kai tace tayi tace to mama.



Suna isa gidan a conpound gidan suka iske Khalid da abba ,zaune alamun maganganu masu muhimmanci sukeyi.


Nusy ce ta nufe su aguje tareda rungume abba da khalid 'murmushi suka sakar mata 'abba yace amaryata yau dai kinyi latti ,ina kuka tsaya ne?


Har zata fadi , saita tuno da zancen fatima .

Tace abba makaranta muka tsaya .


Khalid yai murmushi dan yasan amsar data basu 'shirya mata akai.


Oh m'y nusy shiga daga ciki inazuwa kinji gyada masa 'kai tayi tareda nufar cikin gidan su inda tuni Aisha da FATIMA suka wuce suka barta.



Abba yace kacalle be isa ya daga mana hankali ba 'abashi millions dari biyu ,dan uban yai karya bawai kudin ne babu ba.


Nifa banason mutum mai saka idanu Akan harkokin wasu.


Dafa khalid yace yace tunda har yaciga ba da 'damunka da kira'kuma gobe ne wa'adin da kuka diba .


Ni zankira 'MURHU shine kadai zeyi maganin sa 'wallahi goben nan ze mutu.


Dariya suka 'sa abba da khalid tareda Goran ruwan dake kusa dasu suka dauka suka sha 'suna me jin nishadi tunda zasu kawar da KACALLE.



.


fatima ke waya da kawarta safiyya , sai murmushi take yi.


Safiyya tace la namanta ,ban gayamiki ba wannan id cart din salamatu n'a samo miki inda take .


Cikin kaduwa fatima tace wow amma fa taya kika gano inda zan sameta .


Safiyya tace 'wani abokin aikin mu 'yaimun bincike 'amma ya shaidamu Yanzu bata kasar nan da 3 month zata zo 'ganin iyayen ta.


Dan Allah safiyya kar fa amanta duk sanda ta dawo agayamin ,zanje dakaina ' Sun sha hira 'kafun nan ,sukai sallama.



Deen zaune a dakin sa 'babu abunda yake gani a fuskar sa 'sai hoton fatima' ya ilahi ya furta 'numfashi ya fesar 'tareda soma Safa da marwa adakin sa.


Wai meke samu n'a ne ' tun ranar Dana saka idanuna Akan fatima naji 'komai Nata n'a burgeni.


Son nake inji muryan ta 'nan take yafara tuno faduwan ,datai ajikin sa 'dazun 'murmushi yai , yace Fatima Allah yakareki.


Barin wani tunani yai tareda daukar wayar sa ,dan Kiran abokin sa ,ze rakasa tadin gun babyn sa.



.............................



Yusuf Safa da marwa yakeyi kasancewa sunce Sun kusa karasowa, Horn yaji ya tabbatar sune.


Cike da kasaita da cikar haibar sa yake tafiya 'yayinda duk ma'aikata wajen suka take masa baya.


Suna danna hanci motocin su 'cikin Barack din.


Gabadaya gidan ya kacame dan su ,zagaye duka ,motocin .


Babu bata lokaci sojojin suka fara dirowa daga cikin motar .


Tareda masu laifin.




Bindin bindigar su 'suka fara buga musu sbd kallon da suka yusuf yai musu umarnin daya basu n'a idanu Kenan.


Ba gaggauta sai buga musu 'sukeyi ,wani razananne ihu suka saki 'wanda n'a waje saiya jiyosu 'nan take baki da hancin su 'ya fashe yanata zubda jini masu gudaji'.hannu yusuf yai musu' alamun su tsaya.


Cak kowanne su ya koma gefe suna jiran umarnin sa.


Ku shiga dasu 'shine abunda yace tareda kallon sojojin da sukazo 'ku kuma nan zaku kwana gobe da safe saiku kama hanya.



Yana kokarin juyawa 'mai gadi yataho aguje cike da tsoro da kwarjinin sa.


Yace ranka yadade wayannan yan matan nan ' n'a jiya sunkara zuwa again sunce dan Allah kataimaka 'kabasu dama maganar mai muhimmanci ne.


Kallon mai gadin yai yace su sameni a office .


Soja Ahmed n'a biye dashi abaya...



Yana zaune office sai rubuce rubuce yakeyi kan kansa akasa 'soja Ahmed n'a gefen sa'.


Tsaye yana mai kallon abunda yake rubutawa.


Wani murya suka jiyo zazzakar muryan sunyi sallama .


Yusuf bé dago Kai ya kalle su ba ' ya amsa sallama .


Zama sukai suna kallon junan su. Cikin fargaba da tsoro dayan tace ni sunana rukayya kawata kuma Aisha barka da warhaka yallabai .


Yww yace musu yakara dacewa meke tafe daku?


Batareda ya kallesu ba.


Ahmed sai murmushi yakeyi yace wayannan kajin ko daga ina Haka.


Rukayya tace dan Allah yallabai ko wannan dake tsaye kusa dakai zedan bamu waje mu gana.


Sai asanan ne ya dago Kai ya kalle su.


Ya bata rai yace Ku fadi abunda yakawoku nan ba wajen Wasa bane.


Cikin kaduwa rukayya tace ni............






Rukayya tace nidai dan Allah kace wannan yabamu waje, wani kallo ya Wasa mata n'a kishiga taitayin ki take nan taji hanjin cikinta ya kada yabada kuuuuu.


Kwabe baki Ahmad yai yace azuciyar shi kaji wata zalzalan tsiya ,wai infita , A fili yace ranka yadade Bari nadan baku waje ze iya yuwa case din ta babba ne , bejira cewan shi yafita daga waje , Aisha ta take masa baya akabar rukayya itakadai cikin fargaba.


Rubuce rubucen yakeyi , Beko kara kallon inda take ba.


Muryanta yaji yadokin kunnuwan sa , dan Allah sir yusuf inada babban matsala ne shiyasa nazo wajen naka.


Inajinki ?


Kansa akasa ya tsaida rubutun da yakeyi yana jiran ,tafadi matsalar ta.



Wallahi sata akamin , shiyasa nazo wajen ka tana sunne Kai ,kaman wata munafuka.


Kallon ta yakeyi ,n'a wasu dakiku yana nazartan ta,


Indai case din 'sata ne kije police station 'tareda Mike wa tsaye yana hada takardun sa.


Kina iya fita ,n'a sallame ki , haryakai bakin kofa ,yajiyo tace kaine kamun sata

yusuf .



Cak yatsaya kaman an dasashi tsaye 'cike da mamaki yace nikuma namiki sata ya nuna kansa.


Ran sa yariga da yagama baci dan shi beson rainin hankali .


Tsawa ya daka mata ,ke wawiyar inace Zaki kalli tsabar idanuna kice namiki sata.


Wallahi zuciyata kasace ko zaka harbeni saina maimaita ' yusuf inasonka ,inasonka , inasonka wannan shine dalilin baro garin mu, nazo wajen yau kwanan mu biyu agarin ,saiyau nasa mu ganinka .


Mutuwar tsaye yai ,batareda ya kalle ta, yace inkin gama ki ja mun kofa , kinga tafiya ta.



Fita yai yabarta ,tanata kuka ,mai tsuma rai 'aisha tashigo tace ruky aina gayamiki samun soyayyar sa ,ba Abu bane mai Sauki ,kika jajirce muje gashinan yamiki wulakanci.



Rukayya tace ni sam abunda yaimin be bata min rai ba ,asalima jin muryan sa,yana kara sani 'nishadi ,zanso yawuni magana koda ta banza ce hakan Zemin dadi araina.


Sallamar Ahmed ne yasa ,suka Kai dubansu gareshi' tsaresu yai da idanu yace kufito zan rufe office din .


Sannan zanbaki shawara rukayya , tun wuri kinemi mijin aure ,wallahi yusuf beda lokacin mata.


Akwai yarinyar , danaji ance zaa bashi auren ta ,yar uwarsu amma ko ita 'be kulata 'saidai takirashi tagama surutun ta , amsar dayake bata bewuce naji ko bamatsla ba.


Ruky ta Mike tsaye tareda gyara gyalen ta ,tace kaiko baka tunanin ni zan iya canja shi , inada damar yin Haka ta hanyar mahaifina ,dan yusuf n'a mugun jin maganar sa .



Amma nafison in samu soyayyar sa ,kada ya aureni inzama Mara amfani agidan sa.


Dariya Ahmed ya bushe dashi yarinya naki Wasa wallahi komai matsayin mahaifin indai baiyi niya ba ,baze taba auren ki ba.


Ke bara in baki labari , mahaifin sa ,shakkar sa yake ,dan Haka ki canja Salo 'kufito kuna batamun lokaci karyazo ya sameni anan .


fita sukai jiki babu kwari tare barin office din,.


Soja Ahmed yarufe office Kai tsaye wajen yusuf ya nufa,kansa akasa yace ranka yadade narufe.



Garin ne yadau sanyi 'dawani iska dake tasowa 'nan take sama ta hade alamun hadari ne mai karfin gaske zaai.


Yusuf yace 'Ahmed kaga ,mubar nan kan hadarin nan yasame mu.


Kallon su aisha da rukayya yai da suke kokarin fita daga wajen gidan.


Ajiyar zuciya yasauke yace nosens kawai mata babu aji.


Tareda jan motar 'zasubar gidan ,hadari ne yataho gadan gadan da karfin sa, yafito wajen gidan zesakai kai'' soja Ahmad yace yallabai ji Yan matan nan n'a dazun ruwa n'a Dukan su.

Kallon su yake shima 'yace ai matsalar iyaye ne ,subar yayan su kaman kaji suna yawo .



Daidai kusa dasu yazo da motar shi''


Magana yai yace Ku taso Ku shiga in ajiye Ku.


Ahanzarce suka Shiga sai kakkarwa jikin su yakeyi, babu abunda kakeji a motar sai kira'a muryan Sheik Sudais , lumshe idanun su ,sukai suna shakar daddan kamshi ,


Ruky ta kalli aisha 'suna dan murmushi 'sitt kakeji .


Saida suka nisa' ,soja Ahmed yawaiga yana kallon su ta baya ,yace Ku a ina za'a sauke Ku ne.


Harara suka watsa mai ' Aisha tace hotel zaka kaimu dan mu ba yan jahar nan bane.


Gobe da safe zamu juya .


Kwabe baki yai yace au hotel kuka ce fa, ina kuka baro iyayen Ku.


Ruky cikin tsiwa tace 'mun barosu , acikin bakin ka.


Yusuf 'mamaki ne yacika shi , tunda suke magana be ,samu su baki ba , tsaki yaketa jerowa akai akai .


Burki yaja 'ya waigo yace nakusa layin gida n'a zan sauke Ku nan saiku nemi abun hawa yakai Ku hôtel din.


Aisha ta kalle shi ido cikin ido ta fidda tsoro tace haba ,mallam wannan wulakanci da kake mana yai yawa sbd tace tanasonka shine zakaita wulakanta mu.


Haba dan Allah tun shekaran jiya muke garin nan ,dakyar muka samu ganin ka yau, amma babu wani kyakyawar tarba daga gareka, kamo hannun rukayya t'ai tace dan Allah fito muje Mara zuciya kawai.



Ran yusuf yariga da yagama baci iya wuya ahaka yaja motar direct sai gidan sa.


Suna gidan yashiga katoton falon sa.

Ta Alfarma komai

Ban iya misalta muku kyau da tsayuwar gidan.


Aisha sai kallon ruky take tana turo baki sai girgiza take.


Yusuf yai kaman besan tanayiba duk da yana lure da ita.


Hayewa saman kan step sukai shida Ahmed suka barsu tsaye , su basu ce musu Ku zauna ba.


Aisha tace ke ruky wayannan mutanen mugayen yan rainin wayau ne , zomu je mu zauna c'en tana nuna mata kujerun falon.


...........




Deen a makare yadawo gida karfe 9 n'a dare


Kowa yashige cikin dakin sa, direct dakin umma yanufa 'da sallama dauke abakin sa .


Oyoyo Dana ina kashiga ne?


Umma munda fita da abokina ne,


Dafatan Kaci abinci .


Eh naci abinci barci nakeji zanje in kwanta .


Umma ina fatima take ne.


Tana dakin ta ,tundazu ta bashi amsa.


Saida safe yai mata tareda wuce Kai tsaye dakin fatima.


Ahankali yabude kofar hango ta yai tana waya ,tana ta dariya da Dukan alamun firan n'a mata dadi.


Labe yai yanata sauraron zazzakar muryanta duk da besan me take fade ba.


Yakai kusan karfe shada a Labé wajen shibe wuce ba .


Khalid ya iso da mamaki yake kallon sa, kaiko deen mekakeyi anan.


Inajiran t'ai barci ne ,saina shiga .


Khalid yace ok Saïda safe tareda barin wajen .


Ahankali yabude kofar yashiga taku biyu zuwa uku yai yazo gabanta , yana cije labbansa , waini deen kullum saina shigo dakin 'fatima .


Jin ta kamo hannun sa ,tace haba Khalid wai kullum inkashigo saikamun tsaye akai .


Shiru kakeji babu amsa .

Murmushi t'ai tace Bari to in kunna wutar dakin Inga me kake boye wa .


Kokuwa suka soma yi ,yana rike hannun ta 'beson ta kunna .

Aiko tace wallahi tunda baka magana kullum inkashigo yau saikayi.


Tana kunna wutar dakin .


Ta zazzare idanu awaje tareda dafa kirjin ta, cikin murya mai amo da harshen ta yai mata nauyi ta furta Deeen Deeen Deeen .




Zazzare idanu deen yasoma cikin kuka' yace anty fatima dan Allah.....



Tsawa yaji fatima ta dakamai nan take taci kwalar rigarsa tana ihu , deen amana ta zaka ci , ina matar yayar ,Kana neman keta min haddi 'idanun ta Sun kada sunyi jazir kaman wuta , Allah yasa isa tsakanina dakai ,.kuma wallahi saina Kai wajen Khalid yanzu 'tana kokarin jan sa 'yana Jan cikin sa.


Wallahi anti Fatima ki gafarceni banda niyyar akaita alfasha dake .


Tasss yaji saukan maruka guda uku lokaci daya , rike da kuncin sa 'ya dawo kalan tausayi .


Pls anti Fatima kowani irin hukunci kidauka akaina, amma banyarda kikaini wajen Khalid ba.



Shege dan iska, maci amana ,tanata Dukan sa ,da Dukan karfin ta.


Ganin bashine mafita ba 'tafita aguje a dakin ta kulle shi aciki , direct dakin khalid ta nufa.


Karar buga kofa da karfi ya farkar da khalid a razane ' waye ne ya furta cikin muryan me barci.


Daga cen wajen kofar ta amsa da fatima ce kabude kofa cikin ihu take magana .


Ahankali yasauko daga kan gadon sa, wutar dakin sa' ya kunna ' yana kallon agogon dakin ' karfe shibiyu n'a dare' tareda jan tsaki yace ' ita kuma wannan me takeso a daren nan.


Karar buga kofar yasa shi zira takalmin 'cikin dan hanzari yaje yabude kofar.


Kallon fatima yake da mamaki yanda hawaye shar a idanunta 'lfy meke faruwa.


Kasa , magana t'ai saidai ta kama hannun sa 'taringa jansa ,shikuma yana biye da ita abaya.


Fadamin meke faruwa ne 'wife 'kaide muje tabashi amsa tana sheshekar kuka mai tsuma rai.



Suna shiga dakin , Khalid yakai dubansa ,ga deen suna kallon juna.


Fatima tasaki hannun Khalid tareda zuwa gaban deen ' cikin muryan wacce Aka cuta 'tace Khalid kaga kanin sa ,fyade yakeson yamun inaga bayau bane yafara zuwamin ba , Allah ne yatona asirin sa.


Khalid yai shiru sai kallon deen yake 'deen da tuni kansa ke akasa banda hawaye babu abunda yakeyi.



Saké Kai Duban ta 'ga khalid t'ai tace ina gayamaka abunda kanin ka ,ke shirin aikatamin amma Kai shiru ka Gaza magana.



Buden bakin Khalid 'yace deen kafita kabamu waje nace cikin fada.


Sakaka fatima ke kallon sa 'hawayen ta 'yabushe kace yafita?


Eh nace yafita 'tareda rike hannun ta'.


Deen sanda 'sanda yafita dakin cike da tashin hankali da baa samishi rana.



Khalid yace pls fatima wannan abun dayafaru kidauke shi kuskure ne.


Tasss yaji saukan mari Wanda yasa yake ganin taurari ' ni kika Mara .


Eh kaina Mara 'inba dan iska ba 'ina matsayin matar ka 'inkama kwarto ,adakin ka.


Amma saika cemin wai yafita 'batareda kanunamai fushin ka ba.



Khalid tashi daga kan gadon fatima yai 'cikin daga murya yace .


Eh fatima Haka nace.


Abunda yasa banwa deen magana ba 'nine n'a turo da sanina da amince wa ta yazo dakin ki.


Wani shock jikin Fatima yai jin kalaman Khalid tana kallon da magana.


Cikin kuka' tace khalid meyasa Kai Haka.


Nayi hakane dan nasan bazan taba iya kusantar ki ba 'ina gudun kada sha'awa ta sa kifara 'fita neman namiji awaje 'amma banyi da niyar cutar wa Saidan in taimaka miki .


Cikin kukan dayaci karfin ta 'tace meyasa ka aureni Khalid .


Eh n'a aure ki ne saboda inason ki,inason ganin ki ,cikin gida n'a.


Fatima dake tsaye 'zuciya ta dibeta nan take ta yanke jiki ta fadi a sume.



Innalilahi wa'inna ilai rajun khalid yashiga furtawa yana jijjigata yana Kiran sunan ta' amma shiru yakeji'. Frij Din ta yabude ya dauko ruwan Goran mai sanyi yashafa mata 'stil dai shiru.


Tsoro yakamashi kada fa 'yarinyar nan ta mutu 'ne.


Aguje yasauko daga kan matakalan step yayo kasa.


Tsakiyar falo yasoma ihu yana fadin kowa n'a gidan nan yafito 'fatima ta suma .


Aguje kaman suna farke 'kowa yafito da Kayan barci ajikin , kowa ya tsassare shi da idanu sukai ina take ne ?.


Tana dakin ta yabasu amsa.


Dukansu matan gidan dakin fatima suka nufa aguje har suna tuntube .


Abba da alhaji nura, da khalid ne tsaye kowanne rike da kugun sa '.


Alh nura yace Khalid wai meyasa méta ne Haka .


Nima kawai Haka naganta a sume yabashi amsa 'tareda rike hannun abba , sukai dakin abba dan tattaunawa.



Umma rike da fatima Akan kafafun ta 'tace Inna Farida yarinyar nan Anya tana numfashi kuwa?


Eh tana numfashi 'karmu tsaya bata lokaci .


Aisha je Kira muna deen yazo yadauke mu 'yakaimu asibiti.


Aguje Aisha t'ai dakin deen ,ga mamakin ta 'ganin sa' t'ai yanata kuka.


Aisha tace yaya deen meke damun ka ne.


Idanun sa da suka kada kaman wuta 'yace 'indo wani abune yafadamun a idanuna .


Cemishi sannu t'ai 'tace yaya kazo dakin anti Fatima tana c'en a sume asibiti zaka kaimu.


Tashin hankali da baa samishi rana 'a kidime yabaro dakin yariga Aisha fita.


Deen n'a kallon fatima hawaye cike a idanun sa ya 'ciccibeta direct sai cikin motar.


Su umma suka take masa' baya.



Alh nura dake tsaye shikadai yabi su 'abaya yace to ai baa gayawa mijin ta ba.


Gashi yana dakin abban sa.


Deeen yace pls alh nura ka sanar musu mun tafi asibiti (Sauki) n'a docta Hassan.


Da to.ya amsa musu tareda musu fatan sauka lafiya .



Khalid adakin abba 'tagumi yai .


Abba yace wai khalid me yakawo suma acikin daren nan.


Bawa abba abunda yafaru yai cike da damuwa a fuskar sa.


Tikashi abba yafurta .


Ya kabari ta kwabe Maka 'hakane baa taba samun mistake ba 'sai akanta.

Wai wannan wace irin yarinya ce mai tsaurin idanu.


Khalid rike da kansa dake sarawa yace abba nidai bansan me 'mafita ba.


Abba ya dafashi yi hakuri.dana Bani nan dazuwa gobe zamu san yanda zaa yi inshAllah bazata baka matsala ba.


Tashi muje kasan tana daki


Fitowa sukai 'suka iske alh nura waya yake alamun yayi nisa awayar .


ganin su 'yasa yamike tsaye tareda cewa Bari dasafe zamuyi waya.


Murmushi ya sakalo yace 'aisun tafi asibiti sunce asanaar muku.


Khalid yace wani asibitin Kenan .


Yabashi amsa (Sauki.)


Ok Abba tunda dare yayi mubari dasafe munje kasan banson abunda zetaba lafiya ta.


Cikin gamsuwa da Haka abba ,da khalid sukai wa alh nura sallama 'saida safe 'kowa yanufi 'sashin sa.



......




Deen ,tuki yake 360 amma sai gani yake kaman besauri a hanzarce ya d'Anna hanci motarsa a' asibiti kasancewa me gadi yaji Horn dinsa ya wangale masa Gate.


Umergency umergency Haka yaketa furtawa cikin daga 'murya 'aguje Dukan ma'aikata asibiti suka taho da gado Aka daura fatima.


Su umma n'a biye dasu abaya ,akai urgemency block da ita.


Su 'umma 'inna Farida 'deen 'sumayya' Aisha babu abunda suke furtawa sai innalilahi wa'inna ilai rajun zuciyoyin su 'cike da rauni......




......



Aisha da rukayya' tabe baki sukai suna kallon juna' waishi wannan mutumin dan rainin hankali yatafi yabarmu 'anan ko ga ruwa be ,cemana ba. Céwar aisha.


Rukayya tace ' kiyi hakuri kila wani.uzurin gareshi aciki' hararta Aisha tayi tace wlh kedai kincika sauna wlh ace baki ganin laifin sa' saina nawa tana turo baki.


Yusuf dake saukowa daga sama 'ahankali yake taka matakalan step din .


Ya iso falon TV bangon dakin ya tsurawa idanu 'dasuke kallo 'rike bakin sa yai yace ' to su wayannan sakarkarun harda min karanbani 'azuci yake magana.


Asace yake kallon su' sai yanzu yake karewa rukayya kallo atsanake ' farace tass irin kyakyawa 'ga hanci kaman biro' bakinta dan daidai ,tsaki yaja yace to inci uban me da wannan agwagwan.


Kallon Aisha yake yace itakuma wannan yaukin da shegen tsiwa inama zan buge bakin Nata.

Yana ta maganar zuci.


Fuskantar su yai' cikin hade rai yace 'ga daki c'en yana nuna musu dakin kasa 'cen zaku kwana 'ku tabbatar kun share adaren nan 'kun goge kun wanke toilet .


Aisha sai kallon sa take 'zatai masifa kwarjin sa yarufe mata baki.


Rukayya tace inshAllah amma dan Allah yunwa 'muke ji.



Ai bakusanar dani.zuwan Ku 'ba sannan ni Bana girki 'in akwai wacce ta iya ga kitchen saikuje Ku dafa amma Ku tabbatar kuna gamawa Ku gyara wajen dan kuku n'a ba bawan Ku , bane.


Yana gama fadin Haka yai ficewar sa 'yakoma sama .


Aisha da rukayya sai kallon juna suke' ruky tace uhmmm kedai kinga mu hakura dacin 'abincin nan' saikace mayu girki adaren nan.


Zodai muje kitchen din 'suna Shiga sukaga bred 'da madar peak 'komai n'a buka ta' wow sukace yanda suke mamakin ganin komai' a kitchen din.


Shayi suka hada batareda Sun fito ba anan suka tsya Shan Kayan su.


..........



Acen asibiti sai Safa da marwa sukeyi 'basuda gindin zama.


Likita ne yafito daga umergency aguje suka nufe shi ' .




Likita yaya dai ' kayi shiru kaki magana.



Likita yace ina mijin ta yake.


Cikin zazzare idanu 'sai yanzu suka lura ashe khalid be biyosu ba.


Kunyi shiru 'sauri nake kuban amsa?


Deeen yace nine mijin ta.


.

...

Biyoni likita yace tareda zuwa office dinsa 'deen ya take masa baya.



Umma tace 'to baga irinta nan ace matarka n'a asibiti bakazo ba, saboda Allah abunda Khalid yakeyi yana kyautawa kuwa' yanzu da babu deen Kenan da ya zamuyi ,cikin bacin rai take magana, Aisha ta dafata yi hakuri 'umma kefa kika haifi Khalid 'kinfi kowa sanin halin danki 'kokuwa? tana kallon Inna Farida da sumayya.


Eh wlh tafi mu sanin halin sa Inna Farida ,da sumayya suka amsa mata.


Tokingani umma 'ki kyaleshi da halin sa'tunda ga yaya deen yatafi amatsayin sa.

Mudai jira abunda zaa fadamai '


Allah yasa muji alkhairi Dukan su,suka fada.


....


Deen gaban likita ,tsaye kikam 'likita ya kalleshi cikin tausasa murya 'yace zauna mana .


Zama yai yana fuskantar shi 'yace likita yimun bayani ,me ke samun ta?


Likita ya fuskance shi yace wannan yarinyar zuciyar ta ,ta kumbura 'kuma inhar ta buga akwai babban matsala ' ya amatsayin ta ,na matar ka, baka bata cikakkiyar kulawa da kwantar mata da hankali .


Yanzu dai 'mun samu mun shawo kan matsalar zaa bata gado' saide zuwa gobe 'dasafe zaku iya zuwa ganin ta ,dan yanzu sossai take bukatar hutu .


Akwai magunguna da zamu daurata akai inhar zamu sallame ta 'zata ringa Shan su zai taimaka 'mata .


Amma kuma duk da hk dan Allah aguji abunda ze bata mata rai.


Deen ya Mike tareda mikawa docto hannu 'sukai musabaha 'nagode sossai docto zaa kiyaye tareda barin offi ce din.


Jiki babu kwari 'yazo yasamu su 'umma da suka kagu 'suji bayanin likita ,nan ya zayyana musu komai .


Hankalin su 'yai matukar tashi 'aisha tace to akwai Abunda akewa anti Fatima n'a rashin jin dadi ne ,da bamu sani ba ?


Inna Farida tace 'keko Aisha ai ciki badan tuwo kadai akayishi ba,kila tanada damuwa ne 'fatan mu 'dai Allah yabata lafiya.


Da ameen suka amsa.


Daki suka nema Aka basu inda babu kowa dan anan zasu kwana.


Umma t'ai juyi Akan deen yaje gida dasafe yadawo amma fur yaki .



Washe gari.



Khalid 'da abba' da alh nura Sun fito massalaci 'kai tsaye gida 'suka ' cike da kosawa khalid yace .


Abba Allah yayi dare gari yawaye 'kaga yanzu ne daidai lokacin dazan je 'asibiti.


Gaskiya ne Dana ai bazan so 'akan wata ba' kafita tsakar dare ba' Alh nura yace abba bangane wata ba' mekake nufi?


Naga ai fatima tawuce acemata wata 'matar shi ta sunnah 'murmushi yai Wanda shikadai yasan ma'anar sa yana ayyana aransa 'kodai dagaske dai Khalid baya iya kusantar matan shi ne' inhaka yasan fatima abukace take 'zesan hanyar dazebi.


Abba ya katse masa tunani tareda cewa kaiko nura ban hanaka samun baki cikin hidimar gidana ba.


Tsaki khalid yaja yana mai hararan sa '


Afuwan abba namanta ne 'shiyasa n'a soma baki n'a 'ina ganin kamar yadace inyi magana ne.


Dan Allah gafara c'en 'khalid yace rai abace 'kai kazamin rayuwar da kakeyi Kana tunanin bansaniba ' wlh nura a tafin hannuna 'kake .


Abu nakarshe wlh inka kuskura kasake neman bata mana sunan gidan mu' uhmmm zaka kwashi tsummakaran ka 'kabar gidan nan.


Sadaf ! sadaf ! sadaf Haka alh nura yaja jikin shi yafice 'yabar su 'dan ya lura ,suna son su Kira masa ruwa.


Nusy ce ke saukowa daga matakalan step tana kuka.


Khalid tsareta da idanu yai ,danshi harga Allah ya mance da ita.


Kamo hannun ta yai suka zauna shida abba ' yace haba baby n'a meya sameki?


Cikin kuka' tace banga mama ba.


Kallon juna 'sukai shida abba ' oh nusy mama bata lfy ankaita asibiti jiya 'kinji zata dawo anjima ' kara fashewa da kuka t'ai 'tace nidai daddy ka kaini wajen ta.


Abba yace ' kuje tare man khalid kaga makaranta tabari gobe taje.


Cikin gamsuwa da hakan Khalid ya kwadawa Balaraba Kira 'tareda bata umarnin taje ta shirya nusy 'sannan ta hada brek zekai asibiti a ladabce ta amsa da to.


Tareda juyawa danyin abunda akasata.



.........



Shamsu ne gaban makaranta su 'nusy shiru bega zuwan ta' alamun Sun nuna yau batazoba' cikeda damuwa 'yace gun mai gadin makarantar.


Yace ranka ya dade barka da aiki 'amsa masa yai da barkadai.


Dan Allah tambaya nake' jikar sani yaro' tazo makaranta yau kuwa ?


Me gadi yace 'no batazoba '

Nagode yabashi amsa tareda juyawa .




........



Yusuf 'shida Ahmad Sun gama shirin su 'tsaf nazuwa aiki ' ahanzarce suka sauko kasa.


Ganin 'su rukayya zaune sunacin indomi da Kwaï yaji Kayan miya sai baza kamshi yake.


Lumshe idanun sa 'yai tareda kallon su 'a fakaice .


Ganin sa yasa dukansu suka rusuna 'suna inkwana ' lfykalau ya basu amsa 'ciki 'ciki.


Ahmad ya kwabe baki 'ni bazaku gaisheni ba yana kallon su' rukayya tace sorry ai harda Kai gaisuwan nan' banyarda yacemusu.


Yusuf ganin Sun cika shi da surutu gashi sauri yake 'sbd zeje yahada bayanan dazeyi Akan wayanda sukaiwa kanwarsa fyade .


Kallon su 'yai n'a minti daya 'cikin yanayin da beson magana da mata' yace wata jaha kuka fito.


Aisha tace katsina' da mamaki yake kallon su ya maimaita 'katsina 'sukace eh nan muka mufito.


Ina kuka sanni har kuka biyoni nan garin.



Zazzare idanu 'suka soma yi 'suna inda inda ' ganin zasu bata masa lokaci yace 'inason Ku dauki papper Ku rubuta inda kuka sanni 'zan dawo da azahar saiku ban . Sannan Ahmed zekoma anjima ze tattara mun Ku'yawuce daku katsina tunda c'en ya nufa.


Batareda yajira cewar su ba' yafice daga gidan Ahmed ya take masa baya.


Rukayya kinajin abunda ya fada kuwa wai ya tattara mu ' saikace Kayan wanki.


Uhmmm kasa magana rukayya t'ai 'tace ni Abunda yaban mamaki shine wai mu rubuta inda muka sanshi a pepper' inyazo abashi ya karanta.


Wannan rainin yai yawa cikin kuka' rukayya ke magana wlh Allah yasani inason shi Aisha duk abunda yakeyi bedameni ba' kuma dole yai mana kallon marasa kamun Kai 'tunda muka baro garin mu' muka biyo shi.


Amma wlh kema kinsan inada tarbiyyya Aisha 'badan munyi karya zamuje biki kauye bane ,da wlh bazaa barmu 'mu tafi ba.


Aisha jikinta yai sanyi 'ta dafa rukayya yi hakuri inshAllah inamiki fatan nasara akansa.rungume juna sukai .


....



Yusuf n'a isa Barack duka ma'aikatan subar Abunda suke 'suka jeru tareda Sara masa ' barka da isowa sir.


Yaww barka dai y amsa musu tareda kallon su' atsanake ' cikin tausasa murya yace 'bakin da sukazo da me laifi daga katsina inafatan Sun juya ' kuma kun musu tarba me kyau irin ta ma'aikata.


Eh yallabai anyi abunda yadace 'wani daga cikin su yabashi amsa a ladabce.



Ok good .


Kowa yakoma kan aikin sa.


Ina me tsaron cell yake 'kansa aduke yace gani ranka yadade'muje ka kaini inda Aka kawo masu 'laifin jiya da to ya masa tareda yin gaba.


Yusuf n'a biye dashi abaya yana tafiya kaman Zaki a dawa.


Bude masa cell din 'akai yashiga daga ciki sauran sojojin suna tsaye suna jiran umarnin ogan nasu dan har jikin su 'yafara rawa allurar su 'ta soja ta motsa.


Yusuf cike da takunsa da fuskar sa tamau yashiga ciki' suna ganin sa 'hankalin su 'yatashi dan Sun shaida shi jiya.


Cikin kakkausar murya mai cikeda tsawa yace wanene acikin Ku 'yaiwa Aisha sani yaro fyade .


Cikin kasa da murya yace nine amma da taimakon su.


Mu haɗu a Chapter 7

Kyauta Daga Allah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol