Free chapter 路 Read without an account

Page 19

by Fatima 路 K'ANINA NE

馃拝 *K'ANINA NE*馃拝



*By Fatima Mrs Ahfat*


*Bismillahir rahmanin Rahim*


*Page 19*


______________Bayan sun gama Sallah da sauri ta miki ganin sa da tay yana kokarin janta, cire hijab din tay tana murmushi ta kallesa tace " tunda kayi Sallah da Matar ka samu Lada, sai ka tashi muje ka cika sauran ladan ai"

Ta fada tana sakar masa da murmushi' dan Zaro idanunsa waje yyi da tare da mikewa tsaye yace " da gaske" ya musa fuska tay tana kallonsa tace " Yes' ta fada tana dariya k'asa_ k'asa tare dan jada baba虏 tana jefar sa wani irin smile"

Wani irin murmushi ne ya tsobuce misa yace " yanzu kuwa ai aikin Lada bama wasa dashi" ya fada yana kokarin cab kota, ta juya da gudu zata bar dakin cikin zafin nama yyi taku uku ya cab kota ta fada jikinsa ya matseta gam虏"wa walahi ni ka sakeni abinci nake nufin kaci ba wani abu ba"

Dariya ne yaso tsubuce masa jin yanda ta wani rude lkcn daya, danne dariyar sa yyi bakinsa ya kai kunnenta a hankali ya mata rada" kukan shugub'a ta sakar masa tana dan dukar k'irjinsa tana bubbuga k'afafunta a saman nasa" rintse idanunsa yyi jin wani feeling na saukar masa" a hankali ya sassauta mata rikon Yana dariya yace " Ohoo Babyn sarkin rigema, naga alamu yau kinaji da rigima ko" uhmm toh ba kaine ba" ni kuma me nayi Babyn" fuskarta ta kara cusawa a k'irjinsa tace " uhm ni fa wani mgnr kana sani jin kunya wlh" dariya ya fashe dashi yace " ke da K'ANIN ki kuma meyen abun jin kunya" bubbuga k'irjinsa ta farayi,.yana dariya yace " I'm really sorry Ashe yanzu Yayan ki nake ko"


uhm k'awai ta fada tan脿 janje jikinta daga nasa, domin ita kanta abun na bata mamaki wai itace yau tsaye da K'ANINTA tana zuba masa ruwan shugub'a haka" karantar yana yin fuskarta yyi yace " tunanin me kuma kike my sugar Baby?" Bakinta kawai ta turu gaba tace " ni dai mu tafi" hannunta ya kama suka fita daga bedroom din suna murmushi, direct dining area suka nufa" kujera yaja ya zauna, tana Murmushi tayi savings dinsa tana gamawa tace aci lafiya' ke fa?" Shafa cikinta tay tace " gaskiya a koshe nake dazun naci" shugub'e fuska yyi yace " toh nima bazan ciba" ya fada yana ture plate din abincin gaba" murmushi tay tace " wlh rigimar ka tay yawa k'amar wani dan goye "toh ai rigimar mu daya ya fada tare da janjota ta zauna Saman cinyarta suka fara bata abincin a baki duk da bata so but haka ta daure tana karba, itama basa ta farayi da haka har suka cin abinci sosai suna hira" suna gamawa a tare suka tattara abunda suka bata suka shiga kitchen dashi suka wanke komai suka jerashi suka fito parlor suka zauna suna hiran su"

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiyar musu suna nunawa junan su kulawa na musamman, sosai Mahmud yake kashe Yasmeen da Salon sa da nuna mata so da kauna tun tana tirjewa harta saki jiki dashi sosai domin itama tana jin a ranta tana Sonsa sosai kuma ayanzu tana jin bazata iya rabuwa dashi ba"

Kwana biyu Mahmud ya daga mata kafa, rana na ukun ne sukayi Sallah suka gudanar da komai k'amar yanda Addine ya halanta ayi sukayi suka raya daren, tun Yasmeen najin zafi tana d'aure wa harta fara jin dad'in abun"

K'amar yanda yace haka akayi b'ayan Wata daya ya koma bakin aikinsa, inda Yasmeen tace " ita dai baza tayi aiki ba daman ita a tsarin ta da zaran tay Aure dai bazayi aiki ba, domin tana son taba mijinta da yaran ta kulawa idan har Allah ya basu"

Zaune take cikin parlor sanye take da wando jeans T_ shirt pink color wanda suka mata masifar k'yau sai k'amshi take zubawa kamar anyi barin turare, hannunta rike da wayarta tana chatting sai murmushi take" ji k'awai tay an gungumeta ta baya" tattausan murmushi ta sake tare da ajiye wayarta tace " sannu da dawowa nawa" shima murmushi ya sakar mata yace " a ina hankali ki ya tafi ina ta sallama baki jini ba" ya fada tare dajan hancinta"

Am sorry Nawan wlh da Khadija muke Chat shiyasa amma kayi hakuri " k'aga ka dawo da gajiya muje ka wasa ruwa kaci abinci"

Murmushi yyi yace " an gama my sugar Baby, itama tana murmushi suka haura bedroom dinsa, ta ta yashi rage kayan jikinsa ta shiga toilet ta hada masa ruwan wanka ta fito, murmushi yyi ya jata suka shiga toilet din tare Hakan kuwa ya sata sake wanka suka fito a tare suka shirya suka parlor" zama sukayi suka fara cin abincin a tare yana bata tana bashi domin a yanzu bata iya cin abinci ita kadai, ko ranar da sukaje gida Ummi da Anty Amarya da Mami suka cika musu a binci kala_ kala da k'yar taci ita kadai duk sai taji ba wani dad'i"

A part din kaka sukaci na dare kakus dai sai mamaki take tana binsu da ido Daman yanda suke basa shiri akoi ranar da zasu shirya haka" addu'ae zaman lafiya take musu da zuri'a dai yiban" ko da Daddy da Abba suka dawo suka gansu yanda suka yi k'yau sai nunawa junan su kulawa suke ko a gaban su ba ruwansu da kunya"

Rayuwa ta musu dad'i sosai suke kula da junan su duk bayan sati daya suke zuwa gida su gaishesu suna dan zaga dangi kadan kad'an"

A cikin kwanakin nan sosai Yasmeen take fama da zazzabi but tana daurewa domin tasan tabbas ciki ne da ita, yau dai bayan Mahmud ya fita aiki ne zazzabin ya rufeta sosai tana kwance a saman bed sai rawan sanyi take, Mahmud ya shiga bedroom din yana kiranta, ganin hakin da take cikine ya sashi saurin kara sawa bed din da sauri cikin ruduwa ya dagota Yana cewa" my Yasmeen daman baki da Lafiya shine baki fad'amin ba" a rikice ya fara dubata, drip ya kara mata ya mata Alluran bacci tare da dibar jininta ya kira doctor Aisha tazo"

Ba'a dauki lkcn ba ta shigo parlor ya bata jinin ta tafi dashi, shikuma ya wuce cikin bedroom din ya zauna a gefenta yana shafar sumar kanta yana kallon fuskarta"

After 40 minutes doctor Aisha tay Knocking a parlor, fita yyi ya sameta tsaye tana murmushi tace " congrats Sir Madam dinka na dauke da cikin na wata daya" ta fada tare da mika masa results test din" cikin farin ciki ya karb'a ya duba, murmushi ya sake yace " thanks zakiga tukuncin ki ya fada yana murmushi"

Komawa dakin yyi har lkcn bacci take, zama yyi ya dauki wayarsa ya kira Anty Amarya ya sanar mata, sosai dangi da abokan arziki suka ta yashi murna, koda ta tashi ya hada mata coffee tasha, sosai take shan gata gata ako wani bangare" haka rayuwar su taci gaba da tafiya ko wani bangare suna bata kulawa ta musam man, bayan wata 9 da kwana Tara na kuda ya tashin mata Mahmud da k'ansa ya karbi aihuwar , inda Allah ya basu yaran yan biyu masu kama dasu mace dana miji"

Farin Ciki a wannan dangin Ba'a mgn Yasmeen dai taga gata gun mijinta da yan uwanta, ranan suna yara sukaci sunan kaka Aisha da Alhaji tsuhu, inda suke kiransu Neelah &Neehal Masha Allah Ansha biki suna anyi an gama lafiya"


Sai dai muce alhamdulillah Allah ya raya ya bada zaman lafiya,


Alhamdulillah anan na kawo karshen littafin k'asan cewar shi short story ne, kuskuren da nayi a cikinsa ALLAH ya yafemin Amin 馃げ馃げ



INA GODIYA SOSAI MASOYA NA ALLLAH YA BARMU TARE LOVE U SO MUCH 鉂わ笍鉂わ笍鉂わ笍


Sai mun hadu a sabon book mai sona SO NE salon sa na daban ne da sauran 馃槏


Mrs Ahfat ce 鉁嶏笍

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol